Showing 126001 words to 129000 words out of 365093 words

Chapter 43 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

6205

aiki ba'a samun kuskure, so ba yau bane farau.

Wata allura ya ɗauko, ya haɗa ya yi mata a damtsen hannu, sannan ya kira wasu nurses guda biyu suka shigo bayan ya tattara dik sauran kayan tiyatar ya mai da su muhallinsu, yazama tamkar ba'ayiwa matar komai ba.

Umarni ya yi wa nurse's ɗin da su ɗauki matar izuwa recovery room na ɗan lokaci dan ta samu damar farfaɗowa daga anesthesia.

Daga nan ya zaro wata farar takarda, rubutu ya fara yi cikin kwararre da kuma kyakkyawan handwritten ɗinsa mai bala'in kyau, abin da yake rubutawa a jikin takar shi ne, za'a bar mara lafiyar a asibiti ta yi kwana biyu zuwa biyar dan a kula da lafiyarta, sannan a bata nasogastric tube dan kada cire mahaifar ta hanata cin abinci, a kula da cimar da za'a rinƙa bata, a mayar da hankali a kan dik wani motsinta a cikin ƴan kwanakin nan dan tabbatarwa ta samu ingantaccen lafiya, kaɗa a barta ta yi aiki mai nauyi.

Ya yi dogon note tare da naɗe takardan ya bi bayan nurses ɗin izuwa C-R ɗin. A jikin matar ya ajiye note ɗin tare da ɗauko wata takarda ya yi sign, sannan ya ɗauki wayansa ya matsa gefe kaɗan. Call ya yi kamar na minti ɗaya, ya katse kiran ya fita waje.

Da fitarsa bai fi da mintuna 40 ba sai ga wasu nurses mata guda biyu sun shigo ɗakin, matar suka ɗauka suka fice, suna tura gadon nata har izuwa wajen wani daki da majinyata ke hutawa, suka sanyata a cikin, daga nan suka bar room ɗin, babu kowa a cikin ɗakin sai ita kaɗai, ko'ina tsab-tsab ga kamshi da sanyin AC dake tashi, .

Shi kuma DR MARK bayansu DR JAMES ya bi. Cikin wani glass room ya shiga, komai na ɗakin glass ne except wall. Ɗakin gabaɗaya kewaye yake da kwalabe na glass masu kama da cikin mace, an shirya kwalaben a shirye datsan-datsan, kusan rabi da kwatan kwalaben ɗauke suke da mahaifar mace a ciki, tamkar yadda ake dashen mahaifa wa cikin mace haka aka yi dashen wa waɗan nan kwalabe dake ɗauke da ruwa tamkar yadda mahaifa yake a cikin mace, gabaɗaya kwalaben kuma suna haɗe ne da na'urar dake basu daidaiton yanayi ya hanyar amfani da wutar lantarki. TO FA, ABIN AL'AJABI! ME SUKE YI DA MAHAIFA KUMA?.

Karisawa kusa da su DR MARK ya yi, a natse ya ce. "Done my work"....... Hannu DR JAMES ya jinjina mashi alamar ya yi kokari, sannan ya mai da hankali kan aikin da suke yi. Buɗe wata kwalba mai kama da cryo storage tubes ya yi tare da gyara hands gloves na hannunsa, ya ɗauki wannan mahaifa ta wannan mata, a natse cikin tsananin kula suke komai.

Da kallo ɗaya zaka yi wa yadda suke aikin nan kasan cewa kwararrun likitoci ne na gasken-gaske, in short su likitoci ne da irinsu basu wuce a kirga ba ma a duniya, matakin kaifin ƙwaƙwalwa da bincikensu ya zarce yadda kuke tinani, they're gifted, amma dik da haka cikin taka tsantsan suke aiki yadda zaku san aikin mai haɗari da wahalar gaske ne suke yi, idan aka samu matsala kaɗan komai na iya lalacewa su tabka babban asarar da ba zasu taɓa son hakan ba!.

