Showing 21001 words to 24000 words out of 365093 words
ya ɗan ji kamar zai yi aikin, amma idan ya tuna wannan ɗan banzan wahalar da suka sha yau, kuma a haka ma wai ranarsu ta farko ce, yana tuna wannan zai ce kai shi ina, sai ya ji zafafan kalaman Captain sun goge a kansa. Karfe 7 daidai suka tashi daga horon jarumta, Captain ya basu 5mins su yi alwala zuwa masallacin soji.
Haka kuwa aka yi, bayan sun yi sallar mangariba da ishai karfe 8 suka haɗu a dinner hall suka yi dinner, karfe 8:30 suka kammala, a nan ne Captain ya umarcesu da kowa ya wuce room ɗinsu, suna da damar yin wanka su kwanta, kada su manta gobe 4:30 na asuba zasu tashi. Daga nan ya hura usir kowa ya nufi room ɗinsa.
Noor ya riko shoulder ɗin Vash yana ta faman haki yana nishi sama-sama alamar shi ya yi matuƙar gajiya, shi ma Vash ɗin nishi sama-sama yake sai faman kwaɓe fuska suke yi. Kai tsaye room ɗinsu suka nufa, sai dai kuma suna shiga suka tsaya turus ganin Leo a tsaye a tsakiyar ɗakin hannunsa rike da waist ɗinsa yana kallon wajen da Noor ya ɓata da taɓo ɗazun. Leo ya tsani datti komai ƙanƙantarta, baya zama wajen ƙazanta, wlh idan ya ga ƙazanta a waje ya dinga shirga amai kenan, yana da bala'in kyankyani sosai, zuciyansa ta yi ta tashi idan ya ga ƙazanta.
Ganin yana tsaye yana kallon wajen ne yasa Vash and Noor suka ɗan sha jinin jikinsu, shi kuma Zaysh ya wani ɗale kan gadonsa yana ɗaure fuska tamau irin shi ma no respect ɗin nan.
Wucewa Noor ya yi zai nufi toilet sanyayyar sexy voice ɗin Leo ya daki dodannin kunnuwansu da cewa. "Come over here".
Sosai sun ji shakkarsa, amma Zaynash da ya yake dake ne ya ce. "Yana kiranku ai sai kuzo". Ya faɗa ba tare da ya kalli Leo ba, saboda shakka da tsoronsa, kuma gatse yai masu, ina irin ubanku na kiranku ai sai ku je. Zazzare ido Noor ya yi, da sauri ya saki Vash yana faɗin. "Yanzu zamu goge wajen mancewa na yi"....... Da sauri Vash ya amsa da cewa. "To dama meyasa baka goge ba?".
Mamaki ne ya kama Noor, wai ba su suka ce kada ya goge ba ɗazun? Yanzu kuma sun juya mashi baya. Wucewa Vash ya yi da sauri ya nufi wajen bed ɗinsa. Jakansa ya zaro zai kwashi kayan wanka irinsu lotions da soap ya wuce toilet, bai bi ta kan Noor ba, sai da ma ya ciro katon biscuits mai daɗi ya fasa ya ɗan ci rabi, ya mayar da sauran cikin kayan motsa bakinsa, daga nan ya miƙe tare da kwasan kayan amfaninsa ya wuce toilet.
Back to their age, Zaysh kamar Leo haka yake 23, Vash bai wuci 22 ba, Noor 20, Amma kansu kusan ɗaya, Leo dai ya fisu tsawo ne, Pamira people suna da tsawo sosai!. Yanzu Noor yagama gane dikkansu suna tsoron Leo, sai ya kudurta a ransa sai ya ƙullah alaƙa da Leo su shaƙu sosai ko dan su Zaysh su daina raina mashi wayau.
Mopper room ɗin nasu ya ɗauko, ya zo ya goge ko'ina tsab, ya kara share masu ɗakin kafin ya nufi wajen bed ɗinsa, shiru suka zazzauna cike da al'ajabin farkon ranarsu a GIDAN SOJA, wannan abu ya tsayawa Noor a rai, ba su taɓa zatan haka ba. Ni kuwa na ce abin da baku taɓa zata ba ai yana nan dayawa kuma yana kan hanyar iso ku, GIDAN SOJA ya zarce yadda kuka ɗauka mutanen! har gobe dai inai maku fatan kammala horo lafiya har ku fara aiki!.
