Showing 270001 words to 273000 words out of 365093 words
except ALLAH, get up and go bring what Ammie sent you to get".
Da gudu ta miƙe ta nufi sama tana waigo ƴan'sandan da suka yi kasaƙe suna ganin ikon God...... Harleen ne ya ce. "Kai Faryan kara gudun Ac ɗin nan ka zo mun da small chop".
Ai a ƙule ACP ya ce. "Me kuka ɗauki kanku ne ahalin Khaiza'an? Dame kuke taƙama ne?"....... Dik cikin parlon babu wanda ya ɗago ya kallesu bare su tankasu, sai ma cewa Harleen yai. "Faryan zo mun da bluetooth". Watau ya toshe kunne kada su dame shi.
Ɗaya daga cikin ƴan'sandan dake baya ACP ne ya ce. "Kufito mana da Muhammad Khaiza'an, shi muka zo tafiya da, in kuma baku fito da shi ba zamu bincike gidan gabaɗaya, kuma ba zamu ragawa kowannenku ba, dik zaku tsinci kanku a bayan kanta!". In a harsh way ya faɗa yana wani zazzare masu ido, bai san nan gidan dik tantirancinka sun fika iyawa ba, kuma su ba duka ba zagi, kai bama magana zasu sanya zuciyarka bugawa ne.
"Wai ba daku muke magana bane?!!". ACP ya faɗa cikin ɗaga murya wanda ya sanya Rimsha dake sauƙowa yanzu ta razana ta saki plate and cup na hannunta ya faɗi ƙasa ya tarwatse, Americanon ya malale a ƙasa. Jikinta na rawa ta ɗago da kai ta sauke kallonta a kan mugun watau Harleen, dan tasan ko kowa bai yi mata magana ba shi sai ya yi saboda bala'insa daban ne a gidan nan bayan Aryan.
Ga mamakinta sai ta ga ya harareta ya ɗauke kai bai yi magana ba, take ta haɗiyi yawu gwad jikinta na ɗan kerma. Tana ƙoƙarin raɓawa gefen glass ɗin ta isa wajen Faryan ACP ya damki hannunta tare da sanya mata pistol gun ɗinsa a forehead ɗinta, a dake ya ce. "Ku fito da Khaiza'an ko in fasa kanta!!". Wai irin zai razanasun nan.
Miƙewa Ammie ta yi tana faɗin. "Ku kawo mopper a goge Americanon nan, sannan ku zo da tsintsiya dan kwashe glass ɗin, Faryan bari in ɗan kwanta in huta". Ta kai karshen maganar tare da nufar sama, ta raɓa gefen ACP ta yi wucewarta........... Saura kaɗan Rimsha ta saki fitsari a wando saboda tashin hankali, jikinta ya tsananta kerma, kallonta a kan Uncle Faryan dake girgiza mata kai alamar kada ta tsorata.
Harleen kuwa ko a jikinsa yana cigaba da cin small shop da Faryan ya shigo mashi da shi, suka baiwa bansa ajiyar su ACP, kuma ga shi su ACP ɗin suna shakkar shiga cikin ɗakunan gidan su duba ko Abba yana nan, su da kansu sun san da wuya idan Abba yana gidan, amma sun jajirce sai Khaiza'an's family sun kulasu.
Ganin babu sarki sai ALLAH ne yasa suka ce zasu tafi da Rimsha, idan har suna sonta Khaiza'an ya kawo kansa station. Still dai babu wanda ya kulasu, ACP ya kamata suka nufi waje. Take ta fara kuka hawaye bibbiyu.
Suna fitowa harabar side ɗinsu sai ga motar Aryan ya danno kai, sun dawo da Abba, an je an gyarawa Abban karafunan kafafun nasa. Tin Aryan bai gama parking ba Abba yasa hannu zai buɗe kofar motar saboda ganin Rimsha a hannun ƴan'sanda ya ɗaga mashi hankali. "Abbaaaaaa......" Aryan ya faɗa yan jan sunan.
