Showing 165001 words to 168000 words out of 365093 words
ce. "Ta kasuwannin nama masu ɓoyayyen tsari watau wet markets, kasan na tsara cutar ta yadda zata iya ɗaukar makonni biyu a jikin mutum bata nuna ba, so zata iy makonni uku a jikin dabobbi bata nuna ba, dan haka zamu yi amfani da kasuwannin dabbobi, zamu samo kosassun dabbobi mu yi masu alluran cutan sai mu kaisu kasuwannin, mutane zasu sayesu, dik wanda ya ci namansu ya kamu kenan, idan aka yanka dabbar masu saya suka sayi nama shikenan kuma! Dole cutar zata bazu". Ya nisa kafin ya cigaba da cewa.
"Wani abin birgewa kuma a nan shi ne cutar zata bazu a cikin mutane ne ta hanyar airtight aerosol droplets, zata shiga ta hanci ko baki, ta dai hanyar iskar da mai ɗauke da cutar yake fitarwa kamar numfashinsa kenan, dik wanda ya ci namar dabbar a gida idan ya yi numfashi kusa da wani shikenan shi ma zai ɗauki cutar, daga nan cutar zata ratsa jikinsa har ta shiga huhu, a ƙasa da sati biyu zata fara tarwatsa dik wasu kariyar jikinsa".
"Hanya ta biyu da cutar zata shiga shi me ocular membrane, idan mai ɗauke da kwayar cutar ya taɓa idanun wanda bai da shi yakan iya kamuwa shi ma, ta hakan ma ta fi haɗari, dan zata shiga cikin jini ne kai tsaye daga ido".
"Hanya ta uku shi ne cin abinci mai ɗauke da cutar, kamar namar dabbobin da zamu yi wa alluran, ko kayan lambun da zamu yi wa dajuka feshin cutar, muddin mutane basu wanke kayan lambun da gishiri sosai ba tabbas zasu kamu". Ya kai karshen jawabin yana binsu da kallo.
Dr Kamal ne ya ce. "Nice work, amma kuma wani irin illah zasu yi wa ɗan adam baka faɗa mana ba"........ Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da taɓa screen na computer, ya shiga cikin folder ɗin cutar da kyau, take bayanai suka bayana rututu, ƴar sandar dake hannunsa ya gyara tare da fara yi masu nuni da jikin screen ɗin before ya fara bayani.
"Na faɗa maku wannan cutar ta fi COVID-19 haɗari nesa ba kusa ba, cuta ce dake ƙunshe da DNA da RNA a lokaci guda, shi ne illar farko, illa ta biyu cutar tana lalata lungs, tana sa huhu ya cika da ruwa mai guba, wanda ke janyo mutuwa cikin awanni 72, amma kada ku manta na faɗa maku cutar tana ɓuya a jiki ba'a ganeta da wuri, tana kai 2 weeks kafin ta bayyana, a wannan 2 weeks ɗin cutar zata yi yawo a cikin jinin mutum, ta bi ko'ina ta kashe garkuwar jiki a saiɓaɓe, so zata kashe dik wani garkuwar jiki ta yadda idan ta bayyana jikin mutum ba zai karɓi maganin kowani iri ba sai maganin da na kirkiran wa cutar, sannan sai ta bayyana ne take kashewa a awanni 72".
Ya ja numfashi kafin ya cigaba da cewa. "Illah ta biyu da zata yi wa mutum shi ne acute respiratory collapse, ciwon ɗaukewar numfashi mai karfi, sannan ya haifar da zazzaɓi mai zafin gaske, ciwon kai mai tsanani, da ciwuka a fata irin na bullae kuma irin na monkeypox dake fashewa suna zubar da jini, and za'a su haifar da karancin jini da platelets, wanda ke haifar da zubar jini daga hanci, kunne, idanu, da al'aura, dik zasu faru ne idan cutar ta bayyana a jiki, kuma dik zasu faru da mutum ne a ƙasa da waɗan nan 72 hours ɗin".
