Showing 78001 words to 81000 words out of 365093 words

Chapter 27 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5912

kyau ba!".

One side smiling ya ɗan saki tare da fara typing reply kamar haka. "Gaskiya bana son mace irinki!". A gajarce ya rubuta ya tura mata. Ai tin bai gama cire yatsarta a wajen ba ta fara yi mashi ruwan emoji na hawaye kala-kala. Ya fi emoji 100 ta tura mashi. Da sauri ya hau typing. "Oh sorry, lafa haka nan, da wasa nike".

Yana tura mata ta turo mashi emojin shagwaɓa tana turo baki. Sake sakin one side smiling ya yi kafin ya hau serious typing na amsarta kamar haka. "Kina dikkan abin da kowa zai ji yana son alaƙa dake, kawai ban sanki bane yasa, kin ki faɗa mun wacece ke? Daga ina kike? A ina kika sanni? Idan kika bani amsa zan saki jiki mu yi hira, kuma zaki zama ƙawata". Lokacin da ya tura mata daɗi yasa ta miƙe ta ɗan daka tsalle tare da komawa ta zauna, sannan ta fara typing.

"Promise me that in na faɗa maka wacece ni ba zaka fasa abotarmu ba?"..... Kai ya jinjina tamkar yana a gabanta kafin ya hau typing na ya ɗauki alkawari.......... "Vanisha by name, daughter of GAT, na sanka ne since ban wuci 9 years ba a jinin robar man shafawarmu, kullum da tinaninka nike kwana kuma nike tashi, na ji a raina kamar kai ba a zahiri kake ba shiyasa da na ganka na rikice, please kada ka yi breaking promise da ka ɗauka mun, na zaɓi in faɗa maka gaskiya ne kawai dan nasan dik alaƙar da aka kulla a kan ƙarya bata ƙargo, nasan zaka fahimceni kuma ka mun uzuri". Tana gama rubutawa ta tura mashi kirjinta na dukan uku-uku, cike take da fargabar amsar da zai biyo baya, kada ya ce ya karya alkawari, ina zata sanya ranta in hakan ta faru? Safe kirjinta ta yi tana jiran amsa daga garesa, har ƴar gumi ta haɗa.

Shi kuwa a lokacin da saƙonta ya shigo mashi, natsuwa ya yi ya karanta da kyau. Ai yana zuwa in da ta ce ƴar GAT take bai san time ɗin da ya miƙe zaune ba. Wani irin waro idanunsa a kan wayar ya yi, sai yake ganin kamar bai karanta daidai ba, hakan yasa ya faro karantawa daga farko. Tabbas abin da ya karanta a farko shi ne.

Ɗan ɗauke wuta ya yi, ya gagara yi mata reply, a can kuma tana can cike da zulumi da fargabar jiran amsa daga garesa, shi kuwa ya rasa a wani point ma yake tukun nan.

Me kuke tinanin zai faru? Zai bata amsa ko yaya? Zai cika alkawarin da ya ɗauka? Zai take zokar AZURE ne ko dai zai bi doka ya gogeta daga babin rayuwansa?.
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-12-by-princess-teema

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.




STEP 1________🔥


13-11-2025.🔥


FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥


NOTE. FIVE LIONS babu complete ɗinsa, yanzu nike posting ɗinsa, yanzu aka fara!



E_____________12



Ɗan ɗauke wuta ya yi, ya gagara yi mata reply, a can kuma tana can cike da zulumi da fargabar jiran amsa daga garesa, shi kuwa ya rasa a wani point ma yake tukun nan. Gagara danna reply ya yi, dan ya shiga ruɗani.

