Showing 15001 words to 18000 words out of 244256 words
hankalin abokan aikinta likitoci mummunan tashin yanda zasu iya sanar da ahalin jeerahs da ita kanta fammah din wannan mugun labarin idan ma ta samu rayuwarta kenan to anyi arziki.
Da gaggawa aka sake shiga da ita wani sabon aikin wanda ya saka kowa nutsuwa murna ta dakata tukuna.
#MAMUH
#RAHEEM HAKEEM JEERAH
#MUHAMMAD NASIR IBRAHIM
#JEERAHS
GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee
10
*_HARGITSI_*
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t
*********
Duk wannan tashin hankalin da tsananin da dr fammah ta shiga tin kafin haihuwa zuwa bayan haihuwan captain hakeem jeerah bai samu damar zuwa ba duk yanda yaso zuwan babu ko yar qaramar hakan dan haka yana can cikin matsanancin tashin hankali da damuwa amma duk da hakan ya iya dannewa ya fuskanci aikin dayake gabansa mai mahimmancin da zai qara daga matsayinsa zuwa sama.
Iyayenta kam lamarin yayi musu shigar bazatan da zuciyar mahaifiyarta ta kasa dauka saida aka kaita asibitin da dole likitoci suka riqeta dan haka ba damar zuwa ga yarsu duk yanda suke cikin tsananin damuwanta da babynta.
****aikin da akai mata me tsananin hadari da taka tsantsan ne an dauki lokaci me tsayi sosai kafin aka fito da ita tsakiyar dare zuwa private dakin hutun da zata zauna.
Likitoci da nurses sun gama komai akanta sun fice sun bawa familyn daman shiga amma babu kowace irin hayaniya da ake buqata.
Sun shigo da yawansu sun tsayu akanta cikeda addua da fatar warkewanta.
Har asuba su Ummah na dakin tareda ita kafin gari ja fara haske suka tattara suka koma gida aka bar mutum daya a cikin masu aikinta dan kulawa da ita kafin anjima.
Da Raheem suka tafi sbd ko an barshi bata hayyacinta da zata iya basa nono ko wani abin dan haka suka tafi gidan dashi dan aje a shiryasa.
Wuni guda ta sake yi bata farfadoba bare dawowa hayyacinta dan haka likitoci suka sake dunguma da duqufa akanta damuwansu na ninkuwa sbd akwai abinda suke tsananin gudu da kokarin hanasa tabbatuwa.
*****fatima data kwana ta wuni ta tabbatarda ta warware sosai hankalinta bai kwanta ba ta kasa samun nutsuwa haka ta shirya ta fito tareda khalil wanda ya kaita har asibitin itada babyn tukuna ya juya ya tafi.
Ko data iso dakin babu kowa na familyn jeerah dayake asibitin bayan wadda aka bari ta kula da ita dan haka jikinta ya sanyi musamman data sauke idanuwanta akan fammah din wadda duk wata rahama da kyan gani sun bar jikinta da fuskanta dan kuwa tayi wani duhu fatarta ta bushe bakinta ma ya bushe tana kwance kaman babu rai a jikinta.
Silalewa tayi ta zauna idanuwanta cikeda hawaye tana jin hankalinta ya gama tashi gabaki daya daga karshe kasa riqe kukanta tayi ta sakesa ahankali sbd tsoron daya shigeta dan kuwa haka mahaifiyarta ta koma kafin rasuwarta tabar duniya.
Sai datasha wani irin kuka sosai kafin ta iya dago fuskanta ta kalli saratu dake gefenta tsaye shiru itama tausayin fammah din takeyi sbd yanda ta kasa samun cikakkiyar kulawa da kauna daga dangin mijin daya kamata su kula da ita sbd mijinta da baya kusa.
Tambayar babyn fammah tayi
Saratun ta fada mata yana can jeerah villah an tafi dashi.
Wasu hawayen ta sake sharewa kafin ta juyo da kallanta kan fammah tana jin kaman zuciyarta zata dena bugawa sbd damuwa da wani irin daci.
Shiru sukai a dakin tsawon lokaci sai ga likitoci sun shogo tareda Su daddy da kansu da matayensu harma da Raheem an dawo dashi.
