Showing 234001 words to 237000 words out of 365093 words

Chapter 79 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

6197

ɗaura shugaban da ƴan ƙasa zasu iya fito na fito da shi, suna gani ana zalunntarsu amma ba zasu iya yin komai ba, sai dai su yi ta banbami suna cika baki a media!".

Iska mai zafin gaske Lion ya furzar daga bakinsa, wai yana matsayin leader na IRON FIST kuma ace a ƙasarsa, ƙasar mahaifinsa ake wannan ɓarna? Ya ALLAH, shi kam zai iya haɗiyar zuciya saboda takaici, lallai lokacin yin aiki ya yi, lokacin kawo karshen dik wani azzalumi ya yi. Dama ina baku manta ba IRON FIST sun tafi hutu ai! Tin da suka kashe ministar ba sun ce sai bayan shekara ɗaya ko biyu zasu sake yin aiki ba? To shiyasa kuka ji sun yi shiru suna ta bincike kawai, yanzu lokacin komawa bakin aiki da gaske ya yi, Seraphina zata rage ganin daddy Aryan, dama san suna hutu ne yasa yake da ishasshen lokaci!.

Da kyar Lion ya iya cewa. "Gano WS babban abu ne, aiki ne ma matuƙar wahala, amma zamu tsokanesu ta yadda da kansu zasu bayyana kansu!"..... Kallon juna suka yi, basu gane in da Lion ya dosa ba, suna son karin bayani, hakika sun san gano WS ba abu bane mai sauki, dan WS ɗin na farko ba mulki suke yi, basu a cikin siyasa, su mutane ne dake rayuwa kaman sauran mutane, kila ma suna kusa da kai a halin yanzu, suna rayuwa very simple, amma suke naɗa masu mulki, abin mamaki, su fa basa son hawa gujerar mulki, da suna son hawa da sun hau, su dai suna gefe, amma dik wata kafunci da zalunci suke shiryasa, idan kuna jin ana faɗin masu naɗa masu mulki to su ne.

Tsabar ɓadda kama ma suna tafiya ba security, ba ɗan sanda, babu sojoji, ba zaku taɓa tinanin su bane, kuma suna ko'ina, kunga kuwa kamasu abu ne mai matuƙar wahala, dik duniya harta shugabannin da suke ɗaurawa a kan mulki babu wanda yasan kamanninsu, kai haɗarin mutanen nan ya zarce yadda kuke tinani, su ne mutanen da ko kana kan mulki in baka bi umarninsu ba a cikin ƙasa da 5 mins zasu iya kasheka, baka isa ka guje masu ba, suna koina, suna da ido dake ganinka a dik in da kake, wlh haɗarinsu ya fi na nuclear, sai dai mu ce ALLAH ya karemu ya kawo mana karshen dikkan wasu azzalumai!

Aryan da ya fi kowannensu fahimtar Lion ne ya ce. "Kana nufin siyasar Avaris zamu shiga?"....... Vir ya amsa da. "Ta hakance kawai zamu tsokanesu su bayyana kansu, dan a halin da ake ciki ka kuskura ko magana ka yi a kan shuwagabannin Avaris ɓatar da mutum ake yi, idan kana da rabon rayuwa a daka maka warning a sanya maka tsoro!".

Jinjina kai dikkansu suka yi, dan kuwa haka ne, suna gani a media ta kasar, suna bibiyar dik wani motsin Avaris sosai......... "Ba zamu shiga siyasar Avaris ba, amma dik wani gurɓatacce shugaba zamu tugesa, zamu farkar da matasan Avaris mu cire masu tsoro, hakan zai yi matuƙar tayarwa da ws hankali, dole zasu nememu da kansu dan su ga bayanmu! Kunga daga nan zamu kamasu a sauƙaƙe". Cewar Lion ɗan baiwa mai basira da wayon kama azzalumai, kai Lion ne ya cancanci sunan Smart fa!.

Jinjina kai suka yi, lallai haka ne, wanna shawara ta yi, zasu kamasu a sauƙaƙe!
A natse Vir ya ce. "Ya batun bank ɗin can?"....... Zuba mashi idanu suka yi, alamar suna jiran karin bayani, Lion ne ya ce. "Zamu gane wace bank ce kuma a wace ƙasa take". ....... Aryan ne ya ce. "Awww bank da suke kai kuɗin Avaris ko?"........ Jinjina kai Vir yai. Lion ya ce. "Zamu gane, kuma zamu kwashe dik kuɗin Avaris dake wajen, In Sha ALLAH zamu gina ƙasar Avaris da shi!".

