Showing 258001 words to 261000 words out of 365093 words

Chapter 87 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5888

sama ɗakina sister ɗinki na kiranki". Daga haka bai sake magana ba, ya sauƙo ya nufi waje. Jawota jikinsa Dr Kamal ya yi, ya rungumeta tare da bata sumbata a goshi. Ya saketa yana mata bye-bye. Sama ta haye tana mashi bye-bye ita ma, sai murmushi take yi.

Sai da ya ga hayewarta sannan ya wuce ya bi bayan Dr James suka nufi cikin hospital ɗin.

--------------------------

CRYSTAL PALACE.🔥

Abba khaiza'an's House.

A yau Abba ya shirya sadaki na alfarma, da misalin karfe 8 na dare, ya shirya cikin shiga ta alfarma, ya sanya thobe and bisht, ya naɗa rawani tamkar wani balarabe, amma haskensa kowa ya gani yasan ba balarabe bane.

Kai tsaye ya tasa Faryan da Harleen a gaba, dan dole ya ce su rakasa ya je ya kai wannan sadaki, yana son jibi jumma a ɗaura wannan aure, ba fa fashi ko za'a mutu. Kai Abba namu na amana.

Ga Abba ga grandpa, me kuke tinani a kan wannan kai sadaki?


https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-36-by-princess-teema


ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
[10/01, 9:16 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.


For more information 08161390581 Whatsapp me only.


STEP 1🔥

2025-12-17.🔥



اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E_____________ 36


Kai tsaye benen su Noor suka nufa, ta hanyar sama ma suka bi. Already Abba ya sanar da daddyn Noor zasu zo, dan haka ya shirya tarba na musamman a garesu.

Suna knocking ɗaya aka buɗe masu kofar, uncle ɗan kwalisan mu ne ya fara tarbansu, fuska ɗauke da wannan lallausan murmushin nasu na gado mai kwantar da hankali, yai masu sannu da zuwa, har da riko hannun Harleen yana ƙara masu sannu da zuwa.

Ciki suka shigo, a saman sofa suka zauna, ga kayan cima kala-kala an jibga masu dan girmamawa a garesu. Sama Uncle ya haura. Jim kaɗan sai ga shi ya dawo da dikka family, Aunty Luna, Aunty Lusi da daddy.

Aunty Lusi akwai izza jama'a, a family ɗin su Noor dik ta fi kowa izza, bata da yawan magana, sai kallo da ido, bata shiga sabgar kowa, kuma ta tsani a shiga nata, amma dik da wannan izza nata tana kallon Abba sai da ta ji faɗuwar gaba, ta gagara haɗa ido kai tsaye da shi.

Dik suna sanye da pjs ne a jikinsu, da yake basu jima da tashi daga barci ba. Abba yana daga zauna daddy Noor ya ƙariso ya zauna a kusa da shi, sannan ya miƙa mashi hannu kan su gaisa, Abba bai bashi hannu ba, sai dai ya ce mashi salamu alaikum kawai, daddy Noor bai sa me ya ce ba, ita kanta musabahar ba wai ya saba yi bane, dan ya mutunta baƙin nasa ne yasa ya yi.

Abba ne ya ce Harleen ya kawo trollyn da suka zo da shi. Jawo shi ya yi gaban Abba, sai satar kallon Aunty Luna malam Harleen yake ta faman yi, yana wani ɗaure fuska, kaman wanda aka sanya dole...... A mutunce aka gaggaisa, Aunty Luna and Aunty Lusi suka ɗaga wa su Abba gaisuwa. Aunty Luna sai satar kallon Harleen take yi ita ma, hakika ya yi kyau cikin tail coat ɗin nan, kyansa ya sake fitowa sosai da sosai!.

A dake Abba ya ce. "A addininmu muna yin sadaki, ba zobe ba, dan haka wannan shi ne sadakin, idan yai masu kaɗan suna iya furta adadin abin da suke so sai a kawo masu, nan da jibi nike son a ɗaura wannan aure". Babu wasa a tattare da shi yai magana, ga izza kamar shi ne ubansu har daddyn Noor ɗin!.