"Idan mutum yana da sauran kwana a gaba bai mutu a cikin 72 hours ɗin nan ba to fa zai kamu da cerebral infiltration, dan karfinta zai sanya ta shiga blood brain barrier, watau jinin kwakwalwa ta janyo hauka, da kurmancewa". Ya sake sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa. "Mortality wannan cuta ta fi COVID-19 da yawa, saboda zata kashe mutane 40 cikin ɗari 100 na duniya a cikin kwanaki 5 zuwa 7 da bayyanarta idan ba ayi maganinta da gaggawa ba, wanda kuma kun san da cewa maganinta babu wanda ya isa ya yi ta a duniya! Babu mai maganinta sai makirkirinta". Ya kai karshen maganar tare da sakin wani irin one side smiling na zallar mugunta yana wani ɗaure fuska at the same time kaman wani shaiɗani.
Hannu suka ɗaga suka jinjina mashi, sannan Dr Mark ya ce. "Amma kai tsaye me zai sa wannan cuta ta fi COVID-19 da sauran cutukan baya ban tsoro da firgitarwa?".
Bottle water ya wuce cikin freezer ɗinsu ya ɗauko tare da glass cup, wajen ya dawo, saman sofa ya zauna tare da ɓalle bakin robar ruwan, ya daddala a cup, a natse ya kai ɗan bakinsa. Mai ɗan yawa ya sha tare da ajiye cup ɗin, sannan ya miƙe ya koma gaban computer bayan ya ajiye cup ɗin a saman glasa table dake gabansu.
A natse ya ɗaura hannunsa kan screen na computer, ƙasa ya yi da bayanan izuwa kan amsar tambayar Dr Mark. Cikin natsuwa ya fara bayani kamar haka. "Abin da yasa ya fi COVID-19 ban tsoro shi ne yana ɓoyewa a jiki har tsawon sati biyu ba tare da wata alama ba, sannan yana yaɗuwa ne ta cikin iska, ruwa, goganyar fata, ya fi COVID kamuwa da sauri, bugu da kari shi yana kaucewa rigakafi, wato da wuya allurar rigakafi ta yi aiki da sauri saboda canjin DNA na wuce misali da yake da shi, wannan sati biyu da yake yi a ɓoye a jikin mutum yana sanyawa ya lalata garkuwan jiki ta yadda babu wani maganin da jikin zata karɓa face maganin da na basu da kaina, haɗarinta ya zarce tinaninku".
Dr Kamal ne ya katse shi da cewa. "Hope ka shirya maganinta?"...... Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Ka san bama ƙirƙirar cuta haka ba tare da mun shirya mataninta ba"....... Kai 2D suka jinjina mashi kafin su hau zuba mashi jinjinar ban girma da kwarara mashi gwiwa.
A dake ya ce. "Sai duniya ta gigita zamu fitar da even rigakafin cutar, da rigakafin kawai nike son mu tara billiyoyin daloli kafin mu je kan maganin, dan a wannan karon kamar yadda cutar take special haka maganinta yake special, maganin zamu zuba mashi maƙudan kuɗi na wuce misali ta yadda zai sa a rasa rayuka dan ba kowa zai iya mallakar maganin ba". Cike da zallar rashin imani ya kai karshen maganar.
Watau duniya ta zarce yadda dik ɗan adam yake tinani, zasu kirkiri cuta dan raje yawan al'umma kuma dan kasuwanci, domin kuwa suke da riba, ko rigakafin cutar kawai suka fitar a guje za'a bi maganin dan ana tsaka mai wuya, a rigakafin kawai ba karamin kuɗi zasu samu ba, kun ji sun ce sai duniya ta jigata ta rasa madafa zasu saki maganin cutar, hakan ma da mugun tsada zasu saki maganin ta yadda ba kowa zai iya saya ba.
A nan ina da tambaya! Kun taɓa tambayar kanku cewa waɗan nan cututtuka da suke ɓullowa duniya daga ina suke ɓullowa?...... Bayan na gama jin bayanan Dr James na yi wani tinani fa my people, amma bari in barwa zuciyata wannan tinani, ALLAH yasa shiruna ya zame mun alkhairi! Wai ko dai in faɗa ne kawai?........🤔 Amma ku kuma ku faɗa mun bayan kun gama jin wannan bayani na Dr wani tinani kuka yi? Ko dai har yanzu kuna nan jiya iyau? Ba cigaba?
Sai jinjina mashi su Dr Kamal suke yi suna yaba muguntarsa, suna kuma kara mashi kwarin gwiwa. Shi kuwa sai kara jin kansa na kara girma yake yi.
