Showing 57001 words to 60000 words out of 365093 words

Chapter 20 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5908

ya zauna tare da cewa. "Good morning bro"........ Bai amsa ba sai ya miƙe zaune yana binsa da wani irin kallo mai kama da na tuhuma. Da sauri Noor ya bi jikinsa da kallo kafin ya sake kallo Leo, shi dai bai ga wani abin tuhuma a jikinsa ba.

"Bro lafiya?". Ya faɗa a ɗan rikice, dan wlh idanun Leo rikita shi suke yi, ga su kalar sanyi zubin sleeping eyes, amma sai shegen kirita mutane....... Ganin babu alamar zai yi magana ne yasa Noor ɗan turo baki kaɗan kafin ya ce. "Ka iya gindayar da mutum kasa ya fara zargin kansa"........ A yanzu shakuwa ce sosai ta shiga tsakaninsu a cikin wata ɗaya da ta wucen nan, sun zama tamkar ƴan uwan gaske.

"What kind of dream did you have last night?". In a cool way ya faɗa. Da sauri Noor ya sanya hannu yana rufe fuska, sai kuma murmushi ya kubce mashi. Wani irin kallo mai kama da harara Leo ya jefa mashi wanda yasa ya haɗiye murmushi, sai kuma ya ɗan shagwaɓe fuska. "Kai bro, I don't know her, but she's so pretty and cute".

Shiru Leo ya yi yana kara kare mashi kallo, yaro ya fara girma har da mafarkin mace, wai kyakkyawa ce, Noor ma ɗan duniya ne wasa-wasa. Jiya bayan sun dawo daga training na dare sai barci ya ɗauke sauran da wuri, shi kuma Leo sai da ya yi nafilfili sannan ya kwanta, bayan ya idar da sallar ne zai wuce sai ya ga Noor na mafarki, gabaɗaya sai numfashi yake yi sama-sama tamkar mai push-up ko wani abin mai wahala, har da haɗa zufa, ga bananarsa a miƙe zat. Kamar zai taɓa shi sai kuma ya ce kada ya katse mashi jin daɗi, shi ma da yake ɗan duniya ne wai kada ya katse mashi jin daɗi, shi ne ya kyalesa.

"Sai yanzu zaka ji kunyata?". Leo ya faɗa tare da yunkurawa zai sauƙo ƙasan bed ɗin, da sauri Noor ya biyo shi suka sauƙo..... "Bafa kunya na ji ba, amma bro fatan baka ga komai ba?"....... Girgiza kai Leo ya yi alamar yeah bai ga komai ba, daga nan bai sake yin magana ba.

Kashe wayansa ya yi tare da ajiye wa, sannan ya ɗauki ɗan littafinsa, ya fara ƙoƙarin shinfiɗa gadonsa. Da sauri Noor ya taya shi suka shimfiɗa, ya ajiye wayansa a ƙasan pillow sannan suka nufi waje, dan lokacin sallah ta kawo kai, har an fara tada kabbara.

Kai tsaye masallaci suka nufa, suna tafe kamar wasu kurame....... Bayan sallah sun haɗu a hall da suka saba tsayawa. A nan Captain ya zo ya samesu. Kamar kullum sai da yasa suka rera taken GIDAN SOJA kafin ya ce su nufi wajen da zasu yi weapon combat training. Ai Noor na jin haka ya matsa kusa da Leo, a ɗan shagwaɓe ya ce. "Bro ni ba zan iya rike bindigar nan in yi harbi ba, akwai wahala".

Kallo mai kama da harara Leo ya dalla mashi kafin can ƙasa ya ce. "But in the dream, you said you were strong enough to even harm a woman, right? Isn't that what you claimed yesterday?"....... Da sauri ya ce. "Kai bro mafarki ne fa ba zahiri ba, ku ma ni ban yi komai ba"........... Hannaye Leo ya zura a aljihu bai sake yi mashi magana ba, dan jiya Noor ya goge mashi hadda a mafarkin nan, wai har da sambatu.

