Showing 327001 words to 330000 words out of 365093 words

Chapter 110 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

6200

tana fatan ace ya ga wannan zane.

Shi kuwa cigaba da dannar wayansa ya yi ba tare da ya sake ɗagowa ya kalli in da take bama bare ta ji sanyi a ranta.

-------------------

Tsaye Lion yake a tsakiyar room ɗinsa rike da rigar pjs ɗinsa daya cire, ya kunna light bolb da suka ɗaura a saman tantin wanda ke amfani da solar, haske ya gauraye ko'ina a cikin ɗakin, yana ƙoƙarin ɓalle botiran rigan zai sanya a jikinsa ya fita.

Bakinta a ɗauke da excuse Arya ta shigo cikin tantin rike da hannun yarinyar nan, zata fita ne yarinyar ta ce sam ita ba zata zauna a ɗakin ita kaɗai ba, shi ne Arya ta kamata suka taho tare.

Sake hannunta Arya ta yi game da kamewa ta sarawa Lion tana ɗan yin ƙasa da kai, gabanta sai faɗuwa yake yi na ganin kyakkyawan kakkarfar surar jikinsa, his sixpack was so Masha ALLAH, dole nema ya tafi da tinanin dik wacce ta gansa, gabaɗaya sai ta nemi natsuwarta ta rasa, ai a miliyan ta ɗauke kallonta daga kansa game da sauƙe hannun nata ƙasa.

"Sir akwai abin da yakamata ka zo ka gani, dan bayani da baki ba zai yiwu ba". A dake ta faɗa cikin girmamawa. Kai ya jinjina ba tare da ya yi magana ba. Sake sara mashi ta yi kafin ta kama hannun Jehan su nufi waje tana ɗan waigosa. Cikin tantinsu suka koma, ta zauna a gaban laptop ɗinta game da cewa Jehan ta zauna a saman electric mattress ɗinsu.

Hayewa kai Jehan ta yi tana kallon Arya cike da so, tana son Arya sosai.... Cigaba da abin da take yi Arya ta yi, ita kaɗai a cikin tantin, su V dik suna wajen wutar da suka kunna. After 5mins da kiransa sai ga shi ya shigo sanye da pjs ɗin da yake rike da shi ɗazun, hannunsa rike da wayansa yana pressing, da alama saƙo yake rubutawa.

A dab saitinta ta baya ya ɗan tsaya, sai da ya kammala rubuta saƙon da yake yi ya tura sannan ya sunkuyo kanta game da maido da kallonsa kan laptop ɗin.

Kallon 1 minute ya yi wa laptop ɗin sai kuma ya kai hannunsa sama mouse ɗinta, already hannunta na kai. Ai wani irin yanayin da ta ji ya ziyarce a lokacin da skin ɗinsa ya taɓata ba zai misiltu ba, da sauri ta janye hannunta tana sauke numfashi a hankali-hankali, ga daddaɗar kamshin perfume ɗinsa na kamfanin su Noor dake ta faman tashin kofofin hancinta.

"Wannan ina ne?". Ya faɗa a natse yana mai da kallonsa kan face ɗinsa, ta tsare ƙashin wuyan nan nasa da kallo. Ɗan ɗauke kallonta ta yi game da cewa. "Jiya V ta tura drone mai ɗan girma wajen ne sai suka harbesa, shi ne na tura ƙarami ɗazun dan in ga me yake ɓoye. Waɗan nan mutane sune abin dake wajen".

Cike da mamaki Leo ya sake mai da kallonsa kansu. Wajen tamkar rana, wutar lantarki zaku zaci rana ne, tantuna ne dayawa a kafe a wajen, wlh ya fi sansanin soja haɗuwa, ga wayarin na wutar lantarki da aka yi, amma su sojoji an basu kaya masu amfani sa solar, a wani sashe na wajen mutanen ma gini ne na ɗaki da block da sementi, ta ko'ina matasa ne suke yawo rike da muggan makamai masu rai da lafiyan da babu irinsu a hannun sojoji. Abin mamaki kuma wlh dik matasan nan yara ne da basu kai 20 years ba, suna sanye da rawani a fuska da jallaniya a jikinsu, wasu kuma da irin pakistan riga da wandon nan, sai sha'aninsu suke yi a wajen tamkar a cikin gari.

