Showing 231001 words to 234000 words out of 244256 words

Chapter 78 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

467

farko kuma har a karshe.

Kuka suka zauna suka ringa yi mai ciwo da zallan baqin ciki da dana sani kala kala har tsawon lokaci kafin suka iya tashi kowa ya shige dakinsa.

A cikin daren aka aikowa hajiyar zuwa ganin Samad su gana kafin wucewansa da asuba dan haka jiki a mace hankali tashe ta isa har bangarensa da aka dawo dashi sedai sa securities din da zasu tsaresa har asuba lokacin tafiyar.

Tana shiga a can dakinsa ta taddasa zaune a qasa rakube yana jin bude dakin ya dago idanuwansa da sukai wani mugun zurfin gaske sun bushe kaman wanda aka tono daga rami hakama bakinsa ya bushe sosai kaman wanda yake cin tuwon qasa akan kansa dayake daukan idanuwanta da wani mugun askin da akaiwa kansa sol ta sauke idanuwanta tana jin wani mugun jiri na dibanta ta rintse idanuwanta da karfi tana fasa kuka mai sauti sosai tana ambatar sunansa da isa gurinsa da sauri ta zube qasa tana rungumosa jikinta dake rawa sosai tana sake tsananta kunanta sbd ansauya mata kamanninsa gabaki daya ya koma kaman wanda aka karbo hannun bandits.

Bai iya motsawa ba daga zaunen dayake idanuwansa sunyi jajir babu abinda ya iya furtawa yana jin kukan hajiyar tanayi tana tsinewa Fleet da ubansa da kaf dangin uwar fleet din dana SANAAH tin kakanni tana kira musu balai da masifu.

Yanda take tsine musu ne tana qara daga murya kusan har securities din wajen bangaren suna jinta tanata yi harta dawo rokon Allah ya hana Samad din tafiya allah ya hanasu kaimata shi inda sukeso.

Sai a lokacin ne Samad ya fasa wani irin kuka mai karfi yana sunkuyar da kansa sbd shi kansa yasan hukuncin kaman kisa ne aka yanke masa a dunqule sbd sanin da akai ko gaban ruwa me yawa baya iya tsayuwa zai iya rasa ransa amma aka yanke shawarar aikasa sojan ruwa kuma kai tsaye babu training ba komai zaa kaisa inda yasan wlh bazai taba wuce satiba idan yayi tsanani dan haka yasan babu sauki ko rangwame ko bada second dama a hukuncin sakasa soldier.

Ganin kukan Samad din wanda tinda ta haifesa ya girma ya fara zama saurayi bata taba ganin yayi ba ya sakata qarasa zarewa gabaki daya ta ringa ihu tana kuka tana kiraye kirayen sunaye kaman ta haukace tana tsinewa tana kuma roko dayake dare yayi sosai kusan kaf bangaroran ana jinta tanata wani irin kuka da ihu da neman agajin kada a rabata da danta.

Su maamah da duka kowa yana jinta jikinsu sanyi yayi dukansu sun tausaya mata matiqar gaske sbd a cikin lamarin nata akwai tausayi.

Asubar fari Imran ne da kansa kuwa ya shigo aka fito da Samad din yayi wanka ya shirya a cikin wasu kayan sanyi yayi sallama da mahaifiyarsa datake riqe dashi karfinta tas ya qare sedai idanuwa daqyar aka banbareta daga garesa Dad dinsa yayi magana sosai dashi akan basa tabbacin insha Allah babu abinda zai samesa kuma zai samu sauyi da aminci a rayuwarsa shine fata da adduar dayake masa tareda saka masa albarka a cikin danne komai da kallansa a matsayin dansa jininsa.

Har a cikin ransa Dad bai ji akwai wani boyayyen hukunci a cikin hukuncin Fleet dinba saima gyaran dayake kallo zai kawo a rayuwar dan uwansa dan haka da addua da komai suka rabu shima Samad din yaji ya samu nutsuwa da aminci a cikin tafiyar duk da yana cikin tsoro mai tsananin gaske.

