Showing 360001 words to 363000 words out of 365093 words
1 nasu da Aunty Ummie, ko uncle ɗinsa bai yarda da shi ba, yana dai bashi girma, kuma dik duniya team 1 da Aunty Ummie kawai suke sanin me yake ciki, Aunty Ummie ma wani abin yana ɓoye mata, kamar yanzu da ya ɓoye mata suna daji, and ko su Leo wani abin yana ɓoye masu kamar yadda Leo ɗin ma yake ɓoye masu wani abin, kunga Leo ya ɓoye masu batun aikinsa na shi da Arya, baka isa iya gane ainahin zuƙatan mutane biyun nan ba, dik abin da ka ga ka sani a kansu to su suka yi ra'ayi suka faɗa maka, suna da banbanci wasu halaye, Leo yana da saurin fusata, Zaynish yana da hakurin sai ka turasa bango, Leo idan ya fusata ya yi faɗa komai ya wuce, Zaynish ba'a saran mumini sau biyu a rami ɗaya haka yake, in ka mashi sau ɗaya, ya hakura har ka turasa bango to fa ko waye kai zai zubaka a kwanton shara ne, dik basu da yawan magana, amma in suka fara magana Leo yana faɗar magana kai tsaye daga zuciyansa, ba ruwansa tai maka daɗi ko kar ta yi maka shi dai ya faɗa, ma'ana baya tauna magana, yana da ɗabiar IRON FIST na baka da wuta kuma baka da aljanna bare su ji shakkar mutum.
Zaynish ba shakkar kowa yake ji ba, kawai dai ɗabia ce ta namu na ƴan Afrika, sai mun tauna magana muke yinta, dan haka baya magana kai tsaye, sai ya tauna, idan yaga faɗarta ya fi alkhairi zai faɗa, idan kuma ya ga faɗarta ba alkhairi bane yana fasawa. Dik suna da dogon nazari a kan abu, kuma in suka yi nazari suka yanke hukunci sai an sara masu, suna da mugun natsuwa, Zaynish yana da girmama nagaba da shi sosai, yana da ladabi, Leo baya ji guy ɗin nan, ya raina kowa, gani yake kowa a kasan shi yake, zaka iya nunawa Zaynish iko ya ɗauke kai ya rabu da kai, ka kuskura ka nunawa Leo iko in ta zo da tsautsayi sai dai wani ba kai ba, dikkansu idan suna son abu soyayyar gaskiya suka iya, basu iya rayuwar munafurci ba.
Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar, ya katse kiran nata tare da shiga account ɗinsa, ya sayi kati na kamar 10k a kuɗin Naija, sannan ya bi kiran nata. Cikin sanyin murya ya ce. "Assalamu alaiki"...... Daga ɗayan ɓangaren ta amsa da. "Wa'alaikumussalam"........ Wani irin natsuwa ya kara yi, cikin nuna kulawa ya ce. "Aunty Ummie lafiya na ji muryarki haka? Baki da lafiya ne?".
"Eh to ina zazzaɓi ne, na zo asibiti a dubani, ba wani ciwo bane"..... Kai ya ɗan jinjina, sai kuma ya ce. "Ina yaya Faisal?"......... "Ya dawo jiya yana gida". Shiru ya ɗan yi, ya ɗan yi mamakin jin amsarta, sai kuma ya ce. "Yah Faisal yana gari kuma bai kaiki hospital ba, meyasa?"....... "Babu komai, jiya fa ya dawo da daddare, ya gaji yana barcin huce gajiya".
Tin daga kan yanayin maganarta ya gane karya kawai ta yi mashi, saboda bata saba karya ba, in ta yi sai ya gane. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "Bari in kirasa mu gaisa". Ya faɗi hakan ne dan ya fahimci gaskiyarta, baya son ya ce tai mashi karya saboda na ce maku yana da girmama manya, amma yana da hanyoyi da dama da yake bi dan gyarawa manya kuskure idan suka yi cikin sauƙi.
