Showing 174001 words to 177000 words out of 244256 words
tashi sam bata fito ba da dan zazzabi tace ta tashi dan haka ko Mum sedai tazo dakinta ta dubata tai mata sannu.
A dining harsukai breakfast suka gama bai ganta ba hakama a dishes din dake jere babu ko daya dayake da tabbacin ta saka hannu a aikinsa dan haka tea zalla kadai yasha kadan ya miqe yayi musu sai anjima ya fice.
Sai kusan rana ta fito a shiryenta ta nufi kitchen a ciki taci abincinta tana gamawa ta fito dauke da guava drink dinta da roban ruwa biyu ta koma dakinta tai zamanta acan.
Fammah datazo dakin suka wuni hadda Mum ma ta shigo ta dan zauna cikinsu suna fira da wayar Fammah ta kira Dr mum sukaita magana ta gaisa dasu mommy ma kafin ana maidawa Dr Mum wayar ta bude baki a natse tace
"Dr Mum inason dawowa gida"
Shiru Dr Mum tayi tareda dan shiga mamaki tace
"Lafiya dai ko?
Wani abin ya faru ne?
Dan girgiza kai tayi kaman tana ganinta tace
"Aa ina kewan gida ne kawai kuma na dade"
Sake shiga mamaki dr mum tayi kafin ta dan sauke numfashi sbd sun samu Dad yayi shiru baice komaiba haryanxu amma yanxu tana dawowa fitinarsa zata tashi dan kuwa tasan babu alkhairin dazai biyo bayan wannan shirun nasa indai Hakeem ne.
"Kiyi hkr idan kun tashi dawowa saiku dawo gabaki dayanku kinji"
Shiru tayi kirjinta na sake wani sabon nauyin dataji kaman hawaye zasu ciko idanuwanta dan nesanta kanta takeson yi dashi da matarsa.
Sallama sukai ta ajiye wayar tanajin Idanuwan Mum a kanta da mamakinta tace
"Meyasa kikeson komawa SANAAH bayan duka gamu ga fammanki a tareda ke?
Dan dagowa tayi ta kalli mum din da hana yanayinta ko daya bayyana da yar sakewa tace
"Mum wlh kewan gida nakeyi bantaba tafiya ba na dade haka"
Fammah da sam batama yadda da SANAAH din ta tafi ba jikinta ta kwanta tana cewa
"Tare zamu tafi gwara ma ki hakura kawai"
Murmushi mai sanyi kawai SANAAH din ta sake tana dan jan hancin famman.
Mum da itama sam batajin ta tashi tafiyar yanxu kokarin nunawa SANAAH tayi zamanta tayi tana son cusa mata shaawan qasar.
Zuwa yamma Mum tayi bai dan haka suna sitting room sunata shaaninsu su kuma suna daki suna tasu firar wadda fammah ce mai yi itadai tana zaune shiru tana sauraranta da binta da ido batareda tace komaiba.
Da daddare latti sukaci dinner dinsu wadda sam bata fitoba dan tini tayi tata tai shirin bacci tayi shigewanta dakin Fammah ta kwanta acan.
Yanzu kam ya tabbatarda janyewa tayi daga duk abinda ya shafesa dan kuwa ko yanzu ma babu komai daya nuna tashiga kitchen a cikin abincin da aka jere.
Ms Meenah da itama ta rasa gane yanda ya zama busy a kwana biyun maqalesa tayi a daki tanata zuba masa tambaya da son samunsa yanda ya kamata amma kusan hakan bai samu ba dan kansa dayake ciwon da idanuwansa ma sun nuna sosai dan ja sukai suna sauyawa gabaki daya.
Washe gari a dining din bayan kowa ya zauna yana isowa cikin nutswa har lokacin kansa bai dena masa ciwo mai tsanani ba zaunawa yayi a natse tareda dagowa a natse cikin rashin son ko doguwan magana sbd kamewa ya kalli Fammah ya bude baki yace
"Where is SANAAH?
Is she okay?
Data dena fitowa cin abincin tana ci acan daki??
