Showing 246001 words to 249000 words out of 365093 words

Chapter 83 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5884

ɗagata sai saman shoulder ɗinsa, su Aunty Safiyya sai kallonsu suke yi. Bai direta a ko'ina ba sai cikin room ɗinta, a tsakiya ya direta tare da fara ƙoƙarin yi mata magana.

Haba ganin bata da mafita ne, babu mai iya kwatarta a hannunsa ne yasa ta tuna abin da ta karanta a littafan can, yadda ake controlling fushin namiji, dan haka dole ta yi amfani da wannan dabara, dan wlh tana balain tsoron dukan Aryan, ta j kamshin lahira ranar, bata son ko a mafarki ta ƙara jin even one slap from him.

Da sauri ta datse idanu, ta faɗo jikinsa, hot hug ta bashi game da saka mashi kukan shagwaɓa, tana goggoga kanta a saman lion chest ɗinsa..... Jimmmmm haka ya ji duniya ta tsaya mashi, omg, this kukan shagwaɓa melted his heart over, ga goga kanta a kirjinsa da take yi, ga shi she hugged him tightly, ai ɗauke wuta ya yi, zuciyansa na wani irin spark na shauƙin ƙaunarta....... 👀

Cikin kukan shagwaɓa ta ce. "I'm so so sorryyyyyyyyyy daddy, ba zan sake ba, for give me my gentle chaos"...... Oh God, this gal ta gama da daddy yau, wannan suna da ta kirasa my gentle chaos ya gama narka mashi fushin da ya ɗebo, fushin ya narke ya koma so da kaunarta sabo!. Bai san time da ya rungumeta tightly ba, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fushi ta gudu.

Da jin ya rungumeta ba karamar daɗi ta ji ba, ta ƙara shigewa jikinsa sosai. Shiru suka yi, shessheƙar kukan shagwaɓarta na tashi a hankali-hankali, yasa hannu yana ɗan shafa kanta izuwa kan bayanta. Gabaɗaya ya shige love mood, har ya manta cewa Campaion na IRON FIST yake!.

Sun ɗauki 10 mins a haka, slowly ya saketa, ya raba jikinsu, saman sofa ya koma ya zauna, ya jingina kansa shiru tamkar mai tinanin wani abin, ya ɗan lumshe idanunsa soyayyarta na kara ratsa shi sosai. Ganin haka yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da zuwa ta zauna a kusa da shi saman bed, tana kallon kyakkyawan face ɗinsa.

Ni kam na ce daddy fa ya yi mugun nisa a soyayyar Cherry bloom ɗin nan nasa, sai abin da muka gani, yanzu ita ke rike da ragamar zuciyansa, amma yarinta yasa ba zata gane cewa zata iya juya shi ba, ko Abba ba zai iya juya shi cikin sauƙi ba, amma ita zata iya a sauƙaƙe cikin kwanciyar hankali ma kuwa, amma ba zata gane hakan ba. To me kuke tinanin zai biyo baya? Ga su dai zaune shiru Cherry ta zuba mashi ido, idan ya wastsake ya dawo daga duniyar da ta jefasa me kuke tinani zai faru? Ƴar yarinya da ita tana son fin karfinmu, tasan komai, to thank god dai da bata fara aikata komai ɗin ba daddy ya farga!.

Tin da sun zauna shiru bari mu leƙa wani ɓangare, watakila kafin mu dawo shi ma daddy ya dawo daidai ya wastsake.

--------------------------

Zaune Abba yake a main parlo, yana rike da littafin The Franklin Scandal yana karantawa, hannunsa rike da gold scepter ɗinsa, ya miƙe kafafunsa saman lallausan throw pillow ɗin dake a gabansa, hankalinsa ya karkata kan littafin.

Cikin natsuwa Ammie ta sauƙo ƙasa, tana tafiya tana wuwwurga idanu in da zata gano Rimsha ya jikin Abba, dan tasan lokacin dawowarta daga school ya yi. A gefen Abba ta zauna tare da cewa. "Barka da hutawa ranka ya dade".

Abba gwani a izza da isa, kai tattijon nan akwai taƙama da nuna karfin iko game da fadanci, anya Abba ba jinin sarauta bane ba kuwa?....... Sai da ya ɗauki mintuna kafin ya rufe littafin hannunsa, a natse ya ce da Ammie. "Yauwa sannu da fitowa".

