Showing 198001 words to 201000 words out of 365093 words
my goals, but one day one time".
Dr Kamal ya karisar mashi da. "The game will be over"........ Shiru ya ɗan yi tare da mayar da hankali kan rubuce-rubucen da yake yi. Bayan ya kammala ya cire wasu fareren takarda guda biyu. A saman keyboard laptop dake gabansa ya ɗaura su, sannan ya ɗauki table phone ɗinsa, sister Lazy ya dannawa kira.
Bugu ɗaya ta ɗauka tana wani karya murya. "Jeki turo mun Maya da Zinta". Ya faɗa ba tare da jiran amsarta ba ya katse kiran. Takaici tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu, wani irin dogon tsaki ta ja tare da miƙewa tsaye. Fuuuu ta fita tana wani huci tamkar zata kama da wuta.
Kai tsaye SECTION C ta nufa, yau suka kammala aikin haɗa chemicals da aka rubuta masu a document ɗin, dik sun gama haɗawa, a yau suka koma ainahin office ɗinsu sai ga sabon sammaci, ko hutawa bai bari sun yi ba.
Sai da Lazy ta zagesu fes kafin ta ce su wuce 3D na kiransu. Da sauri suka miƙe, dama kiran suke jira, sun kammala aiki suna jiran su ji result ɗinsu. Sai masifa sister Lazy ke zazzaga masu, amma basu wani damu ba. Suka bi bayanta, a office ɗinta ta tsaya tare da ce masu su wuce ciki.
Da sauri suka shige ciki suna dafe kirjinsu dake bugawa da karfi. Tin da suka shigo ta ƙasar ido Dr James ya fara satar kallonsu har suka iso in da yake, har ƙasa suka durkusa suka ɗaga masu gaisuwa.
Basu amsa ba, cike da bada umarni Dr James ya miƙo masu paper ɗin tare da cewa su yi sign. Jikinsu na rawa suka miƙe suka fara sign da pen ɗin da ya basu. Sai da suka yi sign ɗin suka gama sannan ya miƙe tare da ce masu su ɗauki paper ɗin su biyosa.
Ya faɗa tare da wucewa gaba, da sauri kowacce ta ɗauki nata paper ɗin suka rufa mashi baya. Miƙewa Dr Kamal ya yi ya rufa masu baya yana cigaba da yaba kyau irin na jinin Muhammad, yaran sun haɗu, a cikin ransa ya ce. "Gaskiya karshen Muhammad bai yi kyau ba! Ya yi mana aiki cikin ruwan sanyi yaki, ga shi ya jawa kansa, mun saka shi yin aiki dole, mun kashe banza, mun kuma cire abin da yake taƙama da shi, sannan yau in mun ga dama zamu sake kyankyasan Muhammad sabo tin da muna da spem ɗinsa, mun kashesa kuma muna shirin mallakan ƴaƴansa, su haifa mana masu irin ƙwaƙwalwar tasa, ya zo a banza kuma ya koma a banza, ja da 3D baa haifi mai yin wannan ba!! Mutuwa da kanta tsoron 3D take ji bare ɗan adam".
Ni kam na ce mu faɗawa Dr Kamal cewa IRON FIST jinin daddy Muhammad ɗin ne ko kuma dai mu yi shiru su faɗa mashi? Mu faɗa mashi Lion watau Zayra'an first born of daddy Muhammad yana numfashi a doran duniya ne ko mu yi shiru? Na ce mu faɗa mashi daddy Muhammad ba zai mutu a banza bane ko dai mu yi shiru? Na sake cewa mu faɗa mashi cewa Lion shi kaɗai gayyace, shi kaɗai bataliyar runduna guda ne ko kuma dai mu yi shiru? Na sake cewa mu faɗa mashi Lion ya dame daddy Muhammad a dik abin da suke zato ne ko kuma mu yi shiru?.
To ku ba don abubuwa da suka sha kan IRON FIST ba kuna tinanin izuwa yanzu ba zasu zaƙulo 3D bane? Abubuwa sun masu yawa, ba ƙasa ɗaya ba, suna cikin ƙoƙarin warware wannan basu gama ba wata ta kunno masu kai, amma very soon zasu samu natsuwa, zasu juyo ta kanku ne! Kuna ganin kamar ba wanda zai iya zaƙuloku, to sai dai idan ba jinin daddy Muhammad ba!!
