Showing 117001 words to 120000 words out of 365093 words

Chapter 40 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

6196

yi nadamar nuna mata ainain face ɗinsa, ya nuna mata ne kuma ba dan komai ba sai dan kada shakuwarta da wancan face ɗin nasa ta yi yawa ta yadda hakan zai zame mashi matsala a nan gaba, amma gashi yana shirin kwantowa kansa ruwa, a ransa ya ce dole ya rabata da Rimsha ko kuma ya sanya aje ayi wa Rimsha surgery a canza mata kamanni, dik sai ya ji zafin yadda yarinyar ta ɗauko kamanin dangin ubanta bata yo uwarta ba.

Goge mata baki yake yi amma ya luluƙa duniyar tinani, dan har sai da ta ce. "Daddy is okey". Cire brush ɗin ya yi yana kallon kyakkyawan fuskanta ta cikin mirror, dika-dika tsayin Seraphina ko kirjinsa bata kai ba, shiyasa yake kara ɗaukarta a yarinya kamar sosai. Ɗauraye mata bakin ya yi kafin ya ce ta yi wanka ta zo. Daga haka ya fito waje zuciyarsa cike da tunanin meyakamata ya yi dan cire mata zargin yasan Rimsha da take yi.

A saman bed ɗinta ya kwanta yana tinanin har barci ta yi awon gaba da shi. Lokacin da ta fito daga wanka ya yi barci, a kusa da shi ta tsaya tare da zubawa kyakkyawan fuskansa ido na ɗan lokaci, kamar zata tashesa sai kuma ta fasa, yanzu ɗan zamanta da Madam har ta kara natsuwa da hankali, ta fara sanin daidai da ga daidai ba. Madam Rohisha musulma ce cikakka, dik wani ɗabi'u da abin da ya dace da musulmai shi take koyawa Seraphina.

Yanzu haka ta cusa mata kaunar son rufe jikinta, shiyasa ma kuka ji bata ce yau Aryan yai mata wanka ba, Madam ta faɗa mata jikinta sirrinta ne, kada ta bari kowa ya ganin mata, hakika Madam tarbiya take bata irin yadda uwa take baiwa yarta, amma kuma sai wanda Seraphina ta yi ra'ayi take ɗauka, ga ɗaura ɗankwalinan ba yadda Madam bata yi da ita ba amma yarinyar nan taki, haka take sakin gashi abinta, ko toilet haka take shigewa.

Closet ɗinta ta nufa dan ta shirya. Wandon jeans guntu zuwa gwiwa ta sanya da riga mai kamar hannu, ta wuce wajen Madam ta gyara mata kai, sai tashin kamshi take yi ta dawo room ɗin. Da Madam ta ce ta zo ta yi breakfast sai ta ce tana zuwa. Ta zo ta zauna a saman side sofa tana ta faman kallon kyakkyawan fuskansa.

A daidai lokacin wayansa dake cikin aljihu ta fara kara, hakan ya yi sanadin farkawansa, a kan fine face ɗinta ya sauke idanunsa. Ba tare da ya ɗauke kallonsa daga kanta ba ya ciro wayarsa daga aljihu, ko bai diba ba yasan Lion or guru ne suke giransa, su biyu ne kawai suke da wannan number da aka kira yanzu watau sim 2 ɗinsa.

Idanunsa a kanta ya yi picking tare da karawa a kunne, sannan ya ɗaura yatsansa ɗaya a saman lips ɗinsa yana mata nuni da ta yi shiru. Slowly ya motsa kyakkyawan soft lips ɗinsa wajen cewa. "What's going on? Meyasa kake tambayar ina nike?"....... Ɗan bakinsa kawai Seraphina take kallo, ya yi magana amma ba zaka taɓa cewa ya motsa lips ɗin ba.

