Showing 45001 words to 48000 words out of 365093 words

Chapter 16 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5907

har in ɗaya ya kira gida a gidan kowa yana haba-haba ya haɗasu da abokansa su gaisa, sun zama kaman ƴan uwa na jini da dangin juna, dangin Leo ne kawai babu wanda ya sansu, ba su taɓa ganin ma ya kira gida a gabansu ba, amma su kowa a gidajensu yasan da ƴan ɗaki, sai dai kuma ahalin kowa basu san da Leo a ɗakin ba.

Haka suka kasance cikin farinciki har dare, bayan sun yi dinner sun dawo, dikkansu suka yi wanka suka yi shirin kwanciya. Sai da suka sake kiran gida suka sha hira har zuwa 10 na dare, sannan ne ɗakin ta yi shiru tsit alamar sun yi barci. Leo yana kwance rike da waya yana chatting da gida, shi baya kiransu sai dai chat kawai, saboda shi ƴan gidansu ba zaman banza suke yi ba, dik suna da aikin dake gabansu, basu da lokacin ɓatawa wajen yin wasa saɓanin su Noor masu yi har da video call. So shi idan ya tashi yana dropping masu message ne, dik time da suka zo su yi reply, haka suke.

Around 11 duniya ta yi shiru, kowa ya yi barci, kunna light na wayarsa Leo ya yi tare da sakowa kasar bed ɗinsa, kai tsaye bed na Noor ya nufa. Hannu yasa ya fara tashin Noor. Da yake ɗazu da rana ya sha barci sai ya farka a natse, slowly ya waro idanunsa a kan kyakkyawan fuskan Leo dake ta faman sheki. Ya yi mamakin ganinsa, hakan yasa ya tashi da sauri yana kai hannu saman ido.

Mustsuke idanun nasa ya yi dan ya tabbatar da abin da yake gani. Tabbas Leo ne, cike da mamaki ya ce. "Bro what brought you here?"....... Baya kaɗan Leo ya ja tare da yi mashi alamar ya sauƙo ƙasa. Ba musu ya sauƙo yana cigaba da kallonsa. Hannunsa Leo ya kama suka nufi door. Noor bai musa ba ya fara binsa, buɗe kofa ya yi suka fita waje.

Yana fita ya kashe light na wayansa ya zura a aljihu, a cikin duhu suka cigaba da tafiya har izuwa gym na barrack ɗin. Ko kaɗan Noor bai ji tsoro ba, bai kuma damu da ya tambayi ina za su je ba.

Kasancewar Leo yasan gym ɗin tana can baya ne daga idanun mutane, sai ya kunna light na wajen, take haske ya gauraye wajen. Sake hannun Noor ya yi tare da ce mashi ya shirya. Sai a lokacin ya ɗaga idanu ya kalli Leo da kyau, muryansa na rawa ya ce. "Bro me za mu yi a nan?"........ "Training". A taƙaice Leo ya bashi amsa. Shiru Noor ya ɗan yi, yana son tambayar dalili amma yana shakka.

Ɗaure fuska Leo yai alamar babu wasa a tattare da shi, sannan ya umarci Noor da ya wuce ya fara push-up, dan wlh ba za su yarda da wannan ragon tan nasa ya dinga sanyawa suna ɗaukar karshe ba, dole ya horar da shi horo na musamman wa shi kaɗai. Ganin babu arziki a kan fuskan Leo yasa ya wuce ya fara yi, waya Leo ɗin ya fitar ta duba time, sannan ne ya ce ya baiwa Noor 10 mins yai push-ups guda 100. Zazzaro idanu ya yi, a ransa ya ce to ai ko Captain almost 20 mins ya basu kuma har three times, shi kuma 10 mins at once? Gaskiya wannan zallar mugunta ce, ganin dai babu wasa a tattare da shi ne yasa bai yi gigin yi mashi magiya ba, sai kawai ya fara.