"Ban ga Rimsha ba". Ammie ta faɗa tana miƙa hannu ta karɓi sandar hannunsa, ta kwantar a ƙasa...... "Basu shigo ba ai".... Shiru Ammie ta ɗan yi, can kuma ta ce. "Nasan dik abin da ka yanke abu ne mai kyau, baka yanke abin da bai dace ba, kuma dik abin da ka yanke muna biyayya da kuma mubaya'a a garesa, amma a wannan karon ina neman alfarma dan ALLAH! ALLAH ya kara maka nisan kwana da lafiya".

Bai amsa ba, ya dai zuba mata idanu yana kallonta, tasan halinsa sarai, shirunsa ma magana ce, dan haka sai ta cigaba da cewa. "Dan ALLAH ka bar batun haɗa wannan aure na su Aryan da waɗan can yaran.....". Gagara karisawa ta yi saboda ɗan waro idanunsa a kanta da ya yi, mamaki ne ya kamasa jin yau karo na farko a gidansa ya yanke hukunci ake neman yi mashi katsalandan, abin da ba'a taɓa yi ba kenan.

"ALLAH ya baka hakuri, tuba nike". Ammie mace mai biyayya ta faɗa, sam ita bata son ai wa ɗanta auren dolen nan ne, dan ya ce mata baya so, sun yi waya jiya, ya faɗa mata muddin Abba yai wannan aure to ta sani kome ya biyo baya su suka ja, shi ya gama magana, baya son auren kuma ba zai yi ba! Idan aka matsa mashi ran kowa ba zai yi daɗi bane.

Ammie tasan waye Aryan fiye da yadda Abba ya sanshi, tasan baya magana biyu, lallai dik wacce aka aura mashi sai ta gwammaci da bata zo duniya bama, dan billahil lazi mancewa da cewa ita macece zai yi, dama can maza suke yi wa kallon mata, aikuwa yarinya zata ji a jikinta ne!.

Nisawa Abba ya yi, zai yi magana kenan sai suka ji ana knocking na parlo door ɗinsu. Wayansa dake gefensa Abba ya ɗauko, app na door ɗin ya shiga, akwai camera a jikin kofar ta baya, so idan kuka shiga cikin app ɗin zaku iya shiga Camera ku ga wanene yake knocking kuna daga zaune!...... Uhm duniya ta cigaba, ALLAH ka wadatamu da ire-iren waɗan nan cigaban a ƙasarmu.

Yana dubawa ya ga Aunty Luna tsaye a bakin door. Ai da sauri ya danna door control, options suka bayyana, sannan ya danna open. Take dik wasu locks na kofar ta buɗe, ta ɗan motsa ta buɗe kaɗan. Turowa Aunty Luna ta yi ta shigo. Tana shirye cikin shiga ta alfarma, tana shirye cikin black jean, white top and winter jacket wanda ya zo mata har gwiwa a saman kayan, ta yi matuƙar kyau sosai, tana da natsuwa da hankali.

Gaban Abba ta kariso, har ƙasa da durkutsa ta gaida shi cikin girmamawa, sannan ta ɗagawa Ammie ma gaisuwa. Dik da cewa Abba baya dariya, kai face ɗinsa ba zaku taɓa zatan yasan me murmushi ba, amma har cikin ransa ya ji matuƙar daɗin ganin Aunty Luna, a mutunce ya amsa gaisuwarta tare da ce mata ta zauna, ya nuna mata ƙasa saman carpet, dan shi Abba akwai izzar balai, idan yana saman kujera ba'a zama a sama kai tsaye.

Zama ta yi. Shiru ne ya ɗan biyo baya, sai kuma can ta ce. "Dama na zo ne in baka hakuri kan abin da ya faru, daddyna ma ya ce in baka hakuri, abin bai yi mana daɗi ba, bamu ji daɗin abin da grandpa ya yi ba"......... Still dai fuskan Abba babu fara'a ya amsa da. "Kada ki damu surukata, in kin je gida ki sanar da daddyn naki gobe da kaina ina kawo mashi sadaki".

