Showing 324001 words to 327000 words out of 365093 words
furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa.
Tana fita ya kammala shirinsa tsab. Sannan ya fito ya nufi ɗakin da zasu yi wa macen tiyata. A nan ya isko su Dr Kamal suna jiransa a waiting room. Yana zuwa suka ƙarisa ciki.
Wata macece kwance a kan gadonsu na tiyata, tana sanye da blue gown irin wanda ake sanyawa waɗan da za'ayiwa tiyata, an shirya komai tsab, daga ganin wannan mata zaku san irin matan nan ne na kauye da basu waye sosai ba, basu san komai ba, cutarta aka yi da sunan ciwo za'a cire mata a mahaifa, kunga za'a cire mata shi gabaɗaya.
Cike da taka tsantsan suka fara aikin. Da yake sun kware kuma sun saba yi sai basu ɗauki wani dogon lokaci ba suka kammala komai, bayan sun gama Dr Mark ya ɗauki wata glass ball aka sanya mahaifar a ciki, sannan ya fita da mahaifar ta wata kofa. Su kuma Dr Kamal ya hau haɗa gyara wajen, Dr James yai mata ɗinki tsab, sannan ya ɗauki paper da pen, a natse ya yi rubutu the seme rubutun da ya yi wa matar farko da aka cire mata mahaifa.
Ya rubuta a dinga kula da ita sosai, a bata cima mai kyau har zuwa ta samu sauƙi, ta dinga shan abu mai ɗan ɗimi. Ya rubuta magungunar da yakamata a bata kafin ajiye paper kusa da hannunta, ya ƙara gyarata kafin ya kira nurses su fita da ita. Shi kuma ya bi bayansu Dr Mark.
A in da suke ajiye mahaifar suka nufa, a nan suka je Dr James ya sanya cikin kwalbar, ya saita na'urar dake jikin kwalbar ta fara bada yanayi daidai da cikin mace, suka tabbatar komai yana tafiya daidai, sannan suka nufi in da suka yi sashen eggs ɗin nan.
Kewaye suka fara yi a wajen suna duba dik wasu motsin eggs ɗin. Dr Kamal ne ya ce. "Wai ina Lazy ne yau? Bata bimu ɗaukar rahoto ba".......... Dr James da ya ɗan yi shiru for 2 mins ne ya amsa da. "Ban taɓa sanin Lazy bata da hankali ba sai yau, wai US zata je".
Zazzaro idanu Dr Mark ya yi. "US kuma?". Suka haɗa baki da Dr Kamal wajen tambaya. Kai ya jinjina masu alamar e kafin ya ce. "Kila ajalinta ke kiranta, dik da Hussain baya raye, na tabbata su Zayra'an suna da labarin abin da ta aikata bayan mahaifinsu, na tabbata kafin Hussain ya mutu ya basu labarin komai, tabbas sun san cewa Farooq na WS yana rufe, na tabbata suna can suna neman Farooq ɗin kamar hauka, kunga in suka kamata tasan me zai biyo baya".
Dr Mark ne ya ce. "Wai dama Lazy tasa aka kama Farooq?"...... Kai Dr James ya jinjina game da cewa. "Ita tasa aka kamasa, a lokacin da aka kama Haiza'an aka tafi da shi ta kira Farooq a waya ta shirya mashi gadar zare da sunan an far masu ya kawo masu ɗauki, yana zuwa aka kama shi, na tabbata Mahvir ba zai kyaleta ba, kai su Zayra'an ba zasu taɓa yafe mata ba".
Murnushi Dr Kamal ya yi. "Ai dik a tsananin yunwace suke da nemanta, ta kai kanta ga mutuwa"...... Dr Mark ya ce. "Ba zasu iya ganeta ba fa".
Siririn tsaki Dr James ya ja. "Sai dai idan bata ci karo da Zayra'an Bint Haiza'an ba, ina da tabbacin jinin Haiza'an zasu ganeta tsab, domin su baiwa da ita aka haifesu, kyauta ce daga ALLAH ba daga wasu ba, kuma Lazy ta manta abu guda, jinin uwa fusgan ƴaƴa yake yi, bugu da ƙari ta canza komai amma bata canza murya da gashin kai ba! Kamal ku baku san waye Haiza'an ba, na tabbata da ba zaku yi tantamar Zayra'an zai gane Lazy ba".
