Showing 336001 words to 339000 words out of 365093 words

Chapter 113 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5932

nan zuwa, zan yi maganinki ne.

A fili kuma ya nuna mata wajen zama kan ta zauna. Ba musu ta zauna saman dutsen dake kusa da shi, kamshin jikinsa ta shaƙa game da ɗan lumshe idanu kafin ta ce. "Sir gani nan"....... "Daga yau tare zamu fara aiki, bana son wasa kuma bana son ɓata lokaci, ki mai da hankalinki sosai kan aiki, anjuma by 9 na dare zamu fara aikin". Cewarsa kenan.

Haba wani irin musulmin daɗi ne ya rufeta, sai ta manta da cewa oganta ne, da sauri ta juyo ta yi hugging ɗinsa tana murmushi......... Ai a miliyan sojojin dake tsaronsa suka yi ƙasa da kai suna ɗan murmushi. Shi kam Vash ji ya yi tamkar baya duniyar ƙasa, musamman yadda yaji kirjinta a jikinsa.

Bai san lokacin da ya sauke dogon ajiyar zuciya ba, ya ji tamkar yasa hannu ya rungumeta shi ma, amma ya yi dauriyar rike kansa. Slowly ya ɗan rabata da jikinsa kafin ya ce. "Jeki kawo laptop ɗinki". Da kyar ya faɗa saboda an kashe bakinsa. Miƙewa ta yi ta nufi sansanin nasu.

Slowly ya juyo da kallonsa ya bita da ido, yana jin ba zai iya jurar ganinta ba tare da shiga irin na larabawa ta rufe mashi property ɗinsa ba, ba zai iya dik in da ta wuce sojojinsu suna kallonta ba, ya manta ba musulma bace, kishi ta rufe mashi ido.

Sai da ta kurewa ganinsa ya sauke dogon ajiyar zuciya game da dawo da kallonsa a kan sojojinsu, yaga sun yi ƙasa da kai kamar masu ɗaukar karatun Alkur'ani a majalisar karatu. Ɗauke kallonsa daga kansu ya yi ya mayar cikin tekun nan, yana kallon jiragen ruwa na shawagi a can nesa sosai.

CRYSTAL PALACE.

KHAIZA'ANS HOUSE.

Tamkar Rimsha zata yi kuka ta ce. "My girl ina cikin damuwa matuƙa, please ki faɗa mun ya zan yi?"....... Hannayenta Seraphina ta riko, cike da tsantsar kaunarta ta ce. "Sis, ki natsar da hankalinki waje guda, tin da har zuciyarki bata tsani Uncle Aryan ba to tabbatas zaki iya canza shi, ki yarda dani".

Wani irin zazzaro idanu Rimsha ta yi. "Kin san me kike faɗe kuwa my girl?". A tsorace ta yi maganar..... Kai Seraphina ta jinjina kafin ta ce. "Nasan me nike faɗe, ki natsu my sis, ki saurareni"..

Ba dan zata iya ɗaukar shawarin nata ba ta natsu game da bata hankalinta. Cike da kulawa Seraphina ta ce. "Ina uncle ɗin naki yake?"....... "Tin ranar Friday ban sake sanya shi a idanuna ba, ya fita cikin fushi dan ya ce baya sona". A marairaice tamkar zata sa kuka ta faɗa.

"Yanzu in ce gidansa za'a kaiki ko?"...... Kai ta ɗan jinjina kafin ta ce. "Abba ya ce ya ɗaukeni ya mayar dani gidansa, ban sani ba ko zai mayar dani"..... "Good". Seraphina ta faɗa kafin ta ce. "Ina fatan ya mayar dake gidansa, sis zamu yi nasara, tabbas uncle sai ya zama namu, trust me, zaki mallaki zuciyansa ko yaki ko ya so, ki shirya faɗa domin samawa kanki ƴanci, ki ganki mana, mace kyakkyawa, ga diri, ga komai, tabbas zaki iya samun zuciyansa cikin ƙanƙanin lokaci". With her full confidence ta faɗa.

