Showing 342001 words to 345000 words out of 365093 words

Chapter 115 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

6229

nan Seraphina ta ce ba'a haifi mutum ba, da sauri ta matsa kusa angonta, ta tamke fuska kafin ta bi yarinyar da wani matsiyacin kallo. Aryan dai tamkar ba da shi aka yi magana ba, ya yi banza da yarinyar.

Seraphina dan ta gwadawa yarinyar ita ma A ce sai ta ce. "My gentle chaos mu tafi wajen lotion in zaɓa, daga nan ya isa mu wuce". A shagwaɓe ta faɗa tana riko hannunsa. Tsayar da kallonsa a kanta ya yi, ta marairace fuska tana turo baki.

"Kin fasa sayen vest ɗin ne?". Ya faɗa can ƙasa. Kai ya jinjina mashi. "Yanzu na fasa, sai wani lokaci, kawai ka zo mu tafi". Ta ƙara kankame hannunsa. Ɗan rungumo shoulder ɗinta ya yi game da cewa mu je. Zame jikinta ta yi daga nasa ta tsugunna a ƙasa, tamkar zata yi kuka ta ce. "Ni ka ɗaukeni".

Waist ɗinsa ya riko da hannayensa dikka biyu, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya rage tsawonsa, ya ɗauketa cak tamkar ƴar baby, hannayenta tasa ta saƙalo wuyansa kafin ta kwantar da kanta a gefen lion chest ɗinsa. Wucewa da ita ya yi, sun zo dab zasu wuce yarinyar Seraphina ta fidda tongue ɗinta tai mata gwalo, Seraph ta ji haushin yadda yarinyar ta yi banza da ita ta nufi Aryan ne, ta zage sai ta mashi magana, shi ne ta gwada mata capacity ɗinta.

Ai tsaye yarinyar ta yi tana ganin ikon god, babyn daddy ta goge mata hadda gabaɗaya. Da suka je wajen lotion zai sauƙeta ƙasa ta ce ina bata san wannan ba, wai sai dai ya riketa ta zaɓi abin da take so, ta ƙara ƙanƙame shi game da kwantar da kanta luff sosai. Uhm soyayya ai dole ya yi abin da take dan kada ranta ya ɓaci.

Ya kuwa biya mata, a haka ta karisa sauran shopping ɗin, wai dan fa yarinyar ta ji haushi ne yasa ta ce kada ya sauketa, a haka zasu yi shopping, dik ib da suka gifta yarinyar ta ganta kwance a kirjinsa. Kai Seraphina duniya, kishi da wanga ɗiya ai balai ne, iya kirsa da kisisina.

Har da shafa arab hair ɗin Aryan ta bayan wuyansa tana ɗan turo baki. Shi kam bai kawo komai a ransa ba, kawai dan ya faranta mata yake yi. Bayan sun kammala shopping sai ya ɗauketa suka bakin beach dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin, a lokacin dare ya fara yi, karfe 11 ta yi.

Suna parking a wajen sai ga kiran Lion. Picking ya yi game da karawa a kunne, shiru ya ɗan yi yana sauraron Lion ɗin, after like 20 second sai ya ce. "Kawai ku yi dinner ɗin, sai can dare zan shigo".

Buɗe baki Seraphina ta yi zata yi magana ya yi gaggawar rufe mata da hannunsa yana ɗan zare mata idanu. Kai ya jinjina kafin ya ce. "Zan kula". Daga haka ya ciro wayar ya katse. Zai ɗauke hannunsa daga kan ɗan bakin nata ta yi saurin kamawa ta sumbacesa kafin ta ce. "Daddy da waye kake waya?".

Buɗe kofar moyar ya yi, ya fito ba tare da ya amsa mata ba, sai kuma ya ce. "Wait for me bari in maki oder abincin dare a wancan CRYSTAL RESTAURANT ɗin". Bai jira amsarta ba ya wuce ya nufi wani haɗaɗɗen ɗan karamin restaurant dake wajen.

Fitowa ita ma ta yi, ta tsaya a jikin motar game da takure jikinta waje guda, wani irin sanyi na bugata, akwai sanyi sosai.

