Showing 150001 words to 153000 words out of 365093 words

Chapter 51 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5925

yanzu ya zame masu jiki, yunwa da rashin barci ai abokin aikinsu ne.

V tin tana dan ja baya, tana rike da hannun Romeo ɗinta suna hira har ta saki jiki ta kwanto jikinsa tare da miƙe kafafu suna hira, dik wani motsinta a kan idon Juraiz, har ga ALLAH yarinyar ta tafi da imaninsa. While Arya na ɗaki, ta gama iya dube-dubenta, daga karshe ta rufe laptop ɗin, ta ci abinci kaɗan sannan ta kwanta dan yin barci. Manassa na waje bakin kofa tana latsa waya.

Bayan Agelina ta gama waya da Aunty Lisa sai ta dawo wajen ta zauna, matsawa kusa da ita Unays ya ya yi, cikin salo ya ce. "Hy, good evening". Kallo ɗaya ta ɗan mashi tare da ɗauke kanta kafin ta amsa, dan ma dai yana gaba da ita ne da ba zata amsa ba. Ƙoƙarin janta da hira ya yi, amma ta basar da shi, saboda yaran GAT akwai jan aji wlh, V ce dai mai saukin kai.

Takura mata Unays ya dinga yi da ƙoƙarin sai ta kula shi, ita kuwa tana amsa shi sama-sama, sai ya yi magana uku take amsa ɗaya, a gaskiya Unays karya ne mace ta ce bai haɗu ba, cikakken namiji ne, ga kyau, chocolate da shi, but Angelina bata nuna kamar ya haɗu mata ba.

Sai da 12 ta buga ne, cike da bada umarni Zaynish ya ce. "Dik matan nan ku tashi ku tafi ɗaki". Abin ku da shi musulmi ne, kuma yasan darajar mace. Ɗago ido Noor ya yi ya kallesa, sai ya ga Zaynish baya kallonsa, haka na nufin ba dan saboda Noor ɗin na baiwa flower ruwa shi da V ya yi maganar ba, hasalima shi bashi da matsala da soyayarsu, kawai dai yaga bai dace matan suna cikinsu a wannan lokacin bane.

Ganin ba da wata manufa Zaysh ya yi maganar bane yasa Noor ce mata ta tashi su shiga ɗaki. Matsawa ta yi, sumbata ya bashi a kumatu kafin ta miƙe tsaye, miƙewa Angelina ma ta yi, suka nufi hanyar komawa tantinsu. Dab zasu shiga ciki V ta ji an rike hannunta ta baya, tana juyowa ya jawota jikinsa. Ajiyar zuciya ta sauke, wucewa ciki Angelina da Manassa dake zaune a wajen suka yi.

Haɓar V Noor ya ɗago, cikin zafa ya haɗe bakinsu, hot kiss ya shiga bata, mayar mashi da martani ta fara yi, yasa hannu ya fara shafa tula-tulanta yana lumshe ido. Ita kuma ta kankameshi ta baya tana tura mashi tongue ɗinta.

Sun ɗan ɗauki lokacin a haka kafin ya saketa tare da ce mata goodnight, ya faɗa still yana matsa tula-tulanta bai saki ba. Juyawa ta yi da sauri ta shige cikin tantin nasu, shi kuma ya juya ya koma wajen da suka hura wutan. Tin da ya zo wajen suke kallon juna da Zaysh kaman wasu munafukai, magana da ido suke yi.

Kashewa Zaysh ido ɗaya ya yi kafin ya koma wajen zamansa ya zauna, harara Zaysh ya watsa mashi tare da ɗauke kansa, ya cigaba da dannar wayansa. Haka suka kasance har wayewan gari, basu rintsa ba. Da sassafe su Arya suka tashi, one by one suka fito waje, nan suka isko sojoji masu yi masu girki sun hura wuta. Wucewa Arya ta yi izuwa wajen koramar dan ta yi wanka, tana sanye da white bathrobe.