Shiru Rimsha ta ɗan yi, sai take jin tamkar zata iya, sai take ganin kamar zata iya kallon face ɗinsa yanzu, zata iya yi mashi magana, bata taɓa yi mashi magana ba, bata taɓa kallon fuskansa da kyau ba, sai dai a sace ta window take kallonsa, ko in baya ganinta, magana wannan baya haɗasu, tsoronsa da take ji ya zarce yadda kuke tinani, amma yanzu tana jin kamar zata iya kiran sunansa a gabansa ta mashi magana, kalaman Seraphins sun ɗan shiga kanta sun hura mata kai.

Seraphina kuwa ta dage sai bata shawari take yi, ta dinga tunatar da ita littafin da suka karanta, yadda ake sace zuciyan namiji, dik Rimsha ta san komai, amma tsoron Aryan yasa ta mance komai. Sosai yau Seraphina ta sanyata gaba da shawari masu harfin da tasa ta fara jin kamar zata iya samun kan Aryan.

Sun jima suna hira har kusan mangrib, sannan suka sauƙo suka yi lunch a tare, suna kammala cin abincin sai ga message ɗin Aryan na cewa. "Yanzu ki dawo gida ina jiranki"....... Ai take hankalinta ya koma can, bare ma da ya ce yana jiranta, dik sai ta ji tana son ganin kanta a gida.

A gurguje ta miƙe tana sanar da Rimsha daddynta na jiranta, basu so rabuwa ba, amma haka suka hakura, Rimsha ta rakota main parlo tana cigaba da mata magiyar ta ɗan kara ko awa ɗaya mana, Seraphina ta ce. "My sis idan daddy ya yi kira zuciyata bata iya jira har sai na je na gansa, yana fa gida yana jirana, ki bari gobe ai zamu haɗe a school".

Dukan wasa Rimsha ta kai mata a baya tana faɗin. "Mara kunya, kalleta a wajen, ko kunyata baki ji kike rawan jiki kansa, wai ni me kika yi wa daddyn nan ne da ya mutu a kanki haka? Kullum yana gida tare dake". Cikin zolaya ta yi maganar tana murmushin da ya jima irinsa bai samu gurbi a zuciyata ba..... "Ai daddy ban yi mashi komai bama tukun nan, kin san yana taka mun burki, yana ɗan hanani wai sai mun yi aure, kin san me?". Ta faɗa tare da tsayawa a tsakiyar staircase na sauƙowa ƙasa.

Kai Rimsha ta girgiza alamar a'a bata sani ba. Cigaba Seraphina ta yi da cewa. "Daddy yana hanani nuna mashi love mai kyau sosai, ya ce sai mun yi aure, idan muka yi aure ko, daddy ba zai yarda ko waje ne ya fita ba, kullum zai zama yana gida manne dani, zan narka zuciyansa da soyayya"........ Shiru Rimsha ta ɗan yi, a cikin ranta ta ce ina ma ace ta samu mai sonta sosai, wanda take so sosai ita ma, wanda zata zautar da shi da wannan tarin soyayya da ta iya, ta narka zuciyansa da kaunarta, ta mallaka mashi kanta. Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "ALLAH ya nuna mun aurenki da wannan daddyn dai kowa ya huta tin da kinki uncle Faryan ɗina, nima ki tayani da addu'ar ALLAH yasa uncle Aryan ya sakeni in samu wanda yake sona nike son shi, wanda zan zuba mashi dik wata soyayya da na iya, in zautar da shi da kaunata". Tamkar zata sa kuka ta kai karshen maganar

Dafa shoulder ɗinta Seraphina ta yi. "In Sha ALLAH my sister da uncle Aryan ɗinki zaki yi dik wannan kamar yadda nima da daddyna zan yi hakan, uncle Aryan zai soki, zai ƙaunaceki, zai zauce a kanki kamar yadda daddy ya mun, ki ɗauki shawarina da na baki please, zamu dace".