Zuba mashi idanu suka yi. Abba ya kalli Aunty Luna a lokacin da ya buɗe akwatin kuɗin. "Ƴata idan kuɗin bai maki ba zaki iya faɗar nawa kike so" . Ya kai karshe daidai lokacin da yake zuge zip ɗin akwatin.

Dollars ne zallah, sai ɗanyen gold guda biyu a ciki...... Ai dikka family babu wanda bai waro idanunsa waje ba ganin maƙudan kuɗin da Abba ya buɗe a cikin akwatin nan, ba su taɓa zatan Khaiza'an's family suna da wannan kuɗin ba, suna kallon Abba matsayin bai wuci ɗan majalisa a kuɗi ba, ba su kaisa matsayin gwamna bama, basu san ko shugaban ƙasa ba za gwada mashi kuɗi ba.

Hakikanin gaskiya ba su kawai ba, har su Faryan sun girgiza da ganin kuɗin nan da Abba ya buɗe, ya ilahi, Harleen da Faryan kallon juna suka yi, a cikin zuciyoyinsu suna tambayar kansu a ina Abbansu ya samu waɗan nan maƙudan kuɗaɗɗe? Ga gold, wannan kuɗi ai zai iya saya masu bene guda a CRYSTAL PALACE in da za'a sayar, sai dai a CRYSTAL PALACE ba'a sayar da gida sai dai ka kama haya!.

To dik wannan kuɗin Aryan ne ya baiwa Abba, kun tina dama ya ce zai turo kuɗi, to shi ne ya turo a akwati, kuma wannan gold ɗin Aryan fa cewa Abba ya yi sadakin Rimsha ne ya biyawa Vash ɗan lele, amma kunga Abba da ƙoƙari gold ɗaya ya cire ya bari a gida wai na Rimsha, ya tattaro sauran dik ya kawowa su Aunty Luna dan baya son harkar raini, kada a rainasa! Yana son nuna masu muhimmanci ƴaƴansu, yana so su san ba wai kawai za'a auri ƴaƴansu bane, za'a kula da su ne sosai.

"Abba babu komai, ni ba sai ka bani komai ba". Cewar Aunty Luna, tana magana ta ɗago slowly zata saci kallon Harleen kenan suka haɗa ido da shi, dan shi ma ya ɗago zai saci kallonta. Kashe mashi ido ɗaya ta yi game da binsa da lallausan murmushi.

Ai sai ga Harleen ya fara tari, yana neman ruwa. Da sauri uncle ya ɗauko ruwa a bottle, ya buɗe ya zuba mashi a cup ya miƙa mashi. Karɓa ya yi, ya fara sha, sai da ya sha rabi, sannan ya ɗago ya saci kallonta, still shi take kallo tana murmushi. Harara ya watsa mata, ita kuma ta ɗan turo mashi baki kafin ta sake kashe mashi ido ɗaya.

"Kuna tinanin zaku sayemu da kuɗi ne kenan?". A cewar Aunty Lusi, ta yi maganar a dake, bata ɗaukar raini na ce maku. Ɗago idanu a kanta Abba ya yi, take ta ji dik wani kwarin gwiwa ɗinta ya gudu saboda kwarjinin Abba, ƙawar da kanta gefe ta yi, kirjinta na bugawa da karfi, amma ta daure game da sauke ajiyar zuciya.

A dake Abba ya ce. "Idan hakan muka so ma zamu iya, amma yanzu dai ba sayan naku muka zo yi ba, sadaki muka kawo!". Cike da izza babu wasa a tattare da shi yai maganar, ya bata amsa ne dan yaga tana fa ilmi....... Uncle ne ya ce. "Lusi be patient please"...... Miƙewa Aunty Lusi ta yi zata bar wajen, a cewarta ba zata iya tsayawa ba, kun san tana ji da mulki tin da ƴar siyasa ce, gwamna take nema.

"Koma ki zauna ayi komai a gabanki!". Abba ne ya faɗa on a serious note. Ɗago da kallonta a kansa ta yi, sai ta ji ba zata iya ja in da shi ba, ta rasa kwarin gwiwa, dole ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.