Mum ce ta riga Fammah amsawa da cewa
"Nima har mamakin yanda ta dena zuwa table kwata kwata nake gashi tafara cewa gida takeson komawa ta gaji da nan,
Na rarrasheta fammah ma tayi amma kaman bata hakura bafa,
Ko kai Dad nasu zaka mata magana may be ta hakura pls"
Dago idanuwansa dasuka sake sauyawa yayi da wata yanayin daya saka Fammah jin tension din gurin a jikinta
Ita kanta Mum din idanuwansa ta kalla da jin wani iri amma bata sake cewa komaiba sbd ganin ya bude baki kai tsaye yace
"Tana ina ne??
"Tana dakin fammah ne,fammah je ki sanar mata Dad dinku na kiranta"
Dakatar da fammah din yayi yana sake bude bakinsa yace abarta idan ya dawo zuwa dare zaiyi magana da ita.
Dadin hakan sukaji dukansu dan haka abincin suka faraci hankali kwance da farin ciki banda shi da juice kadai yasha ya miqe ya fice.
Da rana Mum fita tayi bata dawo ba sai yamma sosai tareda baqi suka shige palonta sunata firarsu da turanci tana sake jin kanta sbd a cikinsu mijinta shine babban nasu mazajen.
Fammah ma taje cikinsu ta gaidasu suka dan taba firar da ita kafin ta fito ta barosu ta fita tana waya zataje da mota gidan wata abokiyar karatunta da sukai zata bar qasar yau so akwai sauran takardun da zata karbo a gurinta dan haka tana fita motocin Dad dinta suna dawowa bayan sallar magrib kenan.
Koda ya shigo ba kowa koina shiru Ms Meenah da bakinta suna can baya an hada musu table a kusa da swimming pool na gidan zasuyi dinner dinsu acan.
Kai tsaye bangarensa ya wuce ya shiga shower wadda ta daukesa mintina sosai sbd kansa ya kasa dena ciwo.
Yana fitowa cikin fararen kayan shan iska ya shirya marasa nauyi shirt da wando sai slippers bayan yayi sallah ya fito zuwa dining.
Ba kowa a dining room din dan haka baima zauna ba sbd ya juya yabaro gurin tareda nufar palonsa kai tsaye ya koma ya zauna yana jin sam kansa ba dadi.
Wayarsa ya dauka sbd bazai iya jurewa ba kansa bugawa yake neman yi ya saka kiran Meenah wadda tana dauka cikeda nishadi da wata isa ta ambaci sunansa tana cewa
"Hi my love"
Kai tsaye bai tsaya wata maganar hayaniya ba da nutsuwa yace
"I'm back ina buqatan something liquid mara nauyi"
Cikin kulawa da nuna soyayyarta a bayyane tace
"Ok zansa SANAAH ta kawo maka tinda daman zakai magana da ita"
Tana gama fadan hakan shine ya kashe wayarsa da mamakin ko bata gida ne?
#MAMUH
09033181070
[11/06, 1:47 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
107
Wayar dakin SANAAH ta kira wadda take zaune ta idar da sallah tai shiru tana jin dumi na sauko masa alaman zazzabin datake dan fama dashi duk dare amma batama damu ba sam ita da gaske gida takeson komawa.
A natse da rashin hayaniya takai hannu ta daga wayar tareda bude bakinta da sautinta mai sanyi tace
"Yes"
Jin muryan Mum ya sakata dan kallan wayar kafin ta sake gaidata da girmamawa da nutsuwa sbd tinda mum din ta dawo basu hadu ba tana daki bata fitoba.
"Ki kaiwa Dad dinku wani dan liquid abinda zaici ko sha yanxu nan pls dan bayajin Dadi"
Tana gama fada ta kashe wayarta batareda jiran jin komai daga SANAAH dinba wadda taso cewa itama batada lafiya bazata iya fita ba.
Shiru SANAAH din tayi tana sake jin wani abu mai nauyi ya danne kirjinta na duka kalaman Mum din kaf dinsu.
Wurgi tayi da wayar tanajin sake tsanar gidan gabaki daya da jin wlh bazata iya cigaba da zaman ba.
Sai data jima bata fitoba kafin ta fito ta isa kitchen ta hada masa wani lafiyayyan Cereal dayaji madara sosai amma bata saka sugar ba sbd zaqin madaran is ok banana ta yanda masa a ciki mai dan karfi ta doro a tray ta fito fuskanta a kame normal yanda duk wanda bai taba saninta ko ganinta yake iya fara ganin ta nufi dining taga baya nan harta ajiye zata tafiyarta sai kuma ta dawo ta sauka sbd zai huce ta juya ta nufi palonsa.