Da sauri ta ce. "A'a kada ka kirasa yanzu, please ka bari sai anjuma in na koma zan haɗaku, yanzu yana barci ne"..... Ya gama gano akwai matsala, yadda muryarta ke rawa take ƙoƙarin hanasa kiran....... Kai ya jinjina kafin ya ce. "To yanzu dai an gama dubaki ne?".
"Am..... In.... To .... Dama likita ne ya ce yana son yin magana da mijina, kuma yayanka yana barci shi ne na kira ka yi magana da shi matsayin yayanka". Ta faɗa murya na rawa.......... Ɗago idanunsa a kan Angelina dake kallonsa ya yi, mamakin Aunty Ummie yasa ya ji kamar ana kiran sunansa a waje, a ransa ya ce faɗa suka yi da Faisal ɗin ne? Menene yakefaruwa da har take son ya yi magana matsayin mijinta? Me yake damunta? Lallai akwai gagarumin matsala.
Jin ya yi shiru ne yasa ta ce. "Ba wani abin bane fa, nasan halinka yanzu zaka ɗauka ko wani abin ne"...... Uhm ita da bata yi karatu bane wai take shirin yi mashi wayau, dik da dai ance babba kam babba ne, amma ai ta kwafsa tin a farko, babu rami me ya kawo batun rami da zata ce babu wani abu dan tasan zai ɗauka akwai wani abin, akwai ɗin kenan.
Nisawa ya ɗan yi, ya mai da kallonsa kan laptop na Angelina dan ya ga giftawar wani abin ta gaban drone ɗinsu, hannu ya kai saman mouse ɗinta kafin ya ce da Aunty Ummie. "Babu komai, haɗani da likitan, sannan kafin nan faɗa mun meyakefaruwa da Yah Faisal? Please kada ki ɓoye mun".
Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Gaskiya zan faɗa maka shi ne matsala muka samu da shi, ya dawo gida tin last week ba jiya ba, ya dawo da makudan dukiya, da na tambayi in da ya samesu sai ya ce a haƙar gold yai nasarar samun wani dutse mai daraja ya kai kasuwa, ban yarda da shi ba, na damu sosai, da na tsananta damunsa da tambayar ya faɗa mun gaskiya ina mashi nasiha shi ne ya fara faɗa, ya ce mu koma sabon gidan da ya saya a GRA, na ce ni ba zan koma gidan da ban san da kuɗin me aka saye shi ba, shi ne ya yi ta faɗa wai ina zarginsa, ya ɗauki amaryarsa suka koma can, ni suka barni a tsohon gida wai idan na ga dama in dawo sabon gida in samesu, shi ne takaicin yasa kirjina ya fara ciwo har dai na ɗan kwanta gajerar jinya, yau naga abin yai yawa na zo asibiti".
Tin da ta fara magana ya shiga dogon nazari, gabaɗaya ya ji abin yai mashi some how haka. Sai da ta gama jawabi tas, sannan ya ce. "Haɗani da likitan, sannan kada ki koma sabon gidan, ki jira kira daga gareni tukun nan". A takaice ya faɗa....... Kai ta jinjina alamar to, still ya fahimci akwai abin da take ɓoyewa ba iya maganar kenan ba, amma ya gano bakin zare a iya ɗan wannan bayani da ta mashi, dan haka a haɗa shi da likitan bayan sun gaisa ya ce mashi. "Dr ina son sanin me yake damunta".
Likita ya hau mashi bayani sosai. "Ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin damuwar da take ɓoyewa a ranta, sannan hawan jini yana gab da kamata, shekarunta sun yi kankanta da damuwar da take tarawa kanta, dole kullum kirjinta ya dinga ciwo sosai"....... Ni kam na ce ba dole ta damu ba, ga rashin haihuwa, ga kishiya, ga bala'in dangin miji, ga ba uwa, ba uba, uncle ɗinta ɗaya tilo gidansa babu daɗin kai ziyara saboda bala'in matarsa, babu ta in da Aunty Ummie ke juyawa ta samu saukin rayuwa face wajen Zaynish kawai, shi kaɗai take kira ta ji daɗi, kishiya ta balbaleta da masifa, ta daketa ta zubar mata da ciki, mijin dake bin bayanta yanzu ya samu abin duniya true color ɗinsa yana shirin bayyana, ya ALLAH, ina ake son wanna baiwa ta tsoma kanta ta ji daɗi ne? Ta ji da zafin rashin haihuwa ne ko damenene?.