Daddyn Noor bawan ALLAH shi dai da ido kawai yake bin Abba, to aka ce faɗar da ya fi karfinka sai ka mayar da shi wasa. Su Harleen kam sun san waye Abba, sun san wlh da ya yi niyya sai dai yana zaune a gida yasa a ɗauko mashi family ɗinsu Noor gabaɗaya a kai mashi, har ita mai taƙama da tana neman gwamna ɗin, dik zai sanya a ɗaukesu a kaisu gida, ba zai zo da kansa ba, amma ya daure ya zo da kansa, ai sun samu martabawa sosai.

Miƙewa Abba ya yi tare da cewa. "Wannan shi ne sadakin, mu a addininmu ba zobe bane, addininmu ya baiwa kowa ƴancinsa, ya fitarwa kowa haƙinsa". Ya faɗa yana kallon daddy. Daddyn Noor mutum ne da baya son hayaniya, wlh kamar Noor yake, sai kawai ya bi Abba da ido, shi bashi da damuwa in har yaran nasa suna so ko yau a ɗaura auren.

Daidai lokacin grandpa ya sauƙo, ai yana ganin Abba ya ƙara sauri yana dogara sandarsa, tin bai gama sauƙowa ƙasa ba yana faɗin. "Me ya kawoku gidan nan?". Ai ko kallon in da yake Abba bai yi ba, sai gyara bisht ɗin jikinsa ya yi, ya juya yana faɗin. "Harleen mu je".

Cikin faɗa grandpa ya ce. "Ba zan barku ba, sai hukuma ta shiga tsakaninmu, ba zan hakura ba"......... Ko kallon in da yake Abba bai yi ba, ya wuce gaba, su Harleen ma babu wanda ya kulasa, suka wuce suka fice, sai bala'i yake yi, daddy Noor ya jawosa yana ƙoƙarin rarrashinsa.

Abba kam ko a jikinsa, ba dai abin da ya kawo shi ya yi ba? Ai shikenan, bashi da lokacin su grandpa. Suna komawa gida suka isko Ammie da Rimsha suna ta shan hira. Rimsha na ganinsa ta nufesa da gudu tana oyoyo Abba.

Da buɗar bakinsa sai ya ce. "Amarya yau kin ƙara kyau fa, ko dai fuskar taki tasan ke amarya ce?"....... Ɗan zazzare mashi idanu ta yi. "Abba amarya kuma?". Kai Abba ya jinjina mata, ya riko hannunta suka wuce izuwa cikin parlo, a saman sofa ya zauna, Rimsha ta haye jikinsa.

Abba na kallon face ɗinta ya ce. "Jikata kina magana da yayanki Vash kuwa?"........ Ɗan turo baki ta yi. "Ni Abba Yah Vash yanzu ya daina sona, baya kulani, tin da ya zama soja ya zama masifaffe, lokacin da ya zo har marina ya kusa yi, ni yanzu bani ma da numbersa, bamu taɓa waya ba tin da ya tafi". Ta kai karshe tamkar zata yi kuka.

Hannunta Faryan ya matsa ya riko. "Zo mu je ɗaki, kyale Vash ɗin nan, zo mu je mu buga game"....... Da sauri ta bar jikin Abba, ta bi Faryan suka haura sama. Ammie dake binsu da kallo ne ta ce. "Faryan ya shaƙu da Rimsha sosai". ... Kai Abba ya jinjina alamar haka ne, amma bai yi magana ba.

Wucewa sama Harleen ya yi yana tinanin irin salon Aunty Luna, ta fa buga ƙararrawar zuciyansa sosai.... Abba da Ammie suka cigaba da tsara yadda komai zai tafi a wannan biki na jibi da za'a yi.

--------------------------

Slowly ya waro idanunsa a kan kyakkyawan face ɗinta da har yanzu hawaye yake ɗan gangarowa, ta kurawa face ɗinsa idanu. Ajiyar zuciya ya sauke, sai da ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce. "Cherry baki jin magana, baki ji sam-sam"...…... Ɗan turo baki ta yi. "To daddy ai na ce ba zan sake ba".