Kai suka jinjina kafin Dr Kamal ya ce. "Dik ba wannan ne ma ya fi damuna ba, na damu sosai a kan IRON FIST, ka sani na samu mun sani aiki suke yi domin al'umma, a shirye suke su dakatar da nasarar da muke samu, ina tsoron abin da zasu iya aikatawa, kun san suna da mugun haɗari"....... Siririn tsaki Dr James ya ja. "Ba zasu iya yi mana komai ba, dik bala'i mutum ba zai taɓa iya gano WS-HOSPITAL ba! Ba'a haifi mahaluƙin da zai iya ganomu ko ya dakatar damu ba, dan nasara aka haifomu a duniya!". With ho full confidence ya faɗa, yana jin tamkar dan su aka shinfiɗa kasar duniya!.
Jinjina kai su Dr Kamal suka yi, dan suma sun san a irin tsaron mai masifaffen karfin da suke da shi sai dai in fita waje suka yi za'a iya kamosu, amma a cikin WS-HOSPITAL kam wane mutum ya iya kamasu, kofofin shiga masu shocking na lantarki, sai Dr James ya shigar da password shocking ke ɗaukewa, kuma shi kaɗai yasan password ɗin, ai kunga kuwa ba zasu kamu ba a ganinsu!.
Haka suka cigaba da aiki suna tattaunawa game da nuna cewa IRON FIST ba su isa su dakatar da su ba, sun yarda da kansu kuma sun yi imani sune kawai masu nasara, dan nasararsu aka shinfiɗa duniya.
A gefe kuwa, Sister Zinta ta koma ɗakin jariran, nan ta tarar Dr Kamal ya gaba duba boy ya bashi dik wani abin da ya dace, ta dawo rike da yaron tana lallaɓa shi tamkar kwai a faranti. Ita kuma sister Zinta ta ɗauki wannan haɗaɗɗen yaro mai blue eyes da aka kashe ɗan uwansa jiya, ta rungume yaron tana yabon kyansa, daga nan ta ce. "As from today this is my baby, kuma na bashi sunan Haiza'an".
Ɗan zazzaro idanu a kanta suka yi, sister Maya ta ce. "Ina kika samu wannan suna mai shegen daɗin kuma, Haiza'an, sunan ya yi daɗi"...... Tana ɗan murmushi ta ce. "A laptop na my Dr na ha wani folder an rubuta Haiza'an shi ne kawai na ji sunan ya kwanta mun har cikin raina".
"To waye ya ce maki suna ne? Kika sani ko wani abin ne?". Sister Maya ta faɗa.. tana saɓa babyn a saman shoulder ɗinta ta ce. "Koma dai menene sunan ya shiga raina sosai, koma ba sunan mutum bane, ko sunan wani abin ne ni dai ya mun, in na kira sunan daɗi nike ji, dan haka sunan babyn nan Haiza'an".
Maya tana murmushi ta ce. "Kin san nima sunan ya kwanta mun a rai ya burgeni?"....... "Ai sunan yana da daɗi ne, daga yau sunan wannan baby Haiza'an, haka zaki dinga ce mashi"..... Suna murmushi gwanin sha'awa suka fara cire kayan jariran suna yi masu wanka.
Bayan sun kammala suka sanya masu kayan sanyi saboda weather ta ruwan sama, a nan suka zauna zaman hira, sister Zinta ta sanar da sister Maya cewa ai sun kai babys ɗin ɗakin kula da su ne dan sun kamu da cuta, Maya ma ta gamsu da bayanin, sai suka hau addu'ar yaran su samu sauƙi.
A can gefe kuwa 3D na zaune office ne Dr James suna tsara yadda zasu haɗa rigakafin cutar NEXAPOX-31 kafin su haɗa ainahin maganin cutar, Dr James ya fito masu da tsarin aikin da kuma jerin abubuwan da zasu buƙata domin haɗa wannan magani da kuma rigakafin.