Tana wucewa sai ga Angelina ta fito rike da waya a hannunta, daidai lokacin Leo ma ya fito sanye da sleeping dress ɗinsa, ya ɗaura towel fari a kansa, bai bi ta kan kowa ba ya wuce wajen karamar baya shi ma. Wucewa Angelina ta yi izuwa wajen da ta ga sojojinsu na zazzaune, tana sanye da kayan jiya bata canza ba.

Daga ɗan nesa da sojojin ta tsaya tare da ɗaga wayarta ta kama ɗaukar su Unays hoto, dik suna zazzaune, basu sani ba, ta ga su Unays an mata kyau yau, sai kawai ta tsaya kashe masu hotuna tana murmushi.

Daga bayanta ta ji an ce. "Aiki ya sameki kema, kin faɗa irin cutar V ko?"..... Ba tare da ta juya ba ta amsa da. "To ke Manassa wai ina ruwanki da mu ne? Ke dai ba kin ce Arya zaki biyewa ba? Babu namijin da ya kai ku yi soyayya da shi ko? Na tabbata watarana zaku faɗa tarko ne!"...... Brush ɗinta Manassa ta sanya a baki ba tare da ta sake cewa uppan ba ta wuce izuwa wajen wani dogon bishiya dake gefen su Unays ɗin tana goge bakinta.

Harara Angelina ta bita da shi kafin ta cigaba da ɗaukarsu hoto. Ita kuwa Arya tana zuwa wajen koramar ta ware igiyar bathrobe ɗinta, ta zaresa ta ajiye a gefe, ya rage daga ita sai pant and bra da yake suna sakawa yanzu. Saboda santin da take ji ne yasa ta rufe idanu ta faɗa cikin ruwan dake kwance ƙasar koramar wai dan ma kada sanyi yasa ta fasa shiga.

Ruwan a daidai kirjinta ya tsaya da ta tsugunna a ciki, kana iya hango tudun tula-tulanta a waje, ruwa ta fara ɗeba a tafukanta tana watsawa a fuskanta tana ɗan tsuke baki saboda sanyi, ga ruwan koramar daga sama yana zuba ta baya bayanta, sun kafa tantin wajen da zasu yi wanka fa, amma tsabar iskanci irin na Arya a nan take son yin wanka.

Da yake ta rigada ta shiga sai ta fara jin daɗin ruwan, tsoma kanta a ciki ta yi tare da ɗagawa da sauri ruwan ya biyo gashinta ya hau wanke mata fuska. Cike da farinciki tasa hannu tana sharce ruwan face ɗin nata, slowly ta buɗe idanu kai tsaye sai a kan Leo dake tsaye yana ƙoƙarin kwance igiyar bathrobe na jikinsa.

Ai bata san time ɗin da ta zunduma ihu ba, ya yi mugun bata tsoro, bata ji motsin mutum ba, bata ma kawo a ranta akwai wanda ya ga wannan koramar a cikin sojojinsu ba, ta zaci ita kaɗai ta ga abinta shiyasa ta zo shanawa a wajen taki zuwa toilet da suka kafa.

Ko a jikinsa wai dan ta yi ihu, hasalima bai ɗago ya kalleta ba ya cigaba da kwance igiyar, ya buɗe rigar ga shi yana fuskantarta, daga shi sai shorts irin matsastsun nan da kana iya ganin shatin halittarsa, daga sama babu ko single ne, faffaɗar lion chest ɗinsa a waje, ko kaɗan bai damu ba, ita kuwa ta yi suman tsaye a cikin ruwan, ga shi ta kudurtawa ranta ba zata fita ba tin da ta rigasa zuwa, sai dai shi ya hakura ta gama. E kam akwai case, zan ga da ita da shi waye zai hakura ya barwa ɗaya wajen

https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-22-by-princess-teema

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.






STEP 1🔥


2025-11-27🔥



اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E_____________ 22



Zame rigar ya yi tare da ajiyewa a gefe saman wani dutse. Ai kasaƙe Arya ta yi tana kallonsa, ta kuma gagara daina kallon nasa dik da rikitata da ya yi. Cikin zafin nama ya motsa izuwa dab bakin ruwan, sai a lokacin ta lura da sojojin huɗu dake bayansa wanda sun juya mashi baya suna rike da bindigu dan bashi tsaro.