Ummah data ga fatima batama lura da goyon danyan jaririn dake bayanta ba ta dan yi mata fadan inda ta tafi tin jiyan kafin ta miqo mata Raheem wanda yake cikin lafiyayyan lallausan bargon babys me fari qal yana bacci jikinsa sanye da fararen bodysuit da hula an nadesa sosai.
Hannuwanta biyu ta saka suna wata yar rawa zuciyarta na bugawa da kaunarsa idanuwanta fes akansa tana masa kallanda da mahaifiyarsa na hayyacinta itace zatai masa ta rungumesa jikinta tana sauke ajiyan zuciya tsananin kaunarsu da sonsu su biyu shida nasir dake bayanta tana ratsota ta gaba data baya.
Ficewa tayi sbd bawa su Daddy guri da likitoci saratu na biye da ita.
Suna fita zaunawa tayi a qaramin sitting room din dake dakin ta sake dago Raheem da kai tsaye zaka san balaraba ce ta haifesa ta zuba masa ido cikeda kauna kafin ta fara rero masa adduar dataiwa danta shima.
Basu wani dauki time ba a waje akace su koma ciki sbd Raheem.
Su daddy sun gama komai kuma an gama jero musu komai na halinda fammah take ciki wadda ta rasa mahaifiyarta shikenan ba ita ba haihuwa har anaba hakama fashewan mahaifiyarta ya janyo manyan matsaloli a lafiyarta da gangar jikinta da ba yanzu ne ba itada lafiya sedai a sannu sannu lokaci zai warkar da komai.
Babu wanda ya iya cewa komai a familyn jeerah sbd lamarine daya girgiza duniyarsu da kowa ya dauke wuta.
Fitowa sukai suka bar asibitin dan komawa a san yanda zaayi a sanar da Captain Hakeem.
Ganin fatima da akasan bayan ita Fammah bata buqatan kowa ya saka baa damuba sedai aka kawo musu dukkanin abinda zaa buqata da sakewa.
Fammah bata farfado ba sai a daren ranar shima iya idanuwanta kawai take iya budewa bata iya ko motsawa me dan karfi bare tashi magana ma bata iyawa sedai kallo kawai.
Fatima ce kadai a tareda ita ko data farfado babu kowa nata babu kowa dangin miji,
Lumshe idanuwanta tayi ta sake budewa a hankali tana jin tama rasa kanta bare sanin menene takeji take cikinsa.
Likitoci suka bawa fatima daman gyarata ta dan sake shiryata aka sake gwaje gwaje da sauran abubuwansu suka gama komai suka fice.
Baa bada daman bata komaiba na ci ko sha drip ne da allurai kawai ake bata ba bata lokaci.
Raheem ma a hannun fatima take ganinsa wanda shima ake cikin tashin hankalin yunwar dayake ciki dan kuwa kuka yakeyi sosai ida yatashi.
Yanayin halinda Raheem yake ciki ya sake daga hankalin jeerahs da ita kanta fatima da mahaifin fammah wanda abubuwan sukai masa yawa ga Amminta a kwance gata a kwance babu me sauki a cikinsu.
Shi kansa hakeem dayake can sabon tashin hankalin ya shiga duk da har lokacin baa sanar dashi komaiba na abinda ya samu din me tada hankali.
Likitocin yara manya aka nema suka zo suka dubasa suka bada shawarwarin abinda ya kamata take aka siyo duk abinda sukace da madara kaman zaa bude shagonta.
Fatima aka nunawa komai da bayanin komai na yanda zata ringa basa har lokacin basu bawa tata haihuwan mahimmancin daya kamata suyi tinanin abin zai mata yawa ba.
Ita kanta fammah dake kwance tana dan fahimta da jin wasu abubuwan tausayin fatima tafara yi ganin irin wahala da dawainiyar datake fama da ita a cikin kwanakin da suke tafiya na jinyarta da fama da jarirai guda biyu dama kuma ita kanta da jegon takeyi amma ba wanda ya tina da hakan.
*****wata irin jinya me nauyi da azaba da mawuyacin hali fammah takeyi da babu sauki a cikinta,
Babu daren da bata wani irin kuka mara sauti da taba zuciyar me kallo dan hakanne itada fatiman suke zaunawa suyisa a tare zuciya da gangar jikin kowannensu tana quna,
Fatima rayuwa tayi mata wani irin nauyi a dan lokacin sbd itama lafiyar neman gagararta takeyi sbd jikinta dayake danye amma wahala da dawainiya babu wadda bata yi.