Yana zaune a natse a kame idanuwansa akan flats screen yana kallan da hankalinsa bawai yana kai bane nutsuwan kwakwalwansa yake buqata sosai ko kansa zai dena ciwon dayake fama dashi.
Da sallama ta shigo a natse idanuwanta basu dago ba inda zata ajiye tray din ta kalla tana isa gurin ta ajiye ahankali tareda dan dagowa babu kowace yanayi na sakewa ko sabo tace
"Ina wuni,gashi Mum tace na kawo"
Qarasa ajiyewa tayi tana juyawa zata fice ya bude baki ya ambaci sunanta data jisa da kyau har cikin kanta amma bata juyoba ta tsaya cak daga inda take na tsawon seconds kafin ta juyo kadan ta bude baki tace
"Naam"
Wani irin kallo ya sauke mata da idanuwansa da suka sauya ya sauke kafarsa dake kan daya ya miqe tsaye tareda takowa ya iso gabanta gap sosai har suna shaqar numfashin juna ta dan motsa ahankali tareda yin baya ta dago tai masa wani kallan daya saka yunwar cikinsa bacewa a take kansa na sake sarawa yace
"Yaya kike?
How are yoh
How have been??
Bata dago ta kallesaba sbd wani nauyin daya danne kirjinta da bakinta ta dan ja baya kadan ahankali tareda dago kanta bata kallesaba tace
"Alhamdllh,thank you"
Dan shiru tayi tana jin wani zazzafan kallansa akanta wanda take jin sanyinsa da rasa abin fada akanta dan kaman maganarsa ta qare baisan ta inda zai fara bayanin abinda bama zai bayanun ba.
Dagowa tayi kadan ta kallesa a lokacinda yayi taku daya gareta zai kama hannunta tace
"Inason komawa gida pls"
Kaman daga sama yaji zancen dan haka kallanta ya dan dago yayi tareda juyawa ya koma inda ya taso ya zauna yana jin ciwon kansa ma na dawowa sabo ya sauke wani zazzafan numfashi yana bude baki yace
"Why?
Hannunsa daya ya miqa mata yana kasa riqe kansa yace
"Zo ki fadamun menene matsalar?
Zo ki fadamun abinda ya saka kike wahalar da kanki bayan bakyason ganina bare nasan dalilin"
Wani sabon kishinsa ne ya taso mata ta dago ta kallesa da idanuwanta da suka shiga cikin nasa yaji yana sake rasa nutsuwa da kwanciyan hankalinsa kafin yace komaib tace
"ba komai ni gida kawai nakeson komawa"
Tasowa ya kuma yi wannan karan damuwan dake boye a cikin kansa da mamaki dan bayyanuwa sukai ya nufota bai tsaya komaiba ya kamota gabaki daya xuwa jikinsa ya mata wata riqon da har cikin jininsu suka jisa da wata irin kewan da zata iya kasa dukkaninsu rasa kansu ya kalli fuskanta data rintse idanuwanta da karfi batason kallansa wasu hawaye suka gangaro dags cikinsu wanda ya sakasa binsu da kallo tsigar jikinsa na tashi dan kuwa yasan ba qaramin radadi take ji ba dan haka ya bude hannuwansa ya sakata jikinsa yana rungumeta da wata irin sanyi da tsananin jinta a zuciya da jini da bargo da kowace tsiga ta gangar jikinsa.
Kawai kuka ta fasa masa mai wani irin ratsawa da rashin sauti sosai yana shigarsa tako ina da warware kowane kamewa,nutsuwa da lissafinsa yana jinta.
Kukan take masa sosai tsawon mintina kafin ta zare jikinta daga nasa ta juya kawai ta fice tana wucew dakinta da gudu tabarsa tsaye.
Kasa motsawa yayi yanaji gabaki daya shima gidan da qasar na ficewa daga kansa ahankali.
Ita kuwa tana isa dakinta kan gadonta ta xube tana cigaba da kukan dayake dankare da kirjinta duk kwanakin.
Ahakan fammah ta dawo ta sameta cikin wannan halin tana zaunawa kusa da ita cikin tsananin damuwa da tashin hankali da mamaki ta dafata ta fada jikin fammah din tana cigaba da kukan da saidata jima tana yi kafin ta iya samun abinda yake danne da ita ya dan fada mata.