Ƙara rage tsawonta ta yi ta hanyar ƙara natsawa cikin ruwan saboda ta ɓoye kirjinta, dik da take bata da addini lallai bata yarda a kalle private part ɗinta ba, musamman kirjinta, a cewarta dik wanda ya kalli tsiraicinka ya gama da kai, kuma ba zai sake kallonka da wata daraja ba, kuma zancenta haka ne, ni ban ga amfanin fitar da surar jikin da wasu ƴan matan suke yi ba, dik ranar da namiji a waje ya kalli albarkatun da ALLAH yai maki shikenan kuma, ALLAH baya kuskure, ba a banza ya ce mata ku suturta jikinku ba, amma wasu suna ganin kamar wayewa ce su bar ko'ina a buɗe, wlh dik namijin da yasan ciwon kansa ya fi son macen dake cikin hijabi, yana son sanin ainahin abin dake a cikin hijabin ne.

Ko sau ɗaya Leo bai ɗago ya kalleta ba, ya shige cikin ruwan abinsa, sai dai bai tsaya ta kusa da ita ba, saboda ita tana tsoron can tsakiyar ruwa, ta baki-baki ta tsaya, shi kuma wajen yai mashi kaɗan tin da ruwan ko waish ɗinsa bata kai ba.

Can ya shiga har sai da ya kai in da ruwan ta zo daidai kirjinsa. Gagara motsawa Arya ta yi tamkar wacce ta sume, slowly ta juyo bayanta ta ɗan saci kallonsa. Wankansa yake yi cikin kwanciyar hankali, kirjinta dake barazanar tarwatsewa ta dafe tare da jan dogon numfashi kafin ta furzar a hankali, a idanunta kawai ta fara kallon irin yadda ya cire rigar a gabanta, ya ilahi, ita kanta ta shaida Leo ya haɗu matuƙa, jikinsa tamkar madara, ba tabo ba ciwo sai wannan tsage na gerar tasa da ta ƙara mashi kyau sosai.

A takaice sai da ya yi wankansa ya fito, ya mayar da bathrobe ɗinsa ya bar wajen sannan ta samu salamar dawowa cikin hayyacinta, a lokacin ta ɗan iya samun motsawa, jikinta dik a mace, ta ji ba zata iya cigaba da wankar ba, sai kawai ta fito ita ma. Ganinsa dik ya kashe mata jiki, da kyar ta mayar da kayanta ta nufi ɗakinsu.

Nan ta isko su Angelina dikkansu a ciki suna ƙoƙarin shiryawa cikin kayan aiki, sun yi wanka a tantunan da suka kafa. Da ganinta suka nufeta suna tambayar lafiya? Dan sun ganta tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki ne.

A takaice ta ce masu babu komai, sannan ta wuce ta ɗauki uniform ɗinta, a gurguje ta hau shiryawa, while Angelina and V sun kammala shiri har sun fito da laptop ɗinsu dan yin aikin da ya kawosu.

Tactical trouser and tactical t-shirts Arya tasa, kayan sun yi mugun yi mata kyau, ta goge gashin kanta dake zubar da ruwa, ta shirya tsab tare da zube perfume ɗinta na kamfanin STAR LADIES BODY LUSH, sannan ta nufi wajen laptop ɗinta.

Ita kuma Manassa miƙewa ta yi ta nufo waje dan ba aikinta bane yanzu, tana da free time..... Sosai suka dukufa a kan aikinsu na tsawon good 30 mins, V tana duba ta kudanci, Angelina ta kudu maso gabans, Arya ta yamma maso kudu. Idan a aikin computer ne jama'a to a barwa Arya kayanta, cikin ƙankanin lokaci ta gano motsi a wajen, sannan ta yi amfani da sound-d ɗin jikin drone da ta tura dan jiyo menene a wajen, ta sanya katan Bluetooth ɗinta a kunnuwanta dan ta ji me ake cewa da kyau.