A cikin wannan kwalba DR JAMES ya sanya wannan mahaifa, sai da ya tabbatar zamanta ta yi daidai sosai, sannan ya kunna wata naura dake jikin kwalbar dan canzawa mahaifar yanayi izuwa yanayin cikin mace, take cikin kwalbar ta kawo wuta sky blue mai ɗan haske, ta fara fitar da siririn sauti mai bada vuuuuu kamar vibrate na waya.

Da sauri DR JAMES ya juya ya rungumi DR KAMAL alamar sun yi nasara, matsawa DR MARK ya yi shi ma suka rungumi juna sosai, sannan suka raba jikinsu. A natse suka fara takawa suna bin dik kwalaben dake cikin wajen suna dubasu, tamkar suna duba wani abin haka. Sai da suka tabbatar komai normal sannan suka nufi hanyar fita a tare. Kai tsaye side na dabbobin dake cikin wajen suka nufa, suna tafiya ne a kai ɗaya.

Kewaye suka fara yi a wajen dabbobin, yana da girma sosai wajen, guards dake tsaron wajen kawai sun fi mutum 20, kun ga kuwa ai wajen da girma. Kowani dabba da irin abincin da yake ci, ga kwanon abincin kuma a gabansa an zuba mashi, waɗan nan guards ɗin suke baiwa dabbobin ruwa da abinci, har macizai dikka suke ciyar da su, shiyasa aka samu jiga-jigan guards madaka karti masu rai da lafiya dan kula da su.

Sosai suka yi yawo a cikin wajen, suka tabbatar da komai yana nan yadda ya dace, sannan suka fito suka nufi office ɗinsu. A kan hanyarsu na komawa office suka ci karo da wasu kyawawan nurses guda biyu dake sanye cikin kayan aikinsu, sun yi matuƙar kyau tsab-tsab da su. Face ɗinsu da nose mask suma. Har ƙasa suka durkusa suka gaida Dr's ɗin cikin girmamawa.

Kai na gaji da rubutun, haba, ku ce Princess dakata ki bari haka, ya isa ki huta mana! Amma dik kun yi shiru sai typing nike yi kamar ba'a sona! To sai Monday idan mai dikka ya kaimu!.
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-19-by-princess-teema

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.




STEP 1🔥


2025-11-24.🔥



اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E_____________ 19



Sosai suka yi yawo a cikin wajen, suka tabbatar da komai yana nan yadda ya dace, sannan suka fito suka nufi office ɗinsu. A kan hanyarsu na komawa office suka ci karo da wasu kyawawan nurses guda biyu dake sanye cikin kayan aikinsu, sun yi matuƙar kyau tsab-tsab da su. Face ɗinsu da nose mask suma. Har ƙasa suka durkusa game da sunkuyar da kai suka gaida Dr's ɗin cikin girmamawa.

Hannu Dr Mark ya ɗaga masu alamar sun ji kafin su wuce ba tare da yi masu magana ba. Miƙewa nurses ɗin suka yi suna binsu da kallo har suka kurewa ganinsu, dawo da kallonsu a kan juna suka yi, ɗayar ta ce. "Sister Maya kin san wani abu ne?"........ Kai Maya ta girgiza alamar a'a bata sani ba. "Dr James ya haɗu over, kin san da cewa son gaske nike mashi?". Ta faɗa tana ɗan ciza laɓɓa......... "Sister Zinta i think ai kin same shi kin gama, ko bake kika ce mun ya yi inviting ɗinki zuwa waiting toom ɗinsa a yau da yamma ba?".

"Haka ya ce in same shi a waiting room ɗinsa bayan tashi daga aiki, amma kuma ai ban san dalilinsa na kiran nawa ba! Maybe ma wani aikin zai sanyani, kin san shi baya rabuwa da sanya mutane aiki". Ta kai karshen maganar tana ɗan tura baki a cikin mask ɗin.