Harara Abba ya dalla mashi kafin ya buɗe mota ya fita, da alama har yanzu bai huce ba, Aryan kuma babu alamar zai karɓi wannan umarni, ba zai yarda ya auri Aunty Lusi ba. Fitowa Abba ya yi, yana dogara sandarsa ya isa gaban ACP. Da karfi Rimsha ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ta nufi Abba, amma ACP ya ƙanƙameta, bai saketa ba.
Lokaci guda kuma ya saketa a razane yana kallon Aryan dake tinkarosu tamkar wani zaki, gabaɗayansu babu wanda hantar cikinsa bai kaɗa ba, ACP har da haɗiyar wani yawu da karfi gwad. Da gudu Rimsha ta nufi Abba, tana zuwa ta faɗa jikinsa, riketa ya yi yana cigaba da kallon ƴan sandan.
"Me haɗinku da jikata? Me tai maku zaku kamata?". Abba ya tambaya...... Da kyar ACP ya saita natsuwansa game da ɗauke kallonsa daga kan Aryan dake gab da ƙarisosu kafin ya ce. "Lush family ne suka shigar da ƙara a kan Khaiza'an, batu ne na cin zarafin ɗan adam, ka tilasta masu yin abin da basa so, ka kawo kuɗi ka basu dan kasayesu, cin hanci kenan, kasan kuma corruption haramun ne a ƙasar nan"..….. Abba ya gane karatun, watau grandpa ɗinsu Noor ne da wannan ɗanyen aiki.
A daidai lokacin Aryan ya ƙariso wajen, fuskansan nan tamau babu alamar wasa, a dake ya ce. "A yaushe CRYSTAL PALACE ta yi lalacewar da ƴan sanda zasu iya shigowa cikinta?!"...... Shiru ƴan sandan suka yi, dan sun san ba kai tsaye suka shigo da nufin kama wasu ba, sun yi wa jami'an dake bakin main gate karyar cewa ziyara zasu kaiwa ɗan uwansu a Lush family, shi ne suka samu hanyar shigowa, dan jami'an bakin gate sun duba number Lush family dake jikin littafin CRYSTAL PALACE ɗin, sun kira table phone nasu, suna tambayi cewa suna da baƙi kala kaza ne? Dama grandpa ne ya ɗauki wayan, sai ya ce e suna da baki, shi ne fa suka basu hanya bayan sun cajesu basu ɗauke da komai sai bindigar aiki.
A tsarin CRYSTAL PALACE da yanayin tsaronta babu wani jami'in da ya isa shiga cikinta ya kama wani, babu wannan mahaluƙin, idan akwai mai laifi a cikinta to sai dai a tuntuɓi jami'an dake tsaron CRYSTAL PALACE ɗin, su da kansu zasu yi bincike, idan ya tabbata mai laifi ne, da kansu zaku kama shi, idan kotu ne su miƙa shi kotun dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin, idan hukunci ya dace da shi su zasu yanke mashi, shiyasa na ce maku manyan kai ne ke zama a cikin CRYSTAL PALACE, akwai tsaro, dokoki da ƙaidoji, babu wani abin da ya isa zama barazana ga mutanen ciki, karfin ikon CRYSTAL PALACE ya zarce yadda kuke tinani.
Tsuru-tsuru ƴan sandan suka yi. Aryan ya daka masu tsawa, hakan yasa ACP ya ce. "Dama Lush family ne suka shigar da ƙasa kan Khaiza'an, shi ne muka zo tafiya da shi.......".
Bai iya ƙarisa maganar ba sakamakon gigitaccen marin da Aryan ya ɗaukesa da shi, wai Abba aka zo kamawa. In a harsh way Aryan ya ce. "Ba'ayi mahaluƙin da zai iya taka gidan Khaiza'an da suna kama shi ba!". Da farko Aryan ya so nuna masu ID card ɗinsa na SSO, sai kuma ya fasa, dan basu kai ya tsaya nuna masu waye shi ba, gara ya jibgesu ba'a matsayi nagaba da su a wajen aiki ba, su rubuta a tarihinsu farin kaya ya jibgesu.
