Showing 30001 words to 33000 words out of 365093 words
ɗauketa sai saman shoulder ɗinsa, hannunsa ɗaya rike da drugs ɗinta.
Ita dai shiru kawai ta yi tana kallon ikon God. Kai tsaye elevator ya nufa, daga kan yadda yake tafiya zaku san lallai wannan shahararren gangster ne, tafiyarsa babu wasa ko sanyin jiki. Hawa na biyar ya haye. A wani katafaren parlo mai tsananin kyau ya dakata. Shiru ya ɗan tsaya kamar na 1 minute, sai kuma ya nufi wani door dake fuskantosa.
Yana zuwa ya ɗan taɓa handle na door ɗin sai ga shi ya buɗe kansa. Wani katafaren sleeping door ne, katon bed ne kawai a ciki, yana shinfiɗe da wani haɗaɗɗen bedsheet na alfarma white kala, da one side sofa. Sai kofar toilet and balcony wanda dik da glass aka yi su kun sani.
A saman bed ɗin ya direta tare da ɗaura drugs ɗinta a gefenta, daga haka ya juya bai sake kallon in da take ba. Parlo ya fito, kai tsaye ya nufi wani madaidaicin door dake fuskantar ɗakin da ya fito.
Wani haɗaɗɗen dry kitchen ne a wajen, da alama babu kowa a gidan sai shi kaɗai. Kyakkyawan pot ya ɗauko daga cikin pot set ɗinsa, ruwa ya zuba a ciki tare da buɗe drawers na sama ya ɗauko wani ɗan karamain bottle, wani green leaf ya ɗebo daga ciki, ya zuba cikin ruwan pot ɗin, sannan ya ɗauko wani bottle na honey. Kaɗan ya zuba zuman a ciki, ya kunna gas, a kai ya ɗaura tare da nufo waje.
Yana fitowa ita ma ta fito daga room ɗin da ɗan gudunta tana faɗin. "Mammy I don't want to stay here, please come and take me away from here". Tana kuka sosai da hawayenta. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa, sai ya nufi wani siririn hanya dake kusa da glass wall dining room dake cikin parlon.
Da kallo ta bisa, a ranta ta ce ko dai baya magana ne?. A fili kuwa hawaye na cigaba da tsere a kan fuskanta sosai. Tana ganinsa ya yi amfani da remote wajen sauƙo da staircase daga sama, sannan ya haura sama abinsa ya kyaleta tsaye kamar wata doluwa.
Zaman dirshan ta yi a ƙasa tare da sanya hannayenta dikka biyu ta fara watsa kyakkyawan ash hair ɗinta tana cigaba da kuka. Lokaci guda kuma ta ɗan kwaɓe fuska tana ɗage hanci sama wai jikinta na tsamin datti, dan yau kwanakinta uku a asibiti bata yi wanka ba, kuma babu wanda ya yi mata, tin da suka kawota ma shi sai jita ya je, tana sume aka kaita, daren jiya ta farfaɗo tana kuka kenan aka yi mata alluran barci, bata tashi ba sai ɗazun. Farfaɗowarta jiya yasa aka kirasa a waya ya zo, tin kuma da ya fita wajenta jiyan sai yanzu ya koma ya ɗaukota da likitocin suka sanar da shi ta samu lafiya zai iya tafiya da ita.
Abin da ya sumar da ita kuma shi ne hayakin wutar da su Eagle suka kunna a gidansu. Wannan yarinya ba kowa bace face ƴar Dr Hushaima ALLAH jiƙan rai, da alama kuma wannan mutumi shi ne bahagon murɗaɗɗen mutumin da Dr ta taimaka dik da ban sani ba, hasashe nake yi, naga halinsu na rashin magana iri ɗaya ne da wancan, to wai ma su waye su ne?.
To yanzu dai mu ɗan koma baya kaɗan dan mu ji ya aka yi yarinyar Dr ta tsira?.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-5-by-princess-teema
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
4-11-2025.🔥
FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥
E_____________5
Abin da ya sumar da ita kuma shi ne hayakin wutar da su Eagle suka kunna a gidansu. Mu ɗan koma baya kaɗan dan mu ji ya aka yi ta tsira?.
A lokacin da Dr ta fita ɗakin da gudu ta nufi room na ƴarta a lokacin shi ma ya miƙe daga gadon, in baku manta ba ai bata yi mashi alluran barci ba, so idanunsa biyu, yana jin dik abin dake faruwa. Fitowa daga room ɗin ya yi ta hanyar dafa bango, dan jikinsa dik babu karfi ko kaɗan, da kyar ma yake iya motsawa, amma saboda yasan musifar da yake a ciki sai ya yi tinanin dik yadda aka yi shi ake nema yasa aka shigo gidan again.