"Amma ai idan aiki ne baya taɓa cewa a same shi a waiting room kai tsaye haka, sai dai office, ni a nawa ganin kamar ya kyasa dake ne, in kuwa haka ne ki shirya faɗa da sister Lazy, dan ba zata taɓa yarda wata ta raɓesa ba"........ Siririn tsaki sister Zinta ta ja tare da wucewa gaba tana faɗin. "Idan har na samu hankalinsa ya dawo kaina wacece kuma wata Lazy? Ba dik taƙamar da take mana da nuna ta fimu ɗin saboda shi yana kulata bane? Dame ta fimu? Kada ki manta ita ma fa ɗalibar lafiya ce kawai kamarnu".

"Uhm ni dai ina ji maki tsoron balainta, dan mafaɗaciya ce"......... "Ita ɗin banza, dik taƙamarta dan tana aiki a karkashin office ɗinsa ne, shiyasa nima na zage ina son komawa karkashin office ɗin nasa".

Maya zata yi magana daga bayansu suka ji an ce. "What are you doing here at this time da yakamata ace kuna bakin aiki?"........ Da sauri suka juya, wata malamar lafiya ce dai kamar su, tana sanye da kayan aikinta, kana ganinta kaga irin masifaffun nan masu zubin taliya ƴar murji, idanun nan a tsaitsaye, gashin idon kamar wacce aka shuka shinkafa a ƙasa, suna tsaye zara-zara ga tsawo.

"Sorry sis Lazy". Suka faɗa a tare suna haɗa baki kafin su wuce su cigaba da tafiya zuwa in da zasu ce. Can ƙasa sister Maya ta ce. "Bana faɗa maki ki guji balain sister Lazy ba, kina ganinta tamkar wacce ake yi wa loading na masifa a kanta kowacce rana, kullum da sabon salon balain take zuwa". Cike da tsoro Maya ta karisa maganar.

"Sai kuma ta yi, kawai yanzu inai mata biyayya ne saboda a karkashin office ɗin Dr James take aiki, amma ba wai dan ta fini da wani abu ba". Sister Zinta ta faɗa......... Suna tafiya suna hira har suka shiga wani sashe a cikin hospital ɗin. Wani glass room suka shiga mai ɗauke da tarin chemical dayawa, an shisshirya chemical ɗin a cikin transparent glass, kowani chemical da sunansa a manne a jikin kwalbansa.

Lap gown and hand gloves suka sanya a jikinsu tin daga bakin kofa kafin su karisa cikin wajen, ga tarin computers daga gefe dayawa, kayan gwaje-gwaje suma akwaisu dayawa a ciki.

One thing about sister Maya and Zinta, dik cikin W-S-HOSPITAL ɗin nan sun fi kowa hakuri, hankali, natsuwa, kamala, kame mutunci da kuma kula da kansu, basa da faɗa, basa zuwa wajen hayaniya, akwai girmama manya, akwai tausayi da sanin darajar ɗan adam, sai dai kuma akwaisu da balain son yara, dik in suka ga yaro rasa natsuwarsu suke yi, su yi ta faman ɗauka, sun taɓa ganin jariri a hannun sister Lazy, suka dinga rokonta ta basu su rike, har da durkusawa ƙasa suka yi mata, ta ce masu babyn Dr mark ne, in suna so su je su rokesa, in ya yarda a basu to zata basu su rike.

Su kuma suna balain tsoron waɗan nan 3 doctors ɗin, dan haka suka hakura, amma har ruwan hawaye sai da suka yi, rauninsu shi ne yara.

Wasu kyawawan ƙananan transparent glass bottle suka ɗauko, a cikin wani katan baff, suka zauna a saman wasu chairs dake gaban manyan glass na chemical ɗin, a hankali suka fara ɗibar kowani chemical suna aunawa suna zubawa a cikin bottle ɗin daidai misali, sai sun auna kilonsa kafin su shirya shi cikin kwali, idan kwalin ya cika sai su ɗauka izuwa wajen da ake shirya chemical irinsa su hau shiryawa cikin glass ɗin.