Kai tsaye cikin SECTION D Dr James ya shiga, su Maya na biye da shi. Ɗakin da babys ɗin suke ya shiga da su. Tin daga bakin kofa suke jiyo kukan wannan baby mai kama da Seraphina namu, hakan yasa da Dr James ya shiga ya umarci a miƙo mashi yaron. Da sauri nurse dake rike da babyn ta kawo mashi shi.
Maya tsabar son yara har ta kai hannu zata karɓesa, tamkar zata kwacesa ma, ta manta cewa 3D ne ya ce a miƙo mashi shi. Karɓarsa Dr James ya yi tare da ɗagasa kaɗan yana kallon babyn. Da ya haɗa ido da babyn sai da ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya yi tinanin saboda violet eyes na yaron ne yasa ya ji hakan.
A saman shoulder ɗinsa ya saɓa babyn tare da kallon nurses da suka zube gwiwowinsu a ƙasa suna zuba masu gaisuwa....... "Dik ku kwashi komai naku ku koma hostel ɗinku, daga yau aikinku ya kare a nan". Cewar Dr James.
Dik da suna son sanin meyasa, amma basu yi gigin tambaya ba, saboda babu fuska. A hanzarce suka kwashe komai, da sauri suka fice. Zinta da Maya sai kallon babys ɗin suke yi suna jin tamkar su je da gudu su rurrugumi babys ɗin. Amma babu dama, sun natsu saboda 3D dake wajen.
"Daga yau ku zaku dawo kula da wannan sashe, zan turo nurse ɗaya ta faɗa maku yadda zaku kula da babys ɗin"........ Cike da mamaki Dr Kamal ya ce. "Su biyu kacal? Babys ɗin sun yi yawa ai"......... A dake ya ce. "To aikin me suke yi? Sai su wuni aikin babys ɗin! Dama ban kawosu nan dan su huta ba!". Babban magana, ta ya za'ayi su iya kula da babys guda 55 su biyu kawai? Kuma ba wai sun iya bane, hasalima basu taɓa koda rike baby ba sai yau zasu fara, amma da yake basu san wahalar aikin ba sai daɗi kamar ya kashesu suke ji, har da murmushi.
Miƙawa Zinta babyn hannunsa ya yi yana faɗin. "Kada ki bari ya sake yin kuka!". Tin da ya karɓi babyn yaron ya yi tsit...... Jikinta na kerma ta miƙa hannu zata karɓesa, a lokacin da hannunta ya haɗu da na Dr sai da ta ji wani irin narkakken kaunansa ya ratsa mata zuciya, take ta ji ta kara tsananin son shi. Shi ma wani irin spark ya ji zuciyansa ta yi, amma ya ɗauke kai tare da sake mata babyn.
A natse ya juya ya fita ya barsu tsaye kamar wasu dolaye, bayansa Dr Kamal ya bi yana waigo Maya dake ta faman sakin cool smiling tana leƙa fuskan babyn da Zinta ta rike, basu iya rike baby ɗin sosai ba, sun lankwasa mashi wuya kaɗan.
Suna fita sister Maya ta ce. "Sister Zinta kina ga babys dayawa, to yaran waye? Ko dai a nan sister Lazy ta ɗauko wancan babyn dama? Yanzu kullum zamu kasance da babys ɗin nan? Wayyo daɗi". A kiɗime take magana tana zaro idanu, irin she was so surprised na ganin yaran.
Murmshi tamkar bakinta ba zai rufu ba, da gudu ta nufi wajen sauran babys ɗin, ta zama tamkar zarariya, tana ganinsu tana murmushi, sai tattaɓasu take yi tana tsalle, dik yaran suna ta wasa na ɗaga kafafu da hannaye, gwanin burgewa, yarinyar nan Maya dik kiɗime ta zauce a kan yaran nan.
Ita kuwa Zinta sai faman jijjiga babyn hannunta take yi amma yaki yin shiru, Dr James na bata shi ya fara kukan again, yana ta irin feket-feket kamar yana son yin kukan mai karfin nam, baiwar ALLAH bata taɓa aikin yara ba sai yau, ta ma rasa me zata yi mashi ya yi shiru, sai cewa take yi sorry my baby. Amma ina babu alamar zai natsun nan fa.