Riƙaƙƙun ƴan ta'adda ne dake arewacin ƙasar waɗan da suka samu lasisi a ta'addanci, waɗan da manyan ƙasar ke ɗaure masu gindi, suke jin tamkar sun fi karfin kowa da kowa.

Motsa done ɗin Leo ya yi, ya fara controlling ɗinsa yana bin sassan wajen, ta ko'ina matasa ne ke shawagi, a kallah zasu kai matasa 300 kam. Gabaɗaya mamaki ya hana Leo yin dogon tinani a kansu, mai da kallonsa a kan kilomita nawa ne tsakaninsu da mutanen ya yi, a gaskiya suna da nisa sosai.

Cigaba da kutsawa lungu da saƙo na wajen ya yi, fili ne mai girman gaske, tamkar gari, ga lunguna da wajajen ɓoya ba adadi. Juya akalar drone ɗin Leo ya yi ya nufi wani wajen wanda ya ga lantarki yafi yawaita a wajen dan yaga menene. Bolb na wuta ya yawaita a wannan waje. Tura drone ɗin ciki ya yi dan yaga menene.

Ya ilahi ya lillahi, ai Leo bai san lokacin da ya zabura ya miƙe tsaye daga sunkuyon da yake ba. Jama'a, ta'addaci ya yi mugun karfi a arewacin kasar fiye da yadda kuke zato, wannan ɗakin cike yake tab da computers masu inganci, karfin intanet dake wannan waje kusan za'a ce yafi na cikin gari karfi, ashe shiyasa suka iya gano drone na farko suka harbesa, lallai ƴan ƙasa sun yi mugun sake ta'addaci ya yi girman da in ba ALLAH ba babu mai iya kwatarsu.

Wannan abu ya yi matuƙar gigita Leo, kuma ƴan ta'addan aka horar kan sanin computer da iya sarrafata. TO WAYE YA HORAR DA SU A WANNAN FANNI?.

A wannan waje suna da likitocinsu, suna da masu yi masu girki, suna da dik wani abin da ɗan adam zai buƙata dan more rayuwa, dik yadda kuke tinaninsu wlh sun zarce hakan, wannan shi ne ainahin taddacin arewacin ƙasar ba wata rufa-rufa ko sakayawa, ƴan ta'addan suna rayuwar jin daɗi da ƴanci fiye da ƴan ƙasa, abinci available, ga likita, kuma kullum ƙara yawa suke yi, ga karfin internet da aka ja masu har cikin wannan kungurmin dajin, shiyasa zasu kafa waya su yi video son ransu, su saki baya slow na network saboda karfin intanet na kasar rabi dik su aka baiwa, idan sun tashi zuwa yin ta'addaci sai su tura kalilan daga cikinsu da su matsa daga in da suke zuwa gaba ta bakin fita cikin gari su kafa wasu tantunan, sai su yi shiri su shiga gari, su kashe na kashewa su kwashi na kwasa, su dawo dasu sansanin da suka kafa, bayan kwanaki biyu in komai ya lafa su zaɓi waɗan da aka tsara masu kan ba yanzu zasu sakesu ba, su kutsa dasu cikin daji su kaisu babban sassani wajen babban shugabansu.

Saura kuma su barsu a wannan karamin sansani da suka kafa su karɓi kuɗin fansa, waɗan da aka wuce da su babban sansani sai su haura watanni 6-7 a wajen, wasu ma ko an kawo kuɗin fansa basa sakesu, saboda ba'a basu umarnin su sake su ɗin ba, daga sama ake juyasu suma, haka zasu ajiye mutane suna lalata da su, basa zuwa kama mutane haka kawai sai an gama tsara masu ga waɗan da zaku kama, idan kun kamasu ku ware kaza ku turasu babban sansani, kaza ku karɓi kuɗin fansa daga ƙaramin sansani, dik karshen wata waɗan da suke basu umarni suna kiransu su yi lissafi da su, dama already sun san adadin kuɗin da suke baiwa masu basu umarni dik wata. Dik watan ALLAH akwai adadin kuɗin da suke baiwa manyan ƙasar masu ɗaure masu gindi, miliyoyin miliyoyi suke basu, su kuma manyan su basu kayan aiki, bindigu masu inganci, kayan abinci, kayan more rayuwa da kuma wayoyi masu tsada, sannan ga kayan shaye-shaye da suke basu kala-kala, komai ana zuwa da jirgi helicopter a sauke masu kayan abinci, jirgin bata sauƙa ƙasa, a sama take tsayawa ta sake masu makamai da kayan abinci game da dik abin da zasu buƙata.

