Showing 27001 words to 30000 words out of 365093 words
kowannensu ya haye saman bed ɗinsa, sannan suka fito da wayoyinsu kamar jita. Noor ne ya fara kunna wayansa, dan kafin a basu wayoyin sai da aka shar'anta masu cewa da daddare ne kawai aka lamunce masu su kunna waya, dan haka in zasu kwanta suka kashe wayar basa sake kunnanta sai sun dawo ɗakin bayan horo.
Shi dai Zaynash yaki fito da wayansa, dan yana jin kunyarsu, dikkansu wayoyinsu manya-manya na ƴaƴan manya, nasa ce kawai matacciya, sai yake jin kunyar fitarwa.
Noor yana kunna wayar ya kunna data, nan sakonni suka hau shigowa kamar ruwa, dik kuma na ƴan uwansa mata ne dake ta turo mashi saƙon kukan sun yi kewansa.
Bai bi ta kan kowannen saƙo ba, kai tsaye ya shiga kan number da aka sanya my dad. Video call ya dannawa wannan number yana ɗan gyara kwanciyarsa da kyau, sai ciza laɓɓa yake saboda zafin da jikinsa take yi mashi.
Bugu ɗaya aka ɗauka, dik da ɗakinsu da haske amma fuskan Noor bata fita sosai a call ɗin ba, hakan yasa ya kunna hasken wayar ta gaba. Yana sauke idanunsa a kan wani kyakkyawan mutum mai ɗan matsakaicin jiki, suna kama sosai, fari tas da shi, ga idanu dara-dara farare tas, da alama mutumin ma a kwance yake, kyakkyawan gaske sosai.
Harara ya dallawa mutumin kafin ya ce. "My dad baka yi barci ba?"....... Wani irin cool smiling ya saki kafin ya amsa da. "I'm waiting for your call, how can I sleep?".......... Sake hararansa Noor ya yi. "Daddy gidan Soja akwai wahala, ba zan iya jura ba, ka zo ka ɗaukeni". Ya kai karshen maganar cikin raunin murya. "Pleasure very soon zaka saba".... Zai yi magana daddy yai sauri sake cewa. "No, kawai ka faɗa mun success da ka samu a yau?".
Yana turo baki ya amsa da. "Alot my hero". Wani irin ƙayataccen murmushi dad ya saki kafin ya ce..... "Thats is my son, I know you will succeed, try to bring us a good result"..... "I will try my best dad, where's my Auntys?"....... "They're not here, they're in their room, but Lisa bata nan"....... Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Dad here is my friends da na haɗu da su a nan, they help me and they're so king and perfect". Ya faɗa tare da juyar da wayansa ya nunawa daddy bed ɗin su Zaynash dake kwance shiru.
"Zaynash this is my dad, ku gaisa". Ya faɗa yana sauƙiwa kasan bed ɗin intently, ya zo ya miƙawa Zaysh wayar. Karɓa ya yi, a mutunce suka gaisa, daga nan ya karɓa ya miƙawa Vash ma suka gaisa. Dik da basu magana da Nirash sai ya ji yana son kai mashi wayar su gaisa da daddynsa, wata zuciya ta ce a'a kada ya je, wani kuma ya ce ya je Nirash zai amsa. Daurewa yai tare da nufar bed ɗin Leo.
Sallama ya yi mashi tamkar wanda zai shiga wani ɗakin saɓanin yadda ya je wajensu Vash ba sallama. Ai cikin zafa su Vash suka ɗago kai suna kallonsa, suna jiran su ga Leo zai karɓi wayar ne ko kuwa.
A gaban bed ɗin ya tsaya tare da cewa. "Here is my dad, ku gaisa"...... Leo yana kwance shiru, ya kifa littafin tasa a fuska kamar yana barci, kuma idanunsa biyu, amma babu alamar zai amsa Noor. Shiru ya tsaya zuciyansa sam babu daɗi na abin da Leo yake yi masu, amma ya zasu yi? Dole sai hakuri. Ko sunan Leo ɗin fa basu sani ba, kuma wai suna ɗaki guda.
Jin shiru yasa dad ya ce. "Are you okay pleasure?". Da sauri ya amsa da. "Yes dad". Ya faɗa yana juyawa ya bar wajen.
