Showing 162001 words to 165000 words out of 365093 words

Chapter 55 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5899

what reason zata fita? Is it your room? Su waye ku nema da zaku zo ku samemu a ɗakin mom ɗinmu ku ce ta fita? Is it your room?". A kule ta faɗa tana kallon matar, jinin IRON FIST basa ɗaukar rainin wayau, da farko ta ɗauka bakin arziki ne shigasa tai masu shiru, amma da ta ga basu san arziki ba shi ne ta gwada masu jinin IRON FIST take.

Budurwar ce ta amsa da. "Ke baki da tarbiya ko? Babban mata zaki faɗawa haka? Bata haifeki bane? Ko a gidanku babu manya ne?"..... Wani irin mugun harara Seraphina ta dallah mata kafin ta ce. "Keda gidanku suke da manyan ai naga basu baki tarbiyar adalci ba, kuma basu koya maki yadda ake magana ba". Ta faɗa tana zazzare mata ido, irin ta san bafa tsoronta take ji ba.

Kallon juna yarinyar da mamanta suka yi, sun gano Seraphina ba wacce ake takawa ta taku bane. Daidai lokacin Madam ta fito daga toilet, ta yi wanka har ta shirya a ciki dan da kayanta ta shiga, cikin arabian dress ta shirya.

Ganin suna musayar yawu yasa Madam ta yi saurin cewa. "Safiyya me haka? Daga zuwanki? Ke ba zaki canza hali bane wai?".

Wannan budurwar ce mai suna Suhana ta ce. "Mommy Ummina bata da laifi, wannan yarinyar ce ta zageta"...... "Ya isa haka Suhana, babyn daddy me yakefaruwa ne?"...... Sake hannun Aisha Seraph ta yi tare da miƙewa ta isa gaban Madam, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Mommy daddy yana fushi dani, ya tafi cikin fushi, kuma ina ta kiransa baya ɗauka, daga karshe ma ya katse kiran".

Riko shoulders ɗinta Madam ta yi. "Jeki room ɗinki ina zuwa sai ki faɗa mun me kika yi mashi ya yi fushin dan mu san daga in da zamu fara gyara, Aisha ku je da ita". Ta kai karshe tare da saketa. Da sauri ta juya ta nufi waje ba tare da ta sake kallon in da suke ba, Aisha ta rufa mata baya.

Suna fita Madam ta kalli Safiyya tare da cewa. "Ke baki da hankali ko? Sai kin ɓata mana dik wani shirinmu a kansu kin sa asirinmu ya tonu ko? Yanzu idan kuka fara nuna mata kiyayya kuka ja aka koremu ba shikenan komai ya lalace burinmu ba zai cika ba ko! Meyasa baku da tinani ne?".

A taƙaice Aunty Safiyya ta ce. "Kai Aunty Rohisha, ni fa yarinyar ne take bani haushi, na tsaneta daga kallon farko, na kasa ɓoye tsanar ne yasa na nuna halin"...... Nufosu Madam ta yi tana faɗin. "Gara ki koyi danne abu, dan wlh a kan wannan yarinyar babu irin matakin da ba zasu ɗauka ba, zai ma koremu a gidan nan, kada ki manta saboda ita ya ɗaukomu dan ta yi farinciki, dan haka dik abin da kake son cimmawa a hankali zaka bi da shi har ka cinma, bugu da ƙari ina son ki san cewa gidan nan gabaɗaya kewaye yake da camarori, cikin bedrooms ɗinmu ne kawai babu camera, amma bedroom na Seraphina akwai ɓoyayyen Camera, ranar da na shiga unexpected ina ɗaga kai jikin bulb na wuta ta ƙasa naga karamar camera, da alama basa son Seraphina tasan da camerar ne a wajen yasa ya ɓoye, amma sauran ɗakunan gidan babu, su parlo, kitchen har balcony dik akwai Camera, dan haka ku yi taƙa tsantsan, ku kuji shiga harkar Seraphina a gaban camera".