Murmushi ne ya kubce mata, dan ita dai har ga ALLAH tana matuƙar son Harleen, tin da ta kyalla idanu ta ga haɗuwarsa, gabaɗaya ta rasa kanta, kai jinin Abba ba dai haɗuwa ba, ga iya ɗaukar wanka, kai Masha ALLAH kawai zamu ce.

Ta ɗan yi ƙasa da kai bata ce komai ba, ganin haka yasa Abba ya ce mata. "Ki je sama Harleen yana ɗakinsa, ku gaisa kafin ki koma ko?". Tamkar Abba yasan abin dake ranta, tana son ganinsa ne dama, amma ta rasa yadda zata faɗawa Abba, bata san meyasa dik rashin kunya irin nasu na European amma take matukar shakkar Abba, yai mata mugun kwarjini, ganin cikin idanunsa wannan ta gagara yi, to haka Aryan yake, wlh ba kowa yake iya ganin cikin idanunsa ba, bare Lion da Vir, kai IRIN FIST dikka zaku zaci jinin Abba ne su ɗin, akwai su da balain kwarjini, cika ido, sanyawa mutum zarra, izza, isa da taƙama, yadda kuka ga Abba da karfin halin aurar da yara ko ubansu bai so ba, haka IRON FIST suke da shegen nuna iko a koma inane!.

Miƙewa ta yi, ba kunya ta dinga zubawa Abba godiya, sai ta nufi sama. Ammie kam ta saki ido tana kallonsu, watau Ammie bata waye sosai bane, da sauran hijabin kunyarta in faɗa maku, amma Abba, ba dan wani abin ba, ba dan ina tsoron daddy Champion ba, da na ce Abba taƙadarin ɗan duniya ne! Amma ina tsoron Aryan, na yi shiru!.

Har ta haye sai kuma ta tsaya game da juyowa, bata iya kallon face ɗin Abba kai tsaye ba, tana facing Ammie ta ce. "Daddy ina ne room ɗinsa?"...... Abba dake kallonta ne ya amsa da. "Abba zaki kirani, room ɗinsa na side two daga parlon sama"...... Da okey ta amsa game da cewa thank you Abba tana murmusawan dake kara fito da kyanta.

Ta juya ta karisa cikin second parlo. Kai tsaye ta nufi room ɗinsa. Yana kwance saman bed, daga shi sai shorts and singlet, hannunsa rike da waya yana dannawa, ya rungumo pillow a kirji, while ya ɗaura kafafunsa a kan wasu pillows ɗin, da alama yana jin daɗin yanayin da yake a ciki.

A natse ta turo kofar ta shigo, sarai ya ji an turo kofa, amma ya zaci Faryan ne sai bai ɗago kai ba, dan yasan kofar ɗakinsu ai sai su kaɗai zasu iya buɗewa, dan haka bai zaci wata ce daga waje ba. Ita kuwa Abba ne ya buɗe mata kofar daga in da yake zaune a parlo, tin kan ta karisa ya danna open na side two doors, tana zuwa ta ga kofar a ɗan ture.

Karisowa ciki ta yi, ko kaɗan bai ɗaga ido ba, abin da ya kara burgeta da shi kenan, wannan miskilanci da izzar tasu! Ga ɗan banzan girman kai wai sun fi karfin cewa sorry, zaku shiga hannun nisau ne dan ubanku Abba Khaiza'an, mu zaku gwadawa iskanci? Yanzu lokacinku ne, ku gama shan kamshinku zamu damƙeku ne, Aunty Luna kada ki kyale ɗan air, ki gyara mashi zama, ki ganar da shi mu fa nisa'u ba'a mana wannan shirmen!.

Har ta iso gaban bed ɗin bai ɗago kai ba, sai da ta zauna a dab da shi, tasa hannu cike da yanga irin namu na mata, ga natsuwa ta karɓi wayan hannun nasa ne ya wani irin ɗawo dara-daran eyes ɗinsa a slow motion. Ai yana sauke idanu kan face ɗin mace bai san time da ya zarosu waje sosai ba, sai ya ɗan miƙe daga kishingiɗar da ya yi, ya zauna da kyau yana kallonta babu ko kyaftawa.

Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Good afternoon oga sir".......... Shiru bai amsa ba, sai ma juya idanu da ya yi, ya kalli door ɗin shigowa, kafin a natse ya dawo da kallonsa a kanta. Ɗan ɗaure fuska ya yi, a dake ya ce. "What brought you here?"..

Nisawa ta ɗan yi kafin in a cool way sosai ta ce. "Coming to see your beautiful face, tin ranar baka sake dawowa ba, ka barni da tinaninka a cikin rai, shin ban maka bane? Baka son haɗin Abbanmu ne? Ko akwai abin da baka so a tattare dani ne?". Ta faɗa tana ɗan jujjuya wayansa dake hannunta.

Slowly ya ɗan fara yin ƙasa da idanunsa daga kan face ɗinta, ya fara bin sassan jikinta da kallo. Hakika idan ya ce bata haɗu ba ma ya yi karya, yaudarar kansa zai iya idan ya ce ba haɗaɗɗiya bace, kuma wlh idan kuka ganta ba zaku zaci ta kai 20 years bama, ai kun san yadda jikinsu yake da mugun kyau, gata ƴar kwalisa.

Ganin ya yi shiru yana bin jikinta da kallo ne yasa ta kai hannu saman soft cheek ɗinsa, ta shafi wajen sajensa dake kwance luff kafin cikin salo mai ɗaukar hankali ta ce. "I love this". Tana shafa sajen ta faɗa, sai kuma ta sake cewa. "Ka zo har gida, ka barni for more then 20 mins a tsaye, kana tinanin ka ci banza ko? You most pay it as soon as possible". Ta dakata da maganar tana kallon face ɗinsa da kyau.

Slowly ta mayar da hannunta izuwa kan kyakkyawan wuyansa, ta gangaro zuwa kirjinsa. "Everything of yours is so special"....... Yunkurawa yai zai yi magana kenan ta yi gaggawar mai da yatsanta saman soft lips ɗinsa, ta ɗaura yatsan nata game da cewa. "Shiiiiiiiii". Ta faɗa tana matso da face ɗinta dab shi.

"Now is my time, ka gama naka time da ka je gidanmu". Ta faɗa cikin wani irin romantic way, shi kansa maganar nata cikin wani irin yanayi ya fita, wanda sai da ya sanya gabaɗaya jikinsa ya amsa, to shi tin da ba dutse ba ai dole ƙararrawarsa ta buga! Sai ga malam Harleen ya shiga natsuwarsa, wasu malam shiru ne suka shigesa, tsit kake ji.

Kara matso da face ɗinta dan shi ta yi, ta zame yatsan nata daga bakinsa, suna iya shaƙar numfashin juna, can ƙasa ta ce. "Meyasa ban yi maka a matsayin mata ba? Faɗa mun in ji"...... Ba sai ga malam Harleen da rarraba idanunsa a cikin nata ba, ya gagara yin magana.

Haɗe fuskokinsu waje guda ta yi, ta sanya ɗayan hannunta ta zagayo da shi ta bayansa, ɗayan hannunta kuma ta saƙalo wuyansa, kafin ya farga ta haɗe bakinsu waje guda.......... 👀

Hot kiss ta bashi na just 5 second, slowly ta fara zame bakinta daga nasa, sai dai ga dikkan alamu munahiki bai so ta cire bakin nata ba, dan har ɗan wani kama lips ɗinta yake yi, ta jisa sarai, amma ta basar ta zame bakinta, dan dama burinta ta kwaɗaita mashi, ta kuma rikita shi sai ta gudu ta barshi ta yadda dole ne ma yai tinaninta har ya biyota gida.

Tana zame bakinta ta kalli cikin kwayar idanunsa da suka fara rikiɗewa izuwa ja. "Sai kazo gida"...... Ta faɗa tare da sakesa, ta miƙe tsaye, ai tamkar wawa haka ya zama, sai ya bita da idanu kawai yana kallon yadda take taku tamkar wahainiya, gabaɗaya ya jisa a duniyar sama jannaty.