"Is there any problem?". Dad ya tambaya, da sauri ya girgiza kai alamar a'a, sai ya haye bed ɗinsa ya kwanta zuciya babu daɗi. Haka suka cigaba da hira da daddyn nasa har barci ya ɗauke su Zaynash, sun shafe 2 hours suna hira, da alamar shakuwa da kaunar juna matuƙa a tsakaninsu. Sai can suka yi sallama, ya katse kiran tare da kashe wayar bakiɗaya, daga nan ya hau barci shi ma. Ɗakin ta yi tsit alamar dik sun yi barci harta Leo ɗin ma.
--------------------------🔥
NEW YORK.
CRYSTAL PALACE.
Ayi hakuri da zaman da zan yi wajen bayanin inane CRYSTAL PALACE, zan yi hakan ce dan ba zan sake bayani a kanta ba, kuma zan yi hakance dan na tabbata ba kowa yasan irin ginin da nike nufi ba har sai na yi bayani, bugu da kari CRYSTAL PALACE tana da alaƙa da kusan kowa dake a cikin wannan littafi, dik wata rikici daga cikinta yake fitowa, shiyasa dole zan daure in sha wahalar typing dan fayyace maku tsarinta dallah-dallah!.
CRYSTAL PALACE. Watau duniyar glass masu bala'in kyau da kyalli game da ɗaukar hankali, duniya ce guda mai zaman kanta, cikin CRYSTAL zaku rantse da ALLAH kasa ce or gari mai zaman kanta, wajen da ke haskakawa kamar rana, amma mu shiga cikin domin ku ganewa idanunku.
Katafaren yankin da na tabbata baku taɓa cin karo da irinsa ba. Wasu irin jiga-jigan hyper glass skyscrapers a wajen, gine-gine masu hawa 30 zuwa 50, dik na glasses masu canza launi bisa yanayi gari, suna ƙyalli kamar lu'u-lu'u, tare da golden edges.
Akwai manya-manyan solar gardens, lambunan zamani masu amfani da hasken rana, sannan suke canza launi da dare su bada sky blue light mai ƙara ƙawata wajen da ɗaukar hankali. CRYSTAL PALACE gamayyan gidaje ne masu hawa 30 zuwa 50 da a ƙallah zasu kai 20 a wajen, dikka ƴan haya ne cike a cikin, idan har aka kama maku kuɗin da suke biyan hayan kowani hawa ɗaya a shekara ya isa sayen katafaren gida na alfarma a Abuja Naija, sannan dik kuɗaɗɗen suna tafiya ne wani asusu guda ɗaya, haka na nufin mallakin mutum ɗaya ne.
Akwai infinity sky villas, wasu box masu zubin gidaje ne masu shawagi a iska, haɗe da smart levitation technology, ba kamar gidajen zama bane, a'a, su na yawon shaƙatawa ne a sararin samaniya, idan kun gaji da zaman cikin gida kuna da damar fita ki yanki ticket ku shiga wannan karamun box zai yi sama daku kamar ƙaramin jirgi, sai dai a iya sararin samaniyar CRYSTAL yake tsayawa baya zuwa wani wajen.
Ga watsu rantsasstsun neon quantum roads, titunan da ke haske bisa tafiyar mutane da motocin zamani. Ga wasu magnetic highways, hanyoyin mota da ba sa buƙatar taya, sai fasahar levitation. A saman waɗan nan tituna akwai wasu jiga-jigan Guards madaka ƙarti dake kai komo suna shawagi dan tabbatar da tsaro, kuɗin da ake biyan waɗan nan Guards ɗin kawai arzikin wani kamshaƙi ne a Naija.
Sannan akwai hanyoyi a sama, sky walkways, hanya ce da ta fita daga wannan gini izuwa wannan amma ta sama, kowani hawa akwai hanyoyin da suka sada gine-ginen, ba sai ka sauƙo kasa ka sake hayewa sama idan zaka je wajen mutum ba.
Akwai ƙayatattun wuraren hutawa a ciki irinsu ethereal beach, wani nau'in teku da ke canza launi a bisa lokacin dare ko rana, ba kato sosai bane, an yisa ne dan mazauna CRYSTAL ɗin su mori kuɗin hayansu da kyau. Ba iya su aka tsaya ba, akwai cloud nine resort, wurin hutawa mai shawagi a saman gajimare! Amma shi ma a iya sararin samaniyar CRYSTAL ɗin ne. Lunar reflection park, wani kaɗaɗɗen lambun da ke hasken launin wata, saman lambun wasu kyawawan taurari ne aka yi kwalliya da su dake ƙarawa wajen kyau.