Gefensa Leo ya tsata yana kirgawa, tin Noor na iya kirgawa har ya dawo yi kawai yake yi. Abin mamakin kuma shi ne sun fi tsoron Leo a kan Captain ma, dan kuwa dik wahala da gajiyar da Noor ya yi bai dakata ba, yana tsoron tsayawa ne.

Haka ya dinga yi, tin yana daurewa har ya saki ya fara kuka, ko a jikinsa Leo kam, bai damu da kukan ba, sai ma rungume hannaye a kirji da ya yi yana kallonsa. Ko guda hamsin bai cika ba mintuna goman nan suka cika, nan fa Leo ya ce ya sake farawa daga farko, yau ba zasu tashi daga nan ba har sai ya yi guda ɗari a mintina goma.

Haba kuka sosai Noor ya fara yi, hawaye bibbiyu, daga karshe majina da yawu dik suka fara zuba, Leo ko kaɗan bai ji kamar zai kyalesa ba, haka bawan ALLAHN nan ya dinga maimaita almost sau takwas, amma ya gagara yi a ƙasa da mintuna goma, dik wani sauran karfinsa ta kare, jikinsa ya jigata, kafafunsa da hannayensa kerma sosai suke yi, sai haɗa uban gumi yake yi.

Shi kuwa Leo ya ce ko mutuwa zai yi yau sai ya yi a kasa da mintuna gomar nan, ko kwana ne sai sun yi a nan. Tin 11 ake abu ɗaya har karfe 1 sannan ya samu ya yi a ƙasa da mintuna gomar, sake cewa ya maimaita Leo ya yi, ya maimaita ya kuma yi a ƙasa da mintuna goma, da alama ta shiga kansa sosai wannan horo.

A maimakon Leo ya barsa haka ya huta, sai ya sake sanya shi 100 sit-ups and 80 burpees, yaron nan kuka yake yi tamkar ransa zai fita, Leo bai ɗaga mashi kafa ba, har ta kai dakyar yake numfashi, har yana neman sumewa a wajen, amma Leo bai tausaya mashi ba har sai da ya yi waɗan nan training ɗin dikka. Around karfe 3 ya kammala cikin ƙaida, sannan ne Leo ya ce su tashi haka nan sai kuma gobe..... Babbar Magana, kenan Leo kullum dare zai dinga hora Noor? Lallai Noor yana cikin lukutar musifa, ga horon rana ga kuma na dare, bawan ALLAH ba hutu kenan.

Gagara miƙewa a kan ƙafafuwansa ya yi, dan jikinsa dikka wani iri ɓari mai ban tausayi yake yi, idanunsa har sun kumbura, tsinin hancin nan nasa jajir kamar an shafa wani abin, ƙasan idanunsa dik sun yi jajir.

Ganin ya gagara miƙewa ne yasa Leo tura wayansa a aljihu, sannan ya saɓesa a kafaɗa suka nufi waje. Kai tsaye room ɗinsu suka koma. A saman gadon Noor ya kwantar da shi tare da wucewa nasa bed ɗin. Har ya kwanta sai ya ji Noor na numfashi sama-sama tamkar zai mutu, hakan yasa ya sauko ƙasa, jakarsa ya ɗauko, tare da fito da wani drugs, sannan ya ɗauko bottle water, dan su da shi suke amfani, iya matsayin kuɗin iyayenka iya shagalinka!.

Wajen gadon Noor ɗin ya dawo, miƙar da shi zaune ya yi tare da ɓalle drugs ɗin guda bibbiyu, ya ɓalle bakin robar ruwan, sannan ya bashi a baki. Dole ya buɗi baki ya karɓa, bayan ya sha Leo ya koma bed ɗinsa, ya mai da sauran drugs ɗin, ya kuma ajiye ruwan kafin ya haye ya kwanta. Shi ma Noor kwanciya ya yi, kusan a tare barci yai awon gaba da su.

