Showing 153001 words to 156000 words out of 365093 words

Chapter 52 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

6182

ɗin dik ki miƙo mun".......… Da sauri ta ɗago ta kallesa, ya shirya cikin kayan yaki, waist ɗinsa ɗaure da bullets cover, yana kokarin gyara bindigar hannunsa. Sai da ta ji faɗuwar gaba, take ta ji tsoron su je su mutu a can ya kamata, ita da take cewa zata dinga basu wrong information idan sun tafi yaki sai ga ta cikin tsoron kada su je basu dawo ba, watau ita imani da tausayi a zuciya take ba'a kan fuska ba, ɗaure fuska ba shi ke gwada rashin imanin mutum ba.

Jikinta dik ya mutu ta haɗa bluetooths ɗin ta yi connecting ɗinsu da sautin nata, ta yadda suna kutsawa cikin daji ita kuma tana magana, ma'ana tana directing ɗinsu a kan hanya while tana ganin rahoton da drone ɗinta ke ɗauko mata.

Bluetooth uku ta ɗauka ta nufo shi, a natse ta miƙa mashi tare da cewa. "This is it". ....... Ba tare da ya ɗago ya kalleta ba ya karɓa ya juya, da gudu su Angelina suka fito dan ganinsu, sun sha mamakin ganin dikka mazan sun yi shirin yaki, suna rike da bindigu, babu alamar wasa a tattare da su, dik sun tsaya a layi sun yi shirin mutuwa ko rayuwa.

Miƙewa Noor and Zaynish bluetooth ɗin hannunsa ɗaiɗai Leo ya yi, shi kuma ya sanya ɗaya a kunnensa, cikin sirri yai mashi bayanin yadda zasu tafi, daga nan ya ce su shirya. V na tsaye tana kallon Noor da yake ƙoƙarin sanya bluetooth a kunne, ba zaka taɓa cewa shi bane, fuskan nan babu alamar wasa, lallai ya cika alkawarinsa da ya ɗauka na cewa ba zai bari soyayya ta ɗauke mashi hankali daga kan aiki ba, ko sallama bai zo sun yi ba, aikin dake gabansa kawai yasa kai.

Bayan ya kammala shirinsa tsab sai ya ɗago ya kalleta. Hannu ya ɗaga yai mata alamar heart da shi, slowly ya motsa lips ɗinsa wajen cewa. "I love you". Ko kaɗan babu fara'a a kan fuskansa, yanzu ya tashi daga Romeo ya rikiɗa zuwa AZURE SOLDIER kuma member of DOL!. Kallon shi cike da fargaba kawai take yi, ta gagara iya mayar mashi da martanin love ɗin da ya furta mata, ganin haka yasa ya ɗauke kansa daga kallonta, dan kada ma ta raunata mashi zuciya.

Sojoji 20 suka tafi, suka bar 4 a tare da su Arya dan su basu tsaro, su V suna kallonsu har suka wuce cikin shirin yaki. Bayan sun ɓacewa ganinsu ne suka juya da nufin su koma cikin tantinansu sai Arya ta ji alamar kuka kamar kuma motsi ta can nesa da tantinsu. Cike da jarumta ta nufi wajen, tin daga nesa tana jiyo kukan tana bibiya har ta isa wajen, yana da nisa daga in da suke, sannan wajen bakin ruwan dake kusa da su ɗin nan ne amma ta can.

Tin daga nesa ta hango mutum a bakin ruwan zaune dirshan a ƙasa tana kuka. Da sauri ta karisa wajen, yarinya ce karama da bata wuci 10 years ba, kyakkyawar gaske, irin masu kiwon shanun nan ne. Arya ta ɗan ji tsoronta kaɗan, saboda bata zaci mutum bace, gata a tsakiyar dokar daji, gata kyakkyawa, sannan tana zaune kusa da ruwa tana kuka, sai ta zaci ƴar ruwa ce kawai.

Kamar zata juya, sai ta tina ba'a san sojoji da tsoro da sarewa ba, hakan yasa ta ji kwarin gwiwa, da sauri ta nufi yarinyar. A gabanta ta tsugunna tare da dafa shoulders ɗinta, a sanyayye ta ce. "Why are crying? Where's your mom?".