Kai suka jinjina alamar shawarin ya yi. Aryan ya ce. "Wani plan ne a ƙasa a kan aikin?"........ Lion ya ɗago da idanunsa a kan Vir wanda shi ma shi yake kallo, while su Aryan dikka Vir ɗin suke kallo. Kyafta masu idanu sau biyu ya yi kafin ya ce. "Next week zan shigo, ina zargin wannan bank ɗin yana tsakanin ƙasashen nan guda, France, America ko England!".

Shiru suka ɗan yi, can Lion ya juyo da karfi ya sauke kallonsa a kan Aryan, in a cool way ya ce. "Aryan daga wani bank aka sakawa matar can (mom ɗinsu) kuɗi? Me sunan bank ɗin?". Yanzu tinanin ya faɗo mashi a kai. Shiru Aryan ya yi, sai yanzu shi ma ya ji yana zargin wannan bank ɗin. Yana ɗan zazzare idanu kaman mai wani tinani ya ce. "Wani bank ne wanda ban taɓa jin sunansa bama a duniya sai a wannan rana, kuma tin daga wannan rana har yau ban sake jin sunansa ba, sunan ma isn't complete name, just alphabet ne kawai, something WS-STSW-BANK, haka sunan yake". IRON FIST akwai ƙwaƙwalwa, tsawon shekaru bai manta sunan bank ɗin ba.

Wani pen dake gefensu Lion ya ɗauko, ya jawo wani book dake gefe, WS-STSW-BANK ya rubuta a kan littafin, ya cire WS farko, ya WORLS SYSTEM, ya cire STSW na biyu, ya rubuta STARS WORLD BANK, ya haɗa a ƙasa ya rubuta WORLD SYSTEM STARS WORLD BANK!

Sun sha madarar mamakin ganin yadda a cikin sauƙi ya fitar da sunan, ya ALLAH, watau brain kyauta ne daga ALLAH da ya baiwa IRON FIST, Lion gifted ne!!. To yanzu sun gano sunan bank ɗin, saura su gano a wace ƙasa take!.

Wani numfashi Lion ya ja wanda kana ji kasan na takaici ne, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Any danger is from ws, dik wani balai ma daga can yake fitowa, watau bank ɗin ma nasu ne kenan, da kyau!".

Aryan ne ya ce. "Ni yanzu damuwata ɗaya ne, su Nirash, sun tafi Mission, kuma a Arewacin Avaris, wanda dani da ku dik mun san dik wani motsinsu ana sane da shi, kada ku manta ƴan ta'addan ɗaukar nauyinsu ake yi, kunga kuwa ba za'a bar wasu sojoji su kawo karshensu ba, saboda moriyar abin da ws suke ci".

Guru ya ce. "Su Nirash basu san komai ba, yakamata mu taimaka masu, dik wani motsinsu ƴan ta'addan suna gani, kunga sun shirya masu tin ma kafin su zo"......... Vir ne ya ce. "Su Nirash jinin IRON FIST na gudana a jikinsu".

Lion ya ce. "Dik cikinku kada wanda ya kuskura ya taimakawa su Nirash, ku kyalesu, muma a lokacin da muka yi Mission ai bamu san ƴan ta'addan na ganinmu ba, da muka ji wahala ne muka yi experiencing ɗin suna ganinmu har muka nemanwa kanmu mafita, dan haka su Nirash sune magada IRON FIST ko bayan ranmu! Su zasu zauna a kan kujeran da muke, saboda haka babu wanda zai taimaka masu, su yi faɗa su kaɗai, su sha azaba su kaɗai, su kwaci kansu su kaɗai! Su zama mazan gaske".

Vir ya amsa mashi da cewa. "Suna gama wannan Mission ɗinma zamu turasu horon SSO kafin mu basu horon IRON FIST"....... Kai Lion ya jinjina alamar haka ne, dama abin dake ransa kenan, ya sha alwashin mayar da su Leo tamkar su, su zasu zama magadansu!.