Kai suka jinjina alamar gansuwa, sannan Suhana ta ce. "Mom gaskiya CRYSTAL PALACE duniya ne kuma karshe ne, amma kuma gaskiya suna ji da yarinyar nan sosai, dubi irin daular da aka zuba mata, sannan Camera ta ko'ina dan kula da dik wani motsinta, tsaro sai ka ce zasu iya hana mala'ikan mutuwa ɗaukar ranta in ya zo?". Tana ɗaure fuska alamar hasada dan bata samu irin hakan ba ta faɗa.

Madam zata yi magana Aunty Safiyya ta rigata da cewa. "Gaskiya Aunty Rohi kin iya ɓadda kama, ni ba dan na ji muryanki bama ba zan gane ke bace, kin iya sanya fuskar boge wlh, kuma kowa ya ɗauka fuskanki ce fa". Ta kai karshen magana suna murmushin dake kama dana mugunta. Madam ta ce. "To ya zan yi, biyan buƙata yafi kwana masallaci, dole in yi basaja, dole in ɓadda kama in shiga jikin Seraphina dan cikar burina".

Shiru Aunty Safiyya ta yi tana tinanin makudan dalolin da ta karɓa kan ta fito masu da Seraphina daga CRYSTAL PALACE, a ranta ta fara tsara yadda zata shawo kan lamarin, ta samu ta ja Seraph wajen CP ɗin. Watau sun san a cikin CP dai kam basu isa shiga su ɗauketa ba, dole sai an fito da ita waje, lallai kuwa akwai gagarumin matsala, meyasa suke neman Seraphina? Su waye su? Madam Rohisha da ɓadda kama for what? Meyasa ta shiga rayuwar Seraph? Me manufar su Safiyya? Zasu yi nasara ko kuwa?. Uhm mu leƙa WS-HOSPITAL mu dawo.

---------------------------🔥

WS-HOSPITAL.

Bayan wani lokaci, zan yi skipping na labarin ne kaɗan saboda wani dalili da a gaba zaku gane!.

Gabaɗaya 3D haɗe suke a cikin section D suna duba lafiyar jariran dake cikin cikin uwar da suka kirkira da kansu, yaran sun fara wayo, dan wajen transparent ne kana iya ganin yadda suke rayuwa a ciki, suna motsawa a hankali tamkar yadda suke motsi a ciki uwa, kallonsu daga ta waje abin sha'awa da ɗaukar hankali, dikkansu kuma lafiyayyu ne sosai, dan in baku manta ba su Dr suna tace maniyin namiji su cire mara karfi sai su kara mashi alluran karfi dan ya zama daidai da wancan.

Bari in baku wani haske a nan yadda zaku fi fahimta, nasan kunsan halittar mace da namiji ba ɗaya ba, mace tana da rauni, namiji ya fi karfi, to wannan maniyi mai karfi shi ne na ɗah namiji, wanda bashi da karfi sosai kuma shi ne na ƴa mace, to in baku manta ba na faɗa maku su basa kyankyashe mata ai, maza kawai suke kyankyasa, shiyasa suke karawa maniyin karfi da allurai domin ya basu ɗah namiji ba mace ba, fatan kun gane?.

Idan kunga yadda jariran nan ke motsawa sai sun burgeku, a yanzu sun kai watanni bakwai, sun zama halittar mutun, a kallah zasu kai jarirai 150 a wajen, dikka kuma maza ne, babu mace ko ɗaya, sannan dikkansu farare ne tas da su, da alama sperm ɗin sai an zaɓa ake saya, ba kowanne ake saya ba.

Dr James ne ya ɗan tsaya a gaban na'urar kwalba guda, hannu ya ɗaura a saman oxygen control na jikin gwalbar, kashe wajen ya yi, hakan yasa iska ta daina shiga cikin kwalbar, komai ya tsaya jim. Idanunsa a kan wata ƴar madaidaiciyar touchscreen computer dake jikin kwalbar wanda suke amfani da shi dan duba bugawar zuciyar jaririn, yanayin da yake ciki da sauransu, so ya zuba ido a wajen yana kallon yadda computer ke harbawa da karfi-karfi, zuciyar yaron tana bugawa da karfin gaske ne, saboda rashin iskar shaƙar numfashinsa.