A tsakiyar hall da zasu gabatar da weapon combat training ɗin suka tsaya, koya musu amfani da bindiga da harbi cikin hanzari da tinani za'ayi. Dan Captain yasan basu gama iya sauya harsashi a kasa da minti ɗaya ba, kunga kuwa in basu iya ba akwai matsala, in suna tsaka da yaki bullet ya kare waye zai sauya masu? Musamman ace abokan gaba na harbo masu harsasai! Kunga ai dole su kware sosai.

Nan aka kawo wasu ƙananan bindigu waɗan da ba kai tsaye na gaske bane, dan bullet ɗinsu ma yana cikin cover saboda tsaro. Nan Captain ya umarcesu da kowa ya ɗauki ɗai-ɗai. Bayan sun ɗauka ya kirga daga ɗaya zuwa uku ya ce kowa ya cire bullet dake cikin bindigar a second 30!

Cikin zafin nama suka fara, Noor jikinsa har kerma yake yi wajen buɗe magazine ɗin bindigarsa, inda ake sakawa bullet ɗin kenan, ya ciro bullet ɗin ya ajiye a gefe, shi ne na biyun gama bayan Leo.

Sai dai kuma tin daga kan manyan Generals dake kula da sashen horonsu har izuwa kan Captain da ake komai a gabansa sai da suka tsaya cak na ɗan dakiku a lokacin da suka ga abin da Leo ya yi. A lokacin da ya ɗauki bindigar da aka bashi, abu na farko da ya fara yi shi ne sai da ya fara rufe barrel na bindigar, bututun harbi kenan, sai da ya rufeta, sannan ya buɗe magazine inda ake saka alburushin ya cirota. Mamaki su Captain suke yi, domin kuwa Leo bindigar gaske suka bashi, kuma bullet ɗinta ba'ayi covering ba, sun yi ne dan su gwada shi, yana ɗaukar bindigar daga yanayin nauyinta ya gane komai real ne, shi ne ya fara rufe wajen harbinta kada ta kwace ta harbi wani, kwakwalwarsa tana da mugun gudu ne fiye da tunani, dik a ƙasa da second 20 ya yi wannan aiki!.

Hakika sun shiga mamaki, dik yadda aka yi Leo ya san bindiga matuƙar sani, basu taɓa zatan zai gane komai na gaske aka bashi ba! Shi kuwa bai kawo komai a ransa ba, ya cire bullet ɗin ya ajiye a jefe cikin kwanciyar hankali.

Captain sai da ya ɗauki ƴan mintina a ƙallah biyar kafin ya dawo daidai daga girgizan da Leo ya sanyasu. Sannan ya ce. "A ƙasa da 30 second ku mayar da bullet ɗinku, a ƙasa da second biyar ku ɗauki saitin harbi wa wancan board ɗin".

Tin bai kammala rufe baki ba suka fara, komai Leo yake yi cikin tsantsar natsuwa, a haka ya mayar da bullet ɗin, sannan ya mirgina daga in da yake, cikin zafa ya ɗauki saiti kamar da aka umarcesu. Ganin yadda ya yi yasa Noor ma mirginawa ya ɗauki saiti.

Note, akwai abin da na mance ban faɗa maku ba, dik wani horon da aka yi masu ana maimaita masu shi ne har sai sun kware ya bi jikinsu, sai su fi sati suna maimata horo ɗaya, kunga ni kuma ba zan tsaya mu yi ta maimaita rubutun da muka yi ba, kun gane ai?!.

Harbin tsakiyar board ɗin Captain yasa su yi, hakan yasa suka yi gagawar fara harbi, bullet ɗin kowa na da cover ne, hakan yasa ya fita salun alum ba wata ƙara sosai, shi kuwa Leo yana buga nasa sai da suka ɗan razana, dan ba cover.

Dik wajen room 1 ne basu saɓa saiti ba, suka harbi in da aka buƙata, sai su Unays ke biye masu a saiti mai kyau. Captain ne ya ce. "Yanzu ku kaddara kuna tsaka da yaki bulle ɗinku ya kare, yanzu ku ciro bullet daga waist ɗinku, ku sanyawa bindigunku a ƙasa da one minute sannan ku cigaba da musayan wuta ba tare da ɓata lokaci ba". Ya kai karshe tare da watsu masu bullet ɗaiɗai wanda zasu canza, sannan ya ce. "Minti ɗaya gareku".