Fammah duk damuwa ta shiga ta ringa tambayarta abinda ya faru amma bata iya cewa komaiba sai data shiga bathroom tayo wanka ta fito a natse ta sanar da ita gida takeso.
Kiram mum fammah tayi lokacin baqinta sun tafi kenan dan haka nan dakin tayo tana kallan SANAAH taji hankalinta ya tashi musamman dataga yanda idanuwanta da fuskanta sukai jajir.
Yanda suka daga hankalinsu hadda sanar masa ya sakata jin tausayi da sabuwar kaunarsu har cikin ranta hadda Mum din ta dan sake tana nuna musu ta dena.
Da safe koda ta tashi fuskanta ta sake ja idanuwanta ma sun dan kumbura sbd a cikin tsakiyar daren ma sai datayi sbd kafin Mum din ta wuce gurin mijinta sai data shigo gurinsu tana fidda wani fitinannen kamshi da wasu kayan bacci masu kyau a jikinta duk da ta saka babbar after dress akai kafin ta isa dakin nasa.
Suna tashi da safe SANAAH wankanta tayi ta saka kayanta marasa nauyi doguwan chiffon material budaddiya mai kyau purple ta dauke gashinta a tsakiyar kanta ta koma kan sofa ta lafe batada niyar ma ko fita palo bare zuwa dining din data yafe.
Mum ce ta shigo dakin bayan fammah ta gama shiryawa ta juyo zatai mata maganar fita breakfast.
Cikin adonta itama mum din take dan daidai ta iso tana kallan SANAAH din da bada umarni dan kawai ta tilastata fita breakfast din tace
"Ku fito dukanku oya SANAAH taso banason jin komai"
Juyawa tayi zatai fice SANAAH ta bude baki da dan sauti mai nutsuwa tace
"Banajin yunwa ba yanxu zanyi breakfast ba Mum"
Bata juyoba tace
"I dont care dole ki fito daga yau na hana wannan zaman dakin da kike wanda shine yake sakaki jin kewan gida kina wannan kukan"
Ficewa tayi SANAAH da idanuwanta suka sauya da wani irin damuwa da nauyin kirji mai karfi kasa dawo da kallanta tayi akan fammah zatai magana fammah din itama ta juya da sauri ta fice sbd itama batason wannan damuwan da SANAAH ke shiga gwara ta ringa fitowan.
Fammah na ficewa hanyar palon Dad dinta ta nufa gaidasa tana isa yana fitowa daga bedroom dinsa idanuwansa har lokacin babu saukin komai a cikinsu.
Qarasowa tayi tana dan rungumesa tana gaidasa da cewa
"You dont look good Dad,yaya kan?
Ko kana buqatan ganin likita ne Dad"
Girgiza mata kai yayi a natse yana dan kissing kanta yana bude baki wani hayaniya da son doguwan magana yace
"No Doc, alhamdllh insha Allah"
Fitowa sukai tana masa magana yana sauraronta yana saka kai a dining din matarsa datake kokarin zama fasawa tayi tana nufarsa sbd koda ta fito bai tashi ba daqyar ya iya samun baccin ko yauma sbd tsananin ciwon kan daya hanasa ko baccin arziki.
Gurinsa ta taho tareda dan rungumesa itama da kulawa tana cewa
"Good morning my love"
Bakinta takai zatai kissing gefen fuskansa daidai nan SANAAH ta sako kan da akan idanuwansa fes dan haka juyawa yayi ahankali ya kalli fammah yana dan sake mata wani kyakkyawan murmushin daya hana Meenah isowa da bakin nata sbd juyewan da yayi gurin yarsa.
SANAAH kuwa a natse da wata irin kamala ta iso tareda zaunawa a natse batareda ta dago ta kalli ko inda sukeba.
Mum na ganinta tace "yawwa koke fa baby SANAAH"
Wani murmushin da ya sakasa mata wani lafiyayyan kallo ta sake tana dan daukan cup din juice mai sanyin dake gabanta ta shanye a lokaci daya tareda ajiye cup din har saida yayi dan sautin daya sake sakasa dagowa a natse ya kalli idanuwanta da suke a kumbure hakama fuskanta datai ja.
Ko spoon din dake gabansa bai saka hannu ya tababa ya miqe yana kallan time yace bazai samu tsayawa ba ya fice yana barin Mum da hannunta tsaye datakai zata tabasa cikeda wata sakewa.