Slowly ya dawo da kallonsa a kan jaririn, nan ya ga yaron ya fara motsawa da karfi alamar yana neman iskan shaƙa, ya ware ƴan yatsunsa dake ƴan ƙanana sosai yana ƙoƙarin mikar da kafafu, jikinsa babu kwari bare ya yi wani yunkuri. Mai da kallonsa a kan computer Dr James ya yi, nan ya ga zuciyar yaron ta tsananta bugawa da karfin gaske.

Dawo da kallonsa a kan kwalbar ya yi, unexpected ya ga jaririn ya waro idanu waje, azaba ta yi azaba, babu iska babu shaƙar numfashi ai kunga babu azabar da ta kai wannan. Nisawa ya yi tare da dan lna oxygen control ɗin ya kunna mashi. Haba ai har sai da computer ta yi ƴar kara alamar bugawar zuciyar yaron ta dawo, slowly jaririn ya maida ƴan yatsunsa ya dunkule su kafin ya ɗan juya tamkar yadda suke juyawa a cikin uwa.

Yana juyawa cibiyarsa dake manne da uwa ne ya ɗan naɗe mashi wuya. A daidai lokacin su Dr Kamal suka iso wajen, in a low way Dr James ya ce. "Kamar wannan project ɗin ya fi dik waɗan da muka yi a baya kyau! Karfi da kuma lafiya!".

"Meyasa ka ce baman?". Dr Mark ya tambaya. "Saboda yaran suna da karfi da lafiya, a ƙaida jariri baya iya rayuwa babu iskan oxygen na second 30, amma yaron nan ya kai 1 minute babu iska, kuma da na dawo da iskar bai shiga wani yanayi ba, yakamata nan da 30 days mu yi test na brain and heart ɗinsu dan tabbatar da ingancinsu".

Dr Kamal ne ya ce. "Gaskiya yaran suna da lafiya sosai, nima na shaida duba da yadda suke motsawa da karfi, bamu taɓa kyankyasan yara masu karfi da lafiyarsu ba"....... Dr Mark ne ya ce. "To ko dai akwai jinin FIVE LIONS a jikinsu ne?"........ Siririn tsaki Dr James ya ja tare da wucewa gaba bai sake magana ba, Dr Kamal ne ya ce. "Ga dikkan alamu har yanzu FIVE LION suna ranka Mark". Ya faɗa tare da bin bayan Dr James.

Bayansu Mark ya bi yana faɗin. "Dole FIVE LIONS su tsaya a raina, kuma nasan suna ranku, dan ba'a taɓa shegun jami'an da suka kusantomu irinsu ba, jami'an da suka shirya mission a kanmu, jami'an da basa tsoron mutuwa, jami'an da basu ɗauki ransu a bakin komai ba".

"Hmmm". Kawai Dr Kamal ya ce, na ciki na ciki, su kaɗai suka san me yake a cikin ransu. Kai tsaye wani ɗaki dake a cikin section D ɗin suka nufa. Ɗaki ne wanda kun sani, cike yake da glasses dayawa, sannan kamar chemical lap haka wajen yake, dik ta in da ka juya manyan chemical ne masu mugun haɗarin gaske a wajen.

Sister Zinta and sister Maya suna sanye da chemical care gown, hand gloves a hannu, socks a ƙafa, eyes care a idanu, sun dukufa gaban computers sai aiki tuƙuru suke yi. 3D na shigowa suka miƙe tsaye dan girmamawa a garesu, yanzu almost 4 months kenan suna wannan aikin, tin ranar da suka sanya hannu, barci wannan rabi da rabi suke yi.

Abin da zai baku mamaki kuma basu taɓa sanin aikin me suke yi ba, kawai suna tsamo wasu chemicals ɗin ne su sanya a wasu, amma kowanne sai sun tacesa sun ciri mai karfin cikinsa, idan kun fahimta su Maya ilimin chemical kawai suke da shi.