Sun jima suna tattaunawa suna tsara yadda zasu ɓullowa wannan al'amari. A can kuma Abba nata shirye-shirye wannan coming Friday nan da kwanaki uku kenan zai ɗaura auren Aryan, Harleen, ko sunƙi ko sunso, haka ko daddyn Noor yaki ko ya so su Aunty Luna sai sun zama surukansa ta karfi da ya ji...... Ni kam zanga yadda za'ayi wannan aure, ga Aryan a nan har Seraphina ɗin ma ya watsar saboda wannan shegiyar zuciyar tasu ta gado, Abba ya ja mana aiki. Shi ma daddyn Noor yana ruwa, ko yaki ko ya so sai ya baiwa Abba auren yaransa, ga kakan Noor ɗan zafin rai shi ma kuma ɗan hau, ni ban san yadda za'a kaya bama a wannan al'amari.

Sai around 1 na rana suka tashi tattaunawar, a nan ne kuma Aryan ya ɗauko wayansa dan ya kira Faryan, sai a lokacin ya tina da Seraphina, siririn tsaki ya ja, ya so sherata amma sai ya ji ba zai iya ba, sonta ya rigada ya mamaye zuciyansa. Su Lion sun miƙe sun nufi room ɗinsu dan wanka da shirin zuwa masallaci, while shi kuma Aryan yana zaune, sun katse video call da suke yi da Vir.

Number ɗinta ya shigar zai danna kira sai ya tina ashe ta fara zuwa school, ɗan dafe kansa ya yi da ya tuna ashe yau bai kaita school ɗin ba, siririn tsaki ya sake ja kafin ya shiga binciken kwanaki biyu me take yi a waya. WhatsApp ɗinta ya fara shiga, dan ya yi connecting da wayansa, dik wani chat ɗinta suna sauƙa a wayansa.

Kunna voice nata ita da Rimsha ya fara yi yana sauraro, wani wajen ya ja dogon tsaki, wani wajen ya haɗe fuska, unexpected ya isa in da Rimsha ke zugata kan ya kyale daddynta ta rungume Uncle Faryan, ai bai san lokacin da ya wastsake ya zabura kamar zai miƙe daga kujerar da yake ba, sai kuma ya koma ya zauna, cigaba da saurara ya yi.

Jin takaici na shirin sanya zuciyarsa fashewa ne yasa ya dakatar da voice ɗin, abin da ya bashi takaici kuma yadda daren jiya Seraphina tai wa Rimsha voice cewa. "Nisha ki faɗawa Uncle Faryan ina son shi, daddy ya daina kulani, tin safe da ya kaini school bai sake zuwa ba, zan yarda da maganarki kawai in kyale daddy in so Uncle Faryan". Ya ALLAH wani irin huci da Aryan ya fara yi, kishin ta motsa.

Fita chat ɗin ya yi, ya shiga chat ɗinta da number Faryan da ya gani. Ai yana shiga ya fara cin karo da kalaman soyayya da Faryan ya dinga tashin kanta da su, ga shi shi kuma ba iya soyayyar nan yai ba.

Ai wani irin zafin kishi ne ta motsa, jikinsa har yana rawa wajen fita ya laluɓo number Faryan, sai dai wayar a kashe ko da ya kira. Da sauri ya miƙe tsaye, har ya manta bai kashe computer ɗinsa ba. Yau ba sauƙa ƙasa, ta sama ya bi zuwa benen Khaiza'ans House.

Yana shigowa ya isko Abba a parlo, bai ko kalli in da Abba yake ba, kun san basa shiri, shi Abba ya ce idan Aryan bai bashi hakuri ya janye kalamansa na ba zai yi auren nan ba, ya kuma yarda ya karɓi auren Aunty Lusi ba to kada ya sake yi mashi magana, shi kuma Aryan taurin kai da zafin zuciya, ga ɗan banzar izza, ya ce ba zai bada hakuri ba, kuma aure ba zai karɓa ba, har da cewa kada Abba ya yi ganganci yin wannan kuskure, dan zai jawa yar mutane wahala ne, dan ya rantse da ALLAH ba zai auri su Luna ba, mutum ɗaya zai aura kuma ita ce Seraphina!

Abba na ganinsa bai ce mashi ko sannu ba, sama Aryan ya haye, kai tsaye ɗakinsu Faryan ya nufa. Nan ya isko Harleen ne kawai a kwance yana latsan waya. Yana ganin Aryan ya zabura ya miƙe zaune tare da haɗe natsuwarsa waje guda.