Suna ta faman karanta abubuwan buƙatar. Yau basu yi wani aiki sosai ba, around 1 suka je suka zuba jikin darling Dr James ya sake ɗaukansa video ya turawa World System, hakika bakina ya yi kaɗan iya zayyana maku bala'in da darling yake a ciki, ya rabb, ALLAH ya saka maka, ya bi maka hakkinka bawan ALLAH.
Bayan sun duba shi suka wuce cikin ɗakin haɗa cutar NEXAPOX-31 ɗin, suka shirya kwalaben dake ɗauke da sinadarin cutar a cikin manya-manyan kwalaye, sannan suka shirya a wani ɗakin duhu dake kusa da wajen, daga nan suka fito suka nufi ɗakin kirkire-kirkiren halittunsu da ƙaƙale-ƙaƙalensu....... In Sha ALLAH a wannan kirkire-kirkiren zaku kirkirowa kanku bala'i shehu la'anannu kawai!.
Wasu mugayen kwari dake cikin wasu glass suka sanya guard biyar majiya karfi suka ɗauka suka fitar masu da shi, kai tsaye a bayan motar da ake shirya jariran da Dr Mark yake fitarwa suka sanya katuwar glass ɗin. Kamar kullum Dr Mark ya ja motar ya fita da shi ta cikin wannan hanya da ta ɓulla cikin dokar dajin.
Su kuma suka koma cikin asibiti, da alama an kammala wannan project na kwarin, za'a miƙawa masu shi. Ko wacce ƙasa za'a sakarwa waɗan nan kwari kuma? To koma wace ƙasa ce ALLAH ya kareku daga sharrin WS, dan waɗan nan kwari suka cijeka sai ka kwanta jinya na zazzaɓa mai mugun zafi ga ciwon kai, idan kana da rabo sai ka sha jinya ka warke, idan kuma ba saura kwana mutuwa zaka yi bayan shan azaba.
Wunin wannan rana dai haka suka kasance, around 5:30 Dr Kamal and Dr James suka zo suka ɗauki sister Maya and Zinta. Yaran nan sam basa son tafiya su bar babys ɗinsu, amma ba yadda suka iya, sun gama yi masu wankar yamma suna wasanni dasu kawai 3D suka zo suka ɗaukesu, Maya har da guntun hawayenta wai bata son barin boy, ta ce zata tafi da shi Dr Kamal yaki yarda, ya yaudareta da kalamai har ta aminta ta biyosa suka tafi.
Around 1 na dare Dr Kamal and Dr James suka sake fitowa suka baro ƴan matan nasu a cikin gida. Yau ranar haɗa drugs ne na jini da suka riƙa jariran jiya. Dan haka ba sai na sake yi maku bayani kan yadda suke haɗa magani da jinin ba, already kun sani, na ɓargo da ƙashi ne baku sani ba, idan na zo nan dallah-dallah zan maku. Amma yanzu dai sun haɗa maganin kamar yadda suka saba, suka shiryasu cikin sachet kamar ko yaushe.
Sannan suka sa aka fitar masu zuwa ɗakin shiryasu a cikin kwalaye, sannan suka fitar zuwa General Hospital ɗin. Around 4 suka kammala, suka koma gidansu, sun isko su Zinta na barci, dan yau shayar da su maganin barci suna yi a cikin lemu da suka je yin lunch ba tare da su Zinta sun sani ba.
Hankalin 3D ya fara tashi tin daren jiya da su Maya suka nemi titseyesu kan ina suka je, daga nan suka yanke shawarar rinƙa masu maganin barci cikin dare, dan basu son suga hankalin ƴan matan nasu a tashe, kuma ba zasu iya faɗa masu abin da suke yi ba.
Bayan sun dawo wanka suka yi, suka shirya cikin wasu sleeping dress ɗin, a gefen matan nasu dik suka kwakkwanta tare da jawosu jikinsu, ba jimawa barci ya yi awon gaba da su. While shi kuma Dr Mark yana can yana kwasan hanya zai fitar da kaya daga cikin ƙasan ta ɓarauniyar hanya.
D-------O-------L🔥
Ita kuwa Angelina tana zaune kusa da Zaynish tana aikin satar kallonsa, Unays kuma yana satar kallonta, yana ta ALLAH ALLAH Zaynish ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna.