Abba sarkin izza, aikuwa ya ce Aryan ya ƙara masu, dan shi an walaƙanta shi da har ƴan sanda suka shiga gidansa. Kallon Abba Aryan ya yi. "Abba ka je ciki kawai". A tausashe ya faɗa...... Hannun Rimsha Abba ya riko suna nufi elevator yana faɗin kada Aryan ya raga masu, ya masu hukuncin da gobe ko sunan Khaiza'an suka ji sai sun saki fitsari a wando.
Shi kuwa Aryan Abba na shiga ciki ya ɗauki waya da nufin ya kira jami'an SSO dake benensu, sai ya ga wayar Lion ce a hannunsa, ya ɗan yi mamaki, sai can ya tina ashe ɗazun da ya kwanta jikin Lion suna hira wayoyinsu na haɗe waje guda, da ya tashi ne ya manta ya ɗauki na Lion kenan, dama wayoyin iri ɗaya babu abin da ya rabasu, sai ka kunna hasken wayar zaka ga wallpaper kowa da kalar tasa.
Kiran jami'an ya yi, ya ce su zo su wuce mashi da ƴan sandan nan, su ajiyesu zuwa dare zai nemesu. Bai faɗawa jami'an SSO ga in da yake ba, ƙasa da minti biyu sai gasu sun yi diran mikiya a wajen, suka wuce da su, su ACP idanu ya raina fata, ga shi yana tsoron ɗaga murya kada ya jawa kansa, dan jami'an dake tsaron CRYSTAL PALACE gabaɗaya jami'an SSO ne, amma ba kowa yasan hakan ba, saboda kada ku manta jami'an sirri ne. And yasan dokar CRYSTAL PALACE, ya yi wa jami'an karya ya samu ketowa ciki, idan ya ɗaga murya zai ji a jikinsa ne.
Gara ya yi shiru kawai...... A yayin da dikka wannan abin yake faruwa ita kuwa Seraphina tana can cikin ɗakin Mom ɗinta, ta tada kai da cinyar Madam, Madam ɗin tana gyara mata kyakkyawan silky ash hair ɗinta, tana rike da waya, suna hira da Madam tana ɗan dube-dube a wayar.
Madam ta ce mata. "Baby daddy baki jin magana, kullum sai na ja maki kunne a kan kada ki dinga irin waɗan nan maganganu da daddynki amma baki ji ko?"...... Ta faɗawa Madam dik yadda suka yi da Aryan jiya ne, shi ne Madam take mata faɗa, ta nuna mata illar maganganun, ta kuma gwada mata cewa da kunya aka san mace, tai mata faɗa sosai fa, kuma ta yi alkawarin ba zata sake ba.
Cikin shagwaɓa ta ce. "Yauwa mom, kin tina mun, yau tin safe ma daddy bai zo ba, har na je school na dawo, sai wani katon mutumi ya turo wai ya kaimu schy, ga shi na dawo bai zo ba, bari in kirasa video call". Ta faɗa tana turo baki, yau Aryan bai zo ya kaita asibiti ba, ya je amsa kiran Abba har suka tafi hospital, sai dai ya turo ɗaya daga cikin jami'an SSO ya zo ya kaita, kuma ya dawo da ita a lokacin tashi.
Madam zata yi magana sai ta ga Seraphina ta danna video call tana murmushi, ɗan kawar da fuskarta Madam ta yi tana faɗin. "Ki dai natsu, kada ki yi wa daddy shirme, ki mashi magana a kame cikin natsuwa".
Da okey ta amsa........ A daidai lokacin kiran ya shigo wayan Aryan, jawo wayar Lion dake kwance saman bed ya yi, a tinaninsa wayansa ne, ganin video call yasa ya ɗan yi mamaki, sai kuma ya zaci ko Leo ne, amma sai ya ga an yi saving sunan da Cherry bloom, shi dai yasan da boy ya yi saving number Leo, kuma Leo ne kawai zai kirasa video call sai kuma Vir or Aryan, guru ma yana gida.