"Ina Faryan?". Ya faɗa yana ɗaure fuska!"......... "Ya fita, ina ga ya je ɗauko Rimsha daga school ne, dan 1:30 suke tashi, yanzu kuma 1:25"....... Takaici da kishi yasa bai jira dogon jawabin Harleen ba, yana jin Faryan baya nan ya je ɗauko Rimsha yasa kai ya wuce da sauri.

Yana sauƙowa ƙasa Abba ya taresa da cewa. "Ka bani sadakin Vash and Rimsha, Harleen da naka"....... Ɗaure fuska ya yi kafin ya ce. "Zan dai baka sadakin Vash and Harleen, amma nawa kam babu shi!!". Yana kai karshe ya nufi kofa, har zai fita ya sake tsayawa game da cewa. "Zan turo Faryan ya kawo maka sadakin mutum biyun!". Daga haka ya fice abinsa.

Wani irin shu'umin murmushi Abba ya saki, a fili ya ce. "Yaro yaro ne, dani kake zancen, zan yi maganinka ne, saura kwanaki uku".......... Shi kuwa Aryan yana fita school nasu Seraphina ya nufa, gabaɗaya hankalinsa ya tashi, kishin maza ta motsa, jikinsa har wani tsuma yake yi, har ya manta da cewa Abba ya ja ya tsani har Seraphina ɗin ma.

Ko ya zata kaya a wannan school ɗin!. Ga Faryan, ga Uncle, ga daddy Aryan, ni kam na ce akwai tashin nuclear fa!. Muje hospital mu dawo.

---------------🔥

WS-HOSPITAL.

Yau kam 5:28 daidai sister Zinta ta samu isa office na Dr James, a wannan karon ma sister Lazy ta so tsayar da ita, amma sai taki tsayawa, dama kullum idan ta zo sister Lazy ke tsayar da ita, ta sanyata ɓata lokaci sosai a wajen tsaye, sai ta tabbatar ta wuce lokacin da aka buƙaceta sai ta ce to ta shiga.

Yau kam ko da ta zo bata bi ta kan sister Lazy ba, ta wuce ciki, tana jin sister Lazy na kiranta ta yi banza da ita, dan ta yi alkawarin ba zata sake biyewa wata taɓata mashi lokaci ba.

Zaune ta iskosa a saman chair hannunsa rike da cup na coffe yana sha, dik abin da suke yi da sister Lazy kullum yana ganinsu fa, dama ya bari ne yana son Zinta ta fara kwatawa kanta ƴanci, hakika yau ya ji daɗin ganin tadda ta yi banza da sister Lazy, lallai ta fara hawa kan hanya, ta fara zarra ita ma.

Na ce ba mu faɗawa Dr James yana haƙawa kansa rami ne ko dai mu kyalesa? Ya kafe dole sai ya cirewa Zinta dik wani tsoro, mu faɗa mashi ubansa zata ci idan ta daina tsoron kowa ne ko dai mu kyalesa? Mu tina mashi cewa jinin IRON FIST take ne ko dai mu kyale sa? Yanzu yana jin daɗin ta fara kwatawa kanta ƴanci a wajen Lazy, hmmmm gobe kuma sai kanka dan ubanka! Ai in suka gane darling ɗinsu alluran cuta kai mashi ma daga nan zaka ga zarra irinta IRON FIST, dan billahil lazi ba zasu yarda ka kashe wannan yaron ba yadda ya shiga zuƙatansu!.

Tin da ta shigo ya zuba mata idanu, yana kallonta, har ta ƙariso gaban table ɗinsa, daidai lokacin 5:30 daidai ya buga. Tana ƙoƙarin durkutsawa a ƙasa a gaban table ɗin ya miƙa mata hannunsa yana ware tafukansa...... Da sauri ta ɗago da kallonta a kansa, sai ta ga babu alamar wasa a kan face ɗinsa, sake kallon hannun nasa ta yi kafin ta sake kallon fuskansa, ta tsorata sosai, bata ma gane nufinsa sosai ba, ga shi bata ga sakin fuskan da zata tambayi me yake nufi ba.