Ɗago kai yarinyar ta yi ta kalleta, sai da gaban Arya ya faɗi ganin a fusge yarinyar taso yi mata kama da Leo, amma kama ta jini haka ba ta fuska ba. Ni kam na ce Arya ko dai ko dai? Ko dik damuwa da shi ne yasa kike ganin masu kama da shi?.

Da hannu yarinyar tai mata nuni da wani jarka na ruwanta da take ɗeba, ta zo ɗeba ne ya kwace ya faɗa cikin ruwan, ita kuma tana tsoron shiga, shi ne ta zauna ta hau kuka. Kallon jarkan ruwan nasu Arya ta yi, ta fahimci yarinyar bata jin turanci, a ranta ta ce to wace yare yarinyar take ji?.

Ganin bata da lokacin ɓatawa wajen buƙatar gane yaren yarinyar ne tin da ga su Leo sun tafi kuma dole zasu buƙaci information daga wajenta, sai ta yi saurin miƙewa, cikin zafin nama ta faɗa cikin ruwan, iyo ta yi har izuwa in da jarkan yake, ta fito da shi tare da zuwa ta miƙawa yarinyar, sai da ta miƙar da ita, dik da yakansance yarinyar jikinta dik datti Arya bata kyamaceta ba, ta sanya hannu ta kakkaɓe mata jiki sannan ta ce to ta tafi.

Alama yarinyar tai mata da cewa zata ɗebi ruwa kafin ta tafi, karɓar jarkar Arya ta yi, ta cika mata da ruwa sannan ta ɗaura mata a kai, ta ce ta tafi. Wucewa ta yi tana waigo Arya, ita ma tsayuwa ta yi tana kallonta har ta kurewa ganinta, mamaki Arya take yi ta yadda aka yi mutane ke rayuwa a wannan dajin! Ganin yarinyar ta tafi yasa ita ma ta wuce da sauri ta koma wajen tantinsu.

Canza kayan jikinta ta yi, sai tambayarta ina ta je ta jike su V suke yi, amma bata kula kowa ba, ta canza kaya ta zo ta hau kan aikinta, watau Arya tana da kyakkyawar zuciya, kawai halinta ne a haka na rashin son shiga mutane da ware kai, rashin son hayaniya da ɗauke kai a abu ga tsiwa da riko, amma batu na kirki a zuciya yake, kuma zuciyarta tas yake a kan hakan.

Ita kuwa V sai ƙoƙarin kiran Noor take yi, ta manta basa zuwa farmaki da waya, dik wayoyinsu na tantunansu, daga su sai bullets and gun suka tafi. Angelina na ta faman kallon hotunan da tai wa su Unays ɗazun, while Manassa ta yi shiru tana tinanin guy ɗin da suka haɗu da shi ɗazun da ta je yin brush.

Tana tafiya tana waige-waige kawai ta ci karo da shi, baya ya ja tare da kura mata idanu kafin ya ce mata ita ɗin kyakkyawa ce. Shiru bata mashi magana ba, ta matsa gefe ta cigaba da goge bakinta, unexpected daga bayanta ta ji ya zuro hannu ya karɓi brush ɗin, goge mata bakin ya dinga yi har sai da hakwaranta suka fita. Juyawa ta yi ta ɗan turesa ganin ba zai daina goge mata bakin ba.

Ta ɗaure fuska tamau kafin ta ce. "Waye ya baka izinin ka taɓani ko wani abin nawa?". ........ Yana kallon kyakkyawan face ɗinta ya amsa da. "No body, haɗuwarki ce kawai sila, kuma ai gaba nike dake a wajen aiki, kinga ba sai kin bani izinin yin abu ba, ni ne ma zan baki izini!!"...... Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Kasan wacece ni kuwa da kake maganar gaba kake dani a aiki?!".

"Soja ce ke kamar ni, ke jami'ar computer ni kuma jami'in bindiga, that's all"......... "Haka kake tinani?!"..... Ta faɗa a fusace. Kai ya gyaɗa mata alamar kwarai haka yake tinani. Screen light na wayarta ta kunna tare da juya mashi. Ai yana kallon hoton kan wallpaper ɗinta bai san lokacin da ya saki brush na hannunsa ba.