Wai na ce kun san me ake cewa GAT kuwa? To Nigeria ma bata da muƙamin GAT, sai a manyan ƙasashe ake bada irin wannan muƙami, amma bari in yi maku yadda zaku fi ganewa kila ku gane dalilin Noor na shiga ruɗani da tashin hankali. A Nigeria muƙamin General shi ne babban kuƙami, amma a lokacin da ƙasa zata shiga yaƙi akwai wani muƙami da ake bayarwa wanda ya ɗara General mai ɗauke da 5 stars, wannan muƙami ana kiransa da field marshal, ana bada shi ne kawai a lokacin da ƙasa zata shiga yaki da wata ƙasa, rundunar da zasu jagoranci ƙasar babban da aka fitar shi ake baiwa muƙamin field marshal, bayan yaki ana cire muƙamin dan ba'a amfani da shi. Dan haka Naija dik girmanta bata da GAT!. Irinsu US sau sauran manyan ƙasashe ke amfani da GENERAL OF THE ARMY.

Bari in kara yi maku bayani dan ku fi ganewa da kyau, ku san muƙamin da ake magana a kai. General of the Army yana da 5 stars ne da eagle ɗaya, daga shi sai General mai 4 stars kawai, sai Lieutenant General mai star uku kawai ba wani rank, Sai Major General mai stars 2, Brigadier General mai star ɗaya, Colonel bashi da wani star, Lieutenant Colonel shi ma ba star ba eagle, Major shi ma ba wani star, Captain yana da stars 2 kamar Major General kenan, akwai First Lieutenant mai star ɗaya, Second Lieutenant bashi da star, Sergeant Major of the Army bashi da star, Command Sergeant Major bashi da stars shi ma, Sergeant Major, First Sergeant, Master Sergeant, Sergeant First Class, Staff Sergeant, Sergeant sune suke kasancewa drivers na manyansu ko masu baiwa wani babba tsaro! Corporal, Specialist, Private First Class, Private PV2, Private PV1 dik waɗan nan basu da star, waɗan nan sune muƙaman soja gabaɗaya, to dik waɗan nan da na kirga maku fa a ƙarƙashin GAT suke, kun ga kuwa dole dik wanda ya ji sunansa in yasan me suna take nufi dole ya girgiza!.

"Are okey?". Leo dake kwance rike da waya ne ya tambaya cike da mamaki. Da sauri Noor ya diro kasan bed ɗinsa, V ta yi mashi message ya kai 5 bai iya buɗewa ba bare amsawa. Da zafin nama ya haye bed ɗin Leo, dik hankalinsa a tashe, muryansa na ɗan rawa ya ce. "Bro tashi ka ji wani abu?".

Da ido Leo ya bisa ba tare da ya motsa ba. Sanin halinsa yasa ya fara bashi labari kawai ba tare da ya jira ya tashi ɗin ba. Sai da ya kammala har karshe cike da sa ran zai ga ruɗu a kan fuskan Leo, sai ya ga ya ja siririn tsaki yana dallah mashi harara. Take ya ji jikinsa ta ɗan saki, sai kuma ya ce. "Bro ko baka ji da kyau bane? Ɗiyar GAT fa na ce!".

"Then so?". Leo ya faɗa yana cigaba da dallah mashi harara. Shiru Noor ya yi, kwakwalwansa ta shiga doubting, anya Leo yana kan saiti kuwa? Ana maganar GAT yana faɗin then so what? Anya lafiyansa lou kuwa?.

Katse mashi tinani Leo y yi da cewa. "Bana hanaka jin tsoron wani ɗan adam ba? Baka ji ko?". Leo ya faɗa tare da miƙewa zaune....... Kada ku manta Noor yana da cutar tsoro a cikin kwakwalwansa, dole ya yi wannan rikicewa, dik da ya zama soja ba wai cutar ta rabu da shi bane, time to time tana tashi, idan ta tashi kuma yana rikicewa ya dinga jin tsoron abu, haka idan ya firgita sosai abin yana motsa mashi.