Cikin wani irin murya mai amo ya ce. "A yanzu duniya a tafin hannuna take! Sai yadda na yi da ita! Ni ne Devil wanda da zai yi wa mai gida Dujjal tarba ta ban girma a lokacin da zai iso! Wannan project yakamata na canza mashi suna daga PC izuwa Death is inevitable! Ko kuma a death that wipes out an entire family!!"........ Dr Mark ne ya ce. "Ka barsa a PC ɗin ma ya yi".
(PC yana nufin Population Control, na ji wasunku suna cewa CRYSTAL PALACE ne PC da yake nufi, to ba haka bane, CRYSTAL PALACE fa CP ne ba PC ba kusan ɗaya suke yasa kuka ruɗe)
Dr Mark ne ya ce. "Amma meyasa WS ta hura mana wuta kan mu saki project ɗin nan yanzu? Mun yi da ita ai sai shekaru uku zuwa huɗu gaba, meyasa suka ce lallai mu saketa yazu?".
Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "Kasan a wasu ƙasashen za'a kafa sabuwar gwamnati, ma'ana zaɓe ta ƙarato saura shekara ɗaya da ƴan watanni, sannan kasan akwai manyan ƙasashen da suka gwadawa WS taurin kai, kuma da alama ƙasashen sun tsaya da ƙafafuwansu, suna da karfin tattalin arziki da karfin faɗa aji, sannan da alama suna da power da WS take shakkarsu shiyasa suka buƙaci project ɗin nan dan su gigita kowa, a taƙaice dai gargaɗi mai karfi suke son yi wa duniya, a karkashin ƙasa kuma akwai plan na ruguje ƙasashen da suka kawo karfi suke ganin suna da murya mai karfi, sannan a gefen ƙasashen dake biyayya ga WS kuma su za'a haɗasu da wannan cuta ne domin sabuwar gwamnatin da zasu kafa, a hargitsa ƴan ƙasa ta yadda gwamnatin da ta hau sabuwa ba za'a ga laifinta a farko ba, za'a ce duniya ta shiga rikici, so ko gwamnatin ta yi shekarun mulkinta bata yi wa ƴan ƙasa komai ba za'a ce ai dama wannan balain da ta faru na wannan cuta gwamnatin ba zata iya shawo kan matsalar lokaci guda ba, so kunga a nan dik badakalar da gwamnatin zata yi babu wanda zai mai da hankali ko ya zargesu, daga nan WS zata cinwa abin da take so".
Wannan bayani nasa ya mugun gamsar da su, watau WS basa sakar cuta sai idan za'a samu sabbin gwamnatin dake masu mubaya'a, watau a kowani gwamnati sau ɗaya suke sake cuta ko da wannan gwamnatin zata sake maimaita shekarunta a mulki ba zasu saki wata cuta ba sai idan sabuwar gwamnatin ce zata hau, sannan suna yin hakan kuma dan su ruguje ƙasashen dake ƙoƙarin tasowa! Tab akwai matsala.
Dr Mark zai yi magana suka ji alamar motsi a office na Dr James, Dr Kamal ne ya ce. "Ko su Maya ne?"....... Kai Dr James girgiza kafin ya ce. "Sai dai Lazy"....... Wani irin shu'umin murmushi Dr Mark ya saki kafin ya ce. "Ce mun zaka yi mutuniyarka, James Lazy fa sonka take yi"...... Wani irin ɗaure fuska ya yi kafin ya ce. "Me zan yi da tsohuwar da komanta ya kare? Kada ka manta Lazy ta haura 47 years, surgery ne da magunguna yasa take haka, da kaina in mata surgery ɗin sannan in dawo in kwashi ragowa? Are you out of your sense?!".
Wani irin dariyar mugunta Dr Kamal ya yi kafin ya ce. "Zakuwa ku dace, tana sonka sosai fa, kada ka manta ta yi maka abubuwa da dama a rayuwa, ita ta taimaka maka wajen kawo ƙarshen Muhammad Haiza'an, kada ka manta idan ba da sa hannunta ba baka isa shiga CRYSTAL PALACE har ka sace Muhammad mu yi nasarar cire ƙwaƙwalwansa ba, dan haka Lazy bata cancanci ka ki ta ba". Ya kai karshe yana dariyar shakiyanci da iskanci.