Magana ta ji na mutane, amma bata iya ganinsu, sannan maganar bata iya fita sosai, amma confirm ƴan adam ne suke magana a wajen. A natse ya zare Bluetooth ɗin daga kunnenta, ta ɗaura saman table da laptop ɗin nasu yake, sannan ta miƙe ta fito waje.

Kirjinta na bugawa da karfi ta isa wajen tantin su Leo, daga bakin kofa ta tsaya, yanzu dai taki shiga ƴar kaniya, tana tsoron sake ganin abin da ta gani jiya da kuma ɗazun. Sara mashi ta yi game da cewa. "Sir akwai karin haske".

Yana tsaye a tsakiyar ɗakin yana rike da wayar da ya kara a kunne alamar waya yake yi, amma shi ma maganansa irin na IRON FIST ne, ba zaka taɓa cewa yana magana ba, can ƙasa cikin sanyin murya tamkar baya motsa lips. Tsayawa ta yi daga wajen tana satar kallonsa har ya kammala wayan, yana sanye da kaya irin nata sak, shi ma tactical trouser and t-shirt ya sanya, da yake ya fita haske sosai kuma launin kayan nasu duhu ne sai ya fi yi mashi kyau, shi shi ya yi wa kayan kyau, ita kuma kayan ne suka yi mata kyau.

Ita dai har yau tana mamakin kitson dake kansa, kuma mugun kara mashi kyau yake yi, sai ma idan ya sakesu, wlh ba karamin kyau yake yi ba, amma yafi yawan tara jelar kitson ya ɗaure, idan kunga ya sakesu to yana cikin yanayi mai daɗi ne suma zai barsu su shana.

Bayan ya kammala wayan ne ya nufo waje, hakan yasa ta bashi hanya da sauri, a wannan karon ita ta wuce gaba ya rufa mata baya. A gaban laptop ɗinta ta zauna tare da ɗauko Bluetooth ɗin nata ta mayar kunne, hannunta ɗaya naa kan mouse na laptop ɗin, ɗayan hannunta kuma yana gefen table ɗin.

Ciki Leo ya shigo wanda yasa su V kara natsuwa sosai. A gaban laptop ɗin nata ya tsaya, ta bayanta kenan, ɗan sunkuyowa kanta kaɗan ta gefen shoulder ɗinta ya yi a ƙoƙarinsa na son hango motsin dake wajen. Ai jin yadda ya sunkuyo kanta har tana jin sauƙar numfashinsa a jikinta ne yasa gabaɗaya ta birkice ta rasa natsuwarta, har wani ɗan kerma yatsun kafafunta suke yi.

Shi kuwa ko kaɗan bai kawo komai ba, sai ma hannu da ya miƙa ya ciro Bluetooth na kunnen nata ya sanya a nasa kunnen dan ya ji sautin dake fitowa. A lokacin da ya sanya hannu zai cire Bluetooth ɗin nan dogayen yatsunsa suka taɓata sai da ta ji wani irin shock, shi kam bai ji komai ba, to a bakin aiki yake, dik wani tinaninsa da lissafinsa game da hankalinsa ya tafi a kan laptop ɗin, bai mashi ma kamar macece take zaune a wajen ba.

Jin sautin baya fita sosai da ya sanya Bluetooth ɗin ne yasa ya ɗaura hannunsa a kansa mouse ɗin da hannunta ke kai da nufin ya gyara sautin, bai ma lura da hannunta a wajen ba. Saura kaɗan ta saki fitsa a wando saboda razana na jin skin ɗinsa ya taɓata, da sauri ta zame hannunta tana jan wani irin dogon numfashi.

Bai san tana yi ba, ƙoƙarin clearing na voice ɗin ya shiga yi yana sauke mata numfashinsa mai ɗumi a gefen wuyanta, gabaɗaya ya rikita baiwar ALLAH shi bai san tana yi ba...... Ya nemi clear na laptop ɗin sama da ƙasa bai gani ba, hakan yasa ya ɗan juyo da kallonsa a kanta kaɗan. "Ina clearing voice and rash ɗinki?". In a cool way ya faɗa.