Fammah na cikin mummunan qunci da baqin ciki da dacin zuciyar da takejin kaman zata mutu ne tabar duniya,
Iyayenta na can a cikin mummunan halin jinyar Amminta datakejin kaman bazasu hadu ba hakama mahaifinta tasan yana gap da kwanciyar shima matiqar jikin mahaifiyarta na sake rikicewa a kowane lokaci hakama nata jikin,
Koyaushe ya kirasu kwarin gwiwa yake bata yana danne dacin halinda yake ciki yana tabbatar mata da indai fatima na tareda ita hankalinsu zaici gaba da kwanciya suyi jinyar Ammin dakyau.
Hakeem ma fatima ce wadda ke saka zuciyarsa dan samun qanqanuwr nutsuwa akan fammah wadda a yanxu ta sallama ta cire rai daya rayuwa kwata kwata mutuwar kawai take jira.
A lokacinda akaiwa RAHEEM HAKEEM JEERAH nadin sunansa a tare da dan fatima akai musu yanka da komai akai musu yankan ragunan suna da shanu akai sadakarsu gabaki daya.
Tinda akai yankan sunan babu wata hidimar sunan da zaayi sbd jikin fammah dake kwance har lokacin.
Satinta uku a asibiti harda kwana hudu anata fama jinya ba sauki kafin aka sallamota tareda shawarwarin likitoci akan kada a fita da ita wajen da akeson fiddata a yanzu sbd yin tafiya da ita zai iya janyo matsalar da zaa iya rasata ayi hakuri ayi jinyar a hankali idan tayi healing ko yaya ne sai a fita da ita.
Wannan shawarar dole aka dauka aka dawo da ita gida aka bude babin jinyar da baa gane komai sbd tinda fammah tasan abinda ya gama samunta a ranar ciwonta dawowa yayi sabo sbd tashin hankalin da kowa ya shiga sai data sake kwana biyu a kwance bata san inda kanta yakeba tukuna ta farfado.
Farfadowanta sabo ya dawowa da fatima jinyarta sbd ko ruwa ake bata dawowa sukeyi,
Fammah dake rashin lafiyar da fatima dake jinyar a tare suke wata irin mummunan rama da bushewa da tsiyayewa sbd halinda kowannensu yake ciki,
Fatima ga nata rashin lafiyar dake cinta,ga jarirai biyu da dawainiyarsu ta tsayar da rayuwarta cak guri daya musamman Raheem da har lokacin ya kasa sabo da shan madarar kuka da wuya yake a cikinta wadda tafara sakasa rashin lafiya mai karfi,
Sannan ga jinyar fammah da itace wanketa itace shiryata itace bata abinci duka a kwance ga damuwan rayuwarta datake ciki da danta dama ta fammah duka.
Ta fige ta lalace ta zama kaman me qanjamau babu sauran kowane jin dadi a rayuwarta.
#MAMUH
GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummiGANIN IDO 2026
Mamuhgee
11
*_HARGITSI_*
By
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t
*********
Ahankali ahankali suke tafiyar da rayuwarsu cikin damuwa da dacin jinyar da a yanzu wata uku ake magana kuma har lokacin fammah na jinya sosai sedai ta samu sauki tinda tana zama yanzu hakama tana cin abinci batareda ya dawo ba kuma tana magana sosai sedai babu karfi a tattare da ita da kuzari har lokacin,
Raheem ya koma mara lafiyar kwata kwata shima sbd yunwa data kamasa anyi yawon likitoci dashi har an gaji sam ya kasa zama cikakken lafiyayye dan haka ne aka dawo da kokarin ganin ko zai samu nono ne daga mahaifiyarsa amma a banza sbd koya samu din baida wani amfani sbd kadan ne kuma ita batada lafiyar samun kuzarin shayarwa.
Gabaki daya farin cikin samun Magajin jeerah komawa ciki yake kokarin yi sbd ganin halinda Raheem din yake ciki dan haka suka duqufa nemawa uwarsa lafiya dan ta samu dama da lafiyar shayar dashi.
Suna shiga wata na hudu Hakeem jeerah ya dawo Nigeria garesu dawowan da zai jima bai komaba kuma dawowan da zai jira kiran qarin matsayinsa da zai qarasa sauya rayuwarsa gabaki daya kuma ya qarawa ahalinsa suna da matsayi a idon duniya.