Sun sanya eye protection a idanunsu kafin su fara aikin, suna yi suna hira a in da sister Maya ta ce. "Kin san wani abu sister Zinta?"...... Kai ta girgiza a lokacin da take ɗibar nata chemical ɗin. "Ina son DR MARK sosai, yana burgeni, amma ban san meyasa yake mugun bani tsoro ba, ko motsinsa na ji sai hantar cikina ta kaɗa".

"Uhm watarana komai zai wuce, mu dake mu yi aiki tukuru mu koma karkashin office ɗinsu, kin san basa ɗaukar wanda ba kwararre ba a karkashin office ɗinsu, shiyasa kika ga na kara dagewa dan in zama irin nurses da suke aiki tare da su, kamar dai wancan fitinanniyar Lazy, amma ke ina ga tsoron matar DR MARK kike ji shiyasa kike shankarsa over har haka"..................... "Hmmmm, bana tsoron matarsa, saboda ban taɓa ganin tana masifa ko wani abin mara kyau ba a cikin makarantar nan. Ni babban abin takaicina ma shi ne yadda basa ɗagowa su kalli mutum".

Zinta da shegen son gulma ce tai ƙasa-ƙasa da murya wajen cewa. "Kuma na ji an ce Dr James har hugging na Lazy yana yi, har kiss da sauransu".......... "Ina fatan shiruna ya zame mun alkhairi". A cewar Maya da bata cika son zaman gulma ba, dan ma dai Zinta best friend ɗinta ce yasa idan tana gulma bata tashi ta bar wajen, amma tana ƙoƙarin hanata gulmar, banda haka ita ba'a gulma da ita, kunji ta ce tana fatan shirunta ya zame mata alkhairi, dan tasan abin da Zinta bata sani bane, abin da ya fi kiss Dr James yake yi da Lazy, amma ba zata faɗa ba ko dan ma kada zuciyar Zinta ɗinta ya buga.

"Matsalata dake kenan Maya, komai sai ki ce kina fata shirunki ya zame maki alkhairi, to da kike wannan magana wani zanje in faɗawa ne? Ko dai kina tinanin wani na jinmu ne?"...... Kai ta girgiza tana cigaba da gwada chemical ɗinta, a natse ta amsa da. "Ba wani zaki faɗawa ba, kuma babu mai jinmu, kawai dai manta da maganar, ya batun shirin partyn da zamu yi next month na kammala karatun ajin farko?".

"Na shirya mashi, amma kin san idan na tina karatun aji na biyun da zamu shiga aka ce ya fi kowanne wahala gabana faɗuwa yake yi? Ina jin kamar ba zan iya ba, yanzu wannan karatun ma da ya muka kare? Wahala kan wahala"....... "Zaki iya ƴar uwata". Ta faɗa cike da ƙoƙarin kwarara mata gwiwa...... "Ina sa ran na iya sosai"....... Da haka suka cigaba da hira suna shirya chemical ɗin nan har suka kammala, sannan suka fito, a lokacin yamma ta kawo kai, karfe 5 suke tashi daga aiki sai su koma wajen kwanansu na ɗalibai, za su shiga class daga 7 na safe zuwa 1 na rana, da sun fito zasu wuce wajen practical, karatunsu ba kamar na sauran likitoci bane, su special ne, suna karatu ana haɗa masu da aiki kullum dan su kware.

Kamar yadda AZURE BARRACK take yaye jami'ai gifted haka WS-HOSPITAL take yaye likitocin da babu irinsu a duniya, mayun bincike mayun aiki tamkar ba ƴan adam ba, a yanzu ba zaku gane komai ba, sai tafiya ta yi nisa damu a cikin WS-HOSPITAL zaku fahimci karatun! Mu je zuwa ku dai.

A lokacin da suka fito wajen lap ɗin almost 5:20, a gurguje suka yi shirin tashi, suka cire lap gown na jikinsu da hand glove ɗin, sannan suna shirya tsab. Dawowa wajen sashen su Dr James suka yi, a nan Sister Zinta ta ce. "Maya mu je ki rakani waiting room na Dr James".......... "Kin san halinsa ƙawata, shi baya son ya ce abu a saɓa mashi, ke kaɗai ya kira, idan ya ganmu tare ransa zai ɓaci, kinga hakan zai sa ma ki rasa damar da yake son baki, ba zan so ki rasa wannan dama ba, ki je ke kaɗai kin ji? Zan jiraki a section B".