Sake maimaitwa Leo ya yi cewa. "Bro I'm talking about GAT ooooo". ....... "GAT shi ba mutum bane? Ba haihuwarsa aka yi kamar sauran mutane bane? Ko shi faɗowa ya yi daga sama da yasa ya fita daban?". With full confidence Leo ya faɗa, dan shi wlh baya tsoron wani abin halitta face ALLAHN da ya haliccesa, ga shi da saurin fusata, dan a yanzu haka ya fusata na ganin yadda Noor ya tsorata a kan wani halitta, ya sha faɗa mashi ALLAH kawai ake tsoro haka ba wai halittar ALLAH ba, amma Noor baya ganewa, ALLAH sarki bai san cewa ba laifin Noor bane, cuta ce.

Gabaɗaya kan Noor ya shiga ruɗani, sai yake jin kamar shi ne kunnuwansa basa jiyo mashi abin da Leo yake faɗe da kyau, in ba haka ba yana ganin ba zai yiwu wani ya faɗa magana da ta saɓa ta girmamawa ga GAT ba!.

Call da ta shigo wayar Noor a yanzu ne yasa Noor dawo daga duniyar tinanin da ya afka, kallon wayar hannun nasa ya yi, V ce take kira, da sauri ya ɗago ya kalli Leo, while shi ma Leo ɗin shi yake kallo.

"Bro ina tsoron ɗaukar wayar......". Ya faɗa a raunace. Wani irin kallo da Leo ya dallah mashi ne yasa ya gagara karisa maganar. A sanyaye Leo ya ce. "A ina ka taɓa ganin soja da tsoro ko fargaba? GAT da kake magana ka rikice daga jin sunansa ɗin sai da ya jajirce ya cire dik wani tsoron abin halitta kafin ya taka matsayin da yake, idan ka zage watarana kai zaka ɗaura 5 star with eagle a gaban rigarka da taken GAT ɗin". Ya ɗan dakata saboda ɗan sara mashi da kansa yake yi, Noor yana son ja mashi dogon surutu.

Still dai babu alamar Noor zai kwarara kan nan nasa, ganin haka yasa Leo ya jawosa jikinsa, cikin hikima da dabara ya fara karfafa mashi gwiwa yana gwada mashi lallai dikkan wani abin halitta bai isa ya yi maka komai ba matuƙar ka yarda da ALLAH, dan haka ba GAT ba ko bakin sniper or machine gun bai isa yai maka komai ba, dan haka ya karfafa kansa.

One thing da na manta ban faɗa maku na, su Noor ba musulmai bane, nasan zaku ce Noor sunan musulmai ne ai, kada ku manta ni na yanke sunan nike ce mashi Noor, amma sunansa Nooriel, dan haka ba musulmai bane, shiyasa idan Leo yana ce mashi kada ya ji tsoron kowa face ALLAH baya wani ɗaukar abin serious, dan tin farko bai yi imani da ALLAH ɗin ba, amma zamansa da Leo a yanzu yasa sosai yana jin cewa zai iya musulunta, kuma yana jin cewa lallai ALLAH shi ne mahaliccin kowa da komai, Leo bai taɓa ce mashi ya musulunta ba, yana dai yin ibada a gabansa, a haka kuma abin take shiga ransa, kun san addinin musulunci da shegen daɗi, ba sai ance maka zoka shiga ba, in dai ana ibadar a gabanka dole ka yi sha'awarta sai dai in son zuciyarka zaka bi!.

Sosai ya kwarara mashi gwiwa, bai rabu da shi ba har sai da ya tabbatar ya kore mashi wannan tsoro, sannan dan ma ya kara karfafasa sai yasa ya kira V a yanzu su yi magana, saboda a cewansa idan ya kirata zai kara kwarara kansa. With his full confidence ya danna mata kira, yanzu baya jin tsoron komai.

Kira ɗaya ta ɗaga, har lokacin tana zaune a balcony, ta ci kuka har ta ƙoshi, dan a tinaninta shikenan ya ji cewa ita ƴar GAT ne ya rabu da ita, ta yi ta nadamar faɗa mashi gaskiya da ta yi, har idanunsa suka yi jajir suka ɗan kumbura.