-----------------------

Bin dik wani lungu da saƙo na wannan ɗaki da drone ɗin Leo ya yi, basu gane cewa drone bane, dan na faɗa maku kamar ƙuda yake....... Ya jima a wannan ɗaki yana kallon irin manyan ingantattun kayan aikin da suke da shi kafin ya fita ya sake shiga ɗakin kusa da wannan.

A nan kuwa mata ya gani, mata dayawan da a kallah zasu kai 250 haka, dik sun yi shunfuɗa dun kwakkwanta. Fita ya yi ya cigaba da yawace wajen da girmansa ya zarce yadda kuke tinani, nan yaga wasu matan suna zaune bakin wuta suna girki sanye da manyan hijabai har ƙasa, daga gani ba tambaya kasan waɗan nan sun zama ƴan gida, sun yi jimawar da duniya ta manta da su a wajen, sun sadaukar da rayuwarsu sun mance da iyalansu ma bakiɗaya, ALLAH sarki, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ALLAH yai maku sakayya, ya bi maku hakkinku, dan na tabbatar kuna da yara da ƴan uwa.

Leo bai san lokacin da ya ɗaura ɗayan hannunsa a kan bakinsa ba, ya kusa suman tsaye saboda tashin hankali, yana jin ta'addanci ta'addanci bai taɓa zaton karfin ta'addancin ya kai har haka a arewacin ƙasar ba, a wannan waje yaushe ƙananan sojoji ƴan bar one zasu iya fito na fito da su? Tsakiyar wannan dokar daji, gaba daji baya daji, ba zaka taɓa zatan akwai ran ɗan adam a wajen ba, ia ilahi, sun kafa wajen kafawar da suna iya ganin dik motsin da zai shigo masu, kafin sojojin su iso in da suke already suna ganinsu ta computers ɗinsu, kafin sojojin su farga sun kewayesu sun masu rubdugu.

Wannan ai sai sojojin da suka samu horo biyu suka amsa sunansu sojoji, sannan a haɗa da air force, a masu ɓarin makauniya na wuta sama da ƙasa, ai masu ruwan boma-bomai sau ɗaya shi ne za'a iya masu ba'a zauna tura ƙananan sojoji masu tasowa ana kashesu a banza ba.

Miƙewa tsaye gabaɗaya Leo ya yi tare da juyawa Arya baya, ya ɗan dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi saboda tsananin ciwo da sara mashi da yake yi, musifar ta zarce tinaninsa.

Sai da ya ɗauki good 5 mins a haka, ya saita natsuwansa kafin nan ya juyo, ya dawo ya sunkuyo kanta, ya sauke ajiyar zuciya ya fi sau uku, damtsen hannunta ya ɗan buga kaɗan game da cewa. "You really try, and i really appreciate".

Sosai ta ji daɗi har cikin ranta ganin yau ya yabawa aikinta...... Ni kam na ce bama dole ya yaba maki ba, irin wannan ɓarna da kika bankaɗo ai wlh ba dik kai ba, za'a tara sojoji 1000 ba'a samu biyu masu kwazonki ba ɗiyar daddynta.

Mai da kallonsa a kan laptop ɗin ya yi yana tunanin lallai zai yi aiki tare da Arya, dan ta fi dik mazan nan amfani, team 1 ne kawai suka ɗarata kwazo a wannan tafiya, amma dik sauran wlh ta fisu jajircewa, lallai zai yi aiki da ita, yana son mutum mai jajircewa.