Kafin ta farga ya fashe da kuka mai sauti, hakan ya jawo hankalin Maya a kanta, idanun Zinta ne ya cicciko da kwallah wai babyn yaki ya yi shiru, har ta gaji, kuma tausayinsa take ji, bata son ya yi kuka.
Da gudu Maya ta dawo gareta, a gabanta ta tsaya tare da miƙa hannu ta karɓi yaron, haka kawai suka ji wani irin tsananin kaunar yaron, sai suke jin tamkar jininsu ne koma ɗan cikinsu, har cikin ransu suka jisa.
Rungumesa sister Maya ta yi a kirnjinta, ta fara jijjigasa, amma yaki yin shiru. Hakan yasa ta ɗan yi ƙasa da shi, ta haɗe fuskokinsu, tongue ɗinta ta zura mashi a baki. Ai da sauri ya capke ya fara tsotsa tare da yin tsit.
Aikuwa Maya sai ta hau tuttula mashi yawonta a baki, shi kuwa yana tsotsan harshenta yana shan yawun nata. Tsalle sister Zinta ta yi, tana farinciki wai sun samo hanyar saka babyn yin shiru, kullum idan yaron ya yi kuka haka zasu dinga yi mashi. Wlh kan ka ce me yaron nan barci ta ɗaukesa, da alama shi nonon uwa na gaske yake so ba madara ba.
Ganin ya yi barci ne yasa ta zame tongue ɗinta a hankali, ta saɓa shi a saman shoulder ɗinta, can ƙasa ta ce. "Ina zan kwantar da shi?"..... Nan sister Zinta ta fara rarraba idanu, can ta hango gadon da yake empty, a nan ta gane ga wajensa, ta ce su kai shi wajen.
A hankali sister Maya ta nufi wajen da shi. Kwantar da shi ta yi, suka zazzauna a gefen gadajen masu kula da babys ɗin, suna shirin fara yin magan kenan sai ga wata nurse ta shigo. Da ido suka bita, har katsa ta durkutsa ta gaishesu kafin ta faɗa masu ita ce wacce aka ce ta zo ta koya masu kula da babys for two days.
Fuska ba yabo ba fallasa suka tarbeta tare da bata wajen zama, daga nan ta hau yi masu bayani, suka kasa kunne suna saurara, sai murna suke yi sun samu yara. ME KUKE TINANIN ZAI FARU JAMA'A?.
A ɓangarensu 3D kuwa, wannan meeting room ɗin nasu suka shiga. A saman sofa suka zauna tare da kunna wannan makekiyar computer dake a gabansu, wasu lambobin Dr James ya shigar, take ya danna call.
3 times ya yi ringing sai duhu ya baibaye computer, after 3 seconds sai wasu mutane suka bayyana a gaban screen ɗin. Fararen mutane ne tas, suna sanye da rawani irin yadda larabawa ke sanyawa, kuma suna sanye da thobe a jikinsu, while sun naɗe fuskokinsu da rawanin wanda yasa idanunsu kawai ake iya gani, idanun nasu farare tas da shi.
Mutane uku ne, kuma da alama manyan mutane ne sosai, dan tin daga kan yanayin shigarsu, yadda suke a natse, amma bayan su na zaka iya gano komai dake bayansu ba sai haske kamar kantarki.
Ɗan gyaran murya Dr James ya yi kafin ya ce. "Hope Mark ya iso ku?"..... Ɗaya na tsakiyan ne ya amsa da. "Ya iso mu, mun karɓi saƙo kuma muna godiya matuƙa, kuma zaku ga saƙonku yanzu". Jinjina kai Dr James ya yi. Da rufe bakinsu bai kai mintina biyu na sai computer ta yi ƙara. Yana zubawa alert ne ya shiga babban account ɗinsu na hospital ɗin wanda su dikka suke amfani da shi.