Shiru ya ɗan yi for almost 1 minute kafin ya sake cewa. "Give me some minutes I'm coming". Yana gama faɗar haka ya ciro wayar tare da katse kiran. Miƙewa zaune ya yi idanunsa dik barci, har sun yi ja. Kasan bed ɗin ya sauƙo tare da cewa. "Baby zan dawo anjuma". Ya faɗa yana ɗaura hannunsa a saman shafaffen cikinsa dake ɗan murɗa mashi a hankali-hankali. Bai jira amsarta ba ya yi saurin ficewa. Kai tsaye ya koma benensu da sauri, dan yadda ya ji muryan Lion tamkar akwai matsala.

Yana saƙo kafarta cikin main parlonsu sai ga Leo tare da hero sun fito, Leo yana shirye cikin shigar ƙananan kaya, wandon ripped jeans baki, da polo shirt fari, ya ɗaura winter jacket a sama, ya yi masifar kyau, still dai yana sanye da nose mask a face ɗinsa, kafafunsa cikin socks kuma cikin boot kalar rigarsa, sai tashin kamshi yake yi.

Yana ganin Champion ya ce. "Bro dama wajenku zan je, jibi zan koma, zan je shopping yanzu"..... Guru dake kallon heronsu ne ya amsa da. "Take my ATM card". Ya faɗa yana ciro card ɗin daga aljihunsa ya miƙa mashi. Karɓa ya yi tare da sa kai zai wuce, da sauri zakin ya bi bayansa. Champion ne ya yi wa zakin magana da wani yare, ya ce. "Hero zo mu tafi ka bar Leo ya fita".

Kun san me? Iya wuya basa taɓa yarda su fita da zakin nan waje, kullum yana cikin gida, ɓoyesa ma suke yi saboda wani dalili nasu na kansu, akwai masu kiwon zaki sosai, ko gidansu Noor akwai damisar da suke kiwo, kuma idan zasu fita shan iska a cikin CP suna fita da shi lafiya lou, amma zakin IRON FIST baya leƙa ko kusa da elevator bare fita, kuma wannan zakin tin Leo yana jariri yake tare da su. Mutumin da ya reni Lion kamar shi ya basu zakin, kun san sun girma ne a hannun wani tsohon soja, bari zasu baku tarihinsu da kansu, zaku ji daga ina suka samo karfin zuciya da jajircewa kan duniyar nan, daga wanda ya rikesu har suka girma ne!.

Da gudu hero ya bi Aryan suka wuce ciki. Kai tsaye room na aikinsu ya shiga, dan yasan a nan zai isko su Lion. Kamar kuwa ya sani, zaune ya iskosu gabab computer suna ta aiki. A gaban nasa computer ya je ya zauna tare da miƙa hannu ya taɓa mouse ɗinta. Take ta kawo haske, nan ya ga tarin bayanai da Lion ya tura mashi kan WORLD SYSTEM.

Bayanai ne kamar haka, a natse ya fara karantasu a cikin ransa ni kuma na rubuta maku a zahiri.

Shirye-shirye WORLD SYSTEM ga duniya a cikin waɗan nan shekaru mafi kusa dake zuwa, babban shirinsu na farko shi ne cure duniya ta zama abu guda ɗaya, su fitar da shugaban ƙasa guda ɗaya addini ma guda ɗaya, hakan ba zai faru ba sai sun shafe dikkan addinai na duniya, sannan hakan ba zai faru ba sai sun rage population na al'ummar duniya, dan haka doke su kirkiro ta'addanci, cututtuka, ambaliyan ruwa, girgiza ƙasa, canzawar yanayin sararin samaniya dan a samu yawaitar faɗuwar jirage sama. Babban aikin da suka ɗauko dan rage yawan al'umma a yanzu ya haɗa da, digital identity harvesting, satar bayanan nutane a yau, da yawancin na'urori da apps ana tattara bayananka a ɓoye kama daga kan DNA, yatsanka, kalmomin da kake faɗi, inda kake tafiya, ana amfani da shi wajen gina maka digital clone dan su iya yi maka amfani nan gaba ba tare da izinin ka ba, bafa amfanin kirki zai maka ba, a'a za'a juya kwakwalwarce a lokacin da zasu fito da addini guda ɗaya wa duniya, ba zaka iya yi masu gardama ba, dan sun sace komai naka an juya maka ƙwaƙwalwa.