Suna zaune shiru har Leo ya fito daga wanka sanye da bathrobe white kala mai shegen kyau, ya haɗe kitson kansa waje guda, yana ɗaure da karamar white towel a saman kan nasa, lokaci guda kamahin soap and shower gel ɗinsa ya buɗe ko'ina a cikin ɗakin nasu.
Mamaki ne ya kama Noor dake saman bed ɗinsa, a fili ya ce. "Wannan kamshi tamkar na soap ɗin Companynmu". Basu ji me ya faɗa ba, dan haka babu wanda ya tanka shi.
A saman bed ɗinsa Leo ya zauna tare da kawo jakarsa, ya fito da lotions na companyn STARS LADIES BODY LUSH. Kayan kamfanin kala biyu ne, na maza ya kasance da sunan STARS BODY LUSH, na mata STARS LADIES BODY LUSH. Fito da su Leo ya yi, a natse ya fara murza mayukan a jikinsa, take kamshinsu ya kara bule ko'ina a ɗaki, kura mashi ido Noor ya yi yana mamakin yadda aka yi kayan kamfanin daddynsa ya shiga duniya har nan. Like wow, yanzu ya yarda da cewa Leo ba karamin kai bane, dan ba kowa ya isa amfani da kayan kamfaninsu ba , saboda balain tsadarta, abu mai kyau da inganci ai dole ta yi tsada!.
Robar lotion da Leo yake shafawa a yanzu pic ɗin Noor ne a jiki, dan kyansa yasa su suke yi wa Companynsu tallah, a robar mata hotunan sister ɗinsa ne a jiki, ai na faɗa maku Noor yana da kyakkyawar jiki kamar madara, ga kyan fuska, amma Leo tsabar iskanci bai gane Noor bane a jikin hoton, dan bai taɓa bi ta kan hoton jikin ba!.
Suna gani Leo ya kamma shirinsa cikin pj's tsab, ya haye gado ya kwanta, sannan ya jawo littafinsa na nazarin makamai na lacture ɗin da suka yi ɗazun ya fara karantawa, ya sanya Bluetooth a kunne yadda ma kada ya ji wani motsi ko magana.
Shiru ɗakin ya yi, suna son yin gulma suna tsoron ya ji su, haka suka yi tsit, daga karshen kowannensu ya tashi ya yi wanka, suka zo suka shirya yare da hayewa gado, kwanciya suka yi suka hau barcin gajiya, jiki dik tsamin wahalar horo, shiyasa suna kwanciya ba jimawa sai barci, amma ban da Zaysh, shi bai rintsa ba, sai da ya bari suka yi barci sannan ya diro ƙasan bed ɗinsa, ya fito da........
Masu tambayata batu kan Dr and ƴarta ku dai kara hakuri, zamu waiwayi wajen a next page In Sha ALLAH, akwai dalilin ɗan janyewa!.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-4-by-princess-teema
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
3-11-2025.🔥
FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥
E_____________4
Wayarsa kirar Infinix hot 12, wayar ta ɗan sha jiki kaɗan, screen ɗinta ta gefe ta ɗan tsage, amma lafiya lou yana kallo. Sauƙowa kasan bed ɗinsa ya yi, a nan ya fahimci Leo bai yi barci ba, wucewa ya yi ya nufi hanyar toilet...
A saman WC ya zauna tare da laluɓo wata number da aka yi saving da my Ummie ya danna kira. Yana yi yana duba time. Bugu ɗaya aka ɗaga, sanyayyar muryar mace ce ta karaɗe kunnensa da cewa. "Bloody sai yanzu ka tina da ni ko?".