Kara ɗaure fuska Dr James ya yi tare da cewa. "Stop it! Dik abin da Lazy ta yi she did it because of money, na biyata hakkinta sai kuma ta ce zata yi aiki tare damu, tana sha'awar kasancewa tare da mu, na mata adalci na ɗauketa aiki, sai kuma me? Ta ce tana son ai mata surgery a canza mata kamanni kada ƴaƴanta su gane fuskanta zasu kasheta, haka nai mata surgery na canza mata kamanni, daga karshe ma ta gudu ta baro Washington ta dawo nan da zama, dik na karɓeta saboda girman aikin da ta yi mana, kunsan kwakwalwar Muhammad ba wasa ba, na bata aiki a ƙarƙashin office ɗina dik dan in yabawa ƙoƙarinta, dik ban mata adalci ba?".
Hararansa Dr Mark ya yi kafin ya ce. "Ka dai faɗi gaskiya, ba wani dan kayi mata adalci yasa ka ajiyeta a ƙarƙashin office ɗinka, kawai ka ɗauketa ne saboda nufinka a kan ƴaƴa Muhammad, kana son sperm and brain ɗinsu, kuma kasan ita kaɗai zata iya wannan aiki, saboda ita kaɗai tasan ainahin jininsu!".
Hararansu shi ma ya yi kafin ya ce. "Dik da haka dai na yi mata adalci"..... "Kai ku bar tuna mana baya, bamu taɓa aiki mai tsananin wahaka ba irin waɗan nan ayyuka guda biyu". Cewar Dr Kamal.
"Wani aiki kenan?". Dr James ya tambaya. Dr Kamal ya ce. "Aikin ƙwaƙwalwar Muhammad da kuma aikin ƙwaƙwalwa Namjoon, mun wahala a kan ayyuka biyun nan"....... Kai kawai Dr James ya girgiza alamar wahalar ta zarce ayi magana.
WAYE NAMJOON? WANI IRIN AIKIN ƘWAƘWALWA AKA YI MASHI? NASAN KUN GANE WAYE MUHAMMAD KAM AI! WATAU MAHAIFIN SU LION! KENAN A WANNAN HOSPITAL ƊIN AKA CIRE ƘWAƘWALWARSA? LALLAI AKWAI GAGARUMIN MATSALA NA KIN ƘARAWA KUWA!.
Kamar yadda suke zaune suke wannan hira cikin nishaɗi da tsokanar juna haka suma su Maya suke zaune suke hira. Bayin ALLAH kansu ya shiga ruɗani ne, sun shiga tsananin tashin hankali na ganin irin aikin da aka sanyasu, wannan document da aka basu su karanta, jerin sunayen chemicals da ake son su zaƙulo su haɗe masu ne, wani chemical ɗin idan sun haɗa shi da wani sai an barsa ya yi sati biyu ya gama tsumuwa sai a sake suba wani.
Da farko da suka fara aiki ba su damu sosai ba, sai yanzu da aikin ya yi nisa, suna isa kan manya-manyan chemicals masu haɗari kuma masu tsanani a guba shi ne fa hankulansu ya tashi, sun san idan aka haɗa kaza da kaza ga abin da zai haifar, nan fa suka yi mugun gigita, dik sun sha jinin jikinsi.
Sister Maya ta fi tausayi da saurin karaya, cike da tashin hankali ta ce. "Sister Zinta kina ganin me nike gani kuwa? Me kike tinanin zasu yi da wannan abin?"...... Sister Zinta da ta gama shan jinin jikinta ne ta amsa da. "Sister Maya na fara fita a hayyacina ne ko kuwa dai mafarki nike yi? An taɓa haɗa waɗan nan sinadaran waje ɗaya ne? Kisan kai zasu yi ne?".
Dogon numfashi sister Maya ta ja kafin ta ce. "Babban tashin hankalina shi ne waɗan nan sinadaran da muƙa haɗa waje guda, kamar Dimethylmercury CHH, kin sani, sinadari ne dake shiga jiki a hankali ba tare da nuna alamu ba, sai daga baya ya haifar da matsalolin fata, kumburi, da raunuka masu wari, kuraje masu fashewa su fitar da jini, amfani da shi yana da matuƙar hatsari!"