Suna barin gidan hajiyar ta yanke jiki ta fadi a some babu numfashi a jikinta sbd riqe ake da ita har motocin suka fice.

Kwasarta akai aka wuce bangarenta da ita dan taimaka mata ta farfado ta dawo daidai.

Su maamah ma babu wanda ya fito daman bare Dr Mum da tana can bangarenta da SANAAH wadda take tarairayanta akan yanda dik ta shiga damuwa ta rasa walwala da sukuninta gashi tana lura da sam ta kasa yadda ta hadu da fleet din dan haka take kokarin ganin ta sakata dawowa daidai.

Da daddare Dad ya zauna da Fleet palonsa suna magana sama sama akan abubuwan da suka shafi aiki.

A cikin maganar Dad ya dan yi shiru a natse kafin ya dago ya kalli fleet a tsanake ya bude baki yace

"Akwai maganar Fammah da Al'amin wadda take kwance tin bayan zuwanta can wadda bayan nazari da duba akan duka halayyarsu da tarbiyarsu da kuma sanin matakin da kowanensu yake akai na tsarin rayuwa naga dacewansu da ni nake nemawa Al'amin aurenta a hannunka wanda daurin auren kawai nakeso batareda kowace hayaniya ba sbd mahaifiyarta da bazata taba yadda da aurenba bakuma wai dan ana shakkarta ba sai dan zata iya barazana ga yar tata ta hanata yadda da auren"

Shiru Fleet yayi yana dan dagowa a tsanake ya kalli Dad din kafin ya dan maida bayansa ya zauna dakyau ya bude baki ya korowa Dad din bayanin matiqar Famman da Al'amin na kaunar juna da kuma raayin auren junansu he's ok da hakan ya bawa Al'amin din aurenta.

Ajiyan zuciya da numfashi Dad ya sauke yana cewa ya basa daman magana da yarsa kuma shima da kansa a kwanakin zai isa Italy yayi zama dasu da magana dasu mai kyau.

Da haka sukai sallama fleet ya baro bangaren Dad ya isa bangarensa ya daga wayarsa ya kira Imran yace yana buqatan tafiya italy zuwa ga yarsa dan yanada zama da ita dan haryanxu ma batasan sun rabu dashi da mahaifiyarta ba.
#MAMUH
09033181070
[26/06, 1:49 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

146
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Dad kai tsaye tafiyarsa tareda SANAAH da Dr Mum zaiyita sbd bawa SANAAH daman tafiya itama ta dan samu fita damuwan data kasa cirewa kanta na kunyar kowa da Fleet din da sam ta kasa barin su tsaya a gaban juna.

A nasa bangaren tafiyar tasa shima ta gama kammaluwa dan haka shine ya fara tafiyarsa tafiyar da basu hadu ba sbd ya bari ta sake samun time din kanta ta shirya barinsa ganinta da kansa wanda yake cikin wata irin nutsatsiyar matsuwa da damuwan rashin ganinta a gabansa a cikin idanuwansa dan haka tafiyar shima zata sake saka kansa warwarewa daga wannan damuwan dayake ji na sanin suna gida daya suna rayuwa batareda ganin juna ba.

Bayan tafiyarsa da kwana biyu suma tasu tafiyar ta gama haduwa dan haka suka shirya suka daga aka bar Maamah da mommy wainda zasu tafi Umrah daga can kila zasu iya biyawa kila kuma su tahowansu gida.

Tafiyar SANAAH da Dad da Dr Mum tafiya ce da dukansu suke jinta kaman wata sabuwar rayuwar da bazasu iya hadata da kowa da komai ba sbd tabbatarda cikin dayake jikinta wanda yake 'da ne a gurin 'dansu 'dan da shine jininsu a hade guri daya,
'Da ne da suka riga suka gama sani da tabbatarwa shine daya tak da Allah ya mallaka musu duk irin tsananin son da sukewa juna sunsan bazasu taba samun wani arzikin daya wuce wananna dinba da suka samu kuma suke fatan cigaba da ganin nasa yayan.