Shirinsu na biyu shi ne, mind control & neuro weaponry, fasahar sarrafa hankalin mutane, a baya ba na ce za'a sace bayananku ba? Idan aka gama sacewa sai a fara project kan yadda za'a fara sarrafa hankulan mutane, za'a fara sarrafa mutum daga nesa ta hanyar microwave, EMF, ko chip a kwakwalwa, sauya maku tunani, saka tsoro ko ƙiyayya cikin mutane dan ɗora su akan tafarki ba daidai ba, ku yi ta tsanar juna kuna kashe juna, kuma ko ya za'ayi maku bayani ba zaku fahimci kowa ba, dan abin da aka cusawa kwakwalwarku kenan ku tsani ƴan uwanku, ku ta kisa babu gaira babu dalili, ba zaku taɓa sanin cewa ana amfani sa ƙwaƙwalwarku ake cusa maku tsanar juna da son kashe mutane ba, ku dai gaku nan ne kawai zaku ta kisa, kuna sace ƴan uwanku, babu tausayi babu imani!.

Project ɗinsu na uku shi ne, kashe hanyar abinci, byar da abinci da ruwa da magani marasa kyau a ɓoye, nan gaba kaɗan aiki zai yanke, makarantu babu, asibiti ba za'a ɗauki ma'aikata ba, babu aikin yi dai a taƙaice, hakan zai sa al'umma su koma kan harkar noma da kiwo, dole su koma sana'ar hannu, shiyasa WORLD SYSTEM ta fara kashe ɓangaren sana'ar hannun ba tare da kowa ya sani ba, zasu baku iri mai gurɓata ƙasar noma da muhalli su ce ya fi kyau ku shuka, da zarar kun fara shukasa shi kenan ya kashe naku irin, ko kun shuka naku ba zai fito ba, a lokacin da zasu fito da addininsu guda ɗaya wa duniya zasu ce ku yi imani da shi ko su hanaku abincin nomawa, dama irin da kuke shukawa nasu waye ne? Ko ku yi masu biyayya ko yunwa ta kasheku! Baku da mafita.

Makiyaya ma ba'a barku a baya ba, yanzu haka WOLRD SYSTEM tana ƙoƙarin kirkirar namar da za'a dinga haɗawa da technology pmh, zasu ce maku wannan nama yafi, zasu yaudareku ku karɓesa, zasu yi maku saukinsa, ku kuma zaku so banza, daga nan ku zubar da batun kiwata naku dabobin, zasu rabaku da dabobinku ta hanyar kashe wasu, su ƙone wasu, su sace wasu, daga karshe su hanaku namansu da suk sayar maku a sauki da aka kirkiresa da technology ne ba namar da ALLAH ya bamu ba, dole idan kuna son nama ku yi biyayya ga garesu. Wannan abu bata shafi musulmi ko kirista ba, mai kuɗi ko talaka, zaku sha mamaki a lokacin da masu kuɗin kansu zasu fara nadamar bautawa waɗan can tsanannun, dan kwantan ɓauna suke yi masu a yanzu, babu wanda zai iya gane hakan.

To abu na gaba shi ne, geoengineering, gine-ginen masana'antu dake kwanto ɓaraka wa duniya bakiɗaya, zasu yi gwanjo da jirage da ke fitar da hayaki, zasu kirkirosu ne su sayar da su a arha, jiragen su yawaita, a daina hawa motoci sosai, amma abin da baku sani ba shi ne waɗan nan jirage da zarar sun tashi sama canza yanayin sama suke yi, suna bada chemtrails a sama dan canza yanayi, wannan yanayi shi zai ƙirƙiro fari, ambaliya, da kuma girgizar ƙasa masu girma a jere a jere, wannan fasaha ce ta cikin geo weaponry, ta haka ruwa zai ɗauke a yankuna, koguna su ƙafe, rashin ruwa rashin abinci, dik abin da kuke zato ya wuce nan........ My people a koda yaushe, ko bana raye idan kun tina da Princess Teema or Star Lady ku mun addu'a, sannan ina rokon da ku tayani addu'ar samun damar kamma rubuta wannan littafi.