Fatima tafi kowa farin cikin dawowansa sbd halinda fammah take ciki da suke cire rai koyaushe daga tashin kowace safiya.
Dawowan hakeem ya saka fammah fasa kuka a gaban wani karan farko idan ba fatima ta rokesa ya kaita qasarta gaban iyayenta tayi jinya idanma batada rabon tashi ta cika a hannun iyayenta.
Shi kansa ya girgiza da mummunan ganin da yayi mata da mummunan labarin daya tadda wanda ya saka ya rasa ina zai saka kansa ga Raheem ma sai ahankali.
Irin yanda ta daga hankalinta da son komawa gida jinya ya sakasa fara tinanin amincewa amma ganin Raheem, ai iya rasa ya saka ya raba tinaninsa biyu iyayensa kuwa take suka kasa aminta da hakan.
Ita kanta a lokacin tana tsananin tausayin Raheem dan haka ta yanke hukuncin daya girgiza fatima da hakeem a lokacinda ta fada musu buqatarta.
Fatima dataji zancen kaman a mafarki zubawa fammah idanuwanta tayi shi kansa Captain Hakeem kafe fammah yayi da idanuwansa fararen da suka sauya yana mata kallan tausayi sbd tsoron ko ciwon ya taba kwakwalwanta ne.
Hawaye ne masu zafi suka gangaro mata batareda jin komai ko shakka ko fargaba saima kara jin yadda da hakan datake yi sbd tasan ko bata rayu ba Raheem dinta bazaiyi maraicin uwa ba matiqar fatima na raye dan hakanne ma ta yanke shawaran bawa fatima Raheem ta shayar mata dashi nononta.
Kasa yadda da hakan Hakeem yake kokarin yi amma yanda ta gama kashe masa jiki da wani irin kuka da maganganun da suka sakasa tsoro ya saka ya kalli fatima wadda idanuwanta sukai jajir batada zabi sai wanda suka zabar mata.
Hakeem dinne ya kalleta da nutsuwa da qasqantar da kai dan bata haqqinta na raayin zatayi ko bazatayi ba ya roketa hakan.
Fammah ma zuba mata ido tayi cikeda tsananin kaunar ta kasance wadda zata shayar mata da Raheem kada ya rasa ransa.
Batada zabin daya wuce yin duk abinda zai kawo sassauci da abinda akeso a rayuwar fammah da Raheem dan haka ta amince.
Amincewanta ta kawo sauyi me girma a rayuwar Raheem da iyayen nasa harma da Familyn jeerahs da babu wanda yasan abinda yake faruwa sbd daga fammah sai mahaifinta da Hakeem ne kadai suka san fatima na shayar da Raheem da Nasir a lokaci daya sedai kawai aka ga Raheem na samun lafiya yana warwarewa yana jiki yana zama babyn da suka jima suna tsananin son ganin yana zama.
Kulawa sosai Hakeem yake bawa fatima da fammah sbd dukansu suna buqatar kulawan.
Lokaci yaja samun lafiyar Raheem da fara wayonsa ya saka Zuciyar Mahaifiyarsa samun nutsuwa da amincin data kasa samu tin haihuwansa sbd tsoron rasasa,
Hakama samun lafiyarsa ya saka walwala da farin cikin ahalin jeerahs dawowa gabaki daya anata hidimarsa da nuna masa zallan gata da kaunar daya saka yanxu mahaifinsa ake tsananin tausayi ya qare a gurin jinya da kulawa da matarsa baida walwala baida farin ciki masu aiki ne da fatima ke kulawa dashi abinda bai kamata ba sam dan haka kai tsaye kaman saukan aradu iyayensa suka nemasa suka basa umarnin sake aure sbd samun mai kulawa dashi yanda ya kamata kafin samun dawowan fammah daidai tinda lokaci yaja sosai babu wani cigaba.
Da farko tashin hankalin maganar yaji amma daga baya saiya fahimtar dasu sam baya buqatan hakan musamman tinda shi din ba mazauni bane kada ya tarasu ya tafi ya barsu.
Sam Alh babba Ahmed bai yadda da hakan ba sbd babu wani uzurin daya wuce ya auro wadda ba iya shi kadai zata taimakawa ba hadda ita kanta fammah din.