Bayan likita ya gama mashi bayani Zaynish ya ce. "Na yi tafiya ina nesa, yanzu kai mata dik abin da ya dace, sannan ina son kai mata scanning, ka dubata sosai, idan ka yi scanning ɗin ka duba yanayin karfin ciwon zuciyar tata ya yake, ina jiran ji daga gareka, dik wani kuɗi da za'a kashe ka haɗa mun bill ɗin ka bata ta turo mun". Yana gama magana ya katse kiran, ya kira mai yi mashi canjin kuɗi ya sanar da shi akwai account da zai turo mashi ya saka mashi kuɗi. Mutumin ya ce ba matsala.
Angelina dik da bata jin yaren Hausa ta fahimci lallai Zaynish yana cikin tashin hankali da damuwa. Yana ƙoƙarin bin abin da ya gifta ta gaban drone nasu kenan kiran Aunty Ummie ya sake shigowa. Katsewa ya yi ya kirata yana aikin nasa bai dakata ba.
Tana ɗauka ta ce. "To na sallameka ne da zaka katse?"....... "Sorry, na bada damar a duba mun ke sosai ne"....... Kai ta jinjina kafin ta ce. "Dik wani ɓoye-ɓoyenka dai na ganoka, yanzu dai ina kanwar tawa take?"......... Cike da mamaki ya ce. "Aunty ban gane ba".
"Ina Angelina?". Ta faɗa kai tsaye. Ɗago da dara-daran eyes ɗinsa a kanta ya yi, mamaki yasa ya ɗan kyafta idanunsa sau biyu a kanta, while ita ma shi take kallo, tin da yake bai taɓa karewa fuskanta kallo ba sai yau, ba shakka ya shaida kyakkyawar gaske ce. Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi kafin ya ce. "Aunty a ina kika santa kuma?".
"Awwwww baka ɓoye mun ba? ALLAH ya dubi rokona ne ya bayyana mun ita, maza bata waya in ji ko kuna tare"..... Slowly ya saukar da waya daga kunnensa ya miƙawa Angelina bayan ya sanya a H-Free, yana ta kallonta mamaki ya hana shi kwakkwarar motsi. Karɓar wayar Angelie ta yi tana wani sunkuyar da kai.
"Hello my Aunty". Angelina ta faɗa. Can ya ji Aunty Ummie na dariya kaɗan-kaɗan kafin ta ce. "Fatan kina kula mun da kanina sosai ko?".
Ɗagowa Angelie ta yi, ta ɗan saci kallonsa, taga dai ita yake kallo, yasa hannu ya riko haɓarsa yana mamaki, kasa ta yi da kai kafin ta ce. "Sosai Aunty, ina bashi kulawa na musamman".
Zazzaro ido Zaynish yai a kanta, a cikin ransa ya yi salati ya kai sau 10, wai tana kula da shi, ko yaushe hakan dik yake faruwa bashi da labari?........
"To Please ki kara kula mun da shi sosai, ya fi zinari daraja, sannan in yai maki abu kada ki yi fushi dashi kin ji? Ki faɗa mun in ɗau maki fansa"..... Aunty Ummie bata son su rasa Angelina dan ma kada su rasa samun haihuwar ƴan 4, shiyasa kullum take faɗa mata idan Zaynish yai mata abu kada ta yi fushi da shi ko ta daina kulasa, ta faɗa mata zata ɗauki mataki.
Ai Zaynish kam yanzu kansa ta gama ɗaurewa.......... "Ba zan yi fushi da shi ba Aunty, zan kula sosai"...... Fara'a Aunty Ummie ya ninku, bata da lafiya amma tana dariya saboda son da take yi wa Angelie, ta dinga zuba mata ruwan albarka kafin su yi sallama, bata sake cewa a baiwa Zaynish waya ba ta katse kiran. A ransa ya ce awww saboda wannan ta sake kiransa kenan, lallai ma Aunty Ummie, watau yanzu kishiya zata yi mashi a cikin zuciyarta, mata kenan.