Kai kawai Rimsha ta jinjina, ita kaɗai tasan me a ranta, ita kaɗai tasan waye Aryan. Hannunta Seraphina ta ja tana faɗin. "Zo mu je ki rakani ni kam, daddy na jirana". Ta jata suka sauƙo ƙasa. Babu kowa a parlo sai Abba dake zaune saman sofa yana rike da sandarsa.

Cikin girmamawa Seraphina ta ce. "Abba zan koma"........ Kai ya jinjina mata. "Okey ki gaida gida sai na zo, ki faɗawa iyayenki fa ina nan zuwa mu gaisa".

Da okey ta amsa mashi, har zata fita ya kirata, kyautar wani kyakkyawan zobe ya bata yana faɗin. "First gift from your father in-law"........... Ni kam na ce Abba ya faɗi daidai, aikuwa shi father in-law ɗinta ne amma ta ɓangaren daddy Aryan namu ba.

Karɓa ta yi, diamond ring ne mai bala'in tsada, ta ji daɗi, a tsakiyar yatsanta ta sanya tana mashi godiya, yana kallonta ya ce. "Kin dace da ɗana sosai"..... Ita kam murmushi kawai ta yi game da wucewa tana kara yi mashi godiya.

A kofar parlo Rimsha ta tsaya suka ƙara yin sallama, sannan ta koma ciki Seraphina ya wuce, ko da ta dawo cikin parlo Abba baya nan, ta wuce room ɗinsa dan shirin zuwa masallaci. Sama ta haura ta nufi ɗakinta dan yin wanka ta yi sallar magrib

Benensu kai tsaye Seraphina ta wuce tana sauri sosai. Tana shigowa ta isko Madam a parlo. Oyoyo ta yi wa Madam game da zuwa ta rungumeta tana murmushi. Murmushi Madam ma ta yi tana faɗin. "An dawo?". Kai ta jinjina alamar kafin ta sake Madam ta miƙe da sauri ta nufi ɗaki tana faɗin. "Daddy na jirana".

Da kallo Madam ta bita tana murmushi. Tsayawa ta yi a kofar ɗakin ta yi sallama saboda ya hanata shigowa babu sallama dik da take ba musulma ba. Bata jira ya amsa ba ta faɗo cikin ɗakin.

Yana kwance a kan gado yana waya da guru dake ce mashi ya yi maza ya zo su yi shirin zuwa masallaci, shi kuwa ya ce yana ɗakin matarsa idan guru ya isa ya zo ya fito da shi.

Da gudu ta haye gadon tana faɗin. "Na yi missing ɗinka over my gentle chaos". Ta faɗa game da manna mashi sumbata a cheek ɗinsa. Zuba mata idanu ya yi ya kasa ɗaukewa, yaga ta ƙara kyau sosai ne.

"Daddy na maka kyau sosai ne da kake kallona haka?"...... Shiru bai amsa mata ba. Hakan yasa ta sake cewa. "Ni fa taka ce, ka kalleni da kyau ka sake kallo, kayanka kake kallo, mallakinka ne". A shagwaɓe sosai ta faɗa.... Shi kam ya rasa waye yake koyawa Seraphina manyance da iya magana, dik ta gama goge mashi hadda.