Sai da ta fice ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, ɗan lumshe idanu ya yi yana tariyo daɗin soft lips ɗinta, ya ALLAH, shi kaɗai yasan me ya ji, a ƙasan zuciyansa ya ce zuma, a fili kuma da miskilancin ta motsa sai ya yi gaggawar kawar da tinaninta, har da sa hannu ya fara goge bakinsa yana jan dogon tsaki, shi a dole zai yi avoiding ɗin abin, bayan kuma ƙasan zuciya ta kyatsa har da lashe baki, munahiki bai so ma ta dakatar da kiss ɗin iya haka ba.

Ita kuwa tana fitowa ƙasa ta sauƙo, a cikin ranta taka faɗin ta kunnasa kenan, da kansa zai kawo kansa ne ma, tana sonshi so na tsakani da ALLAH, ga shi bata da matsala, wayayyiya ce kuma sosai, bata bari kanta ya kulle.

Yadda ta bar su Abba haka ta iskosu, ƙasa ta ɗan duƙa tana yi masu sallama kenan suka ji knocking. Abba dake rike da waya ne ya duba wanene? Can ya gano grandpa ɗinsu Noor ne. Buɗe masu kofa ya yi. Cikin faɗa dattijon ya afko ciki, yana wani muzurai tamkar zai saka duka, cike da sababi ya fara zazzaga masifar ina jikarsa? Ai Aunty Lusi ta faɗa mashi nan ta yo, ya sha alwashin ba zai rabu da Khaiza'an ba, zai sace mashi ɗiya ya lalata.

Tin da ya shigo yake wannan balai har ya kariso tsakiyar parlon. Daidai lokacin Faryan da Rimsha suka shigo. A natse Harleen ya sauƙo ƙasa jin banbamin dattijon. Shi kuwa daddyn Noor yana office bai san wani waina ake toyawa ba, shi dai kawai ya ce Aunty Luna ta zo ta bawa Abba hakuri a madadinsa tin da Aryan ya hana shi shiga.

Da sauri dattijon ya zo ya rike Aunty Luna yana faɗin. "Basu yi maki komai ba ko?".......... Faryan da ya shigo yanzu ne ya ce. "Ammie ina son yin magana dake". Daidai lokacin grandpa ya nuna family da sandar hannunsa, cike da masifa ya ce. "Ba zan kyaleku ba! Dole hukuma ta ɗauki mataki a kanku, dole a shiga tsakanina da ku! Sai na gwada maku karfin dukiya! Sai na ɗaure dikka zuriarku, mutanen banza kawai". Aunty Luna na kokarin dakatar da shi amma ina, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba.

Wucewa Harleen ya yi, ya zauna a saman carpet kusa da Abba tare da miƙe kafafunsa, tamkar bai ga grandpa ba, while ita kuma Rimsha ta nufi sama tana faɗin. "Ammie bari in cire uniform ɗina ina zuwa in baki labarin Seraphinata yau ma". Ammie dai bata da aiki kullum sai sauraren labarin Seraph, dik Rimsha ta addaba masu.

Faryan da ya zauna kusa da Ammie tare da kwanto da jikinsa a jikin Ammie ɗin ne ya ce. "Ammie na gaji, zo mu je in baki wani labari".......... Abba ya ce. "Gulma zaka kai mata ko?". Yana ɗan murmushi ya ce. "Kai Abbanmu, ai mu bama gulma, wani labari zan bata fa, ina wannan kawar Rimsha Seraphina ɗin?".

Jinjina kai su Abba suka yi, dan dik wanda yake tare da Rimsha yasan labarin Seraphina. "To yarinyar yau saura kaɗan daddynta ya mun duka, wai dan kawai Rimsha ta ce mu yi dropping ɗinta a gida, zamu ɗauketa sai ga daddynta, labarin nike son baiwa Ammie fa Abba"....... Abba na ƙara tsare gida ya amsa da. "Waye shi da har ya isa ya taɓaka? Waye shi? Dame yake taƙama? Autan nawa zai taɓa? Waye ubansa a faɗin US!". On a serious note Abba ya yi magana......... Ni kam da nike laɓe a gefe na ce waye ubansa kuma ya wuce Muhammad Khaiza'an dake wannan magana! Ko ya kuka ce ƴan amana?.

Watau Khaiza'ans family muggan ƴan mannin hauka ne, sun baiwa banza ajiyar grandpa, tamkar basu san yana wajen ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login