Cigaba da tafiya ya yi har zuwa wajen staircase, zai taka stair ɗin kenan su Eagle suka banko parlo door. Ganinsu yasa ya fasa sauƙa, dan jikinsa babu wani karfin da zai iya kwatar kansa, sai ya matsa baya, a maimakon ya koma room ɗin can sai ya kara gaba, a nan ya ci karo da room na ƴarta, buɗe door ɗin ya yi ya shiga ciki.
Yana sanya kai daidai lokacin yarinyar ta farka, ta zauna a saman bed tana faɗin. "Mammy I want to dring water". Laluɓar hanya a cikin duhu ya yi izuwa wajen switch, sai da ya kusa kewaye room ɗin kafin ya gano switch ɗin. Kunna light ɗin ya yi, take haske ya gauraye room ɗin.
Da sauri Seraph ta ɗago kanta ganin haske tana faɗin. "Mammy a little water......". Bata iya karisa maganar ba ganin mutum a tsaye ga bandeji a hannu, bugu da kari bata iya ganin face ɗinsa. Wani irin razana ta yi tare da zazzaro voilet eyes ɗinta a kansa.
Wani irin kallo ya bita da shi, wanda ita bata san yana kallon nata ba saboda nose mask ɗinsa, ga p-cap daga cikin hular jacket ɗinsa.
Cigaba da zazzare ido a kansa ta yi, tana kallonsa from up to down. A daidai lokacin ya ji motsin mutanen, a tinaninsa suna shigowa room ɗin ne, sai dai kuma a lokacin suka wuce da Dr zuwa ICU ɗinta. Jin motsinsu yasa ya daure tare da takowa izuwa wajen bed ɗin nata. Hannunsa ɗaya mara ciwon nan ya sanya tare da ɗaukar yarinyar, tana ƙoƙarin kurma ihu ya yi amfani da hannunsa mai ciwon ya rufe mata bakda tafukansa.
Wajen view ɗinta ya dawo, da kyar ya iya buɗewa, tana ƙoƙarin kwace kanta ya dake suka fita ta view ɗin, a saman wani ɗan dakali a wajen ya zauna da ita a jikinsa. Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi da iya karfinta, ganin zata iya ja su faɗi kasa tin da wajen ba wani mai faɗi bane, irin dakalin nan ne da ake yi na saman window ɗin toilet ko na ɗaki hakan nan ne, to a wajen window toilet suka zauna, ganin zata ja su faɗi ne yasa ya sanya hannunsa ya zame hular jacket ɗin kansa, ya ɗan kawar da p-cap na kansa gefe dan ta samu damar ganin idonsa, sai ya zame hannunsa daga bakinta ya ɗago haɓart suna fuskantar juna.
Wani irin zaro ido waje tai tamkar kwayarta zasu faɗo ƙasa a lokacin da ta ga jajayen idanunsa tamkar wuta, dik da bata kalli face ɗinsa gabaɗaya ba ta wani irin mahaukacin razana, take ta kame waje guda kamar ta sume, dan numfashinta ya ɗauke, idanunsa sun yi wani irin ja tamkar jini ne a ciki, dik wanda ALLAH ya bashi ikon haɗa ido da wannan guy a wannan lokaci ko bai suma ba kaɗan ne zata rage mashi saboda firgici.
Ganin ta ɗauke wuta ne yasa ya mayar da hulansa, slowly ya kwantar da kanta a gefen chest ɗinsa, ya ɗan rintse idanunsa saboda tsananin zafin da hannunsa yake yi mashi, alluran kashe zafin ta fara sauƙa, kun san dole akwai zafi. Yana jin motsin yaran Eagle suka shigo room na yarinyar.
In takaice maku labari har suka kashe Dr yana wajen da yarinyar, ba zai iya zuwa ya ceci Dr ba, saboda shi kansa taimako yake nema a yanzu. Jin shiru alamar sun bar ɗakin yarinyar yasa ya kokarta ya miƙe da ita, daga alama shahararren ɗan ta'adda ne, yadda yake da dauriya da karfi kamar wani doki, dik yadda aka yi ya sha gwagwarmaya ba kaɗan ba.
Da kyar ya lallaɓa ya kama room view suka komo cikin ɗakin, ya so dira ƙasa ya bar gidan, amma ha zai iya dira da ita ba, kunga ga ciwo a hannu, ga kuma nauyinta, jikinsa ba karfi, idan suka dira a tare zata iya jin ciwo koma ta bugu a in da ba zata rayu ba, shi ma kuma haka. So dole ya mayar da ita cikin ɗakin, bata ko motsi.