Duba aikin nasu 3D suka yi, komai na tafiya yadda yakamata, jinjina masu Dr Kamal ya yi, da alama ya fi su Dr James sauƙin kai, fitowa suka yi daga cikin room ɗin izuwa side na dabbobi watau section B. Yau wajen a cike yake da kukan dabbobi kala-kala, ga waɗan nan jiga-jigan guards ɗin suna ta aikin kai komo.

Sanya gabaɗaya guards ɗin suke da kayan kariya a jikinsu, da alama aiki tuƙuru suke yi. Gaban wasu manyan guards biyu 3D suka tsaya, matasan nan suna rike da zabga-zabgan macizai guda biyu, sun mace kan macizan jikin wani kwalba, sun ɗaura hakwaran macizan a bakin kwalbar, sannan sun matse tsakiya wajen cikin macizan, macizan sai fito da wani green ruwa daga bakinsu suke yi yana zuba a cikin kwalbar.

Wannan green ruwa shi ake kira da neurotoxic, hemotoxin, sinadarai ne masu matuƙar haɗari da illah, dan suna hana jini gudana a jiki, and yana lalata jijiyoyin jini, a hankali ya lalata tsokoki jikin mutum, to wannan sinadaran suke matsowa daga jikin macizan.

Jinjina kai 3D suka yi alamar aiki na tafiya da kyau, sai suka matsa kusa da wasu guards dake mace sinadaran corpion mai suna chlorotoxin, watau wani sinadari ne dake shafar jijiyoyi, yana haddasa raunin jijiya daga nan shanyewar jiki, shi ma sinadarin da yanayin yadda suke tatsansa a jikin dabobbin, kowacce dabba tana da sinadari mai cutarwa kuma tana da mai amfani, dan haka kowanne da yanayin yadda ake fitar da shi, kunga maciji tana da sinadarin da ake iya yin maganin ciwon zuciyaa da shi, kunga wannan ba mai cutarwa bane, amma su a nan mai cutarwa suke fitarwa.

A nan ma sun tabbatar komai ma tafiya daidai sai suka wuce gaba. Nan ma wasu guards ne ke ta faman matse sinadarin dart frog mai suna batrachotoxin, sinadari ne da idan ya shiga jikin mutum yana toshe sodium channels, yana haddasa bugun zuciya ta tsaya cak, amma a hankali yake aiki na likitoci guda ba...... Nan ma duba aikin na tafiya daidai.

Gaba suka ƙara wajen masu tatsan dafin pufferfish mai suna tetrodotoxin, watau sinadari ne da idan ya shiga jikin mutim yana toshe jijiyoyin jini, yana sanya numfashi ta dinga ɗaukewa tana sama-sama kamar mutum zai mutu. A nan ma komai na tafiya daidai.

Wucewa gaba suka yi wajen guards dake tatso tsinadarin cone snail mai suna conotoxins, shi wannan sinadarin idan ya shiga jiki yana hana jijiyoyi aiki, yana haddasa shanyewar gaɓoɓi ya baka sassaiɓar mutuwa ba mutuwa da gaggawa ba, sai ya gana maka azaba a jiki.

Oh ni Princess Teema na shiga uku, ko me suke yi da wannan sinadaran? A tinaninku me suke yi da shi?. Kai idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba, ALLAH ka kawo mana agaji, ka dubemu da idanun rahama ka dafa mana, ALLAH ka jiƙanmu ka jiɓancin al'amurranmu.

Sai da suka tabbatar komai na tafiya daidai kafin su fito daga wannan ɓangare, kai tsaye suka koma wannan ɗaki na meeting ɗin nasu da suke zama. Dr Mark ya ɗauko glass cup da wani tangamemem drink ya nufi saman sofa. Dikkansu zama suka yi a kan sofas ɗinsu, Dr Mark ya tsiyaya drink ɗinsa a cup, dan shi karatu ta fi shigansa idan yana yi yana sipping drink mai sanyi, kuma ɗan banza kullum Americano yake sha.