Cikin zafin nama suka fara canzawa, wasu jikinsu sai rawa yake, wasu har da miƙewa tsaye, dan suna ganin a zaune buƙata ba zata biya ba. Dikkansu sun canza a ƙasa da minti ɗaya, amma room 1 sun canza ne a ƙasa da second 10 kacal saboda zafin nama da zafin jini irin nasu. Cikin zafa suka fara saita board ɗin suka yi harbi again.

Sosai Captain ya ji mugun daɗi, haka ya sanyasu suka dinga maimaitawa har sai da ya ga sun mai da shi kamar ruwan shansu, sannan ne ya ɗaukesu suka nufi wajen da za su yi hand to hand combat training. Ba kullum yaƙi da bindiga ake yi ba, akwai in da faɗar hannu yake da amfani, musamman ga waɗan da ake son kamawa ba kashewa ba, waɗan da ake son bayanai daga bakinsu, so dole su iya faɗa da hannunsu a cikin wannan sati gabaɗaya, daga yau zasu fara.

Sannan a nan aka koya musu dabarun ƙwace makami daga hannun abokin gaba. Sai da Captain ya fara koya masu yadda zasu daki abokin gaba, da yadda zasu karya hannu da kafafun mutane, shiyasa zaku ga wlh karyawa mutane hannu karamin aikin soja ne, sun kware a wannan sabga, to koya masu shi ma musamman ake yi, yadda zasu karya a take!

Sai da ya gama koya masu wannan sannan ya umarce su suyi faɗa da junansu, wanda ya faɗi sai ya sake gwabzawa da wani har sai ya iya kare kansa, sai sun kware a iya jibgar wasu amma su kada su bari a jibgesu.

Nan fa suka fara kallon juna, Leo bai zaɓi Noor ba, saboda yana tausaya mashi, yasan ma ba zai iya gwabzawa da shi ba, dan haka sai ya ce Juraiz ya zo su gwabza, dan ya gansa chocolate color, ga shi kakkarfa. Zaysh ya ɗauki Ameer, shi kuma Unays ya ce Noor ya zo su gwabza, har cikin ransa Leo bai so ba, dan ba zai iya ganin irin dukan da Unays zai yi wa Noor ba, dan yasan Unays ɗin ya fi karfin Noor, kuma yasan Unays bashi da tausayi, yanzu har cikin ransa yake jin Noor!.

Captain na cewa start suka fara gwabzawa tamkar wasu mayunwatan zakuna, duka suka fara kaiwa junansu babu tausayi babu tausayawa, kowa ya iya allonsa ya wanke ne. Wani irin naushi da Unays ya kaiwa Noor a baki sai da bakin nasa ta fashe, take jini ta fara zuba, sosai Leo ya ji zafin haka, sai ya ji tamkar jikinsa aka nausa, a ransa ya ce bashi Unays ya ci, dik duka ɗaya da ya yi wa Noor sai ya biya shi. Amma shi kuma ga shi ya yi wa Juraiz mugun duka har ya baje a ƙasa yana numfashi sama-sama, kuma yake cewa zai ramawa Noor.

Zaysh babu tausayi ya yi wa Ameer mugun duka shi ma, har ya fasa mashi baki, daga karshe ƙasa Ameer ya zube yana numfashi sama-sama. Ba karya Noor ya daku a hannu Unays duka mummuna ma kuwa, har sai da Captain ya shiga tsakaninsu, dan yaga Unays kamar ya mayar da abin gaske ne over, kun san dama yana jin haushin ƴan room 1, shi ne ya fara sauƙewa a kan Noor.

Ba Leo kawai ba, hatta su Zaysh sun ji takaicin dukan da Unays ya yi wa Noor, jikinsu har tsuma yake yi na ganin yadda bakin Noor yake jini har ya kumbura!.

Shi kansa Captain bai ji daɗin dukan ba, amma ya za'ayi? Dik cikin horo ne. Haka suna ji suna gani aka sake haɗa Noor da wani saboda doka ce in aka kada kai sai ka sake da wani. A nan ma Noor duka ya ci ba karya. Aka sake haɗa shi da wani, da team 1 suka ga fa za'ayi mashi mummunar illah sai Leo ya ce a haɗa shi da shi. Da sauri Captain ya aminta, saboda shi ma tausayin Noor ya gama cika shi.