Kiran Ummie ne ya shigo wayar Zaynish. Ciro wayar ya yi daga aljihunsa. Kashe kiran ya yi game da kiranta. Bugu ɗaya ta ɗauka, kara wayar a kunne ya yi game da cewa. "Assalamu alaikum". A yadda ya yi magana ko Angelina dake kusa da shi bata ji me ya ce ba.
Daga ɗayan ɓangaren Ummie dake zaune saman sabbin sofa set ɗinta da ta yi wa kanta ne ta amsa da. "Waalaikumussalam ɗan uwana"....... "Ina wuni Aunty Ummie?"........ "Lafiya lou Alhamdllh ya aiki da abokan aikin naka?"....... "Suna nan lafiya, ya gida da Yaya Faisal? Ya dawo ne?".
Kai ta ɗan girgiza kafin ta ce. "A'a bai dawo ba, ya dai turo mana saƙo jiya, ina su Noor? Kwana biyu ban jisu ba?"..... Kallon in da Noor yake ya ɗan yi kafin ya ce. "Suna nan lafiya, Aunty Ummie kina mana addu'a sosai ko? Kin san yanzu addu'a kawai muke da buƙata".
"Sosaima, kullum sai na yi maku, ALLAH ya kare mun kai, yaushe zaka dawo ka fara aiki a nan dan ka ɗauka mana fansa? Ka kore mana ƴan ta'addan nan?"......... Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Sai mun kammala wannan FIVE MISSION ɗin, a wannan lokacin ne muke da zaɓi, ko mu zauna a Avaris mu yi aiki ko kuma mu yi applying Nigeria or Niger dik wanda kika zaɓa mun, so in mun gama FIVE MISSION muna dan ƴancin zaɓar ƙasar da muke son yin aiki".
Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Zan yi tinanin in da zaka yi aiki, amma yanzu dai yaushe zaku gama?"...... "Very soon In Sha ALLAH, ke dai ki cigaba da yi mana addu'a".
"In Sha ALLAH addu'a kam ba fashi, yanzu dik ajiye wannan magana, batun aure na kiraka mu yi"...... Kada ku manta ita bata san sun tafi mission ba, ya ɓoye mata dan kada ya ɗaga mata hankali, yanzu ta ɗauka suna barrack ne shiyasa ta ɗauko mashi batun aure.
Ƙasa ya ƙara yi da murya wajen cewa. "Kai Aunty Ummie, na faɗa maki bani da zaɓi a kan mace, kawai ki bani dik wacce tai maki, ki zaɓota, na baki wuƙa da nama, ko wacece kika kawo zan aureta, na yi alkawari, amma ki kawo wacce zata girmamaki fiye da yadda zata girmamani, wacce zata soki kamar yadda nike sonki, wacce zata maki biyayya tamkar yacce zata mun, wacce zata kula dake tamkar yacce zata kula dani, idan ba mai wannan ɗabi'u ba bana so kada ki kawota!"...…. Murmushi ne ya kubce mata, cike da farincikin irin yadda ya bata muhimmanci a rayuwansa ta ce. "Ina wacce ka ce ka taɓa gani? Wacce ka fara jin sonta a ranka? Bana son ka rasa soyayyarka ta farko".
Nisawa ya ɗan yi game da cewa. "Ban san in da take ba, na faɗa maki tin daga ranar ban sake ganinta ba, dan haka ni nama mance da ita, kawai ki nemo mun taki"......... "To shikenan zan kuwa nemo maka haɗaɗɗiya, kana zuwa hutu sai aure kawai"........ Kai ya ɗan jinjina kafin ya ce. "A'a, mu ai muna da lokacin yin aure, sai mun samu umarni daga sama, idan kin samo matar ki sanar dani sai in shigar da buƙatar auren a tsare, idan manyanmu sun yarda shikenan in na dawo sai ayi komai".
Da to ta amsa kafin ta ce. "To ka kula da kanka, ka ci abinci ka yi ibada mai kyau, a dik in da kake ka sani ALLAH yana ganinka, kada ka cutar da kowa, ka zauna da kowa da zuciya ɗaya, hakance zai sanya ba zasu iya cutar da kai ba, a dik in da kake ka tausayawa mace, kaga mai raunice, ka tausayawa kanka, ka tina kai maraya ne, baka da kowa sai ni, ba zan iya jurar rashinka ba, ka tina hakan, ka rinƙa addu'a da alwala kafin kwanciya barci, ALLAH ya yi maka albarka".