Washegari, yau ta kama Saturday, babu horo suna off. Tin da sassafe suka tafi yawace-yawacensu a cikin barrack ɗin, dan ba'a yarda su fita waje ba idan suna karar horo. Zaynash ya ce bari ya je yawo ta wajen dajin da suke zuwa horo ya gani, sai ya ɗauki camera ɗinsa wai zai ɗaɗɗauki wajen horon nasu hoto, in sun yi passing out ya kaiwa Ummie ta ga wuraren, dan haka sai ya nufi ma'ajiyar kekunan horonsu, ya ɗauko keke guda ya haye kai, sanye yake da three quarter jeans baki da lallausan t-shirts ash color, ya yi kyau sosai, sai ya ɗaura army p-cap a kansa. Vash kuma fita ya yi dan ya samu damar kallon sauran matasan sojojin. Noor har yanzu yana ta faman barci wahala, Leo yana kwance saman gado bai sauƙa ba tin bayan sallar asuba da ya dawo, idanunsa biyu kuma!.

A natse Zaysh yake tuƙa kenan nan nasa yana ɗan kalle-kalle, ya sanya helmet a kansa wanda ya ɗauka a jikin keken, kowani kenen akwai hular kwanon a ɗaure a jikinsa, dan dokace basa hawa keke babu shi. Wata doguwar hanya ya miƙa, nan yaga matasa dayawa a kan keken, wasu suna dawowa, wasu kuma suna tafiya, a ransa ya ce yau ba training sai yawo, watau kowa ya je ganin wuraren da muke zuwa horo dan ya ɗauki hoto ya ajiye tarihi.

Yana sharan wata kwana da zata sada shi da cikin dajin suka ci karo da wata keke da ta sharo kwana ita ma, hakan yasa sarkan keken ya zube ƙasa, saura kaɗan su faɗi daga shi har wancan ɗaya mai keken. Amma suka yi saurin sanya kafafunsu a ƙasa. Kusan a tare suka ɗauko ƙasa, ya tsayar da kekensa a gefe, shi kuma wanda suka yi karon ya tsugunna yana ƙoƙarin gyara sarkar keken nasa da ta zube.

Da yake yasan shi ne da laifi da ya shiga kwanar da gudu, sai ya yi saurin tsugunnawa a wajen tare da kama sarkar yana faɗin. "Sorry bari in gyara maka".......... Miƙewa tsaye ya yi ya bar mashi sarkan ya gyara. Tsab ya mai da shi ya gyara tare da rike kan keke ya miƙe tsaye, a sanyaye ya ce. "Sorry ba da gangan na yi ba, na shiga duniyar tinani.......". Bai iya karisar da maganar ba ganin cewa macece ba namiji ba.

Zazzaro ido ya yi, ta cire hukar kwanon kanta, ta kuma ɗan buɗe zip na ƙatuwar jacket ɗin jikinta da ya hana ake iya kallon kirjinta har a gane macece, daga ta ƙasa wandon jeans dogo ne a jikinta, kafafunta da Boot bakake, hannunta da army hands gloves, ba ta yadda zaka iya gane macece har sai da ta cire hular kwanin dogon gashin kanta da kyakkyawar face ɗinta ya bayyana.

Ai kusan suman tsaye ya yi a kallonta, ga shi da helmet a kansa mai cover, bata iya ganin face ɗinsa, hakan yasa ya zubawa kyakkyawan face ɗinta idanu, bai iya ɗauke kallonsa daga kanta ba, sai da ya ga ta motsa ta miƙa hannu zata karɓi kan kekenta da ya rike ne yasa ya farga, da sauri ya ɗauke kallonsa daga kanta tare da fara juye-juye yana neman namijin, dan bai gama yarda ita ce mai wannan keken ba yafi tinanin da ya tsugunna gyara sarkan ne namijin ya gudu mace ta zo. Kun san a matasan sojojin harda mata? Ban taɓo maku ɓangarensu bane saboda labari bai biyo ta nan ba, amma harda matasan mata dake sha'awar shiga aikin.