Kimani dala miliyan 200 ne ya shiga cikin account ɗin. Hannu Dr James ya ɗaga ya jinjina masu alamar komai ya tafi daidai. Kai suma suka jinjina kafin na gefe ya ce. "A gaskiya waɗan nan kaya suna mana kaɗan, bamu ki kowani shekara mu dinga samun jarirai 500 ba, ku kara kokartawa". Cikin harshen turanci suke magana.
Kai kawai Dr James ya jinjina masu alamar ya ji, daga haka suka yanke kiran. Suna yankewa sai ga wata kira ta shigo. Ɗaukar kiran ya yi, wasu mutane ne suma su biyu zaune a saman kujera, amma suma baka iya ganin background ɗinsu, suma dai fuskokinsu a rufe yadda zasu san ba aikin ALLAH suke yi ba.
Dr Kamal ne ya ce. "Meke da akwai?"...... Ɗaya daga cikin mutanen ne ya amsa da. "Kaya muke so kimanin 300 a wannan shekara"..... "Zan iya". Shi ne abin da Dr James ya faɗa kawai kafin yasa hannu ya katse kiran nasu, sannan ya shigar da sunansu a list na masu son jarirai shekaran nan...... Ya rab, wai rai ne ake cikinsa yadda kuka san ana cinikin kayan sawa? Tambaya wai me ake yi da jariran ne? Uhm zan warware komai In Sha ALLAH.
Yana katse kiran ya zauna tare da cewa Dr Kamal. "Yakamata ace izuwa yanzu dik shekara muna kyankyasan 1000, 150 zuwa 200 ya yi kaɗan, mu kanmu a nan muna da buƙatar guda 300 a kowani shekara, amma ka duba guda 55 kawai muka barwa kanmu, abin ya yi kaɗan".
Jinjina kai Dr Kamal ya yi game da cewa. "Haka ne, matsalar mahaifar ce, yakamata mu kara mayar da himma, idan ta kama mu kara masu kuɗi mu koma saya 100 million dan mu samu sosai, yanzu mahaifareda muke da shi a ƙasa dik bai wuci 200 ba fa"...... Shiru Dr James ya yi, nazari ya fara yi kan yadda zasu bi ko ta halin ƙaƙa su samo mahaifa, ya ci alwashin kyankyashe jarirai 1000 a wannan shekara mai zuwa..
ALLAH sarki ƴan matan da ake cirewa kwai sun shiga uku, yanzu za'a haka takurawa eggs ɗinsu, zasu sake matsawa jikinsu da magunguna dan su dinga sakar masu kyau sasai, imagine ƴan mata guda 50 ne zasu bada eggs guda 1000, ya ALLAH waɗan nan yara sun shiga uku, wannan azzalumin Dr James ɗin yanzu zai yi ta danƙara masu allurai da magunguna, dole kowani wata jikinsu ya bada kwai sama da guda 10 zuwa 20, innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Wlh da wannan shegiyar tiyatar da ake masu, a zura masu karfe a gaba a zuƙo kwayayyen ma ai kawai balai ne, bare magungunan da ake ɗirka masu, wannan tiyata ta fi komai wahalar da su, imagine karfe a gabanka, a zura har cikin cikinka, har wajen mahaifarka, a zuƙo ruwan eggs ɗinka, kai ya ALLAH ka tsaremu, ALLAH dik yadda zamani zata juya ALLAH ka taimaka mana ka barmu da imaninmu, kasa mu fi karfin suƙatanmu.
Dr Kamal ne ya ce. "Bari ma in kira waɗan da muka bawa contracts na nemo mahaifar mu ji, shin guda nawa aka samo?"...... Jinjina kai kawai Dr James ya yi, tare da jingina da jikin sofar ya shiga tsara irin yadda zai takurawa jikin ƴan matan nan su bashi eggs guda 1000 a ƙasa da watanni biyu, innallilahi wa inna ilaihir rajiun.
Jama'a zaku yi mamaki idan na ce maku wannan computer da ake hada-hada da shi, ake saye da sayarwa daga ƙasashe da dama ta cikinsa, zaku yi mamaki idan na ce maku lallai mallakin daddyn Lion ne, da wannan computer ake iya buɗe dik wasu mataƙan tsaron hospital ɗin nan, da wannan computer ake juya dik wasu abubuwa, komai a kanta yake, dik wasu bayanai da abokan cinikayya, dik wata ɓarn da komai, tana da mahaukatan matakan tsaro wan daddynsu Lion da kansa ya sanya mata, baka isa bibiyar na'urar ba, kuma baka isa iya buɗeta ba, da karfin tsiya suka kwaceta daga hannunsa bayan sun sacesa, suka ɗauko har da Computer!.