Ɗan ja baya daga kusa da ita ya yi, with do respect ya ce. "Sorry madam". Ya ganta tare da daddynsu ne da su Arya, shi ne ya kiɗime haka, ya ga GAT. Harara ta dallah mashi tare da miƙa mashi hannu kan ya bata brush ɗinta, da sauri ya duƙa ya ɗauko ya miƙa mata, karɓa ta yi ta wuce ta nufi hanyar shiga room ɗinsu. Sai dab zata shiga ɗakin ne ta juyo ta saci kallonsa, ya yi mugun tafiya da imaninta, amma tin da yana tsoron daddynta sai ta yi ya ja mashi rai da barazana kafin ta sake da shi.

A TINANINKU DA WAYE TA HAƊU?.

To su Leo sai dai mu ce ALLAH ya tsare ya maido mana da ku gida lafiya, ya baku iko a kan waɗan nan ƴan ta'addan, su Arya ALLAH ya dafa maku ku naɗi information na komai da taka tsantsan ba tare da ƴan ta'addan sun gano drone na camerarku ba, ku naɗi komai ku bawa su Leo namu a kan lokaci kuma daidai ta yadda zasu yi aiki cikin hikima da kwarewa!. Kun ji halin da ƴan team DOL suke ko? To mu leƙa asibiti kafin mu wuce CP.

--------------------------🔥

WS-HOSPITAL.💔🥲

Zaune Maya ta isko Dr Kamal yana aiki a desktop computer dake gabansa, idanunsa sanye da eyes care, ga dikkan alamu ba aikin wasa yake yi ba, ya dukufa haikam.

Excuse tai mashi har sai da ta jira ya bata izinin shigowa bayan ta wuce PA ɗinsa kenan. A saman visitor chair ta zauna, cikin girmamawa ta ce. "Good morning sir"....... Bai amsa ba, hasali bai ma ɗago ba, yana cigaba kawai da aikinsa. Shiru ta zuba ido tana kallon irin haɗuwar office ɗin nan, komai na cikin office ɗin luxury one ne, ga wani haɗaɗɗen kamshi dake tashi.

Zaman good 30 mins ta yi kafin ya ɗauke idanunsa daga kan computer ya mai da shi gabaɗaya a kanta, slowly ya zame hannnunsa daga kan keyboard na computer kafin ya cire eyes protection dake idanunsa. Sai da ya cire ta fahimci ita yake kallo, ƙara natsuwa ta yi game da yin ƙasa da kai, tana jin kirjinta na dukan uku-uku.

"Maya". Ya ambaci sunanta can ƙasa. Da sauri ta ɗago kai. "Good evening sir". Dan sai a yanzu ta tina ashe yamma ce ma ba safiya ba. Bai amsa gaisuwar ba sai ya fito da wasu tulin takardu ya tura mata gabanta, sannan ya ɗauki pen ya miƙo mata. "Sign here". Ya faɗa in a low waye sosai.

Da yake suna shakkarsu da tsoronsu, bata tsaya tambayar document na menene bane kawai ta karɓi pen ɗin ta hau signing, paper dake ciki dikka ya dinga buɗe mata tana signing. Sai da ta kammala sannan ya ɗauko wani document ya miƙa mata. "Wannan shi ne project da kika yi signing na kin karɓa a yanzu, 24 hours gareki ki karanta document ɗin nan jibi da safe za'a fara project ɗin, so a yanzu kin dawo karkashin office ɗin nan da aiki, kina iya tafiya".

Cikin girmamawa ta amsa tare da karɓar document ɗin sannan ta miƙe ta fito cike da farincikin ta baro side na chemical ta koma side na manyam 3D da kowa ke tsoro......... Da kallon ƙasan ido ya bita har ta fita, wayansa ya ɗauka, rubutu yai short kafin ya ajiye wayar, ya miƙe ya buɗe door dake cikin office ɗin, a tinanina toilet ne a wajen, sai da ya shiga naga wajen ya sha banban.