Ɗan jujjuya wayar ya yi yana son tabbatarwa da wayansa ne kuwa? Daidai lokacin kiran ta katse, yana ƙoƙarin kunne wutar ya duba wayar waye sai ga wani kiran ya shigo, wayoyinsu fa idan basu da numberka kiranka ba zata shigo ba, sanin haka ne yasa ya ce dole na gida ne yake kira, dan haka bari ya ɗaga ya ga wanene dik da bai san wayan waye bane a tsakanin su ukun, nasa ne ko na Aryan or guru?.
Picking ya yi a daidai lokacin da ta ɗaga kai tana kallon Madam tana cewa. "Mom daddy baya ɗaukan kiran, kila ya bar wayan a wani waje ne"........ Ta kai karshen maganar tare da dawo da kallonta a kan screen ɗin. Ai wani irin razana ta yi ganin jade sexy eyes na Lion yana kallonta.
Ihu ta kurma tana miƙewa zaune, ta saki wayar a ƙasa tana faɗin. "He's the one! He's the one who killed my mom! Haka idanunsa yake, with this nose mask ya zo gidanmu, this is his eyes, mom he's the one!". Muryanta na rawa kirjinta na bugawa da karfi take maganar, lokaci guda kuma ta ɗauke wuta ɗiff, ta sulale ƙasa zata faɗi Madam ta rikota da sauri.
Kit Lion ya katse kiran yana jan siririn tsaki, ya janye nose mask na fuskansa ƙasa yana mamakin yarinyar yadda aka yi ta rike kamanninsa, wai da wannan nose mask ɗin ya je gidansu, da yake su IRON FIST nose mask ɗinsu kala ɗaya ne, dik duniya kuma su kaɗai ke da irinsa, su suka zaɓi design da suke so Company ta buga masu, shiyasa Seraphina ta ce da wannan nose mask ya je gidansu, hakika da irinsa ne sak ba banbanci.
Lallai yau akwai rikici tsakanin Aryan da Seraphina idan ta farfaɗo, sai ya faɗa mata dama yasan wanda ya kashe mammynta kenan, a gefe guda kuma akwai rikici tsakanin Aryan da Lion, sai ya faɗa mashi dama yana tare da Seraphina, sai ya faɗa mashi ma'anar Cherry Bloom, e kam akwai case!! Yau dai na ce bari in barku ku ɗan shana ba sai mun leƙa WS-HOSPITAL ba, ku huta da tashin hankalin na yau kam.
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-38-bg-princess-teema
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
[10/01, 9:16 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-19.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Dedicated to all Aryan and Zayra'an fans.🫀♥️
E_____________ 38
CRYSTAL PALACE.
Gyara kwanciyarsa Lion ya yi yana tinanin meyasa Aryan yake zuwa wajen yarinyar nan har haka? Shi fa ya ce su bata rayuwa mai kyau ne, amma a nesantata da su, baya son ya buɗe idanu ya ganta a kusa da su ko kaɗan.
Kun fahimci wani abu jama'a? Lion ya tsani mata, amma har yanzu zuciyansa da sauranta a kan Seraphina, a yanzu ba wai ya tsaneta kai tsaye bane, ya tsani ta zo kusa da shi ne, dan yasan sai ta zame mashi rauni, Seraphina amana ce a wajensa, domin ya cika wannan amanar yasa bai barta ta ƙare a cikin gidan Dr sun mutu tare ba, bai ceci Dr ba, saboda suna da muguwar gaba a tsakaninsu, but ya ceci Seraphina, ya fita da ita ta window, bayan an kunnawa gidan wuta ya zo ya ɓoyeta cikin jaccuzi.