Jikinta na rawa, ta so komawa cikin motar amma babu dama, dan tana fita motar ta rufe kanta, bata san yadda ake buɗeta ba. Unexpected idanunta suka sauƙa a kan beach na wajen, ya ALLAH, zazzare idanunta a kan ruwan ta yi, bata san lokacin da ta raba jikinta da jikin motar ba, da gudu ta karisa wajen tekun tana kallon fitilun dake wajen, ga hasken wata na haska ruwan.

Rufe idanu ta yi ta sake buɗewa, a fili ta ce. "Wajen ya haɗu, yaushe zan samu cikar burina na keta cikin teku a jirgin ruwa in je kasar da rana take fara fitowa? Wayyo sea".

Lokaci guda wani iska mai sanyi ya busata, hakan yasa ta yi gaggawar takure jikinta waje guda, hannunta suka fara rawa, tana son kallon ruwan kuma tana son komawa wajen motar ta laɓe kada sanyi yai mata illah.

Shiru ta takure a wajen tana ganin haɗuwar ruwan. Unexpected daga bayanta ta ji an ɗaura mata abu a saman shoulder, kamshin perfume ɗinsa yasa ta gane shi ne. Da sauri ta juyo ta faɗa jikinsa, ya rufeta da suit ɗinsa da ya cire, ya gyara mata da kyau, dama suit ɗin ya ɗaura mata a shoulder ɗinta.

Zuro hannayenta ta bayansa ta yi, ta yi tighting ɗinsa sosai tana faɗin. "Daddy yaushe zaka ɗaukeni mu ratsa teku mu je kasar da rana yake fitowa ta cikin jirgin ruwa?"...... Can ƙasa ya ce. "Very soon, after our marriage". Ɗago kanta ta yi, suka ɗan zubawa juna ido, sai kuma ya rabata da jikinsa game da sanya mata suit ɗin nasa. Ya kama hannayenta suka nufi wajen haɗaɗɗun kujerun da aka tanada kusa da beach ɗin dan cin abinci.

A nan suka zauna saman kujerun dake kallon juna, ya zuba mata ido yana jin tamkar ya mallaketa ya gama, a daidai lokacin kuwa Abba na can suna plan da Ammie kan a cikin satin nan zai kawo ziyara gidansu Seraphina, Ammie ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari saboda dama Seraphina ta shiga ranta.

Sai shagwaɓa take zuba mashi tana ƙarawa, shi kuwa yana ta biya mata, a wannan dare ya shirya masu abubuwa dayawa, dan har wajen CP zasu fita.

Ƙayattatun abinci aka kawo masu waje, da kansa ya dinga ciyar da ita, sai santi take yi tana karawa, sai da ya cika mata ciki tab, sannan ya ci ɗan kaɗan, ya tashi ya kama hannunta suka nufi cikin mota, daga nan suka nufi ainahin main gate na CP ɗin, sai murna take yi yau zata fita waje, shi kuwa sai farinciki yake yi na ganin tana murna.

------------------------------🔥

D-------O--------L🔥

Around 1 na rana, bayan sun yi sallar azahar sun yi lunch, suka zauna Noor yana ɗaukar karatu wajen Leo, while Zaynish ya haɗa kayansa ya nufi bakin ruwa dan yin wankin kakinsa, ya ce ba zai iya baiwa ƙananan sojoji su yi mashi ba, saboda shi in mutum ne yai mashi wanki yana ganin baya fita, ya fi so ya yi da kansa.

Vash yana zaune a kan wani dutse yana shan mangoron da sojojinsu suka ciro a wata bishiya da ta nuna gwanin ban sha'awa.

A can kuwa, Arya da su Angelina suna ɗaki, Manassa na zaune gefen mattress rike da drink a cup a hannunta tana sha, while Angelina na rike da laptop, yanzu ta mayar da hankali kan aiki sosai, saboda Zaysh baya ɗaukar wasa.