Da sauri ya hau girgiza mata kai yana faɗin. "A'a Ummie, tin da safe na so kiranki amma ban samu dama ba, mun fita training ne yau"........ Sanyayyar ajiyar zuciya ta sake sauke kafin ta ce. "ALLAH sarki, ka ce kasha wahala kenan?"...... "A'a Ummie, babu wata wahala, ke dai ki cigaba da tayani da addu'a kawai, in fito da kyakkyawar result, in zama babban soja dan kiji daɗin rayuwarki, zan cika maki burinki matuƙa".
"In Sha ALLAH ina tayaka da addu'a bloody na, ka kara dagewa ka ji? Ina kewarka sosai".......... "Ni ma ina kewarki sosai Ummie na, ki kula da kanki kin ji?"........ "In Sha ALLAH zan kula, kai ma ka kula, kaga kai kaɗai nike gani in ji daɗi ko? Kai kaɗai ka rage mun a duniya"...... "Haka ne, amma nima ai kin san ke kaɗai ke gareni ko?". "E haka ne". Ta bashi amsa a taƙaice, da alamar barci a voice ɗinta.
"To shikenan ina yayana?". Ya faɗa yana gyara zamansa......... "Yayanka yana barci, nima tinaninka ya hanani rintsawa, na damu ina son jin ya ka wuni, na kira layinka sau ba adadi amma baya shiga".
"ALLAH sarki, ai na kashe wayar ne dan in samu damar yin abin da yakamata, yanzu dai ki je kin kwanta, sai da safe zamu yi waya tin da kin ji ina lafiya"......... "To shikenan, kada ka manta da alwalar barci da kuma addu'a, sannan ka dinga cin abinci sosai, ka kuma mai da hankali a kan aikinka, kada ka manta da karatun Alqur'ani da littafan addu'oi".
Tin da ta fara magana yake jinjina mata kai har ta kai karshe, sannan ya amsa da okey In Sha ALLAH zai yi dik abin da ta ce. Albarka ta sanya mashi daga haka suka yi sallama ya katse kiran. Shiru ya ɗan yi tare da kurawa wayar tasa idanu, can kuma ya shiga gallery ɗinsa, ya fito da wani hoto nasa shi da wata kyakkyawar mace, fara tas mai kyan fuska, sai murmushi take yi cikin hoton, ga ta da dimple mai ɗaukar hankali irin nasa.
Shiru Zaynash ya yi yana tinanin mafita a garesa, ya so faɗawa Ummie cewa aikin soja akwai matuƙar wahala, amma ya gagara, dan baya son fara bata wani damuwa daga tafiyarsa, idan kuma bai faɗa mata ba ta ya zai dinga samun kwarin gwiwa? Zai iya idan ba'a karfafa shi kuwa?.
Waye Zaynash? Mu ɗan ji tarihinsa kaɗan. Zaynash maraya ne da bashi da uwa kuma bashi da uba, sai yar uwarsa guda ɗaya mai suna Ummie, wacce suka yi waya a yanzu kenan! Ummie ita ta reinesa tin yana karami, mahaifansu sun rasu tin yana da shekaru huɗu a duniya, ita kuma tana da shekaru 13 a lokacin, haka ta renesa, daga cikin ƴan uwa babu wanda ya kula da su, saboda mahaifinsu bai mutu ya bar komai ba sai kangon gida da ko kofa babu da kuma gona, haka Ummie ta juri yunwa na cikinta, ta juri dik wata wahala wajen renonsa, ta shiga kalubale da dama saboda shi, sau uku ana ƙoƙarin keta mata haddi dik saboda neman abincin da zata bashi ya ci a lokacin da yake kukan yunwa.
Sun rayu cikin kunci da talauci, ba makarantar boko sai ta islamiya, ita ma islamiyar makocinsu ne mai makarantar yasa ya ɗaukesu kyauta. Sun mai da hankali har Ummie ta haddace Alqur'ani mai girma, kakarsu wacce ta haifi babansu ita ma tana gidan nasu ne, amma da yake ta tsufa sosai sai yazamana bata iya taimaka masu da komai sai dai ma su su taimaka mata, dan haka Ummie ke ciyar da su. Shi kuma Kanin babansu ɗaya tilo a duniya yana can wani gari yana rayuwa, tin da ya tafi neman kuɗi bai dawo ba.