Miƙo mashi wayan Angelina ta yi tana ɗan ɗagowa ta saci kallonsa. Bai karɓa ba sai ya ce. "A ina kika san Aunty Ummie?". Ya yi maganar babu wasa a tattare da shi...... Can ƙasa ta ce. "Maso tsuntsu shi ke binsa da jifa ai".
Ya jita sarai, amma yai kamar bai ji ba, ya sake tambayarta ina ta san Aunty Ummie. Ɗan turo baki ta yi wanda ya ƙara mata kyau, tana ƴan kame-kame, sai ta ce. "I took her number from your phone, dana ga hotonta ne naga ta mun kyau shi ne na ji ina sonta sosai, shi ne fa na kirata muka gaisa, daga nan ta zama Auntyta nima".
Sosai ya ji daɗin kalamanta, musamman yadda ta ce daga nan ta zama Auntynta, amma bai nuna alamar ya ji daɗin ba, sai ya ɗaure fuska game da cewa. "Waye ya baki izinin taɓa mun waya?".
"Sorry sir"....... Cikin faɗa ya ce. "Waye ya baki izinin taɓa mun waya i said?!"............. Muryarta na rawa ta ce. "All because of you ne"...... "Because of me?". Ya faɗa yana pointing kansa da yatsa. Ya tamke fuska tamau, babu wasa a tattare da shi........ Kai ta jinjina. "Yes, because of you sir".
"How because of me?"......... Ta ɗago ta kallesa, ido cikin ido, babu tsoro kafin ta ce. "Because I love you, and I love those who are close to you, shi ne yasa na kirata, i like her from the button of my heart"......... Ya rabb, kashe mashi baki ta yi, bai taɓa jin kalmar love daga bakin wata daban ba Aunty Ummie ba sai yau, sai ya ji wani iri.
Hannu ya miƙa ya karɓi wayansa, ya ɗauke kallonsa daga kanta, ya rasa amsar da zai bata sai ya jawo laptop ɗinta dan su cigaba da aiki. After like 5mins yana nazarinta a cikin ransa sai ya ce. "Shekarunki nawa da har kika san wani abu wai love?". Ya yi maganar ba tare da ya kalli in da take ba.
"16 years now, and nasan komai ne because of you, i love you and i love everything about you"....... Bai ɗago ya kalleta ba ya ce. "Don't say this word out again, bana soyayya kuma ba zan yi ba, kada ki sake cewa kina sona!". Ya kai karshe tare da miƙewa ya fito dan shirin yin sallar la'asar. Ita kam ko a jikinta, gargaɗinsa bai shiga kunnenta ba, ta ɗago ta bisa da kallo har ya kurewa ganinta, murmushi ta ɗan yi kafin ta ce. "Sir baka san wacece Angelina ba, wait and see, zaka fara soyayya ne ma babu wanda ya sani, dani kake magana".
Ta cigaba da aikinta, ta dinga kewaye da drone ɗinsu a wajen tana tina kalar abin da zata dinga mashi.
After some minutes, around 4:30 ya dawo cikin ɗakin. Normal kayansa jeans and t-shirt ya ɗauka ya fito waje, da kallo ta bisa tana tina in sun fara soyayya ita zata dinga saka mashi kaya, dan tasan wanka zai je ya yi ya shirya, ta ɗan yi tagumi tana tinanin irin kulawar da zata bashi.
A haka ya dawo ya sameta, ya ce. "Bani drone ɗinki". Ya faɗa ba tare da ya kalli in da take ba. Da sauri ta fito mashi da su guda 10, dama 12 aka basu, ta tura biyu cikin daji.