A ransa ya ce. "Yanzu wannan kyakkyawan mai zubin taliyar ma a training na soja take kenan? To yanzu wannan ba zata karye bane ma?". A fili kuma karɓar kan kekenta da ta yi ne ya dawo da shi daga tunanin da ya afka. Ya gagara sake yi mata magana, yana gani ta mayar da helmet ɗinta a kanta, sannan ta gyara ta haye kan keken ba tare da ta yi mashi magana ba. Sai da ta gyara hands glove na hannunta kafin ta fara tuƙa keken ta bar wajen.

Mutuwar tsaye ya yi yana kallonta har ta kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke tare da jawo nasa keken, ya hau ya cigaba da tafiya zuciyansa cike da tinanin dama akwai kyawawan ƴan'mata a barrack ɗin nan kenan? Kaga wata zaka ce an kure halitta a kanta!
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-7-by-princess-teema

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.


STEP 1________🔥


6-11-2025.🔥


FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥


E_____________7


A can gefe kuwa Leo sai da ya gama kwanciyansa ya miƙe ya yi wanka, shirinsa ya yi cikin ƙananan kaya masu kyau, yau ɗin ma dai ripped jeans ɗin ne, da alama ripped sun fi yawa a cikin kayansa, kyansa ya kara bayyana, amma kuma ya ɗan rame kaɗan alamar wahala a tattare da shi.

Har zai fita daga room ɗin sai kuma ya dawo ya hau shin Noor daga barci, dan yana son koyawa yaron komai a tsari. A firgice Noor ya tashi yana ambatar sunan daddynsa, da alama mafarkinsa ya yi, wlh ba dan GIDAN SOJA ba ba'a tashin Noor daga barci, saboda ciwon nan nasa, yana firgita, amma yanzu har ya fara sabawa da tashin nasa da ake yi.

In a cool way Leo ya ce. "It's breakfast time, get up and let's go eat"........ Jin voice ɗin Leo yasa Noor sauke ajiyar zuciya, a natse ya ɗago jajayen idanunsa a kan Leo ɗin, tamkar zai yi kuka ya ce. "Please brother let me sleep, I really want to sleep". Da kyar yake maganar.

Sosai Leo ya ji tausayin yaron ya kama shi, sai ya ji yana buƙatar jin labarin Noor, kamar zai fita, sai kuma ya fasa, komawa saman bed ɗinsa ya yi, ya zauna tare da jawo jakarsa, buɗewa yai. Biscuits manya-manya masu daɗi ya ciro kwali biyu, da hannu ya yi wa Noor alamar da ya zo. Ba musu ya sauƙa ya je, gefensa ya nuna mashi, zama ya yi yana ta faman daka hamma.

Miƙa mashi biscuits guda ɗaya Leo ya yi, ba musu ya karɓa yana cigaba da kallonsa. Ɗan nisawa ya yi kafin a natse ya ce. "I want to know your history, who are you? Why don't you want to focus on the work that brought you here?".

Da sauri Noor ya waro idanunsa a kan Leo ɗin, lokaci guda ya ji murmushi ta kubce mashi, wani irin musulmin daɗi ya ji, wai yau Leo ne yake kula shi haka? Har yana neman jin tarihinsa? Bai san cewa dikkansu a ɗakin sarai Leo yana karantarsu ba, dik wani motsinsu yana sane da su, shi mutum ne da ya tsani haɗa hanya da dolaye marasa basira, sai da ya gama karantarsu tsab a ɗakin sannan ne kuka ga ya ɗan fara kula Noor, ya fahimci a ɗakin dikka babu dolo sai dai rashin mai da hankali a kan aiki, amma dikkansu akwai kaifin basira.

Shi Noor na daban ne a cikinsu, kwakwalwansa tana da saurin gudun tinani, akwai wani baiwar da ALLAH ya ajiye a tattare, kawai tsabar sangarta ne da shiririta da ƴan uwansa mata da daddynsu suka yi mashi har tai mashi over yasa baya taɓa abin arziki, amma da zai taimaka mashi wlh za'ayi alfahari da shi a hukumar soja, zai kafa babban tarihin da zai yi wuya a sake samun wanda zai sake kafa irinsa.

Shin kun yarda da zancen Leo dake cewa Noor zai kafa babban tarihi? Wace iriyar tarihi kenan? Wace iriyar baiwa ce a tattare da Noor? Mu je zuwa.