Shigowa cikin room ɗin V ta yi, tana ɗan ɗingisa kafa, ba jimawa ta farka daga barci ta yi wanka, tana sanye da kaya marasa nauyi. Kallo suka bita da shi, suna shirin yin magana sai gani suka yi ta ɗauki wayanta ta nufi waje, bayanta suka bi da kallo. Kusan a tare suka miƙe Manassa rike da cup na drink ɗin suka biyo bayan V dan su ji meyasameta, sun ga idanunta sun yi jajir sun kumbura tamkar ta sha kuka, ga shi tana ɗingisa kafa, abinku da shagwaɓɓaɓiya sai shagwaɓe fuska take yi.

A bakin tantinsu suka isko V tsaye tana ƙoƙarin kara waya a kunne, Arya rike da hannun Jehan, Manassa ta zauna a wannan dutse dake bakin tantin nasu tana kora drink ɗinta, Angelina ta tsaya gefen Manassa ɗin, suka tsaya jiran ta kammala waya.

A natse murya can ƙasa ta ce. "Hello friend". Ta faɗa tana ɗan matsawa daga kusa da su Angelina, taga miss call ɗinsa sama da 20 ne daga daren jiya zuwa yau, shi ne ta ce bari ta kira ta ji menene, wannan causin ɗin nata ne.

Daga can ɓangaren ya ce. "Ina kika shiga ne beb, tin jiya ban jiki ba, dik na damu, na yi kawarki sosai, naki kewar daddaɗar muryar nan taki"........ "Sorry friend, nima ai na yi kewarka kuma na yi kewar daddaɗar muryanka ɗin, aiki ne ya sha kaina, yasu Aunty Bee?".

"Suna lafiya to ya aiki?"....... Ɗan juyawa ta yi zata amsa da lafiya idanunta suka sauƙa a kan Noor dake tsaye ta bayan tantinsu, ya yi folding hands ɗinsa a kirji, kallonta kawai yake yi, fuskanta a tamke tamau, dik ya canza. Ya shiga cikin tantinsa ne yaga bata ciki, to sanin bata jin daɗi yasa ya ce bari ya dubota, sai ya bi ta bayan tantin nasa zai shigo nasu kenan ya ji tana cewa ta ki kewar daddaɗae muryan friend, shi ne ya tsaya a wajen.

Ai jikinta take ya hau rawa, ta wani irin mugun shan jinin jikinta, da sauri ta zare wayar daga kunnenta, tana ƙoƙarin yi mashi magana ya matso cikin zafa ya kwace wayar, wancan karon ma da ya raga mata dan bai san me mata yake nufi gabaɗaya ba, aikuwa yanzu ya sani, dan haka bai ga dalilin da zai sa wani ya nemi shiga harkarsa ba, yanzu auren sunnah ma suka yi bana zobe ba, kuma ya je duniyar sama jiya ai sai shiru.

Jikinta na rawa ta sake mashi wayar tana kallonsa. Bin kan screen ɗinta da kallo ya yi, sai ya kara wayan a kunnensa, a daidai lokacin Friend yake ce mata. "Da gaske voice ɗina na maki daɗi beb?"........ Wani irin tsananin takaici ne ya turnuƙe zuciyansa, a fusace ya ce. "Who the hell are you?!".

Zuba mashi idanu su Manassa suka yi, zallar kishi ne malam a kan fuskansa, har idanunsa sun ƙaɗa sun yi jajir. Kit Friend ya katse kiran, dan a tinaninsa oganta ne a wajen aiki. Bin kiran Noor ya yi, amma ba'a ɗauka ba, cikin zafa ya ɗago da kallonsa a kanta.

Hannu ɗaya ya zura cikin aljihun combat trouser dake jikinsa, ji ya yi tactical tshirts dake jikinsa ma zafi take haɗa mashi tsabar ya fusata, abin takaicin yai mata warning a farko ranar, amma yau ta sake yi.

Cike da zafin kishi ya ce. "His voice is so sweet, and you missed him so much, who's he?!". In a harsh way ya faɗa, hakan ya ja hankalin sauran sojojinsu dake sansanin, amma dik sai suka yi ƙasa da kai tin da ogansu ne a wajen.

Gagara bashi amsa V ta yi, idanunta suka ciko da kwallah, hannunta sai kerma suke yi........ "Okey you love his voice, you missed him? You love him right? You want to marry him?". Cikin zafin kishi ya faɗi maganar, bai ma san me yake faɗe sosai ba.