Da aka haɗasu sake jiki Leo ya yi Noor ya yi nasara a kansa, sannan shi aka haɗa shi da wani, dik dai abin da suke yi manyansu na kallonsu. A wannan horo dai ba'a tashi ta daɗi ba, dan bakin Noor a kumbure dam suka nufi wajen breakfast.

Da kyar Noor ya iya cin abinci saboda yadda bakinsa take yi mashi zafi ga kumburi, sai da Leo ya mashi kalaman jarumta, sannan ne ya ci. Bayan sun gama karyawa aka ɗaukesu zuwa wajen da zasu yi guerrilla warfare training. A nan aka koyar da su yadda ake amfani da muhalli dan samun nasara a yaƙi.

Kowa ya shiga cikin maɓoya, dan dole ne su ɓuya kuma su yi tafiya a kwance ba tare da an gan su ba, kamar kwantan ɓauna kenan. Sannan aka koya masu yadda zasu ɓuya su saje da ciyayi dan kare kai, da yadda in sun ɓuya zasu fito da bindigunsu su yi harbi. Dan dole suyi hari ba tare da sun bayyana kansu ba, shi ake cewa yakin sunkuru.

Sai da suka yi awa guda a wannan horo sannan aka ɗaukesu zuwa wani tapkeken ruwa da aka yi shi musamman dan yin river crossing under attack training. A nan Captain ya koya musu yadda za su tsallake ruwa cikin gaggawa a yayin farmakin makiya, su tsallaka ana harbinsu da bindiga ta baya, dole su koyi kaucewa bullet a cikin ruwan. Kuma dole su iya yin iyo a cikin ruwa mai gudu, ana koya musu yadda ake ratsa ruwa ba tare da abokan gaba sun gan su ba, dole su natse cikin ruwa su rike numfashinsu suna tafiya har su haye. AIKIN SOJA BA NA RAGWAYE BANE MY PEOPLE'S, BA DIK KAI BA WLH! WAI DAN MA BAKU GANIN AZABAN A ZAHIRI, A RUBUTU BA ZAKU FAHIMCI AZABAR SOSAI BA, SAI KUN GANSU SUNA NISHI SAMA-SAMA TAMKAR RAI ZAI YI HALINSU A KAN IDONKU TUKUN NAN, A NAN NE ZAKU JI ZUƘATANKU SUN KARAYA, KUN TAUSAYA MASU.

Duk wanda bai iya tsallake ruwan a cikin lokaci ba sakowa zai yi. Haka suka dinga fama, waɗan da akwai pool a gidansu sun yi kokari, amma an sha ruwa kam, an kuma ci azaba, sai numfashi sama-sama suke yi tamkar ba zasu kai labari ba, amma a haka suka jure.

Bayan dikka wannan wahala sai aka kaisu in da zasu yi attack simulation, waje ne da aka shirya masu tamkar farmakin gaske, su kwaci kansu, unexpected suka fara jin farmakin.

Cikin zafin nama suka fara fito da kwarewarsu a fili, abu na farko da suka fara yi shi ne rarraba kansu zuwa team by team dan su kwaci kansu su kuma yi wasa da hankulan abokan gaba, na biyu suka fito da dabarun ɓuya, na uku suka haɗa kai a wajen dan ganin sun yi nasara. Abin ya yi matuƙar bawa manyansu mamaki, like wow, suna da basira. Sai ma da Captain ya ga suna yi wa juna magana da ido a lokacin da suka ɓuɓɓuya a wajaje tantunan dake wurin, magana sosai suke yi da ido na yadda zasu yi su tsira, kai abin ya bawa Captain mugun mamaki, bai taɓa zatan kwakwalwarsu zata yi sauri basu dabara da mafita ba, sai ga shi kuma sun yi.