Cigaba da kallon wajen ya yi, a cikin wani tanti suka gano wani waje tamkar makaranta, ga board da komai, kuma ga alamar rubutu a jikin board ɗin, amma ya gogge ba su iya gane me ake karantarwa a wajen ba, amma tabbas makaranta ce wajen karantar da ƴan ta'adda.

Babban abin da ya ƙara baiwa Leo mamaki shi ne yadda suke pacaka da ruwar roba bama pure water ba, sun fi bayin ALLAH na cikin gari yin rayuwar ƴanci da jin daɗi. Dik da basu ga ainahin cimarsu ba, amma sun fahimci cima mai kyau suke samu, dan sun ga buhu-buhun shinka ta waje, foreign rice kenan.

Tin Leo na mamaki har ya daina, ɗan ƙara rage tsawonsa ya yi game da cewa. "Keep watching they're movements, idan wani sabon abu ya bayyana ki sanar dani, and dik abin da kika gani wanda bamu gani a tare ba make sure you write it down for me, bari in yi meeting da su Zaynish, i will be back in the next 2 hours". Ya kai karshen maganar game da miƙewa tsaye.

Waje ya nufa cikin zafa. Bayansa ta bi da kallo tana jin tamkar ta jawosa ta dawo da shi ya cigaba da magana a kurkusa da ita kada ya dakata, amma ba yadda ta iya, tana gani har ya fita. Yana fita ta ce. "Jehan come close to me in baki yi barci ba".

Da sauri ta ɗago kai jin ta ambaci sunanta, bata jin turanci, bata gane me Arya ta ce ba, sai da ta nuna mata alama da hannu sannan ta miƙe ta zo kusa da ita, a gefenta ta zauna, Arya ta ɗan jawota jikinta tana faɗin. "Zan koya maki computer my girl"...... Ita dai Jehan bata ji komai ba, kallon laptop ɗin kawai take yi. Arya kuwa ta cigaba da aiki, wani lokaci idan ta yi pressing wani abin sai ta cewa Jehan wannan abu kaza yake nufi, dik da yanrinyar bata jin yaren amma tana fahimtar nufin Arya tin da in tana mata bayani tana gwadawa da hannu.

A can kuwa, Leo ya yi wa Noor message kan ya kira Vash and Zaynish su same shi a ɗaki yanzun nan. Ba'afi 5 mins ba sai gasu sun bayyana. Umarni ya basu kan su zazzauna, a dake suka karɓi umarni, suka zazzauna suna fuskantar juna.

Cikin natsuwa ya zayyana masu dik abin da ya gani a cikin wannan daji ɓangaren aikin su Arya. Hakika hankulansu ya yi mugun tashi, amma sai suka daidaita natsuwarsu, Noor ya ce. "Okey, the reason why our seniors always saying North is different? Oh, kenan they already knows that akwai gagarumin matsala?".

Vash ya amsa da. "Of course, but keep all this aside, let's focus on wancan hayakin, mu gano menene, wannan case ɗin babba ne, sai mun fara gano hayakin mecece a wajen can before mu takalo faɗa da waɗan can riƙaƙƙun yan ta'addan".

Jinjina kai suka yi, sun gamsu da kalaman Vash, dole su fara da batun hayakin nan, dan waɗan nan riƙaƙƙun ƴan ta'addan sai sun shirya masu.

Gyaran murya Leo ya ɗan yi wanda yasa dik suka ƙara natsuwa suka kuma yi tsit. A natse sosai ya ce. "Zamu raba aikin nan yadda zai fi yi mana sauri da kuma sauƙi"......... Basu gane nufinsa ba, sai suka bisa da kallo suna jiran dogon bayani.

"Kowani soja a cikinmu zai ɗauki jami'a ɗaya su yi aiki a tare, hakan zai tafi daidai, zamu tafi da fly drone ɗinsu na sirri, idan mun je wajen hayakin zamu rabu ne kashi huɗu, kowanne zai kama hanyar da zai bi, a kan hanyar da zai bi zai saki wannan drone, jami'ar da suke aiki da ita zata na duba mashi hanyar da yake bi ɗin tana bashi information a kai, hakan zai sa suma matan su bada himma, for now kunga su ukun dik basu bada himma ba, ɗaya ce mai fafutuka".