"Please stop it, stop saying that, It's not what you're thing......". Tamkar zata sanya kuka ta yi maganar..... Wani irin mugun kallon da ya dallah mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar. Cikin fushi yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta ya maka wayar tata da ƙasa, take ta tarwatse raga-raga. Hannu bibbiyu ta sanya ta toshe bakinta jikinta na tsananta kerma, hawayen da take ƙoƙarin rikewa ne ya fara zuba tamkar an buɗe tap, da kyar ta iya ɗagowa ta kalli rikitatcen face ɗinsa da gabaɗaya ya canza, har ja fuskar tasa ta yi tsabar fushi. Sai ma in ya tina ta ce i missed you and i missed your sweet voice, ya rabb, sai ya ji tamkar zai haɗiye zuciya.

Muryarta na rawa ta fara ƙoƙarin sake yi mashi magana ko zata dace. Cikin zafa ya ɗaga mata hannu game da cewa. "Don't say anything here!!". Ya faɗa yana pointining ɗinta da hannunsa. Ba shiri ta haɗiye abin da take son faɗe, jikinta ya tsananta kerma sosai wanda yasa ta gagara iya rike kanta dama ba lafiya ba, sai kawai ta durkushe ƙasa a wajen, wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi.

Da gudu Angelina ta kariso in da take, durkushewa ta yi ta rungumi V a jikinta tana satar kallon Noor dake ta uban huci tamkar zai kama da wuta. Gabaɗaya takaicinsu ya gama cika Arya, ji take tamkar ta shake V da ta zubar masu da mutunci take baiwa namiji hakuri a kan laifin da bata aikata ba, yaushe ta ce tana son friend?. Ita dai Manassa abin da kowa ya sani ne, watau komai normal, bata wani damu ba, dan faɗa tsakanin V da Noor ai ba sabon abu bane, zama su shirya ne babu wanda ya sani, ranar da suka yi wancan uban faɗa waye ya taɓa zatan zasu shirya? Ba sai ga shi ko kwana ɗaya ba'ayi ba har sun shirya! Dan haka su rataye kansu idan sun ga dama ita babu ruwanta.

Noor ne ya cika baƙin kishi, ga ɗan banzan saurin fushi, ya koyi saurin fusatar Leo, in ban da haka yanzu me abin fasa mata waya daga jin tana magana da wani? Ko damar yin magana yaki bata, shi sarkin zuciya.

Siririn tsaki Arya ta ja tare da juyawa da sauri ta bar wajen, dan zata iya kai duka idan ta cigaba da tsayawa. Manassa dai hannu ta miƙa ta ɗauko drink ɗinta dake ƙasa ta cigaba da sipping, dan ita faɗar ma sugar yake mata, ai in basa faɗar basu cika masoya ba. Juyawa Noor ya yi cikin fushi zai bar wajen. Da sauri muryarta na rawa ta ce. "Please, my heartbeat, just listen to me, give me one chance to tell you who I truly am, don't be upset with me for a mistake I never made, let me hold your trust close to my heart".

Ai ko kallon in da take bai sake yi ba, da sauri ya wuce gudun kada ya kai mata duka, dan wlh ya rike kansa ne, ba dan haka ba time ɗin da take cewa friend voice ɗinka da daɗi da sai dai ta ji hakwaranta a ƙasa ya zubar mata saboda balain kishi. Ita ma bata ji, gata mai aboki, ai taga aboki yau kam.

Wucewa ya yi ya barta a wajen, ta rungume Angelina tana wani irin kuka mai ban tausayi, dama ga ciwon da ya ji mata. Shi kuwa cikin tantinsa ya koma, ya zauna a gefen mattress yana huci. After like 5 mins ya miƙe cikin zafa ya fito. Suna nan in da ya barsu, Arya da Jehan ne kawai suka koma ciki.

Su ya nufo gadan-gadan, yana zuwa ya ɗauki V cak sai saman buɗaɗɗiyar kirjinsa, cikin zafin jini ya wuce cikin tantinsa da ita, ba zai iya barinta tana kukan nan ba dan yasan bata da lafiya, kada wani ciwon kuma ya kamata.