SANAAH kuwa tinda ta shigo bata kalli inda yake dinba harya miqe ya bar gurin.
Itama bata iya cin komaiba bayan juice din data ringa dirkawa cikinta tana rage zafin cikinta da sanyinsa.
Suna gamawa tabar dining din Mum rana nayi tajasu suka fita yawo.
#MAMUH
09033181070
[11/06, 3:25 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
108
Basu dawo ba sai dare dan haka tana shigewa bata sake fitowaba sai da safe wanda sbd kada ace ta fito dining ya sakata tashi da azumin lada kawai shi kuwa a ranar sbd kada ma kaucewa komai bai fito breakfast dinba haka ya fice saidai a office ya dan ci abincin a luxury restaurant dinsu abinda baima taba yiba.
Sbd tana azumi basu fita koina ba sai washe gari shima ta kuma tashi da azumin da hakanan suka fita din basu dawo ba sai dare shima.
Da safen ma kusan daga shi har ita babu wanda yazo dining dan wannan karan ta daukanwa ranta indai dining ze sakata ganinsa ta ringa azumi kenan daga yanxu har lokacinda zata tafiyarta.
Mum bata gane komaiba harkar gabanta kawai takeyi dan tanata abubuwan yi kafin ace tafiyar zaayi dan haka ta dena zama kwata kwata ita kuma SANAAH ta qauracewa fitowa kwata kwata koyaushe tana daki bata kuma barin ko a wayar yarsa yaji motsintaba,
A cikin azaba da wuya take azumin sbd sam bata iya jure yunwar amma taurin ranta yaqi barinta denawa,
Shi kuwa sati daya akai ana hakan ya hakura ya fara fitowa dining din sbd tinanin ganinta amma sam bata zuwa ta dauke wutarta koina kaman bata gidan.
Sati kusan biyu aka kuma dauka tana cikin wannan halin bai kuma taba sakata a idanuwansa ba ko motsinta bai taba ji ba,
Ana cikin hakan ta sake daga hankalinta gabaki daya ta tada na mutanen gidan da gida takeso ta hana kowa sukuni kaman qaramar baby dan ko mum da batada damuba tashi hankalinta yayi da ganin yanda SANAAH din duk ta rikice da rigimar gida takeso,
Kowa a cikinsu rarrashi da tarairayanta yake akan ganin ta nutsu amma sam ta rufe idonta rigimar da basusanta da itaba ta ringa musu da aikin kuka.
Duka wannan tashin hankalin datake yana sane dashi amma taqi barin ya ganta ko kadan ta saka zuciyarsa a matakin da ko fita aiki ya dena kwata kwata hakama koyaushe yana office din cikin gidan yana bawa Meenah daman futa duk inda takeson zuwa da dawowa duk lokacinda taso sbd ita ta kwantar da hankalinta ko yayane tabari ya ganta yaji abinda yake damunta da rarrashinta amma sam ta bijire karshe ma sbd kada ya ganta Mum din take bi su fita sau dare.
Karshe Dad dinta ta kira ta sanar masa tanason dawowa gida ita.
Dad jeerah dake jiran a tabata yayi musu abinda zasusan da shirunsa na jira ne yanajin ta fada hakan ya sanar dasu su dawo masa da Yarsa dan baisan zama a matsayin me takeyi acanba abasa ita tinda dai haryanxu baiji labarin an bata matsayinta ba.
Sake rarrashinta Mum tayi da fammah amma ba alaman zata hakura dan haka dole aka fara shirin komawan.
Shi kansa tafiya ce a gabansa mai mahimmancin daya kamata yayi tin last week amma ya kasa tafiya koina din dan haka shima ya yanke hukuncin komawan tasu Nigeria din indai hakan zai saka ta sauko ya kuma samu ganinta.
Imran aka saka ya fara shirin tafiyar tasu wadda ta daka Mum zama busy sosai da gaske sbd ta gama duka abubuwan datake so kafin ta tafi din.
Fammah ma duk yanda SANAAH din ta koma musu rigimammiya haka ta ringa lallabata suna fita nasu yawon da yin siyayya da yan abubuwan datake buqatan yi kafin barin qasar.
Ba tareda shi zasuyi tafiyar ba dan shi saiya biya Miami dole kafin ya samesu dan haka ana saura kwana daya su wuce akai musu