Dan kuwa yadda kuka san bar na shaye-shaye haka wajen yake, ga wani dim light purple kala, wasu manya-manyan glass ne shake da abubuwan sha kala-kala wanda na tabbatar kuɗinsu ba zai faɗu ba, dan tsadaddun kayan drinks ne a wajen.

Daga gefen glass ɗin can ɗan nesa wasu sofa set ne a wajen, ga kuma irin torch creen computer ɗin nan tangameme a wajen sofa set ɗin, da alama wajen shirya project ɗinsu ne. Ɗakin sai kamshi yake yi.

Wajen sofa ɗin ya karisa, a saman ɗaya daga ciki ya zauna, yana zama sai ga Dr Mark ya shigo, kai tsaye wajen glass na drinks ɗinsu ya nufa, wani tangamemen bottle ya ɗauko da glass cup, a wajen sofar ya dawo. Abin mamaki drinks ɗin da sanyi sosai, da alama glass freezer ne a wajen. Ɓalle bakin bottle ɗin ya yi, ya zuba drink ɗin a cup, sipping ya ɗan yi tare da cewa. "In zuba maka ne?".

Kai Dr Kamal ya girgiza tare da cewa no. Zama ya yi ya cigaba da sipping a hankali cikin natsuwa, babu wanda ya sake ce da wani uppan.

To mu bi sister Zinta kuma. A lokacin da suka shiga office na Dr James da sister Lazy jikinta sai kerma yake yi, umarni Lazy ta bata da ta tsaya a tsaye, ita kuma ta zauna a kan visitor chair. Tana zama Dr James ya ce. "Get out!".

Wani irin kululun bakinciki me ya turmuke zuciyanta, jikinta har kerma yake na takaici, ga shi ba yadda ta iya da shi, haka ta miƙe tsaye cike da kunyar ya walaƙantata a gaban Zinta. Tana miƙewa ya ce. "Zinta have a seat". Ya faɗa still bai ɗago ya kallesu ba. Wucewa Zinta ta yi, ta zauna a saman kujerar da Lazy ta tashi, ita kuwa Lazy da wani mahaukacin sauri ta nufi waje, dan gab take da haɗiyar zuciya ta mutu.

Kamar yadda Dr Kamal ya baiwa Maya files and documents haka Dr James ya baiwa Zinta ta sanya hannu, sannan ya ce tana iya tafiya. Daɗi tamkar ta mutu saboda ya ce a tare zasu yi wannan project ɗin, sai sun kammala project ɗin zata koma aiki a section C ɗinsu, ko a iya haka ta yi nasara, zata samu damar zama kusa da shi, ga shi idan suka shiga project suna iya ɗaukar watanni 6 zuwa 8 kafin su kammala, gwargwadon yanayin project ɗin dai. To kun ji yadda sister Zinta ma ta kare da Dr James, to mu koma kan su Dr Kamal.

Suna zaune shiru babu wanda ya yi magana Daidai lokacin Dr James ya shigo ta kofar office ɗinsa, dikkansu daga office ɗinsu suna iya shigowa cikin wajen. So ya shigo hannunsa rike da tarin takardun. Saman sofa kusa da su ya zauna tare da ajiye files ɗin a kusa da shi. Natsuwa suka yi dik suka bashi hankalinsu. Wani document ya ɗauko tare buɗe files ɗin, glass na face ɗinsa ya gyara kafin ya ce. "Information daga ƙasar AVARIS. A dikkan government hospital na 30 states da kasar Avaris take da shi mun gama rarraba files ɗin nan, a cikin ƙasa da 24 hours mun samu mahaifar mata sosai daga asibitoci sama da 20".

Dr Mark ne ya amsa da cewa. "Fin haka ma zamu samu, saboda kowa yana cikin yunwa da buƙatar kuɗi, kowa burinsa ya yi kuɗi, kunga a irin wannan yanayi ko da maginyata basu sayar dan ra'ayin kansu ba likitocin zasu cire masu ba tare da yardansu ko saninsu ba, dan 80 million ba karamin kuɗi ba!". A natse ya yi maganar, ya faɗa yana sipping drink ɗinsa.