Cikin toile ya kaita, a cikin jaccuzi ya kwantar da ita tare da fitowa, dispenser dake room ɗin nata ya ja zuwa toilet ɗin, da kyar ya ɗaukesa ya ɗaura a saman Jacuzzin, ya rufeta, sannan ya fito, ya koma ta view, ya dinga lallaɓawa a hankali ya sauƙo, a lokacin sun kunnawa gidan wuta sun fita. Shi ma fita ya yi.
Yasan da wuya wutar ta kamata, dan a cikin Jaccuzi ya kwantar da ita, ga disperser ɗin da ya ɗaura mata, shiyasa washegari ya tura yaransa su ɗaukota da dik sauran abin da ya rayu a gidan dan ya rama alkhairin mahaifiyarta a garesa, ta sadaukar da ranta a cetansa, yana kwance a gadon asibiti ya turosu.
Shi ne suka zo suka ɗauketa, sun sameta sume a cikin Jacuzzin, amma hayakin wutar tai mata illah, ga kuma wutar ta kakkama dik wasu robobi a cikin toilet ɗin ta cinye, ko jami'an da suka zo basu san tana ciki ba saboda wannan rufeta da ya yi...... To kun ji abin da ya faru! Yanzu mu koma kan labarinmu!.
Ta jima zaune a wajen tana shan kukanta, tana ganinsa ya sauko ƙasa, ya wuce kitchen ya sauke ruwan da ya ɗaura a pot, ya sanya rariyar tea ya tace ruwan a cup, sannan ya ɗauka ya koma sama ba tare da ya kalli in da take ba. Ganin ba zai kulata bane yasa ta miƙe ta koma cikin room ɗinta cike da kunci, tana son sanin ina mammy ɗinta, meyasa aka kawota wannan irin dream house da take mafarki kullum! Suna da arziki sosai, amma CRYSTAL PALACE ba dik kai ba, sai ta zama ƴar kauye a nan.
Saman bed ɗinta ta koma ta kwanta tana cigaba da kukanta babu mai rarrashinta, ga shi bauɗaɗɗen nata ya yi sama abinsa, yana zaune a balcony yana shan tea ɗin da ya dafa cikin kwanciyar hankali da natsuwa abinsa. Bayan ya kammala ya umarci robot dake aiki a gidan da su haɗawa yarinyar abinci, su tabbatar ta ci, sannan su bata magani kamar yadda yake a tsare, kuma su yi mata wanka, yana gama basu bayani ya ɗauki wani tail coat ya sanya a jikinsa bayan ya yi wanka ya cire waɗan can, ya fita ya bar gidan, ita kaɗai a dik wannan girman gidan kamar wata mayya, ba uwa, ba uba, ba kawa, ba aboki, babu kowa sai robot, wannan ma kawai ai tashin hankali, ga shi baƙon waje.
Haka robot ɗin nan suka hau aikinsu, tamkar mutane, suka shirya komai suka kai mata, maza ne su biyu. Tana kuka suka iskota. A saman table suka ajiye kayan abinci, ɗaya ya taka zuwa in da take, da hannu ɗaya ya ɗagota, bai direta a ko'ina ba sai a saman sofar dake kusa table ɗin.
Tana ta faman faɗin. "I don't want, please let me go"..... Ina babu wanda ya kulata, dan su ance su tabbatar sun bata abinci, dan haka a baki suka fara tura mata dole, abin da umarni suke karɓa, in kuma suka karɓa sai sun cika ko mutuwa ake yi.
Da taga babu sarki sai ALLAH sai ta hakura ta dinga karɓar abinci a natse kawai, ba sai an mata ɗure ba. Sosai ta ci kafin ta ce ta ƙoshi. Sai da suka tabbatar, sannan suka ɗauko magungunar, shi ma a baki suka bata ta sha, sannan ɗaya ya ɗauketa zuwa toilet, dan har da wanka aka ce su yi mata, tana cewa bata so, amma ina, ko a jikinsu, suka haɗa ruwan wanka. Dik tinaninta mutane ne shiyasa take ce masu bata so.
Tana ji tana gani yai mata zindir, ya jefata cikin ruwan katafaren glass Jacuzzi tamkar wata kayan wanki. Hannu yasa ya wanketa tas. Ai yau taga ikon ALLAH, kuka ta dinga yi tana kiran sunan Mammy ɗinta, amma ina bata jinta.
Dawo da ita ɗakin suka yi bayan sun nannaɗeta cikin towel, a kan gado suka jefata kafin su kwashi kayan abinci su fice, sun gama aikinsu kenan. Fashewa da sabon kuka ta yi, ta kifa kanta da gwiwowinta tare da jawo bargo ta rufe tsiraicinta. Kyakkyawan ash hair ɗinta sai ɗigar ruwa yake yi.