Ta ja numfashi kafin ta cigaba da cewa. "Ga kuma sinadarin cantharidin CHO, sinadarin da ake samu daga wasu kwari masu haɗari, yana sa kuraje su kumbura su fashe su fitar da ruwa wani lokaci kuma har jini suna yi. Ga kuma sinadarin ricin CHNO, sinadarin dake haddasa kumburi da kuraje masu zafi sosai. Hallau ga arsenic trioxide AsO, sinadarin dake sa mutum jin daɗi rayuwa a farko, amma daga baya yana haddasa cututtuka na fata, kumburi, da kuraje masu wari. Dik da wanna suka sake cewa mu zuba thallium sulfate TlSO a ciki, mugun sinadarin dake haddasa matsalolin fata da kumburi ba tare da an yi saurin gano shi ba". Ta kai karshe tamkar zata yi kuka, dik da basu san me za'ayi da waɗan nan sinadaran ba tabbas sun gigita da haɗawa, suna jin kuma tamkar ba zasu iya cigaba da haɗawa ba.
Na ce kun tuna cewa da Dr James yana gabar da project ɗinsa, a abubuwan da ya kirga cutar take haifarwa har da kuraje masu fashewa su yi jini? Nasan yanzu kun gane daga wani sinadari aka samu wannan, sannan ya ce ciwon yana shiga ne a hankali, yana ɓuya na sati biyu kafin ya bayyana a jiki, kenan kunga irin sinadaran da aka zuba mashi yasa zai ɓuya a jiki na tsawon sati biyu, lallai akwai matsala, mu leƙa CRYSTAL PALACE mu dawo.
CRYSTAL PALACE.
Shirye suke cikin tsadaddun tail coat masu bala'in kyau launin dark blue watau navy da ya yi masifar fito da tsantsar kyansu, ku hasko fararen fata a cikin navy blue ya zasu kasance?.
Musamman Aryan and Lion da suka cire face mask ɗin fuskansu a yau suna karisa shiryawa, barema Lion da ya fito daga Pamira blood, hasken irin pure white ɗin nan ne mai balain kyau.
Ya ilahi, tamkar ka samu waje ka zauna ne ka yi ta faman kallonsu kawai kada ka ɗauke idanu, idan kuka kalli lips ɗin Lion oooooo, ya ALLAH, zaku zaci ya sanya pink janbaki ne, ya ciza kala sosai yana wani irin kyalli, hakama lips na Aryan, bakin Lion irin round lips ɗin na ne mai masifar kyau, ga shi ɗan karami, lipa ɗinsa suna da ɗan cika daidai masha ALLAH. This two guy complete face ɗinsu ya haɗu, ga sexy gorgeous body, a gaskiya Lion yana kama da Leo sosai, kamar an tsaga kara, hatta hair ɗinsu golden white dake ta faman sheƙi kamar gold idan ya ji gyara, ya ALLAH, na sake cewa ya ALLAH.
Na Lion ya sha kitso kalba a wajen Aryan, ya ɗaure mashi gashin nasa yai mashi tuntu da jelar, kitson tai masifar kara mashi kyau na gasken-gaske. Shi kuwa Aryan arabs hair garesa, kada ku manta shi bakuraishe ne, gashinsa irin dark blue ɗin nan mai sheki wanda zaku zaci ma baki ne in baku kallah sosai ba, gashin ɗan daidai ne a kan nasa, bata wuci zuwa bayan wuyansa ba, yadda dai gashin larabawa yake, yana kwance luff yana wani irin sheƙi, ga wasu gajeru guda biyu da suka zubo mashi ta gaban goshi sun yi nannaɗa sosai, while na bayan kuma suna kwance kuff sun yi bayan wuyansa. Ya ALLAH idan kuka ga Aryan ko, yadda yai gyaran gashinsa tamkar shararren ɗan soyayya, ga dikkan alamu yana cikin soyayya!.
Shi kuwa guru ba zan ce komai a kansa ba saboda yana sanye da nose mask, yana zaune gefen bed rike da waya yana latsawa.......... Bayan Aryan ya bar wajen Seraphina ya fita