Akwai Crystal sphere arena, wajen taruka, wasanni, kallon cinima dan kallon film ko wani abin, da wajen nishaɗi da aka yi amfani da fasahar hologram.
Irin solar da ake amfani da shi a CRYSTAL yana bada wutar lantarki ba irin solar da aka sani bane, domin kuwa su haɗe yake da views ɗinsu, idan rana ta daki glasses na windows ɗin sai wutar lantarki ta samu, batiransu na chanji wanda yasa ko dare ce wuta bata taɓa ɗauke masu.
Babu ƴan aiki a CRYSTAL PALACE, domin kowani gida akwai robot dake aiki bisa umarnin mazauna wannan gida. Akwai SOLARIS CORE, wani katafaren gini ne wanda ya kasance cibiyar kasuwanci, a nan kasuwansu yake, super market kala daban-daban a ciki dan yin shopping ba sai sun fita waje ba. Dan a kara ƙawata CRYSTAL PALACE kawai sai aka yi wasu floating luxury malls a saman, idan kana so zaka iya zuwa can ka yi shopping ɗinka hankali kwance. KAI TURAWA FA SUN CI GABA, YANZU NASAN WASU SUNA NAN SUNA TINANIN ANYA AKWAI DIK ABIN DA NA KIRGAN NAN A GASKE KUWA? TO DIK AKWAISU SARAI, IN BAKU JE IN DA SUKE BA KUN KARANTA A NOVEL ƊINA, SHIYASA NA DAURE NIKE MAKU BAYANINSU DALLAH-DALLAH DAN KU GANE, NAIJA MA MUKE DA KANANAN GINE-GINE IRIN ESTATE BARE SU? AI SUN SHAHARA A GINE-GINE SHIGEN CRYSTAL PALACE TIN TINI.
Ga wani katafaren elysium cloud lounge, wajen cin abinci ne a sama mai balain kyau da ɗaukar hankalin wanda aka tsara shi sosai. Yanayin tsarin tsaron wajen, akwai irin drone security ɗin nan, ƙananan jirage dake kula da tsaro dare da rana, da zarar sun ga wani motsin da basu yarda da shi ba zasu hau kara take Guards su ɗauki matakin gano meke gudana ko wace barazana ke zuwa. Ga irin bio scanning entryways, babu wanda zai shiga yankin ba tare da kowa dake cikin gidansa ya gane waye ya shigo CRYSTAL PALACE a yau ba! Dan akwai tv da aka haɗa da bio scanning ɗin a kowani gida dake wajen.
Dik da haka akwai quantum shielding system, tsarin wall da aka kewaye wajen mai amfani ne da wutar lantarki dan kare yankin daga barazana ta waje, ko jingina daga waje ka yi da jikin bango sai ka ji shocking, kuma bulletproof ne wall ɗin, ga wani katafaren CRYSTAL PALACE HOSPITAL a takaice mu ce CHP, hospital ne dan kula da lafiyarsu, asibiti ne wanda shi ne na huɗu a duniya wajen karfi da kayan aiki game da manyan jiga-jigan likitoci.
Gate guda biyar ne na shigowa CRYSTAL, wanda kuma dikka gate ɗin suna da mahaukatan tsaro na ban mamaki, ba sai na faɗa maku haɗuwar gidajen dake cikin CRYSTAL ba, saboda makurar haɗuwa ne, dik wanda kuka gani cikin CRYSTAL babban kai ne, ya kai yadda ba'a tinani, wane karamin kai da iya kama haya a cikinsa.