Drone ɗin ya karɓa, ya duba karami a ciki, ya ce ta mashi connecting da laptop ɗinta, ba musu ta yi, tana gamawa ya miƙa mata hannu kan ta bashi drone ɗin, da sauri ta ɗaura hannunta kan nasa tana kallonsa, ta zaci ya miƙo hannu zai kama nata hannun ya miƙar da ita ne, dan tasan in sun haɗa drone ai sakinsa suke yi ya tashi, shi kuma me zai yi da shi da zai karɓa? Shiyasa ta zaci hannunta zata bashi.
Ɗago da kallonsa a kanta ya yi. Da sauri ta ɗauke hannunta, tamke fuska tamau ya yi kafin ya ce. "Bani drone ɗin". A hanzarce ta miƙa mashi tana haɗe natsuwanta waje guda....... "Akwai in da zamu je, so expect my call at anytime". Ya kai karshe tare da ɗan satar kallonta, dan yaga tana ƙoƙarin miƙewa.
Miƙewa ta yi, ta haɗe natsuwanta kafin ta ce. "Safe journey, and take good care of yourself". Ta haɗe hannayenta tana ɗan jujjuyawa cikin salon soyayya ta faɗa. Bai kalli in da take ba ya juya da sauri ya nufi fita. Gab zai fita muryarta ta katse shi da cewa. "Sir"........... Cak ya tsaya, ya ɗan juyo da kansa ban da jikinsa, fuskanta ya kalla yana jiran jin me kuma.
"Don't forget that I love you, kada ka mana wasa da kanka, ka sani ni da Aunty Ummie kana ranmu, ba zamu iya juran wani abin ya sameka ba, ka kula sosai please, good luck in whatever you go to do, I like you and I love you, I can't change that, because it's not something I chose for myself, I will wait until the day you begin to feel for me the same way I feel for you in my heart". Cikin raunin murya ta kai karshe, da ɗan shagwaɓa mai karawa kalaman soyayya armashi ba romantic shagwaɓa ba.
Bai yi magana ba, ya juya kawai ya fice da sauri. Da sauri ta biyo bayansa, ta zubawa tafiyar jarumtarsa idanu har sai da ya kurewa ganinta, ta ɗan jingina da jikin tantin tana tina ina ma ace ya yi accepting soyayyarta, ai da ta bashi kyakkyawar kulawa kafin ya tafi wanda har ya je ya dawo ita zai dinga tunawa.
To mu sake ɗan komawa baya kaɗan a side nasu Manassa. Da yake yau suka fara aiki a tare, sun wuni suna ɗaki, suna aiki yana tsokanarta, ya ce mata. "Ba wai bana sonki bane, amma akwai dalilin da yasa dole zai daina sonki". Ta tambayesa meyasa baya kulata sosai ne, kuma ya ce yana sonta.
Tana aiki tana ɗan turo baki ta ce. "Wani dalili". Sai da ya ɗan faki idanunta ya saki one side smile kafin ya ce. "Saboda a gida an ban mata, ance dole ita zan aura, bani da zaɓi".
Jama'a ba sai ga Manasa da ruwan hawaye ba? Da sauri ta ɗago ta kallesa, idanunta suka cicciko tab da kwallah, kirjinta na bugawa da karfi, ta gagara iya yin magana. Ganin haka yasa ya ja hankalinta a kan aiki, ya nemi mantar da ita maganar, amma a cikin ransa ya yi alkawarin hukuntata ta wannan hanya, ba yanzu zai bayyana mata cewa ita yake so ba, sai ya yi wasa da hankalinta da sunan yana da mata a gida kamar yadda ta yi wasa da hankalinsa a kan iya aljana ce.
Ai wunin wannan rana dai wanna aiki ta yisa ne kawai, amma bata san me take yi ba, har lokacin da ya zo tafiya, ya shirya ya zo sallamarta bayan sun yi connecting na drone ɗin. A dake ya ce. "Zan je wani waje, wait for my call".
Kai kawai ta jinjina taki yin magana, taki ɗagowa ta kallesa. One side smile ya ɗan saki tare da riko hannayenta. "Baki mun fatan in dawo lafiya ba, ko dai kin fasa sona ne?". Cike da sonta ya faɗa...... Tana gab da fashewa da kuka, tana wani irin huci na zuciya a kusa ta ce.