Tana ɗauka ta fashe mashi da wani sabon kukan, dan zuciyarta a kusa take. Ɗago eyes ɗinsa ya yi suka kalli juna da Leo, hararansa Leo ya yi kafin ya koma ya kwanta tare da jawo bargo ya rufe har kansa. Ajiyar zuciya Noor ya sauke, slowly ya sauƙa daga gadon, da sauri ya fita zuwa balcony wai kunyar Leo yake ji.

Tsayuwa a wajen ya yi tare da manna wayar a kunnensa, ya zura hannunsa ɗaya a aljihu kafin a sanyaye ya ce. "I'm so so sorry for the delay in responding to your message, wani ɗan abu ne ya ɗauke hankalina"...... Haba lokaci guda ta ji tamkar an sauƙe mata dik wani nauyin dake kanta jin cewa ba daina yi mata magana zai yi ba, amma dik da haka sai ta cigaba da kukan dan ta kara ratsa zuciyansa da kyau.

"Please stop crying! Yana taɓa mun zuciya"........ Cikin kuka ta ce. "Ni dai ka rarrasheni in kana son in yi shiru"..... Yadda ta yi magana voice ɗinta ya huda zuciyansa sosai, har wani ɗan shock ya ji, one side smiling ya ɗan saki kafin a cikin ransa ya ce. "Yau ga shi a hannun rigimammiya, wai ya rarrasheta kawai, to shi ko ta ina ya iya rarrashin ne ma?".

A fili kuma sai ya ce. "Okey me kike son in yi yanzu kenan?"...... Tana turo baki tamkar tana a gabansa ta amsa da. "Ka mun kalamai masu daɗi"....... "That's all?"....... Kai ta jinjina tare da cewa yeah. "Okey, get ready to accept my cool and sexy words".

Da sauri ta ce. "Done, I opened all my ear, I'm listening now!". Ta faɗa har tana tuntuɓen harshe...... "See her, rigimamma kawai, wai I'm listening, har kina haɗe words, kece auta ko?".... Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Kamar kai ba, nasan kaima ai kai ne auta"...... "Who told you?"........ "Aunty Lisa". Ta bashi amsa a taƙaice. Ɗan girgiza kai ya yi cike da mamakin yadda lokaci guda Aunties ɗinsa suka aminta da ita, har da bata labari.

Jin ya yi shiru yasa ta fara jansa da hira da salon soyayyarta mai melting heart har bai san time da ya saki jiki ya shiga biye mata ba, suka raba dare suna hira, dan ko da su Arya suka dawo room ɗin bata daina wayar ba, sai da daddynsu ya shigo ne ta ɓoye wayar ba tare da ta katse kiran ba, Noor na jin dik abin dake wakana.

Yau da yake yana da baƙi bai zauna hira da su ba, sai ya yi masu goodnight ya fita kawai. Su Arya suka tattaro laptop ɗinsu suka shiga aiki dan gyara kwarewarsu, ita kuma V ta cigaba da wayarta da heartbeat ɗinta. Sai around 3 na dare sannan ya ce su kwanta dan da safe zai wuce US, akwai sammako kenan a gabansa. Kada ku manta tsakanin Avaris da US ba nisa, suna kusa sosai.

Abin ku da sabon soyayya, sam bata so su yi sallama, ita ko kwana zasu yi a haka a shirye take, amma ta hakura dan girmama buƙatarsa, suka yi sallama ba tare da ya yarda ya furta mata kalmar so ba, dik hiran da suka yi bai yarda ya furta kalmar ba, ba wai dan bata yi mashi ba, no, kawai dai ya ce tukun nan, sai ya gama sanin wacece ita da yadda take gabaɗaya. Ita ma bata damu da ya furta mata ba, a cewarta a hankali zai furta ba sai an ce ya yi ba, dan haka da suka zo yin sallama ma ce mashi ta yi take care, goodnight and have a nice dream, bata kawo zancen love ba, amma tana kiransa da heartbeat.