Tafiya ce mai sanyi da nutsuwa da tsari da asali rashin hayaniya da wata sanyayyar kauna wadda take gudana a tsakaninsu da ita kanta hakama dayake dukansu a waye suke ilimi da hutu ya ratsa rayuwarsu babu ruwansu da abinda yake gudana a tsakanin junansu sbd soyayyar Dad da Dr Mum din fili take suke kuma dan nunawa ba tareda jin damuwan SANAAH ba hakama itama SANAAH din bata damu ba sam bata ma wani ji abin wani iri ba bayan jin hakanma yana sakata jin damuwanta na dan tafiya sbd tana farin cikin ganinsu a tare sosai dan haka koda sukai kwana biyu a wata qasar kafin suka iso italy babu wanda yaji takura hankalinsu kwance yake musamman Dad dayake jin rayuwansa ta samu nutsuwan da babu a cikinta babu kowa a tare dasu babu kowace damuwa da tashin hankali da hayaniya daga nutsuwa sai kwanciyan hankali.

Ranar da suka iso italy Al'amin ne da kansa yazo airport daukansu da wata motarsa daban kuma BMW X5 fara yana sanye da wasu Ash D&G da fcap bai sako glasses ba sbd girmamawa ga wainda yaxo daukan dan haka koda ya fito ya tarbesu tin daga nesa Dr Mum ta sauke idanuwanta akansa tana sauke ajiyan sbd a take taji zuciyarta ta sake aminta dashi dari bisa dari ga Fammah dan haka da murmushi dukansu mai tsananin kyau da kulawa tareda nuna farin cikin ganinsa suka sake musamman Dad daya miqa masa hannunsa sa sakewan dake tsakaninsu bada shekaru ko matsayiba yace

"Daga karshe dai Mr Al'amin khalil a gabana"

Murmushi mai kyau da asalin nutsuwa Al'amin ya sake yana kallan Dad din da sakewa da kaman amintar dake tsakaninsu ba shekarunba yace

"Welcome to italy Sir Jeerah"

Dariya Dad din ya sake mai tsari suna kama hannun juna da kyau da murmushi akan fuskansu sosai.

Dr Mum data shiga mamakin irin wannan kusancin da shaquwan tasu kaman babu duba matsayi da shekaru a cikinta burgeta hakan yayi taji wani farin cikin ganin ba qaramar kauna da soyayya Dad kenan ya nunawa Al'amin ba da sukai irin wannan kusanci da sakewan da babu a tsakaninsa da yayansa daya haifa.

Cikin girmamawa sosai yana kasa kallanta sosai Al'amin ya juyo ya kalleta yana bude baki da kulawa da nutsuwa da rashin hayaniyarsa ya gaidata yana mata sannu da zuwa ta amsa tana jin kaunarsa sosai na qaruwar mata dan kamewansa da nutsuwansa a bayyane take.

SANAAH datake kallansa ya kalla yana sake mata murmushi me sanyi tareda bude mata hannu ta shiga jikinsa tana sake murmushi da farin cikin data kwana biyu rabonta da shiga.

Juyawa sukai suna dunguma mota a motarsa ya dauki Dad da Mum da SANAAH dake gaba zaune sai Mr Sideeq ya shigo wata motar tareda kayansu suka nufi kai tsaye masaukin da aka tanadar musu na wani sabon gidan dayake kusa da gidansa sosai.

Suna isa gidan da komai da aka tanadar masa na luxury yayi daidai da tsarin da zasu iya rayuwa mai dadi da tsari a ciki dan haka kai tsaye komai aka shigar dashi dakin Mr Sideeq yana can harabar gidan daga gefe daya shima babban room and bathroom mai kyau da girma.

SANAAH ma da dakinta a palon farko sai palon kurya dayake dauke da master bedroom da wani dakin daya daban nasu Dad din da Matarsa.