To a haka dai suka rayu har Ummie ta zama budurwa. Da yake suna da balain kyau kamar ƴaƴan larabawa hakan yasa samari suka fara tururwar zuwa neman aurenta. A lokacin bata yarda ta kula kowa ba, ta cigaba da karatun islamiyarta har ta zama Ameera a islamiyar tasu, malamin ya ɗauketa tana karantarwa a wajen dik wata yana biyanta kamar 5k a kuɗin Naija. Da wannan 5k ɗin take amfani ta haɗa da ɗan aikatau na mutane da wanki a gida da takewa mutane, ta haɗa kuɗin ta sanya Zaynash makarantar boko dake ɗan babban gari kusa da su, ta ce ya yi karatu zai taimaka masu a rayuwa tin da shi namiji ne.
Zaynash yana primary 4 a school uncle ɗinsu kanin babansu ya zo garin ganin gida bayan tsawon shekaru. Ya jajanta halin da suke ciki, ya kuma yaba da ƙoƙari irin na Ummie, daga nan ya ce zai tafi da su birni su yi rayuwa a can. Bai yi ƙasa a gwiwa wajen ɗaukarsu su koma can ba, suna zuwa can kuma wani fitina ta tashi ta tsaya na matarsa, ta ce waɗan nan ƴan kauye ba za su zauna mata a gida ba, an yi juyin duniyar nan taki yarda, a na haka kakansu ta faɗi ta rasu, dalilin kenan da yasa matar tasa ta hakura su Ummie suka zauna, imani ya ɗan shigeta ganin mutuwar tsohuwar a gabanta.
Su Ummie sun yi zaman shekara ɗaya a gidan amma cikin rashin daɗi da takura, ga kuntatawa da Auntyn tasu matar kawun nasu take masu, dik ta sallami ƴan aikinta su Ummie suka zama masu mata bauta, sun ci kwakwa matuƙa kafin kanin Auntyn tasu da ya dawo daga bautar ƙasa ya ga Ummie ya ce shi fa ya yi mata, yaga tsantsar kyau, Auntyn tasu ta so hana auren amma ALLAH ya yi sai anyi, Ummie ta auri wannan bawan ALLAH. To shi ma dai ba wani kuɗi yake da shi ba, yawon neman aiki yake yi, ɗan makaranta ne.
A lokacin Zaynash ya kammala primary, dan zuwansa babban gari ya cigaba da karatu, uncle ɗinsu ne yake biya mashi kuɗin makaranta. In taƙaice maku labari har yanzu Ummie tana cikin talauci da kunci ga takurar dangin miji musamman wannan Aunty tasu, dik ta shafe mata bakin fenti a family shi ne yasa basa sonta ko kaɗa. A lokacin da Zaynash ya kammala secondary school sai ya ce shi makarantar sojoji zai tafi, ya zaɓi hakan ne kuma bisa ra'ayin Ummie, tana son ya zama babban soja dan kawo karshen ta'addancin dake faruwa, saboda ƴan bindiga ne suka kashe iyayensu, suka shiga har gida suka yi masu rashin mutunci, sannan suka yi garkuwa da su, da ba kuɗin fansa shi ne suka kashesu suka baiwa karnika gawarwakinsu.
In kara takaice maku yanzu auren Ummie da mijinta shekara biyu kenan, bata taɓa haihuwa ba, hakan yasa dangin mijin suka kara sakota a gaba, zagi da cin mutunci kala-kala suke yi mata, kannensa da Auntynsu matar uncle ɗinsu sun hanata shan iska, da ta yi magana ace juya bata haihuwa. Dalilin kenan da yasa Zaynash ya kara mai da hankali dan ya zama babban soja ya ga ya fitar da Ummie daga cikin kuncin da take a ciki, yana balain son ƴar uwarsa kamar yadda take mutuwar son shi. Dama da zai zo GIDA SOJA uncle ɗinsa ne ya yi mashi komai, amma sai da ya sayar da gidansu na kauye da konarsu, sannan ya cika ya kawosa nan, dan AZURE ba dik kai ba, makaranta ce na ɗan wane da wane, uncle ɗinsu ya kashe makudan kuɗaɗɗe kafin Zaynash ya samu wannan makaranta, and da kyar Auntynsu ta bari uncle ɗin nasu ya yi mashi komai ɗin, ita kuma Ummie kuɗi kimanin 50k a kuɗin Naija ta bashi, wannan dalilin yasa ya baya son kawo mata abin da zai ɗaga mata hankali, ya yi alkawarin daurewa dan ya ga ya cinwa narasa. Amma fa bai tsammaci haka GIDAN SOJA yake da wahalar gaske ba. A TAKAICE KENAN RAYUWAR ZAYNASH, DAN HAKA DIK YADDA ZAKU GA YANA GASA DA SAURAN YARA DAN YA ZO NA FARKO KADA KU GA LAIFINSA, BURINSA NE HAKAN DAN TSAMO ƳAR UWARSA DAGA WAHALA, SHIYASA YA DAGE!!.