Wani irin kallo ya dallah mata kafin ya ɗan yunkura ya zauna da kyau. "Kullum sai kin ce ba zaki sake ba, kuma ki sake, ke baki gajiya da bada hakuri ne? Kin san cewa ke kaɗai kika taɓa baiwa Champion na Iron Fist hakuri ya hakura ko? Bamu son kalmar sorry". In a cool way ya faɗa.

"Daddy waye champion kuma?". Tana shessheƙa kaɗan ta faɗa...... A maimakon ya bata amsa sai ya kawar da zancen da cewa. "Kada ki sake ce mun daddy daga yau"..... Ɗan waro idanunta a kansa ta yi, sai kuma ta ce. "To daddy wani suna kake son in kiraka?".

Kallon gefen ido ya dallah mata da waɗan nan idanun nasa irin na Abba. "Da wani suna kika kirani a lokacin da kika shirya yaudarata?"........ "Kai daddy, kai daddy, ni na yaudareka kuma?". A shagwaɓe ta faɗa. Shiru bai amsa mata ba, yana dai kallonta.

"Daddy ka yi magana"........ "Awwww kin manta sunan kenan ko? Dama yaudara ce abin?". Kai ta girgiza alamar a'a, sai kuma ta ce. "My gentle chaos". Ta faɗa tare da ware tafukanta ta rufe fuska tana murmushi. Zuba mata idanu ya yi, yana kallon yadda wai sihirtaccen kyau yake bayyana a face ɗinta.

Slowly ta zame hannunta daga kan fuskar tata, waro idanu ta yi da nufin ta sake yin magana, unexpected ta gansa dab da face ɗinta, ya matsota sosai. Ɗan razana ta yi, zata ja baya ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman waist ɗinta ta baya, ya jawota dab da shi sosai ta yadda suke shaƙar numfashin juna, idanunsa a kan kirjinta, slowly ya ɗago da idanun, ya yi sama izuwa kan dogon wuyanta kafin ya mayar da kallonsa a kan fuskarta.

Ta zazzaro idanunta a kansa sosai. "My gentle chaos, this name melted my heart, kin iya zaɓan suna my cherry". Yadda ya yi maganar a kurkusa da ita ya ALLAH, sai da zuciyarta ta yi wani sabon spark na kaunansa.......... Kyakkyawan murmushi ta saki tare da sanya tafin hannunta ɗaya, ta shafi kyakkyawan soft cheek ɗinsa, ta sanya ɗan yatsarta a dimple ɗinsa kafin ta ce. "Daddy k.......". Yatsar da ya ɗaura mata a saman soft lips ɗinta ne yasa ta haɗiye sauran maganar.

Gabaɗaya sai ya ji yana buƙatar jin wannan soft lips ɗin a cikin nasa, taɓawar da ya yin nan ya jefasa cikin tsananin buƙatar kiss. Da sauri ya janye hannunsa baya, ya ɗan yi ƙasa da eyes ɗinsa sai kan kirjinta. "Don't call me daddy again". Da kyar ya iya faɗa saboda wani irin yanayin da yake jinsa a ciki.

"Sorry my gentle chaos, mantawa nike yi, kuma kaga na saba kiranka daddy ne shiyasa"........ Ɗan janye jikinsa baya ya yi daga dab ita, still idanunsa a kan kirjinta, a ransa yana cewa kullum sai ƙara girma take yi, yakamata ace a matsayin matarsa take ƙara wannan girma, ya koma saman sofa ya zauna.

Ta gano yana kallon kirjinta, sai ta ce. "My gentle chaos, kaga yanzu kirjina yakara girma sosai ko? Har ya kusa kai na Rimsha, dama a school suna ta cewa bani da breast lokacin, yanzu ga shi na yi manyan breast nima, rigima zan dinga yi masu, dama a lokacin da muke school na Golden Root Rimsha sai ta dinga ɗaura belt a wajen cikinta dan breast ɗinta su fito sosai, nima yanzu rigimar zan dinga yi ina ɗaurawa"........ Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi, shi fa yanzu ya daina mamakinta, dan ta rigada ta goge mashi hadda, yarinya babu abin da bata sani ba, uhm.