Daman hutawa daga tafiya Al'amin din ya basu yana tafiya yabarsu zuwa anjima tukuna.

SANAAH wanka tafara yi sbd mutuwan jiki da rashin karfi takeji so tana shiga ruwan zafi ta saka ta fara gasa jikinta sosai kafin ta fito tayi sallan Azahar da time din yayi ta kwanta take bacci mai karfi da dadi ya dauketa bata farka ba sai yamma tana bude idanuwanta ahankali da fammah dake zaune a gabanta tafara cin karo tana zaune ta zuba mata ido tana mata wani sanyayyar kallo mai sanyi da nutsuwa da kulawa.

Itama lumshe idanuwanta tayi ahankali tana sake budewa akan fuskan Famman tana kallan fuskanda take ta narkar da zuciyarta da matar da kaf gabobin jikinta ta sake lumshe idanuwanta batareda ta motsaba ta bude idanuwanta suna cikowa da wasu hawaye masu sanyi tana sauke wata sanyayyan numfashi da jin inama shine a gabanta kaman yanda yace original din ba copy ba.

Fammah da itama kallan SANAAH din takeyi da dukkanin mutuwan jikin rashin ganin Al'amin a kan idanuwanta tsawon kwanaki sbd boyon da sukewa juna yana nesanta kansa da ita sai Dad dinta yaxo ta gansa yaje gurinsa sun hadu shima basu hadu face to face ba bai bari sun kasance tare a gaban na fleet ba sosai ya tafi wanda hakan ya sake sakawa Fleet ganin qimarsa sbd yanda yake kaucewa kowace hanyar da shedan zai iya tasiri akan zuciyarsa da amanar datake kansa na yarsu da suka basa.

Ganin SANAAH a gabanta da asalin kamanninsa akan fuskan SANAAH ya sakata zaunawa tana kallanta da rasa tinaninta da zuciyarta da walwalanta data jima da rasawa akan soyayyar da ita tata wahala ce mai karfi suke sha kawai.

Dauke idanuwanta tayi akan SANAAH tana dan sauke ajiyan zuciya da bude baki daga inda take zaunen tace

"Are you missing him this much ne da zaki mun kuka anan??

Tashi zaune SANAAH tayi ahankali tana kallan fammah da idanuwanta da suka sake marairaicewa tana neman sauko da hawayenta sai kawai ta matso kadan ahankali ta sauko gadon tana zaunawa gefen fammah da shigewa jikinta tana fara mata hawaye da kasa cewa komai sbd harga Allah tayi tsananin kewanta itama datake son fada mata abubuwa da dama amma sbd akan mahaifiyarta ne sai bazata iya fada ba dan wata kusar tafi wata hakama tasan dole har abada bazasu taba komawa yanda suke asalin asali ba sbd uwa ta daban ce.

Rungumeta famman tayi tana dan shafa bayanta da cewa

"It's ok,its ok,Dad ne???

SANAAH batasan lokacinda murmushi ya kufce mata ba ta gyada kai tana sake shigewa jikin fammah din da itama cikin karfin hali tai murmushin tana jin dadin yanda abubuwan suka koma daidai sbd tana waya da mahaifiyarta amma bata fada mata komaiba kaman yanda bata nuna mata komaiba kuma tajita a cikin wani irin sanyi da rashin son hayaniya ko kadan kaman ba itaba hakama Dad din baice mata komaiba shima da alama duka hankalinsu ya kwanta hakama babu labarin kowace tashin hankali da aka kuma yi dan haka takejin nutsuwa da kwanciyan hankali soyayyar Al'amin ce kadai take neman kasheta a cikin sanyi.

Shiru sikai na dan lokaci kafin suka saki juna suna kallan juna da murmushi da farin cikin ganin juna suna fara magana...

SANAAH miqewa tayi tafara shiga bathroom bata wani jimaba ta fito tayi sallah tana idarwa suka fito sbd yunwar SANAAH.