To a duniya gabaɗaya irin CRYSTAL PALACE guda huɗu ne kawai, kun taɓa jin labarin THE LINE NA SAUDIYA AND THE CIRCLE NA DUBAI? to su ne guda biyun CRYSTAL cikon na uku sai kuma wani a nan cikin US ɗin shi ne na huɗu, sai dai THE LINE AND THE CIRCLE kunga mallakin gwamnatin kasashen ne, kuma bama a fiddasu ba, shi kuma CRYSTAL mallakin wani mutum ne wanda su kansu mazauna wajen basu san ainahin mai wajen ba, dan an ce ya fi shekaru 10 da mutuwa, wasu sun ce yana prison and ɗauresa life in prison, dan haka yanzu wajen tana karkashin kulawar wani ne daban, to koma dai menene mu je zuwa dan abin dayawa. A takaice yadda Crystal yake kenan. Gidajen cikin CRYSTAL ɗin nan dikka an kama hayansu, babu empty, kada ku manta gidaje ne guda 20, kuma dikkansu benaye ne masu hawa 30 zuwa 50, amma dik wasu manya dake jin kansu a ƙasar sun kama haya suna ciki da family ɗinsu, dan yanayin tsaruwar wajen da kuma karfin tsaronsu, dan ko tsuntsuwa bata isa wucewa ta sararin samaniyarsu ba na'ura zata harbota ko ta kaɗata wani waje, zallar basira da technology aka zuba wajen tsara wannan gini, shiyasa ya fita daban......... Wannan ma na takaita maku haɗuwar CRYSTAL PALACE wlh.
-----------------------
Kai tsaye mu wuce Crystal Palace Hospital, watau CPH. A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da suka yi mata mugun nauyi, tana son motsa jikinta amma ta gagara, da kyar ta yi karfin halin waro idanunta waje. Ya subhanallah, idanun nata sun yi jajir sun kumbura matuƙa, sun zama abin tsoro.
Zazzarosu sosai ta yi tana bin in da take da kallo, ganin bata gane ko'ina bane wajen yasa ta ɗan motsa lips ɗinta da suka yi mata nauyin tsiya, tongue ɗinta tamkar an ɗaɗɗauresa, da kyar ta iya cewa. "Mammy, mammy where are you?".
Shiru babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta yunkura zata miƙe, sai ta ƙasa, a nan ta ji alamar jikinta a ɗaure yake, ƙoƙarin sauƙo da kallonta izuwa jikin nata ta yi, a daidai lokacin aka turo kofar room ɗin wanda hakan yasa ta wurga eyes ɗinta can. Wani mutum ne ya shigo hannunsa rike da wasu ledojin drip guda biyu. Sanye yake da tail coat, kafafunsa na cikin wasu haɗaɗun cover shoes masu tsadar gaske, fuskansa a sanye da nose mark, kansa sanye da hat, gabaɗaya kayan jikinsa bakake ne harta socks dake kafafunsa.
Yana shigowa ya sauƙe kyawawan dara-daran eyes ɗinsa a kanta, while ita ma shi take kallo, dik da yana sanye da nose mask hakan ba zai hana ka gane cewa haɗaɗɗe bane. Yana da tsawo sosai, ga cikar halittar, dik in da ake neman namiji wannan ya kai.
Ganin idanunta biyu yasa intently ya iso gaban bed ɗin, a gefe ya ajiye drip ɗin kafin ya mai da kallonsa a kanta da kyau. Can ƙasa ya ce. "Had luck". Ya faɗa yana kai hannu zai riko nata hannun. Da sauri ta janye baya, da kyar ta iya sake cewa. "Who are you and where is my mammy?".
A maimakon ya amsa mata sai ya kai hannu ya kama nata, a natse ya zare mata drip da ya kare yana faman jan jininta. Bayan ya cire ne ya zauna saman sofar dake kusa da ita, bai sake yi mata magana ba, da ganin haka ita ma bata sake yi mashi magana ba, ta yi shiru tana tinanin ina mahaifiyarta take?!. Daga karshe ta yunkura, a hankali ta miƙe zaune a tsakiyar haɗaɗɗen bed ɗin da ba zaka taɓa cewa na majinyata bane.
Ƴan kafafunta ta yi ƙoƙarin zurowa ƙasa, sai dai ina, gadon yana da tudu bata iya taɓo ƙasa ba, ɗan shagwaɓe fuska ta ɗan yi, kamar zata yi kuka, kai kallonta a kansa ta yi, ya sunkuyar da kai shiru tamkar ba mutum a cikin ɗakin. Turo baki ta yi tare da gyarawa ta matsa bakin bed ɗin sosai. Dirowa ƙasa da karfi ta yi a in da ta tafi gabaɗaya zata faɗi ya miƙe kafansa ɗaya ya tareta, ashe dama yana kallonta, da ta faɗo forehead ɗinta zai bugu da tiles ɗin ne, sai ya tare kan nata ya bugu da kafarsa.