Idan bai yi niyyar cikawa mahaifinta amanar ba zai kyaleta ne a gidan cikin jacuzzin ta mutu, amma saboda ya cika alƙawarin da yayansa ya bar mashi, yana kwance gadon asibiti ya turo jami'an SSO suka zo gidan da daddare a washegarin ranar da abin yafaru, suka shiga suka ɗauketa, baya ga haka in ya so zai iya watsar da amanar da yayansa ya basa a lokacin, amma sai bai yi hakan ba, dan dik duniya bashi da biyun mutane biyun nan, daga Hussainin daddynsa sai Yayan nasa, ko zai yi fushi a kan komai ba zai yi fushi a kan mutane biyun nan ba, dan ya cika amanar gabaɗaya ya ce a bata rayuwa mai daɗi, kada ta nemi komai a rayuwarta ta rasa, ta rayu tamkar ƴar sarki a cikin kingdom, amma kada a bari ta sake ganinsa, kada a bari ta sake zuwa in da yake, ya tsani ganinta
Kun san meyasa baya son haɗa inuwa da ita kuma baya son su haɗa inuwa da mata? Domin confirm sai mata sun zame rauninsu, kuma haka ne, in dan ya ɗauki Seraphina suna gida ɗaya, ko baya sonta ya tsaneta a hankali yau da gobe suna haɗuwa sai ya zama cikakken uba a gareta, idan haka ta faru kuma zata zame rauninsa na farko, idan wani abu ya tashi ko shi ba'a iya farmakansa ba ita za'a farmaketa wanda hakan zai raunata shi sosai, tana zuwa school ai, za'a iya cutar da ita ko ta nan, amma kunga yanzu tana rayuwa a gefe, bai saba da ita ba, hasalima bata san shi ba, ko kasheta aka yi ba zai ji zafin komai ba.
Tabbas mata raunin maza ne, komai jarumtar namiji idan kunga an kaisa ƙasa to ku duba a tafiyar da aka kaisa ƙasan an haɗa da mace, idan ana son galaba a kan namiji sai da sa hannun mace, haka ALLAH ya yi zuciyar namiji, macece rauninsa. Kuma hakazalika mace tana zama karfin namiji! Dik in kaga namiji ya yi nasara a rayuwa ku duba gefensa akwai mace, shiyasa MANZON ALLAH (SAW) ya umarci maza da su nemi mace ta gari, dan yasan mace itake juya kaso 65 zuwa 70 cikin ɗari na rayuwar namiji, idan ya samu mace ta banza babin wahalar rayuwansa ya buɗe kenan, idan kuma ya samu ta kirki, babin jin daɗinsa ya buɗe kenan, Manzon ALLAH (SAW) baya kuskure, da ya ce ku nemi ta garin kawai ku nema ne, dan mata sai shirin ALLAH!.
Da kun san tarihin daddyn Lion hakika da zaku ƙara gasgata me nike faɗe, daddyn Lion yarinman da ya taso cikin gata da tsantsar kulawa, ya bar gida kan ya cewa mahaifinsa sorry, daddyn Lion mutum mai zafin zuciya da taurin rai tamkar zaki, mutumin da ya taso cikin addinin bautar rana, an gwabza yaki da kakasa dan neman ƴanci daga turawan mulkin mallaka, jarumta gadon masarautansu ne, saboda zafin zuciyansa ya gwammaci ya bar gida, ya bar gata da iyayensa kan ya bada hakuri.
Ya komo US, ya rayu kaman sarki saboda dukiyan da mahaifiyasa ta basa a lokacin da yake barin gida, daga bisani ya gane yana da baiwa, zai iya abubuwa dayawa, ya tsaya ya jajirce sosai, a tafiyarsa ya haɗu da macen da take iya canza akalan rayuwansa, dik duniya a lokacin idan ya yi fushi ita kaɗai take ce mashi calm down, ta taushesa ya haƙura.
Macen da ya so fiye da kansa, macen da ya sanar sirrinsa fiye da ɗan uwansa Hoosain, macen da in ta ɓata rai sai US ta tsaya na ɗan lokaci saboda fushinsa, idan ka taɓata to jini ne zai zuba, da dik wanda ya taɓata baya yafe mashi koma wanene, harta mahaifinta ya taɓa marinta a gabansa kafin su yi aure, kafin mahaifinta ya sauke hannu ya rama mata ɗaya tamkar dubu, daga mari ɗaya sai suma, kai tarihin daddyn Lion abu ne mai tarin darasi, zaku ji complete tarihin ba zan rage komai ba a gaba, dan ni wlh tarihinsa ya fi mun