Shi ma Dr Kamal bayan ya gama kiran dik waɗan da suka baiwa contracts kan samo mahaifar mata, ya ji guda nawa aka samu, sai ya sanar da su yanzu ba 80 million zasu saya mahaifar ba, sun ƙara ya zama 100, a nemo masu kawai, yana gama basu bayani shi ma ya jingina da jinin sofa ya hau tunanin yadda zai angwance da Maya.
A can Avaris kuwa dik ya haukata likitoci suna ta faman sace mahaifar bayin ALLAHN da basu ji ba basu gani ba, sun ji karin kuɗi, gari ya fara rikiciwa, kowacce mace ta zo asibiti ace mahaifarta ya lalace sai cirewa, wasu masu ciki ace ba zasu iya haihuwa da kansu ba sai aiki, daga yi masu aiki a sace mahaifa.
Yanzu ta kowani asibiti a faɗin Avaris halin da ake ciki kenan, magana har ta fara yawa, dan har IRON FIST sun fara jin kishin-kishin ɗin maganar, amma da yake akwai wani babban aiki a gabansu sai basu mayar da hankali a kan wancan batu sosai ba.
CRYSTAL PALACE.🔥
Lokacin da Aryan ya koma sai ya isko Lion cikin wata shiga ta alfarma, wani irin tsadaddun tail coat fari tas yasa mai kwalliyar zubin na sarauta, tin daga kan cover shoe dake kafarsa zaku san waje na musamman zai je. Ya cire bandejin dake forehead ɗinsa, amma bai cire na hannunsa ba, saboda ya fi jin ciwo a hannun nasa, na kai kaɗan ne.
Sai tashin fitinannen kamshi yake yi. Cikin zolaya Aryan ya ce. "Yau mai girma granny zata yi babban bako kenan?"........ Guru dake zaune yana dannar waya ne ya amsa da. "Zaka bisa ne?"....... Da sauri Aryan ya girgiza kai yana faɗin. "Tab! Zuwa RING OF POWER ai sai shi ɗin! Mutanen da in sun gammu tamkar su zare mana ranmu, dan dai kawai ba yadda suka iya damu ne". Ya kai karshe tare da wucewa ciki, saboda ya tina baya, da alamar sosuwar rai a kan fuskansa.
Guru ne ya ce. "Let me see him"..... Lion dai bai ce komai ba, ya ɗauki wayansa ya fito waje. Kai tsaye sama ya haye, sai wajen sauƙar private jet ɗinsu, sai tashin kamshi yake yi, yau fuskansa ta banbanta da kowacce rana, yana ɗaure tamau tamkar hadari, idanunsa sun nuna alamar yau babu mutunci.
Jiga-jigan guards 8 ne a saman wajen su ke kewaye da jet ɗin, dikkansu cikin bakaken suit masu balain tsada, babu alamar wasa a kan fuskan kowannensu. A tsakiyar wajen ya tsaya, sai kuma ya juyo baya. Yana juyowa guru da Aryan suka zo suka yi hugging ɗinsa, rungumesu shi ma ya yi, still bai yi magana ba, babu ma alamar zai motsa kyawawan laɓɓan nasa.
Sun ɗauki 5 mins a haka kafin ya sakesu ya nufi cikin jet ɗin nasu. Cikin zafin jini guards ɗin suka take mashi baya izuwa cikin jirgin, sai da ya shiga ya zauna sannan guards biyar suka shiga tare da shi. Kansa a ƙasa yana kallon wayarsa, amma a zahiri su Aryan yake kallo, yana mugun son mutane biyun nan, a duniya a yanzu dai wlh daga Leo ɗinsa sai su yake so, kai baya ma iya banbanta su ya fi so ko Leo.
Idan baku manta ba a farkon littafin nan na faɗa maku Leo yana da kaka, amma kakan nasu basa tare da su? To