Jinjina kai suka yi, sun yi na'am da wannan shawara....... A kan Noor Leo ya tsayar da idanunsa kafin ya ce. "Bayan aiki ban ce ku ɓige da wani abin ba, dan ma dai an ɗaura ne ba halin in haɗata da wani da na maka canji".

Noor ya gane karatun, watau Leo ya gano cewa shi lover boy ne, shi ne har da yi mashi gargaɗi, siririn murmushi ya ɗan yi kafin ya ce. "Amma ai ya halatta idan ta binciko mun abu mai ma'ana in na ji daɗi in bata sumbata a cheek ko?"...... Kunnensa Zaynish ya kama, ya ɗan murɗa kafin ya ce. "Da a iya wannan zaka tsaya to da sauƙi, nasan halinka sarai, zama ka iya mantawa da aiki kuke yi ka zarce wani wajen, ni shawarata a rabasu, a haɗata da wani ɗin kawai tin da a bakin aiki muke, shi ma a haɗa shi da wata".

Vash na murmushi ya ce. "Wannan shawara ta yi, kawai a rabasu"...... Buge hannun Zaynish Noor ya yi game da cewa. "In ga yadda za'ayi a haɗa matata da wani kato! Ni da kayana? A ina aka taɓa hakan?". Yana tamke fuska ya faɗa, wai dan ma su san ba da wasa yake yi ba.

Shi dai Leo bai ce masu komai ba, ya jawo laptop ɗinsa, ya fito da sunan dikka sojojin da suka zo da su wannan Mission ɗin, sojoji bar one su 34 ne, sai bar 2 team 1 and team 2 su 8, sai kuma su Arya su 4, dik in an haɗa su 46 kenan.

Fito da information a kan su Arya ya yi, ya zari V daga cikinsu ya turawa Noor Information ɗinta ta email ɗinsa kai tsaye ta sauƙa a laptop ɗin, a ƙasan information ɗin ya zayyana mashi aikin da zasu yi tare, dokokin aiki da tsare-tsaren da ya dace!.

Kada ku manta team 1 dik suna da laptop a halin yanzu...... Daga nan ya zaƙulo bayanan Angelina ya turawa Zaynish da nashi bayanin shi ma. Fito da bayanan Manassa ya yi, ya san ba jami'a bace, surgeon division general ce, amma dik da takasance likitar sojoji a jikinsa yana jin tana da sani kan aiki irin nasu Arya, kuma ya san dik da take surgeon general to fa anbata horon kare kai, dan wannan dokar AZURE ce, harta likitocin sojoji suna karɓar hoto dan kare kansu.

Dan haka sai ya ce. "Arvash kira mun Manassa yanzu"....... Miƙewa Vash ya yi, ya fito. Zaune ya iskota suna hira da Juraiz, ta ɗan saki jiki tana biye mashi, a tinanin Juraiz V ce ba Manassa ba, dan shi baya iya rabesu fa, shiyasa ya tsaya sai tsarata yake yi.

Take kishin larabawan ta motsa, tamke fuska ya yi sosai game da cewa. "Ke! Sir Nirash na kiranki". Yana faɗa ya juya ba tare da ya kalli in da Juraiz yake ba. A hanzarce ta miƙe, bata lura da yanayin face ɗinsa ba, da sauri ta rufa mashi baya suka shiga tantin Leo.

Kamewa ta yi ta sara mashi kafin ta ce gatan nan......... A dake ya tambayeta game da aiki irin nasu Arya shin tana da kwarewa a kai?..... Kai ta gyaɗa game da sanar dashi cewa dik abin da su Arya suka sani ita ma ta sani kamar yadda dik abinda ta sani a ɓangaren nata aikin suma sun sani. Ya ji daɗin jin hakan, sai ya ce. "You can go". Ya faɗa game da dawo da kallonsa a kan laptop ɗinsa.

Take ya kwashi bayananta ya turawa Vash da bayanin yadda zasu yi aiki a tare........ Ita kuwa ta zo dab zata fita Vash ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login