Daidai lokacin ita ma ta juyo da kallonta a kansa saboda yadda cool voice ɗinsa ya ratsa kunnuwanta ya yi mugun tafiya da ita, sai ta ji tamkar yana romantic mood ko kuma shagwaɓa yake yi mata, alhalin ba haka bane, kunnuwanta ne kawai ke jiyo mata hakan.

Zuba mashi idanu ta yi, ta manta ya tambayeta ta gagara yin magana..... "Are you okey?". Ya faɗa yana zare kallonsa daga kanta, waɗan nan jade eyes ɗin nasa masu kalar sanyi sun kara rikitata, sai da ta haɗiyi wani irin yawu gwad kafin ta iya amsa mashi da. "Bari in fitar maka dasu". Dama ta ɓoyesu ne a wani waje saboda V dake addaba mata da clearing na wakokin soyayya..

Bai yi magana ba, ya dai jinjina kai. Da sauri ta kai hannunta saman nasa dake kan mouse na laptop ɗin da tinanin idan ta ɗaura hannunta ai zai cire nasa, sai ta ga akasin haka, domin kuwa hankalinsa ya tafi kan cikin kungurmin dajin da drone da V ta tura yake ɗauko masu video, ya mayar da kallonsa kan laptop na V, ko kaɗan bai ji hannun Arya a kan nasa ba.

Ita kuwa jin ɗumin hannunsa yasa ta mance me zata yi, unexpected ta tsinci kanta da fara shafa skin ɗin nasa da golden hair kalar na kansa ke kwance a hannun nasa luff. Jin ana shafa mashi hannu ne yasa ya dawo da kallonsa a kan hannun nasa, da sauri ya juyo da kallonsa a kanta wanda ya yi daidai da ta juyo dan ta saci kallonsa ita ma.

Ganin angry face ɗinsa mai rikitar wannan, ga waɗan man jade eyes ɗin nasa ne yasa ta ji a take natsuwarta ta dawo, har ɗan ɗauke wuta ta yi kafin ya sha jinin jikinta, da sauri ta ɗauke kallonta daga kansa tare da fara ƙoƙarin cire hannunta a kan mouse ɗin, sai ta ga ya rigata cirewa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta haɗiyi yawu mai wuyar wucewa gwab, sannan ta fara kokarin aikinta.

Bayan ta fitar masa ta ɗauke hannunta ya mai da nasa ya shiga ciki, har yanzu dai jikinta na ɗan rawa, amma ta daure har ya gama abin da yake yi, ta yi mamakin ganin yadda ya kware a computer, har ta ji kamar ta yi bincike a kansa! Me ya haɗa shi da computer da zai iya sarrafata har haka?. Tana can tana tinaninta shi ya kammala abin da zai yi har ya fita waje, da sauri ta miƙe ta nufi kofa dan ta sami damar binsa da kallo, an kuwa yi haka, ta zuba mashi idanu har ya shiga cikin tantinsa.

Su Angelina dai sai kallonta suke yi a sace, sun sha mamakinta. A fili ta ce STERIOUS, MYSTERIOUS, watau sterious mutumin da ba'a iya fahimta, mai ɓoyayyen hali kenan, ta gagara fahimtar a sahun mutane kirki zata sanya shi ne ko a na banza, shiyasa kawai ta bashi wannan suna STERIOUS.

Su Angelina dai suna ta kallonta, ta ɗan jima a tsaya a wajen kafin ta juyo ta dawo ciki, ta zauna a gaban laptop ɗinta tana cigaba da bibiyar abin, ta sanya Bluetooth a kunnenta, nan ta ji Leo ya gyara sautin maganar na fita sosai, lallai ƴan ta'addan ne a wajen, ga shi suna magana cikin farinciki da shanawa.

Tana ƙoƙarin yin magana kenan sai ji ta yi Leo dake tsaye a bakin kofa ya ce. "Ki haɗa ƙananan bluetooth


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login