Aryan ya kammala karanta wannan bayanai Lion ya sake turo mashi wasu kamar haka. A dik cikin ƙasashen dake duniya AVARIS ce kasar da ta fi cancanta a garesu su fara aiwatar da wannan project ɗin, kasar tana da dik abin da suke buƙata, shiyasa suka sanyawa ƙasar ido, fitinar yau daban ta gobe daban, kuma abin mamakin shi ne manya masu gudanar da wannan tsari cikin barisa da hangen nesan mafiya yawa daga cikinsu ƴan Avaris ɗin ne, saboda ƙasa ce dake da tarin ƴan baiwa, suke basu tsari da abin da ya dace. Yanzu dole mu fara aiki a kan Avaris kafin mu cinwa WORLD SYSTEM.

Ɗago kai Aryan ya yi bayan ya kammala karanta wannan jawabi, sai ya ce. "Bro i saw one message in the morning cewa an samu sabbin ƴan ta'adda da suka fito a kasar Avaris two days ago, ƴan ta'adda ne masu haɗarin da suka fi waɗan da suke cikin ƙasar a yanzu". Ya yi magana dikkansu shi da guru kallonsu a kan Lion suna jiran jin me zai ce, ni kaina ina jiran jin me Lion zai ce, dan nasan zancensa gaskiya ce zai faɗa, fasa kwai zai yi.
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-18-by-princess-teema
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.




STEP 1🔥


2025-11-21.🔥



اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E_____________ 18




Lion bai yi magana ba for almost 5 mins, sannan yai masu dropping messages na bayanai a computers ɗinsu. Sun san bayayin dogon magana, dikkansu basa tsawaita magana, amma na Lion and guru is worst, magana ta minti ɗaya ba zasu iya yin bayani ba, sun gwammaci zaman typing su tura ba magana ba, shi Champion idan ta kama yana daurewa ya yi magana har na mintuna biyu.

Already sun saba dama dik abin da suka tambaya a rubuce yake turo masu amsa, suma a rubuce suke tura tambaya, sai basu wani damu ba, a natse suka buɗe message ɗin kamar haka.

"Kun taɓa ganin yadda ƴan ta'adda suke fitowa dan kansu kawai ne? Ƴan ta'adda! Wasu jama'a ce da ake kirkirarsu musamman dan a fitinawa al'umma, kun taɓa tambayar kanku ina iyaye da ƴan uwan waɗan nan ƴan ta'adda? Kun taɓa tambayar kanku meyasa ƴan ta'adda suke da horo kan sanin makamai tamkar yadda sojoji suka sani? Za'ayi musayan wuta da ƴan ta'adda da sojoji, idan bullet ɗinsu ya kare a ƙasa da minti ɗaya suke sake sanya bullets a bindigunsu tamkar yadda aka horar da sojoji sanya bullets a bindingu cikin gaggawa, kun taɓa tambayar kanku ya aka yi suka iya dikka wannan? Ko dai a kullum kuna rigingimu tsakaninku da ƴan uwan da kuke tare da su cewa sune ke kasheku?".

Wani dogon note ya sake tura masu kamar haka a kasan wannan. "Terrorists! Kalma ce wacce aka kirkira, ƴar ta'addan dake Avaris waɗan da ake ta ikirarin sun addabi al'umma dikkansu kauyawa ne, dakikai ne da basu taɓa shiga class ba, ya aka yi suka iya karatun sanin makamai karatun da ya fi kowanne wahala? Sanin ita kanta bindiga ba karamin wahala bace, ya aka yi suka san dikka wannan? Ya aka yi suke da bindigun da suka fi na sojijin Avaris karfi da sabonta? Ta ina suke samo makamai masu karfi da kayan aiki tamkar jami'ai? Sun fi wasu jami'an ma kayan aiki in gantattu! Why?"