Ta san maganar Maya gaskiya ce, ba'a mashi abin da bai ce ba, amma tana mugun tsoron zuwa ita kaɗai ne, dan shakkarsu take ji. Cigaba da kwarara mata gwiwa Maya ta yi har ta yarda zata tafi ita kaɗai, tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi waiting room ɗin nasa dake gefen office ɗinsa, kafin ka shiga office ɗinsa kofar room ɗin yana daga gefe. Ciki ta shiga bakinta a ɗauke da excuse.

Babu kowa a ciki sai wani irin ni'imantaccen kamshi dake tashi, ga sanyin Ac dake buga ko'ina, sofa set set guda ɗaya ne a cikin room ɗin, a tsakiyar sofas ɗin akwai wani lallausan Dubai rug a wajen, sai karamar dispenser, sai kuma wata karamar freezer daga gefe dan zuba drinks su yi sanyi, ga kuma wata karamar show glass mai ɗauke da glass cups masu kyau kuma very luxury. Ɗakin dai ya haɗu sosai.

A saman sofa ɗaya ta zauna, tin da suke basu taɓa shigowa sashen su Dr James ba, dan su aikinsu a wajen Chemicals yake, ta wannan ɓangare suka fi kwarewa, sai sun je aji biyu zasu koma sashen dabbobi, daga sashen dabobi dama sai babban sashe watau na su Dr James. Zaman good 30 mins ta yi, sai faman tinane-tinane take yi da kalle-kalle, ta yi tinani ya fi dubu kan dalilinsa na kiranta, amma ta rasa gane dalili, sai kawai ta yi shiru.

Ta gaji da zama da zuba idon ganin shigowarsa, amma shiru, sai a lokacin da cire tsammani, ta shiga wata tinanin, ta manta da zai shigo sai ta ji an turo kofar room ɗin. Tin daga ƙasa ta fara kallonsa, yana sanye da sportswear ba kayan aiki ba, da alama ya ɗan jima da tashi aiki, still fuskansa da nose mask, and ya ɗaura jacket a kan kayan saboda wani irin fitinannen sanyin da ake zubawa, kafarsa sanye da ankel socks and crops farare.

Ai yana shigowa ta miƙe tsaye a wani irin slow tana kallonsa, kowani motsi nasa a kan idanunta. Dr James irin mazan nan ne masu burge mata da shiga rai, ga shi da salo ɗan gaye.

A saman sofa ya kariso ya zauna, sai da ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ya gama shan kamshinsa kafin ya ce. "Get out of my office!". A ɗan kaifafe ya faɗa, saboda ya ji haushin yadda ta kara 30 mins a kan lokacin da ya bata, shiyasa bai shigo da takardun da zai bata ɗin bama, ya ga lokacin da ta shigo ɗakin ta Camerar dake ɗakin, karfe 5:30 ta shigo, shi kuma 5 yasan suke tashi, kuma 5 ya ce ta zo ta same shi, shi ne zata ɓata mashi lokaci, ba zai ɗauki wannan iskanci ba.

Tsoro da shakkarsa yasa bata yi ƙoƙarin bashi hakuri ba, da sauri ta wuce ta fita. Tana fitowa suka ci karo da sister Lazy dake ƙoƙarin shiga office ɗinsa hannunta rike da tarin files na manyan ayyuka dana rahotannin dabbobi.

Tana ganin sister Zinta ta fito daga waiting room ɗinsa ta dakata tare da juyowa gareta, sai dai kafin tai mata magana Zinta ta wuce da gudu tana ƙoƙarin toshe bakinta saboda wani irin kukan da yake shirin kubce mata, ta ji zafin rasa wannan dama, tin bata wuci 16 years ba take


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login