Tin sautin kukanta na fita, har ya daina fita, daga karshe barci mai nauyi ne ya ɗauketa a wajen, bata san lokacin da ta kwanta kudundune a cikin bargon ba, ta hau barci, ta ci kuka ta ƙoshi ja'ira. To kun ji halin da Seraph ƴar Dr take a ciki, mu haɗa kayanmu mu koma Barrack.
Note, Seraph shekarunta 10 a duniya yanzu, yarinya ce sosai.
-------------------------🔥
GIDA SOJA!. AFTER ONE MONTH.
A wannan wara ɗayan dik horon da aka yi masu a farko-farko ne ake ta maimaita masu dan ya bi jikinsu da kyau, ba'a ɗaura sabon horo ba, tin suna iya mantawa har wannan horo na farko ya ratsa jikinsu sosai. Shiyasa na tsallake tin da ba zan yi ta rubuta maimaicin horo ba!.
A yau Monday watansu guda kenan a GIDAN SOJA, a yau zasu fara shiga horo sabo kashi na biyu.
Kamar kullum karfe 5:30 na asuba, bayan sun yi sallar asuba, dik sun hallara a wannan fili, a yau dai Noor ya fito, dan za su shiga sabon horo, a wata guda da suka wucen nan dik kullum sai Captain ya tashesa da duka, amma yau da yake za'a shiga sabon babi ya daure ya taso.
Sun kasance a cikin layi kamar kullum. Cikin zafin nama Captain ya tako, ya iskosu a wajen. Saman stage ya haye tare da ɗan yin gyaran murya. Da sauri suka haɗe natsuwatsu tare da buga kafa, suka sara mashi. Jinnina kai ya yi kafin ya ce. "1, 2, 3 start!" Cikin ɗaga murya.
Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA...... "We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, united as one, well never fall. Oh we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, a thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, our oath is strong, we'll see it through. Oh we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!".
Suna kai karshe ya ce. "Kamar yadda kuka sani ne, a yau zamu sabonta maku horo, zamu matsar dashi izuwa matakin gaba, ina fatan kun shirya?". Ya kai karshe da alamar tambaya. Wani irin kamewa suka yi alamar sun shirya ba tare da magana ba.
Rarraba idanunsa a kansu ya ɗan yi kafin ya ce. "A yau zaku fara ne da endurance run for 10km". Babbar magana, gudu fa ba tafiya ba, na 10Km da matsala. Dayawa daga cikinsu sun ɗan ɗauke wuta, amma ganin babu fuskan wasa yasa suka daure.
Maryan Captain ne ya katsesu da cewa. "Lokacinku ya fara daga yanzu, kada ku manta lokacinku yana kirgawa ne! So attention".
Wani irin tsaki Noor ya ja tare da rike kai, har ga ALLAH ya gaji, ba zai iya jura ba fa. Ganin matasan sun fara gudu sun bar shi a wajen ne yasa yai gaggawar bin bayansu da ɗan gudunsa, kada a barsa a baya.
Gudu na tsawon kilomita goma ba tare da tsayawa ba. Dik wanda ya yi baya, sai ya sake farawa daga farko. Babbar magana, kuma kun san dik wanda ya yi baya sai ya faro ɗin nan ne, babu tausayi.
Haba haka suka zage dantse suka fara gudu babu wasa. Sai dai bayan kamar minti 30, gwiwowinsu sun fara raunata, amma ba wanda ke da damar tsayawa, dan ma wai a wata ɗayan can sun ta maimaita horo sun ɗan samu karfi da kwari ne, da sai yaya kenan?.
Noor da ya tabbatar da gaske idan ya yi baya zai sake komawa daga farko, kuma ko mutuwa yake yi ba zasu yafe mashi ba, kilomita goma ba biyu kamar ta baya ba, yaushe zai koma baya ya sake dawowa, ai sai ya zage, yasa dikkan karfinsa wajen gudu. Da yaga kamar ba zai iya bama sai ya kwarara zuciyansa tare da yin shahada ya kama hannun Leo.
Ko kaɗan Leo bai kalli in da yake ba, amma da ya fahimci Noor baya son faɗuwa ne yasa ya kama hannunsa sai ya juyar da hannun nasa ya rike Noor ɗin da karfi suka fara gudu sosai a tare, hakan ya yi mugun karawa Noor kwarin gwiwa ba kaɗan ba.
Lamarin da ya yi mugun baiwa su Zaysh mamaki kenan, how comes Leo zai kama Noor? Kai kamar a mafarki?. Shi kuwa Leo ganin Noor ya dage sosai ne yasa ya kara kankame hannun nasa.
Abin da ba'a taɓa ba wai Noor ya zo na farko, sai yau shi da Leo su ne farkon isa wajen, tsalle ya dinga yi yana murna tamkar wani karamin yaro, kamar ma bai gaji ba fa, dik kuma daɗin Leo ya taimaka mashi ne yasa