Dik abin da take faɗe guru na jinta, dik sai ya ji wani iri, a ransa ya ce. "A dole a gidan nan su dinga rasa natsuwar Champion ɗinsu, ashe dole dik after 1 hour ya gudu wajenta, irin wannan shagwaɓa mai narka zuciya da kalamai masu zafin nan, ai komai taurin zuciyarka sai ta narka maka shi, ka ji wani irin shagwaɓa mai melting heart, ya rabb, gaskiya nima ina buƙatar irin wannan kulawa da soyayyar, wai tayi kewansa over"........ Ni kam na ce to malam guru irin wannan kula da soyayar dai a waje ɗaya ake samunsa, a wajen mace kawai zaka iya samunsa, matan da kuke cewa basu da amfani, to dik duniya macece kawai zata yi maka irin wannan soyayya da kulawar, yauwa gara ma ka dawo cikin hankalinka, ko ya kuka ce jama'a?.

Zare wayar daga kunnensa Aryan ya yi, a daidai lokacin take cewa Aryan. "Daddy yau naga soft lips ɗinka ya ciza red sosai, kamar in yi kissing ɗinsa fa". Tana murmushi mai kwantar da hankali ga shagwaɓa, ko kunyansa bata ji kwata-kwata, ta tsaresa da waɗan nan dara-daran violet eyes ɗin nata tana wani turo baki.

Katse kiran ya yi game da dallah mata harara kafin ya ce. "Ban ce ki dawo da wuri ba? Me ya sanya kika je kika yi zamanki a can?". Yana ɗaure fuska sosai ya faɗa, sai kuma ya miƙe zaune yana kallonta.

Ɗan turo baki ta yi, ganin babu alamar wasa a tattare da shi ne yasa ta sauƙo ƙasan bed ɗin, a gabansa daidai in da ya sauke fararen kafafunsa ta tsugguna, hannayensa ta riko cikin nata, cikin girmamawa da sanyin murya ta ce. "Ka yi hakuri daddy, ba zan sake ba, hira ce ta yi daɗi yasa na manta ka ce in dawo da wuri".

Ai gabaɗaya ta narka zuciyansa, ga girmamawa, ga soyayya kuma ga shagwaɓa, sai ya rasa me zai ce mata ma, ya tsareta da ido kawai, yana mata wani irin musulmin kallo mai narka zuciya.

"Please my whisper baby ka yi magana mana, na ce na zan sake ba, first and last i promise, ka ji nawan?". Tana turo baki ta faɗa, bata san dik ta rufe mashi baki ya rasa abin faɗe bane.

Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke game da riko hannayenta da ta kama nasa hannun da su. Ya ɗan matsa ƴan yatsunta cikin tafukansa har sai da ta ce wash......... Cikin wani irin low voice ya ce. "Komai zafin da na ɗauka sai dai in ban zo wajenki ba, komai ɓacin ran da nike ciki sai dai in ban haɗu dake ba, dik gudu suke yi, my cherry, kin san dik wata hanya da zaki bi dan ki faranta mun, nima yau zan sanyaki farinciki na musamman, jeki shirya, kada ki ci komai, yi wanka kawai ki shirya bari in yi sallar magrib da ishai ina zuwa in baki wata bazata".

Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi game da miƙewa tana faɗin. "Thank you so much my gentle chaos". Ta faɗa zata wuce. Miƙewa ya yi rike da hannayenta, ya ɗan kura mata idanu kafin ya ɗan rage tsawonsa, ya ɗan sumbaci gaban goshinta kafin ya saki hannayenta. Suna bin juna da kallon kauna ya wuce ya nufi benensu dan ana gab da kiran sallar mangrib. Yana fita ita kuma ta faɗa toilet cike da begensa da sabon soyayyansa.

A tinaninku bazatan me zai bata?.

----------------------

IRON FIST.

Mu ɗan koma baya kaɗan kafin mu cigaba. A ɗazun bayan Aryan ya kammala waya da Seraphins ya bata izinin tafiya, da suka gama wannan rikici da Vir ya bar wajen room na Lion ya shiga. Babu kowa sai ya fita zuwa ɗayan room ɗin, nan ya isko Lion tsaye yana shiri cikin tail coat fari tas, a gefen bed ya zauna yana faɗin. "Ina da tambaya".