A saman mattress ya kwantar da ita, a tsawace ya ce. "Ki mun shiru, idan na sake jin koda tarinki ne sai kin gane kuranki". Babu wasa a tattare da shi ya faɗa. Hannu tasa ta toshe bakinta game da haɗiye kukan nata, tana kallonsa cikin ido, ya dallar mata harara kafin ya miƙe ya fice ya barta kwance, sai shessheƙar kuka take yi.

Lamarin Noor da V sai su wlh, ga balain kaunar juna ga zafin kishi, ga kuma faɗa, kai suna bani ciwon kai.

After some hours.

Bayan sun yi sallar mangrib da ishai, sojojin dake sansanin suna hakin wuta, har team one suna tare a bakin wuta except Leo dake cikin ɗakinsa, V tana ɗakin Noor kwance zazzaɓi ya rufeta saboda kukan da ta sha ga ciwon da angon nata ya bata jiya, sai zazzaɓi ya rufeta, har yanzu kuma Noor yana kan dokin zuciya, yaki sauraranta, da ya kawo mata abincin dare ma tana son yi mashi magana ta faɗa mashi tana jin zazzaɓi sai ya dakatar da ita, ya wuce ya fita ba tare da ya ji me take son ce mashi ba.

Su Angelina suna tare da Arya a cikin ɗaki suna hira, shiryawa Arya ta yi cikin normal kayan gida kamar yadda Leo yai mata message, wandon jeans baki da top ash, ta ɗauki karamin pistol da ake basu dan kare kai, sannan ta ɗauki laptop ɗinta cikin rucksack ɗinta, bata yi wa su Angelina magana ba ta wuce ta fita.

Da sauri Jehan ta taso tana nuna mata alamar zata bita. Riko hannunta ta yi, ta miƙawa Angelina ita tare da cewa. "Zan je wajen sir Nirash ne, akwai aikin da zamu yi, ki kula da ita". Ta kai karshe game da rage tsawonta ta sumbaci goshin Jehan, sannan ta saketa ta juya.

Da sauri ta nufi tantin Leo, tsaye ta iskosa ya kammala shirinsa cikin combat trouser ɗinsa da normal tshirt, yana kokarin sanya wuƙaƙensu na sojoji a mazaunansu a jiƙinsa. Kamewa ta yi game da sara mashi kafin ta ce gata nan. Bai yi magana ba ya wuce gaba, bayansa ta bi, suka fita ta baya babu wanda ya sani, ko su Noor basu sani ba.

Tafiya mai mugun nisa suka yi har zuwa in da gwamnati ta gina ginin office ɗin sojojin ruwa dake ɗan nesa da bakin ruwan. Dik juriya irin ta Arya sai da ta gaji a wannan tafiya, shi dai ya wuce gaba, ko sau ɗaya bai waigota ba, ga rucksack na laptop ɗinta da ta goyo a baya ko shi bai karɓa mata ba.

Haka ta jure wahalar har suka isa, dik jikinta ya yi tsami. Tsarin ginin offine ɗin nan ya tsaru kam, ga tsawo sosai. A jikin katangar ta baya suka tsaya, Leo ya juyo da kallonsa a kanta, tana tsaye tana ɗan haki. Can ƙasan maƙoshi ya ce. "Zaki iya haurawa?".

Kallon tsawon katangar ta yi, ya yi tsayi sosai, amma da yake basu san kalmar no ba sai ta ce. "Yeah sir".

Hannu ya miƙa kan ta bashi rucksack ɗinta. Ba musu ta cire ta miƙa mashi, karɓa ya yi ya goya a bayansa game da tura wayansa cikin anjihunsa, ya haɗe hannayensa dikka biyu ya ware mata tafukansa.

Baya-baya ta koma, sai ta zo da gudun gaske ta taka kan hannun nasa da ya haɗa mata, ta daka tsalle shi kuma ya ƙara ɗagata da hannun nasa, ta kama saman katangar ta haura, a hankali ta fara nishin gajiya. Sauke rucksack ɗinta dake bayan ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login