Gyara zama ya yi, take ya ji barcinsa ta gudu, a natse ya ce. "My name is Nooriel Fayruz Zaheeran, ainahina European ne, mahaifina European ne, mahaifiyata ƴar kabilar scandinavian ce a kasar Mexico yankin Amurka kenan, amma mu mazauna CRYSTAL PALACE ne a cikin Us, mahaifiyata ta rasu a ranar da nike shirin zuwa duniya, na taso a tare da sisters ɗina mata su uku, sune komai nawa, sai daddyna". Nan ya kwashi dikkan labarinsa, yadda daddynsa ya kwallafa rai kan neman ɗah namiji, dukiyar da ake jiran ya kula da shi, da komai da komai ya bashi labari.

Kai jama'a ashe dole Noor ya haɗu ba karya, mahaifinsa European, mahaifiyarsa scandinavian a Mexico, kun san da cewa kabilun scandinavian suna daga cikin top ten kabilu mafiya kyau a duniya? Tushensu a Sweden suke, amma suna iya zama a ko'ina. A top ten ɗin ma su ne na 4 a kyau! Shiyasa ɗan yaron nan ya haɗu, ga kyawawan European eyes masu ɗaukar hankali. Mutane dayawa basa banbanta Europe da Ethiopia na Afirka, to bari in banbanta maku, idan kun ji Ethiopia to nan gida Africa ake nufi, amma idan kun ji Europe yana ɗauke da ƙasashe kamar haka, United Kingdom watau Uk kenan, ko ku ce England, ita ce uwa ga Europe gabaɗaya, sai Ireland, France, Spain, Portugal, Belgium, Netherlands, Luxembourg, Germany, Switzerland, Italy, Austria, Poland, Czech Republic, Slovakia, Hungary, Slovenia, Croatia, Bosnia and Herzegovina, Serbia, Montenegro, Kosovo, Albania, North Macedoni, Greece, Bulgaria, Romania, Moldova, Ukraine, Belarus, Lithuania, Latvia, Estonia, Finland, Sweden, Norway, Denmark, Iceland, Russia ta wani ɓangare sashen turai ne, wani ɓangaren nasu kuma yana sashen Asia, su dai suna tsakiya. Haka Turkey suna tsakiya, Andorra, Monaco, San Marino, Vatican City, waɗan nan su ne Europe, kuma sune ainahin turawa ba Amruka ba, America dik ƴan bariki ne a cikinta bakin haure! Na faɗa maku ne da dayawan lokuta idan na ce Europe sai in ji kuna fassara mun shi da Afrika! To ba ɗaya bane!.

------------------------

Nisawa Leo ya yi jin labarin, a ransa yake mamakin jin sunan Fayruz Zaheeran, tabbas ya taɓa jin wannan suna, amma a ina? Ya mance, gefe guda kuma mamaki yake yi jin cewa Noor ya fi to ne daga CRYSTAL PALACE, like wow, waje ɗaya suke, dan shi ma Leo daga can yake, suna gini guda amma basu san juna ba. Da ya tuna suna gini guda sai ya ce kila a nan ya taɓa jin sunan Fayruz Zaheeran ɗin, lokaci guda kuma ya sake tunawa ashe fa suke da mallakin STARS BODY LUSH, zai iya yiwuwa ma a jikin mansu ya ga sunan.

Jin labarinsa yasa ya ji tausayinsa matuƙa, sai ya guduri niyyar taimaka mashi da gaske, a farko ya fara bashi horo ne saboda kansa ya daina sanyasu ɗaukar last, yanzu kuma zai bashi horo ne a matsayinsa na maraya ya tsaya ya karfafa kansa. Tin daga wannan rana Leo ya fara horar da Noor horo ta musamman, ya ja shi a jiki sosai, su Zaynish sai mamaki suke yi yadda aka yi Leo yake jan Noor a jiki har suna magana, sun kuma yi mamakin yadda aka yi Noor yanzu baya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login