Amsa, a bayan kowani ɗan ta'adda ko ɓarawon daji akwai manyan dake bashi umarni kuma dake koya mashi aikin ta'addanci, ƙalilan ne daga cikin ƴan ta'addan suka fito daga kasar Avaris ɗin, kalilan ɗin kuma jahilan ciki aka kwasa game da yi masu karya da sunan jahadi suke yi wa musulunci, da rashin iliminsu aka yi amfani wajen sanyasu aikata abin da suke yi! Amma ainahin ƴan ta'addan idanu baya ganinsu, mutane ne da aka kirkiresu, tsawon shekaru aka horasu, mutane ne da basu da wani dangi bare su san daɗi dangi har su ji tausayi, basu da iyaye, su kawai an kirkiresu ne saboda taaddaci da kashewa, shiyasa ba zasu ji tausayin kowa ba, ba zaku taɓa gane kan wannan rigima a yanzu ba, sai bincike ya natsa damu cikin WORLD SYSTEM komai ya yi nisa zaku gane mecece ainahin ta'addanci, su waye ainahin ƴan ta'addan da ake dangatawa da musulmai alhalin basu ma da addini kwata-kwata, dik wanda yake matsayin member na wannan taaddancin bashi da addini wlh! Ko kiristoci na kwarai basa kisa haka ɗai, saboda sun karanta Annabi Isa ya haramta!.

Tin da suka gama karantawa suka natsu tsit suna nazartar kalaman Lion, dik abin da ya faɗa gaskiya ce, ba yadda za'ayi ace rana tsaka ƴan ta'adda su bayyana a waje, su kori jama'a a kauyuka su kwacesa su zauna, lallai tsawon shekaru ake ɗauka wajen horasu a kan hakan, tamkar yadda ake hora sojoji, idan an gama horasu sai su bayyana, ba ƴan ƙasar Avaris bane, bakin haure ne, wlh ainahin ƴan ta'addan ba ƴan kasar bane! Suna amfani da ƴan ƙasar ƙalilan daga cikin jahilan da sukaki karatu ne, sai su fake a bayansu suna taddancin, ƴan kasan da ake yi wa kallon ƴan ta'adda lallai karnukan farautar jiga-jigan dake laɓe a bayansu ne, manyan basu fitowa fili su yi aiki kai tsaye ne saboda gudun aga banbancin launin fata da sauyin harshe, shiyasa suna gefe suna koyawa karnukan farautar tasu ɓarna, ban da haka dakikin da bai je makaranta ba yaushe yake iya magana da correct English? Baku taɓa jin ƴan ta'addan suna turanci ba ko? To iyayen gidansu dake koya masu harbi da bindiga da sauransu turanci kawai suka iya! Dole su koyi turanci na magana yau da kullum.

(Can naga wani ɗan ta'adda a media yana video yana cewa we have a lot of informance everywhere, I said eyeee this guy hear English well-well, he pass me da na yi FGC makarantar da ba'a magana da kowacce yare a cikinta sai turanci, ashe ni dik shirme na iya, ga wani a kwana can ya kware ba tare da zaman class ba. ALLAH kai mana kyakkyawan karshe, ba lallai a yanzu ku gane in da na dosa ba, saboda tushe nake son ɗauko maku, but keep reading, zaku gane sosai a gaba!)

Nazarta kalaman Lion for almost 10 mins suka yi, sannan Champion ya hau typing kamar haka. All what you said is true, but ƴan kasar ba zasu taɓa fahimta ba, everything is damage now.

Typing amsa Lion ya yi da cewa. Shiyasa aka shirya masu rikicin addini, rikicin akida da rikicin ƙabilanci dik dan kada a bar hankalinsu ya natsu waje guda har su iya fahimtar gaskiya, kasan ƴan kasar Avaris ba dai ƙwaƙwalwa ba, ko dame kake ji sun bugeka a kaifin tinani da basira, shiyasa ba za'a barsu su natsu har su yi tinani ba dan an san confirm sai sun gane gaskiya, wannan dalilin yasa rayuwarsu aka mayar da shi tamkar season film, kowani sati da sabon season da za'a shiga masu, a kowacce rana da kalar episode da ake buɗe masu suna kallah, an rikita tunaninsu, idan zasu aikata laifi ma baka ga sai sun kawarwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login