While shi ma abin da ya ce mata kenan, have a nice dream like your beautiful face. Ta dinga murmushi jin ya yaba kyanta, a haka dai suka yi sallama, ta kashe wayar ta kwanta.

A yayin da dikka hakan ke faruwa shi kuwa GAT ya je sun sha hira da daddyn Noor dasu Aunty Lisa a room da aka baiwa daddy. Sai satar kallon Aunty Lisa yake yi, amma bai amayar da abin dake ransa ba. Dik in ta motsa a kan idanunsa ne, tin bata gane ba har ta fara ganewa, dan dik in ta ɗago sai sun haɗa ido, zata ga ita yake kallo, da farko bata ɗauki hakan a komai ba, sai daga baya da ta ga kallon ya yi yawa sai ta fara jin wani tinani a ranta.

Da yake wayayyiya ce, ba kauyanci da shirme a kanta, sai ta ce. "Daddy I'm feeling sleeping"...... Daddy Noor ya amsa mata da ta je ta kwanta mana. Dan ta tabbatar da zarginta ne ta yi hakan, miƙewa ta yi tare da yi masu goodnight ta fito izuwa room da aka saukesu.

Tana fitowa ta ɗan yi gaba kaɗan sai ta tsaya, shiru ta yi tana tinanin meyasa GAT yake kure mata kallo haka?. Bata dawo daga duniyar tinanin ba sai ganin mutum a gabanta ta yi yana faɗin. "Meyatsayar dake a nan pretty?".

Ɗan firgita tai kafin ta ce. "Daddy me ya fito da kai?"........ Waskewa GAT yai da cewa. "Nothing, kawai zan je room ne"....... Ta gano saboda ita ya fito, amma ta nuna bata gane ba ita ma, ta basar tare da yi mashi goodnight zata wuce. Da sauri ya ce. "Let me escord you!".

"Thank you daddy". Cikin ladabi ta faɗa...... "Nevermind dear". Ya faɗa a lokacin da yake isa dab ita, da hannu ya nuna mata hanya ta wuce ya rufa mata baya, dik wani takunta a kan idanunsa har suka isa room ɗin, har ciki ya rakata, a gaban bed ta tsaya tare da cewa. "Thank you daddy".

Kai kawai ya jinjina, ya gagara yin magana kuma yana jin kamar ba zai iya juyawa ya tafi ba. Ganin haka yasa ta ce. "Daddy akwai wani abin ne?". Kai ya girgiza mata alamar a'a babu, amma ya gagara tafiya. Da ta sake tambayarsa rasa me zai ce mata yasa ya ce. "Room ɗin ya yi maku ne ko a canza maku?".

Dik wani take-takensa ta ganosa amma ta basar tare da cewa. "Ya yi sosai daddy"........ "Ba wata damuwa?". Ya faɗa a ɗan dake. Kai ta gyaɗa zuciyarta cike da mamakinsa. "Goodnight". Ya faɗa tare da juyawa, da kyar ya iya daina kallonta ya nufi waje. Dab zai fita ya jugo dan ya saci kallonta, sai suka haɗa ido, ashe shi take kallo, da alama ita ma ta folawa haɗaɗɗen GAT namu, uba ga su V ai kun san ya haɗu.

Still goodnight ɗin nan dai da yaki karewa shi ya sake ce mata kafin ya juya, hannu ta sanya ta toshe baki tana murmushi, dan dik ta gama ganosa. Nauyinta da yake ji yasa bai sake juyowa ba dan kada su sake haɗa ido, sai ya yi zafin namar ficewa, yana jin nauyinta sosai, musamman yadda take ce mashi daddy, yana jin kamar ba zai iya tinkararta da kalmar so ba!.

Yana ficewa ta daka tsalle tare da faɗawa saman


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login