Dr Kamal ne ya ce. "Yunwa ya cinye kowa a ƙasar na AVARIS ba dole su sayar ba, gwamnatin AVARIS bata son biyan ma'aikatan lafiyar government hospital ɗinta albashinsu yadda yakamata, basa son sauke hakkinsu, kasar ga yunwa da wahala dole wasu likutocin su yarda sayar ko majinyata basu sani ba". Cikin kwarewa suke magana, one after the other, yadda zaku san ilimi ya ratsa ƙwaƙwalwalensu matuƙa.

Bari in maku karin haske dan zaku fi gane maganganunsu, sayan mahaifan mata suke yi da kimanin kuɗi 80 million a kuɗin Nigeria, to ni kuɗin Nigeria na sani shiyasa da su nine kwatance, kuma shi masu karatu zasu fi ganewa.......😌

To sun shigar da buƙatarsu ta hanyar turawa manyan asibitocin gwammanati na kasar Avaris takarda, wani Minister suka baiwa wannan kwangila da makuɗan miliyoyin daloli, shi kuma ya shiga asibiticin gwamnati ya yi zama da manyan gurɓatattun likitoci ya faɗa masu buƙatarsa, su kuwa take suka yi na'am sun ji miliyoyi.

Dr James da kansa ya kirkiro wani magani da ya sanyawa project ɗin suna da silent killer, wanna magani ya bawa wannan minister dan a rabawa gurɓatattun manyan likitocin asibitocin, zasu baiwa mata a matsayin wani magani na karin lafiya, ko idan mace ta zo ta ce tana ciwon ciki yayin period sai su bata shi a matsayin maganin warkar da ciwon cikin, idan kin sha zaki yi ta fama da ciwon cikin ne, amma fa a farko in kin sha zaki ji saukin ciwon cikin, daga baya bayan kwanaki sabon ciwon ciki zai ɓallo maki mai zafi, da kin zo asibiti zasu ce maki mahaifarki ta samu matsala sai dai a yanke! Ba zaki kawo komai a ranki ba, zaki aminta a cire maki mahaifarki saboda a rabaki da ciwo.

Ministern da aka baiwa wannan kwamgila a kan Miliyan tamanin aka sayi kowani mahaifa a wajensa, shi kuma ya cewa likitoci in sun samu mai sayar da mahaifar ya saya miliyan hamsin, su kuma Dr ɗin suna saye miliyan 30 idan kin yarda zaki sayar, kasuwanci kan kasuwanci kuke ji.

To wasu matan fa mazansu ake magana da su, wani da ya kawo matarsa asibiti za'a jasa jefe, a shirya a kuma kwaɗaita mashi kuɗin, idan likitocin sun ga ɗan kauyene ma basa ce mashi saya zasu yi, sai su ce ciwo ne, ya aminta a cire maki, wani mijin kuma azzalumi ne, bai gama sauke maki hakkinki na aure ba, zai cutar dake ya sayar maki da mahaifa ba tare da kin sani ba, idan ya shirya da likitocin kan zai sayar masu zai karɓo wannan maganin ya baki, da kinsa zaki fara ciwon ciki, idan zai kaiki asibiti wannan asibitin da suka gama cinikin zai kai, already ya karɓi kuɗin mahaifarki 30 million baki sani ba, sun san komai Doctors ɗin, kina zuwa zaace aiki za'ayi maki, daga nan a cire maki mahaifa ba tare da kin sani ba, sai dai ki ga kin daina haihuwa, kuma ba zai taɓa barinki ki je wani asibitin ba, sai dai ya dinga cewa ki je wannan asibitin da aka maki aiki sun fi kwararrun likitoci, dan bakinsu ɗaya.

Ya ilahi, sun fi yi wa matan kauye da basu san komai ba hakan, kun san dai manya matan masu kuɗi basa zuwa asibitocin gwannati ai, a kan mu talakawa abin yake karewa, babu abin da ya fi taɓa mun zuciya irin mazan dake zaluntar matansu su sayar masu da mahaifa ba da izininsu ba, ya ilahi, wlh da babu lahira akwai matsala, amma Alhamdulillahi tin da akwai hisabi, amma bin da ciwo.

Meyasa yanzu abu kaɗan mahaifar mace ya samu matsala? Why? Meyasa zata haihu ace ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai a mata Cs? Why? Meyasa ciwon da bai zo a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login