"Waye ya ce maki ana rigima da breast?". Ya faɗa ba tare da ya sake kallonta ba. "Ana yi mana daddy, ai breast shi ne mace, kaga da breast da hips suke diri, idan mace tana da shi maza za su sota, dole nima in gyara nawa, in ɗaura belt su fito sosai dan in ja hankalin maza........". Gagara ƙarisa maganar ta yi sakamakon wani irin kallo da ya wurga mata cikin zafa.

Blinking eyes ɗinta ta shiga yi tana ja da baya. Da farko ya so ɗaukar zafi, amma ya fahimci yanzu ba ɗaukan zafi yakamata ya yi ba, already wannan karatu ya shiga kanta, so ba yadda za'ayi ya goge mata, zafa ko duka ba zai canza komai ba, kawai ya gwada mata illar hakan shi ne mafita, ya ci sa'a ma ai da bata zuwa ta yi gaban kanta, take faɗa mashi komai, kunga ya samu hanyar gyara. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce.

"Kina son jan hankali maza?". Da kyar ya furta maganar saboda kishi, kun san larabawa da shegen kishi...... Kai ta gyaɗa mashi alamar..... "Me zaki yi da mazan idan kika ja hankalinsu?".... Shiru ta ɗan yi, can kuma kai tsaye ta ce. "Sex mana daddy"....... Hasbunallahu waniimal wakil ya furta a cikin ransa sama da sau 30, shi dai boarding bata tsinana mashi komai ba face bakinciki.

A cikin ransa ya ce zaki ga yadda ake sex, sai nasa kin tsani even jin wannan suna, ALLAH ya kaimu ranar da zaki zama tawa, daga ranar ko a kusa dake aka kira sunan sex sai kin firgita, ƴar ƙaniya, bata ma san ya ake ji ba, ita dai kawai an kwaɗaita mata abin, burinta kawai ta yi ta ji ya yake.

Ganin ya tsareta da idanu ne yasa ta ce. "My gentle chaos kai ma kana son sex ko?"........... Nisawa ya yi tare da ɗauke kallonsa daga kanta. Girgiza mata kai ya yi alamar a'a, sai kuma ya juyo sai yi mata magana kenan muryanta ta katse shi da cewa. "Amma kuma shi ne kake kallon breast ɗina? Me kake kallo a wajen idan har ba feeling.........".

Gagara ƙarisa ta yi saboda yunkurawa da ya yi zai kai mata damƙa a wuya, ai a miliyan ta ƙarisa hayewa saman bed ɗin da baya-baya. Cikin zafa ya miƙe, ya yi ƙoƙarin danne kansa ya bita a hankali amma ta turashi bango. Baya ta fara yi tana son sauƙa gadon ta other side ɗin.

Ai cikin zafa ya haye bed ɗin, danƙo kafafunta ya yi, ya jawota gabanta, in a harsh way ya ce. "A yaushe na faɗa maki ina son sex? Kuma a yaushe kika ga in kallon kirjinki?". Babu wasa a tattare da shi yai magana, yana kallon cikin idanunta dake tsaitsaye na rashin jin magana.

Kukan shagwaɓa mai narka mashi zuciya ta saka mashi, muryanta na rawa ta ce. "Sorry my gentle chaos, ba zan sake ba"........ Wuyanta ya damƙo, cikin fushi ya ce. "Wai ya zan yi dake ne Seraphina?"........ Aikuwa da buɗar bakinta sai cewa ta yi. "Ka aureni kawai".

Dintse idanunsa ya yi, koma menene laifin kansa yake gani, bai taɓa ganin laifinta ba. Slowly ya zame hannunsa daga wuyanta, in cool way ya ce. "Tabbas zan aureki, kuma tabbas zan canzaki, tabbas zan goge maku abubuwan dake kanki". Ya faɗa yana ja baya daga kusa da ita.

"Daddy yaushe zaka aureni ɗin?". Ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login