Hakika kunnuwansa sun yi mugun sabo da jin kalaman Aunty Ummie na nasiha kullum, har ya haddace, dan haka da In Sha ALLAH ya amsa mata. Sai ta sake cewa. "Ina sonka sosai rabin raina".
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, bai san daɗin iyaye ba, amma a kanta yasan ainahin menene soyayya, ta sadaukar da komai saboda shi, lallai soyayyarta ce ake cewa true love........ "Nima ina sonki sosai Aunty Ummina, ba zan taɓa son wani abu rabin son da nike yi maki ba, ki kula da kanki, dik abin da yake damunki ki yi gaggawar sanar dani kin ji?".
Da okey ta amsa mashi, daga haka suka yi sallama, ya shiga gallery ɗinsa, hotunanta ya fitar ya fara kallon yana tina yarintarsa, lallai Aunty Ummie ita ce komai ɗinsa, tai mashi komai, a rana sai ta kirasa sau biyar ko mantawa bata yi, ga hidimar shago dana gida, amma baya sanya ta manta da shi, kome ta ɗauka zata kai baki sai ta tina shi, ta ce shin shi ya ci ko bai ci ba? Yana samun irin abin da take ci ko baya samu? Dik ta damu.
Ya jima yana kallon hotonta kafin ya ɗan nisa, unexpected wayan nasa ya kubce ya faɗi ƙasa a gabansa. Da sauri Angelina ta ɗauko mashi wayan, kurawa hoton da yake kallo ɗin ido ta yi. Bata san lokaci da ta ce. "Wow, she's so beautiful"........ Slowly ya ɗago kallonsa a kanta wanda tin da ta zauna a wajen ko sau ɗaya bai ganta ba, har cikin ransa ya ji daɗin yadda ta furta words kan hoton.
Murmushi ta ɗan yi game da miƙo mashi wayar tana faɗin. "Is she your sister?". Ta faɗa tana mai da kallonta a kansa......... Bai amsa mata ba, kuma bai karɓi wayar ba. Bata damu da bai amsa ba ta sake cewa. "You look alike, amma tafika kyau saboda ta fika hasken fata, and ta fika big-big eyes, wow ta yi kyau sosai, anya ba zan cewa daddyna ya auro mana ita ba? Ta yi kyau sosai, na ji ina sonta".
Har cikin ransa ya ji Angelina ta burgesa, dik wacce zata so Aunty Ummie, hakika zata sace zuciyansa. Ganin bai karɓi wayar bane yasa ta zaci ya ji haushin abin da ta yi ne, sai a lokacin ta tina ashe oganta ne, taɓa wayansa ba da izininsa bama ta yi laifi, da sauri ta ce. "Sorry sir, it can't happen again". Ta faɗa tana sake miƙo mashi wayar, cikin muryar girmamawa tai maganar.
Hannu yasa ya karɓa yana ɗauke kallonsa daga kanta. Ƙasa ta yi da kai, haka kawai sai ta ji murmushi ya kubce mata ganin yau ɗaya ya ɗaga ido ya kalleta, abin da bai taɓa yi a, ba zata mance wannan rana ba, kuma haka kawai har cikin ranta ta ji Aunty Ummie ta shiga ranta, ta yi matuƙar burgeta, har ta ji cewa lallai tana son yin magana da ita. Zanen heart ta yi a ƙasa tare da zana dogon kifiya a tsakiyar heart ɗin kafin ta yi rubutu da yaren daddynta a saman heart ɗin, a ƙasa kuma da turanci ta rubuta. "Zuciyata ta makance kan mutum ɗaya, ta rufe ruff kan mutum ɗaya, bana ji, kuma bana ganin kowa sai shi, shi kaɗai ne zaɓina, shikaɗai nike gani in ji daɗi, i love you forever and ever"...... Ta gama rubutun tare da miƙewa ta bar wajen, ta koma kusa da Manassa ta zauna zuciyarta cike tab da tsananin begensa,