Kasa fadawa kowa maganar yayi sbd yasan qarin aure garesa a yanxu ba abinda yake a tsarinsa bane tukuna musamman a yanzu da fammah ke jinya irim wannan amma yasan bazai kuma iya kauce hukunci idan iyayensa suka yanke ba.
*****Maganar qarin aurensa ta saka yaji yana son kai fammah din gida yanzu sbd kadama taji kota sani gwara ta tafi daga baya idan ta samu lafiya zai sanar mata sbd lafiyarta.
Su kuwa iyayen nasa babu bata lokaci aka fara shirin hadasa aure da daya daga cikin yan uwansa amma kowacensu nada maneminta kuma suna son juna dan haka aka ba bata lokaci kuwa aka hadasa da yar Ambassador Nuhu Sultan.
Auren gata da gata ne zaayi musu dan haka tin a gurin neman auren maganar ta fara bayyana a duniya tana yaduwa.
Fammah da fatima duka basusan abinda yake faruwa ba anata hidima da shirin yin auren wanda Sam ba wata hayaniya zaayiba sbd kada a tada hankalin fammah.
Tinda kwanakin bikin suka matso fammah ta fara rasa gane kanta sbd zuciyarta da lafiyarta dataji suna nauyi dan haka tayi sanyi ta rage kuzari sosai.
Fatima ma da tini ta zama uwar yan biyu ganin yanayin fammah sai ta dauka jikin ne ya dawo tinda yanzu haka yakeyi gashi a lokacin su Raheem din sun wuce shekara daya sosai biyu suke neman cikewa dan haka yayesu daga nono take kokarin yi har lokacin babu wanda yasan Raheem na shan nono.
Ana saura sati daya daurin auren Hakeem daya rasa inda zai saka rayuwarsa gurin sanar da fammah sai gashi kwatsam ta samu labarin daga bakin mai aikinta ta amanarsu itada fatima wato saratu.
Fammah sam bata yadda ba sbd tasan abune da bazai taba yiyuwa ba daga Hakeem dinta da bazai taba mata kishiyaba sbd sanin baa yimusu kishi hakama a daidai lokacinda take cikin wannan mummunan halin na jinya me wuya sama da shekara ga mahaifiyarta data rasa har abada itada haihuwa sedai kallo.
Kati da duk abubuwan bikin dake trending saratu ta nuna mata a waya ta zubawa wayar ido zuciyarta na kasa yadda har lokacin daga karshe ma jintane da ganinta suka dauke dan haka da gaggawa Fatima da itama ta kasa yadda ta kira hakeem din.
Kafin hakeem ya iso gidan daga inda yake nesa sosai mummunan kiran daya qarasa dakatar da rayuwar fammah cak ya shigo wayarta Na rasuwar Mahaifiyarta Ammi.
Mummunan halinda ta shiga dole akai gaggawar kiran ambulance wadda dole itace zata iya kaita asibi sbd ta sanqame.
Duk inda ake shiga tashin hankali fatima ta shiga ta firgita ta rasa inda zata saka kanta.
Kowa ya shiga fargaba da tashin hankalin ganin halinda fammah ta shiga dan haka aka fara gaggawan hada tafiya da ita Morocco din.
Shi kansa hakeem tashin hankali da damuwa kashi kashi yake ciki dan haka ya matsu yaga ta farfado.
Fatima dai bata wani shiga cikin ahalim jeerahs dinba tana gefe da Nasir da Raheem da baya wani yadda da kowa idan ba ita ba sai mahaifiyarsa da baima san itace cikakkiyar uwar data haifesa ba.
Fammah jikinta yayi nauyin da bata farka ba sai washe gari kuma tana bude idanuwanta akan Hakeem suka sauka wani abu yaxo ya danne maqoshinta da kirjinta sedai rashin uwarta datai a yanzu shine abinda yake gabanta dan kuwa ta rasa duniyarta kenan.
Bata cewa hakeem komaiba ko kalma daya bata iya furta masa ba abu daya ta nema daga iyayensa da kanta shine tafiya gida a cikin wannan halin datake ciki taji ta gani.
Iyayen nasa sun tausaya mata sun kuma jajanta rashin mahaifiyarta.
Babu wanda tayiwa maganar auren Hakeem kaman yanda bata bawa kowa damar yi mata maganar auren