Shiru Lion bai kulasa ba. A dake ya ce. "Wai wannan gida naka ne kai kaɗai ko namu?"...... Banza da shi Lion ya yi bai amsa ba. Ganin hakan yasa ya ce. "Ɓata bakina ma nike yi da na tsaya yin magana da kai a kan wannan issue, ina da right na yin abin da nike so a gidan nan, dan haka zan kawo sister ɗita wannan gida, ta zauna damu for some days, ba zata shiga harkarka ba, bama zata zo in da kake ba".

Tamkar babu Lion a ɗakin, ya cigaba da abin da yake yi, sai da ya kammala ne ya kalli in da Aryan yake. "Get ready to go to Dad's house now, there's something we need to check". Yana gama faɗa ya juya ya fice abinsa. Miƙewa Aryan ya yi, ya fito ya sanar da su Vir su shirya, sai ya dawo dan shiryawa.

After like 1 hour suka fito shirye cikin kaya iri ɗaya, tamkar ƴan huɗu. A main parlo suka iso Lion zaune, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ya ɗaga kansa sama tamkar mai tinanin wani abin, ya yi shiru.

Ƙashin maƙogwaronsa Aryan ya ɗan taɓa kafin ya ce. "Let's go". Ba tare da ya yi magana ba, ya miƙe tsaye kafin ya waro jade eyes ɗinsa masu kama da sleeping eyes ɗin nan, yau sai ya yi kamar wanda yake cikin maye ma, dik yadda aka yi barci yake ji.

Jerawa suka yi zuwa main door na fita. Suka shiga elevator suka yi ƙasa, dik da suna sanye da wannan nose mask ɗin nasu na gado dik wanda ya gansu sai ya sake waigawa ya gansu, mazajen gaske.


*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*

https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-47-by-princess-teema

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥

[10/01, 9:16 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.


For more information 08161390581 Whatsapp me only.


STEP 1🔥

2025-12-31.🔥



اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️


No editing.💔


E_____________ 47


A harabar benen nasu suka tsaya, key ɗin wata dalleliyar mota Lion ya fitar daga aljihun coat ɗinsa. Miƙawa guru key ɗin ya yi, dikkansu da kallo suka bisa suna mamakin ganin yau da motarsa na ainahi zasu fita.

Wannan mota dad da kansa ya saya masu su huɗun iri ɗaya, to tin bayan rasuwar dad ɗin suka rufe motocin, dik wani abin da zai sanya a gane suna da alaƙa da Haiza'an sai da uncle yasa suka ajiyesa, dalilin kenan da yasa basa fitowa da Hero, domin kowa ya ga wannan zaki sai ya gane zakin Haiza'an ne, dan wannan zaki ya shiga tarin dad dama duniya bakiɗaya, kuma a jikin Zakin a gaban goshinsa akwai rubutun sunan dad da aka yi mashi da wuta, shiyasa kowa ya gansa zai gane na dad ɗin ne, shiyasa ko waje basa leƙowa da shi, yana gida.

Sun yi mamakin ganin zasu fita da wannan mota, motocin nasu dik plate numbersu sunan Haiza'ans family ne a jikinsa, shiyasa suka jinginesu. Tin da suka ga Lion zai fita da wannan mota suka fahimci ya shirya fito na fito da duniya bakiɗaya kenan, lallai kuwa akwai kura, uncle da duniya ta ɗauke ya mutu yana ƙoƙarin tada tarzoma kenan, zai sanya IRON FIST su bayyana a duniya, zasu jingine aikin SSO kenan ko yaya? Ya Aryan zai yi da Seraphina da ta tsani IRON FIST? Me Khaiza'ans family zasu ce? Abba zai yarda da cewa Aryan shi ne Champion na IRON FIST?.

Fito da motar guru ya yi, Lion ya shiga gidan gaba, Aryan da Vir suka shiga gidan baya. Kai tsaye


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login