Jikinta ne ya fara kerman tsoro, idanunta na rawa daga hannunsa zuwa face ɗinsa. Cup ɗin hannunsa ya ɗaura a saman table, ya sanya ɗayan hannunsa yai ƙasa da nose mask dake face ɗinsa, ya ALLAH, ashe haka yake kyakkyawa sosai?.

Zazzaro eyes ɗinta a kan face ɗinsa da kyau ta yi, unexpected ta ga ya kashe mata ido ɗaya, blinking eyes ɗinta sau biyu ta yi dan ta tabbatarwa da kanta abin da take gani, da gaske ne shi ya kashe mata ido.

One side smiling ya sakar mata tare da jinjina mata kai alamar ta zo. Jikinta ya yi sanyi sosai, dik da tana tsananin sonsa, ta jima tana fatan wannan rana ya zo cikin rayuwarta, amma yau da ya zo sai ta tsinci kanta da jin tsoron da shakkar tinkararsa.

Gagara motsawa ta yi, tana jin tamkar mafarki ne kawai. Miƙa hannunsa ya yi, da yake basu da nisa, kama nata hannun ya yi, jawota ya yi ta taho garesa, a saman laps ɗinta ya zaunar da ita. Ai ji ta yi tamkar ba ita ba, tana jin tamkar ba'a duniya take ba, bata yarda gaskiya bace, ta fi yarda mafarki ne.

Hannu yasa ya tattare hair ɗinta zuwa gefe guda, ya kwanto da kansa wajen shoulder ɗinta ta gefen wuyanta, tamkar zai yi mata raɗa a kunne, ya ɗaura ɗayan hannunsa a saman shafaffen cikinta, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Tsorona kika ji ne?".

Wani irin jan numfashi ta yi tare da saukewa a hankali, sai yanzu ta gane ba mafarki bane da ta ji voice ɗinsa a kunnuwanta. Ajiyar zuciya ta kara daukewa tare da ɗan juyo da face ɗinta ta gefen da ya kwantar da kansa, kirjinta na bugawa da karfi, can ƙasa ta ce. "Na ƙasa yarda da gaske ne, ina jin kamar mafarki nike yi".

Sumbatar gefen cheek ɗinta ya yi kafin ya ce. "Ba mafarki bane, bai kamata ki razana ba tin da kin jima kina sona ko?"...... Kai ta jinjina mashi alamar e haka ne........ "Kin shirya rayuwa dani?". Ya faɗa yana shafa mararta zuwa saman cikinta.

Rashin sani ya fi dare duhu, da sauri ta gyaɗa mashi kai cewa ta shirya rayuwa da shi. Juyo da ita da kyau ya yi, ya rungumeta sosai a jininsa, ya ɗan matseta kaɗan, ya ɗago da kai suna fuskantar juna....... "Kin shirya mallaka mun kanki?". Ya sake faɗa can ƙasa.

Nan ma kai ta gyaɗa mashi alamar ta shirya....... "To nuna mun kin shirya ɗin in gani". Yana magana yana moving hand ɗinsa a jikinta, from her back to her neck....... Ɗago idanu ta yi suka kalli juna, ta ɗan turo baki kafin ta ce. "To ka rufe ido"....... Ya ɗan buɗe idanunsa a kanta kaɗan kafin ya ce. "Kina jin kunyata ne?"....... Kai ta jinjina alamar e. One side smiling ya sakar mata kafin ya ce. "Yanzu fa kin zama tawa, shi ne kike kunyata? Ya zakiyi a ranar da zan ce ki mun wanka mu fita office?".

Ya ALLAH bata taɓa expecting jin irin waɗan nan kalamai daga garesa ba, sai ta ji gabaɗaya notikan kanta suna warwarewa, ta kara zaucewa a kansa, dama kenan ya iya soyayya dik wannan tsare gida da iskancin da ya cika mashi ciki, ya ALLAH.

Jin shiru bata amsa shi bane yasa ya ce. "Ki gwada mun kin shirya rayuwa dani ba sai na rufe ido ba"...... Kai ta jinjina, ta sanya hannayenta ta saƙalo wuyansa, sai ta rufe idanunta kafin ta ɗaura soft lips ɗinta a kan nasa. Kissing ɗinsa ta fara yi a hankali.

Yah ALLAH. Ji ya yi gabaɗaya ya bar wannan duniya, hakika yana sonta sosai, irin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login