-------------------------🔥
Ya jima sosai zaune a wajen kafin ya miƙe tare da kashe wayar tasa, sannan ya dawo cikin ɗakin. Still dai idanun Leo biyu yana karance-karance da nazartan makaman da aka koyar da su yau. Ko ɗago kai bai yi ya kalli Zaynash ba, yana cigaba da abin da yake yi. Shi kuma Zaynash sai kallonsa yake yi har ya isa saman bed ɗinsa, ya kwanta tare da jawo bargo zuciyansa cike da tinanin yadda zai rayu a GIDAN SOJA. Ya so ya ɗan yi karatun abin da aka koya masu ɗazun kafin ya yi barci, sai dai ina, gajiyar wahalar da suka yi tasa barci ta yi awon gaba da shi. Shi kuwa Leo ya yi karatu har 1 na dare, kafin ya miƙe ya ɗauro alwala, ya zo ya yi nafilfilinsa, daga karshe ya rufe da shafa'i da witiri kafin ya kwanta dan ɗan rintsawa shi ma!.
4:30 ASUBA.
Wannan busa ta jiya ita ta tada su, sun sha mamakin ganin yau ma Leo idanunsa biyu yana zaune a tsakiyar gado yana duba waya. Tambayar kansu suka shiga yi wai shi wannan baya barci ne?. Basu san yanayi ba, amma tin 4 yake farkawa, kuma sai 1 yake kwanciya, barcin 3h yake yi.
Da wani irin ciwon jiki Vash ya farka, ga in da aka zane shi jiya ya yi ruɗu-ruɗu ya kumbura, idaninsa jajir, jikinsa dik babu kwari. Da kyar ma ya iya tashi, intently ya diro kasan bed ɗinsa, cikin wani irin matsanancin hali ya nufi toilet ba tare da ya yi wa kowa magana ba, shi kaɗai ya san me yake ji.
Dirowa ƙasa Zaysh ya yi ya nufi toilet shi ma, jikinsa dik tai tsami. Noor kam komawa ya yi ya kwanta, har da kukan shi jikinsa ciwo yake yi mashi, dan haka wlh ba zai iya tashi ba. Wanka su Zaysh suka yi tare da fitowa suka shirya. Leo already ya yi wanka ya shirya, dan tim 4 ya tashi, yanzu kuma 4:30, wannan 30 mins sun ɗaukesa shiryawa.
Bayan sun kammala shiri ne Vash ya ce bari ya tashi Noor. Zaysh dake ƙoƙarin ɗaure jakansa ya ce. "Ka kyalesa ba, zai tashi da kansa ne"....... "No brother, kasan halinsa, bari in tashesa kada a mashi duka"........ Cigaba da abin da yake yi Zaysh yai bai sake yin magana ba.
Slowly Leo yai switch off na wayarsa tare da ajiyeta a saman bed ɗin, ya ɗauko littafin karatun makamansa na jiya ya diro ƙasa da shi, jakansa ya buɗe tare da mai da book ɗin, sannan ya shinfiɗa bed ɗinsa da kyau, ya naɗe bargonsa, ya ɗauko army p-cap sabuwa daga cikin jakan ya sanya a kansa, daga nan ya nufi waje ba tare da ya kalli in da suke ba.