Slowly ya ɗago da kallonsa a kan face ɗinta, bai yi magana ba yasa hannu ya kama nata hannun, da hannu ɗaya ya ɗagata tare da miƙewa tsaye ya jefata kan gadon. A kan face ɗinta ya tsayar da idanunsa, still dai babu alamar zai yi magana. Yanayinsa yadda kuka san wani shahararren gangster haka.
Komawa ya yi ya zauna tare da ciro wayansa daga aljihu, intently ya fara latsa wayar yana typing message. Ɗan zuba mashi idanu ta yi, sai kuma ta turo baki, take dara-dara violet eyes ɗinta suka cika tab da kwallah, a fili ta ce. "Where are you mammy? I'm so scared here, come and take me away from here". Cikin kwararriyar turancinta ta yi maganar, voice ɗinta ba dai daɗi da sanyi ba, ga zallar madarar shagwaɓa.
Yana jinta sarai, amma ko motsi bai yi ba, yana cigaba da latsa wayarsa. Ganin babu mai kulata ne yasa ta lallaɓa ta koma ta kwanta shiru. Kyakkyawar yarinyar karshen haɗuwa, gashin kanta light ash very silky haka, ga wani irin sheki da yake yi, violet eyes ɗinta dara-dara farare tas da su.
----------- silent for almost 40 mins ne ya biyo baya kafin wasu nurses guda biyu suka katse masu shirun ta hanyar shigowa. Ɗaya hannunta rike da wata ƴar CPH-note-b, ɗayar kuma hannunta rike da babban leda mai shaƙe da magunguna. A gaban bed ɗin suka tsaya, mai rike da magungunan ne ta miƙawa guy ɗin tana faɗin. "Here's her drugs, make sure she's taking it on time".
Hannu yasa ya karɓi magungunan ba tare da ya kalli in da suke ba, ita kuma ɗayar nurse ɗin miƙa mashi note-b ɗin ta yi, saƙon sallama ne, takarda ce mai ɗauke da sunan CRYSTAL PALACE HOSPITAL da sauran bayanan yarinyar, me dalilin kwanciyarta, kwananta nawa, kuɗin da aka cajesu, kai komai dai, a karshe time da date da aka sallameta. Sannan takardan nashi ne, dan idan ba mazauna CRYSTAL ba babu wanda yake da irin takardan, din in zaka kwanta jinya sai ka zo da notebook ɗin, a nan za'a cigaba da yi maka rubuce-rubuce har ranar sallama!.
Nan ma karɓa ya yi, ba tare da ya yi magana ba ya miƙe tsaye, gentle ya tako zuwa gaban bed ɗin. Hannu ɗaya yasa ya ɗauki yarinyar sai saman shoulder ɗinsa, bai bi ta kansu ba ya nufi waje.
Yana fitowa wasu jiga-jigan guards masu zubin gangsters su uku suka take mashi baya da gudu. Kai tsaye wajen wani dankareren mota ya nufa, tin kafin ya iso wasu guards madaka karti dake kusa da motar suka ɓalle mashi back door. Ciki ya jefa yarinyar kamar yaki, sannan ya shiga gidan bayan shi ma.
Da sauri suka mayar da door ɗin suka rufe, da wani irin gudun karti suka nufi sauran motocin dake wajen, da gudun gaske suka ja motocin suka kutsa cikin C-P (CRYSTAL PALACE) Ita dai taga ikon God, sai kawai ta hau binsu da kallo, tam daina magana tin da har yanzu ba'a samu mai iya amsa mata ba.
Ɗaya daga cikin shahararrun ginin da ya fi ƙawatuwa a wajen suka nufa, shi hawa 10 ne kawai, sannan shi gabaɗaya glass nasa sky blue ne babu mix. A parking lot na gidan suka paka motocin, da gudu wasu kartin guards dake shawagi a gidan suka nufo motocin. Nasa suka fara ɓuɗewa kafin na kowa. Fitowa ya yi cikin zafin nama, yasa hannu ya