Dining a cike sika samesa Al'amin ya aiko da komai an jere a dinin da fresh fruits dan haka suna sallan magrib gabaki dayansu da Dad da Mum sukai dinner cikin kulawa da kauna.

Suna gamawa daki suka shige suna shigewa Fleet na shigowa gidan sanye da fararen Diors Da suka maidasa kaman sabon matashin da rayuwarsa take cikin shekarun rashin hayaniya da hutu.

Fammah Dr mum taje ta kirawa ta fito Su Dad sukai magana da ita sosai suka kuma tabbatarda raayinta akan aure ta kasa fada musu komai saidai mahaifiyarta datake nuna musu ayi magana da ita wadda jinta kawai Dad yayi yana yanke shawarar ma kawai bazaa jira komaiba zaa daura aurenta da Al'amin din a nan italy idan yaso tana qarasa gama program dinta nan da sati biyar ta koma gida ayi biki acan ta tare kawai.

Dad dinta bai musawa hakan ba dan haka kai tsaye kuwa Dad yanke daura auren Friday nan da 4days kenan.

Fleet na barin gidan Dad ya fara wayoyinsa yana sanar wainda ya kamata su sani musamman Mommy da kansa ya kirata suka jima suna magana itama kai tsaye tayi naam da duk abinda Dad zai yanke akan yayanta tinda shine uba a garesu.

Su Maamah kuwa farin ciki suka shiga mai tsananin gaske suna jin matsuwan ma ta gamo ta dawo ayi biki.

Dr tayi farin ciki sosai da hakan sosai dan haka koda ta sanar da SANAAH take taji duka damuwanta ta tafi farin cikin ganin mutane biyu datake kauna sosai zasu kasance daya.

Washe gari Al'amin a tsanake yazo gidan sanye da Fararen kaftan masu kyau da suka fito dashi wani mutum din daban.

Tareda su yayi breakfast amma banda Fammah da bata fito ba sam dan anan ta kwana tama dawo nan sai ranar da suka tafi kila.
#MAMUH
09033181070
[26/06, 4:09 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

147
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Bayan gama breakfast dinsu Dad zaunawa yayi da Al'amin ya sanar masa da komai da suka yanke take Al'amin din ya dago cikin wani irin slow da nutsuwa ya kalli Dad din wani nauyin dayake danne da kirjinsa tsawon lokacinda zuciyarsa take tsananin azabtuwa da son Fammah jeerah yaji yana motsawa da wata irin sabon nauyin yana qara toshe kirjinsa dayake jin rayuwansa bazata taba moruwaba ayanxu idan ba famman ya samu ya mallaka ba a matsayin wadda zai qarasa rayuwa har mutuwa da ita.

A irin kallan da yayiwa Dad da kasa cewa komai Dad din ya hangi wata azababbiyar soyayyar fammah dake cikin jininsa wadda yake riqewa da dannewa da duk wata karfi da jarumtarsa.

Godia kawai ya iya yi a cikeda nustuwa da cikar burin daya kasa yadda da zai cika din.

Wata maganar Dad ya janyo masa wadda sam ya kasa cirewa da dauke tinaninsa akan maganar anbasa auren fammah jeerah zata mallakinsa.

Ganin hankalinsa ya kasa dawowa daidai sam kwata kwata ya sanya Dad din sakin murmushi yana dawowa akan maganar auren wanda zaa daura a kwanaki kadan Al'amin ya zuba masa idanuwansa yana bin kowace kalma da lafiyayyan nutsuwa da bita daga karshe wani murmushin da baisan yama sakeba ya saki yana sake godiyar data saka Dad shiru yana kallansa da murmushi akan fuskansa yana cewa

"Kodai zamu bar daurin auren nan ne sai ta gama an koma Nigeria gabaki daya?"

Kallansa Al'amin yayi yana dariya mara sauti da girgiza kai yana cewa

"No no ai baka magana Biyu"

Dariya Dad yayi yana cigaba da maganar datake saka bakin Al'amin din buduwa yana magana kaman ba shi dinba da babu hayaniya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login