Manyansu sun ji daɗi sosai. Daga nan suka nufi masallaci, bayan sun yi sallah suka yi lunch sannan suk nufi class. Yau an koya masu karfin gudun kowani bindiga, illarsa, dalilan da yasa yake kwacewa a wasu lokutan, goge dattinsa, cansa wasu sassa nasa, da faidar kowacce, kowacce lokacin da ya dace ayi amfani da ita.

Sun ɗauki awa biyu a class ɗin kafin su fito su sake komawa wajen horon harbi, dai saiti shi ne babban abu a fagen yaki, in baka da saiti ma kana iya harbin kanka, dan haka dole ka kware sosai. Daga wajen saiti da yamma suka wuce wajen horon hannu, dan ƙara gwada kwanci, suka yi gym na yamma sosai zuwa karfe 7 suka tashi horo. Masallaci suka nufa, bayan sallar mangrib and Isha'i suka nufi rooms ɗinsu.

Vash and Zaysh a tare suka jera zuwa yaronsu a maimakon su koma roon ɗin nasu. Noor and Leo kuma ɗaki suka koma, Leo ya je yana shafawa Noor magani a bakinsa da ta kumbura sosai. Sai sannu yake yi mashi, Noor sarkin son jiki tuni ya kwanta mashi a jiki har da kukan shagwaɓa, yau ya tuna da su Aunty Lusi, yadda yake yi masu ya hau yi wa Leo yau, shi kuma ya daure yana ta biye mashi, dan Noor ya shiga ransa matuƙa.

A gefe guda kuwa su Arya bayan sun dawo da school sun yi lunch V ta ce zata tafi wajen daddy, da sauri Arya ta hanata ta hanyar cewa su je su buga basketball a wajen game ɗinsu. Ba dan ta so ba ta yarda, kuma babu rabon haɗuwarta da Noor nan kusa!.

Arya ta raba masu team, suna sanya sportswear iri ɗaya kaunin milk color. Arya ta ɗauki basketball ɗin nasu suka nufi wajen wasanninsu. Katafaren fili ne da GAT yasa aka ƙawata masu shi, kayan wasanni ne kala-kala a cike a ciki, akwai wajen football, basketball, snooker, har wajensu whots akwai, kwallon kwando da komai dai.

Raba kansu suka yi team biyu, Arya da Manassa, Angelie and V. Akwai wasu zaratan sojoji dake tsaron wajen wasan, suna tsaitsaye tamkar saƙaguna suna satar kallonsu Arya. Ga shi sportswear ɗin nasu guntun wando ke zuwa tsala-stala cinyoyinsu dake wani irin glowing, very soft. Daga sama rigar tasu mai ƙaramar hannu ce, kayan dai yai masu kyau sosai.

Da suka fara ball ɗin dik in da suka yi idanun sojojin nan a kansu yake, musamman V da ko'ina yake cike dam, ai tana tashin kan mutane. Cikin nishaɗi suke wasanninsu cike da kaunar juna, Arya dai ta yi wa V wayau ta hanata zuwa ganin masoyi Leo.

A can cikin barrack kuwa zama Vash and Zaysh suka yi a saman wasu kujerun dake arear wajen horonsu. Suna zama Zaysh ya ce. "Bro kasan akwai mata a training ɗin nan?". Da sauri Vash ya amsa da. "Yeah, three days ago na haɗu da wata kyakkyawa a kusa da Senior staff side".

Shiru Zaysh ya ɗan yi kafin ya ce. "Ni kuma almost a month ago, mun yi karo da wata, kuma tin time ɗin ban sake ganinta ba"......... "Bar zancensu kira mana Ummie mu gaisa, na yi kewarta, jiya bamu yi waya ba"....... Watau idan kana da kyan hali kowa nemanka zai dinga yi!.

Wayansa ya je ɗaki ya ɗauko ya dawo, yana kunnata saƙon Ummie na shigowa. "Koman dare idan ka samu lokaci ka kirani". Shi ne abin da saƙon ya ƙunsa, haka kawai ya ji faɗuwar gaba, cikin zafa ya laluɓo numberta ya danna kira.

A lokacin tana zaune saman kujerarta da ya gama shan wahala, dama ba wani qualityn kirki ba. Kiran na shigowa ta yi gaggawar ɗagawa, muryanta na rawa ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login