Dr James ne ya miƙe tsaye tare da kunna light na tangamemen touchscreen computer dake gabansu sofas ɗin nasu, ya ɗauki wani sanda siriri dake wajen ya rike da hannu dan ya ji daɗin bayani. Hannu ya ɗaura kan screen na computer, pressing ɗinta ya shiga yi cikin kwarewa for like 5 mins, sannan ya ɗauke hannu.

Take wani rubutu ya bayyana a kan screen ɗin, P-C shi ne sunan project ɗin, idan baku manta ba project da suke yi da su Maya kenan, sai yau zasu mana bayanin wani irin project ne.

NEXAPOX-31 shi ne ainahin sunan da suka sanyawa wannan aiki, a jikin folder na aikin ma sunan dake rubuce kenan. Cikin folder ya shiga kai tsaye. Take wani dogon jawabi ya bayyana. Kara natsuwa su Dr Kamal suka yi dan sauraran wannan aiki, gagarumin aiki ne da sun jima suna yinsa, ba tin yau bane, ya haura shekaru 5 suna shiryasa, yanzu ne da aka hura masu wuta daga can WORLD SYSTEM shi ne suke son kaddamar da aikin cikin gaggawa su fito da shi, dakon jiransu ake kamar hauka, hakan zai tabbatar maku makudan biliyoyin daloli ne a kan wannan project ɗin.

A natse ya ce. "Menene NEXAPOX-31?". Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan su Dr Mark da suka kara natsuwa, one thing, dikkansu 3D ɗin nan Dr James kamar malaminsu yake, ya fisu kwarewa a kan komai, bugu da kari shi yake yin dik wasu manyan project irin NEXAPOX-31 da sauransu, sai ya kammala shirya manyan abubuwa game da project ɗin, sannan yake zama kamar dai yanda suka zauna yanzu ya zayyana masu irin project ɗin, amma a tare suke yin komai, sai dai ba lallai su san kai tsaye ga abin da suke shiryawa ba, sai an yi tafiya mai nisa yake zama yai masu bayani, daga nan su karisa a tare! Fatan kun fahimceni?.

"NEXAPOX-31 wata..........

https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-24-by-princess-teema

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.





STEP 1🔥


2025-12-1.🔥



اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E_____________ 24


"NEXAPOX-31 wata cuta ce mai ƙwayoyin virus, tin da nike project a kan cututtuka ban taɓa yin makamancin wannan ba, ya sha bamban da dik wata cuta da ya wanzu a baya, wannan cuta na ciro kwayoyin cuta da dama daga jikin dabbobi masu haɗari kamar su bats, rodents, and reptiles da sauran dabbobi, na jima ina shirya wannan project ɗin"...... Ya ɗan nisa kafin ya cigaba da cewa.

"Na faɗa maku ta zarce cututtukan da suka wanzu a baya irin COVID-19, HIV, Ebola da dai sauran manyan cututtuka masu haɗari da suka gigita duniya, to wannan ya damesu ya shanye, domin kuwa shi ne cuta na farko da yake ƙunshe da DNA da RNA a lokaci guda, wadda ke ba ta damar canzawa da wuri da tserewa immune system watau garkuwar jikin ƴan adam". Ya sake ɗan dakatawa ya nisa kafin ya cigaba da cewa.

"Wannan cuta zata yi balain girgiza duniy fiye da yadda su COVID-19 suka girgiza duniya a baya, chemicals da na ruɓar tsawon shekaru uku a wannan cuta ba karamin abu bane, dole wannan cuta ta gigita duniya, hankula zasu tashi, asibitoti zasu cika, rayuka zasu salwanta, tattalin arzikin duniya zata girgiza, manyan ƙasashen da cutar zata fi shafa zasu shiga wahala, tattalin arzikinsu zai ruguje, za'a rufe ƙasashen ba shiga ba fita, kuɗi ba zasu shiga ba kuma ba zasu fita ba, zasu cinye abin da suka tara, wahalar zata zarce yadda ake zato".

Ya dakata yana mai da numfashi. Dr Mark ne ya ce. "Good job, gaskiya wannan cuta da alama da zafinta take tafe, amma a wannan karon ta yaya (WS) World system suk shirya baza cutar ta isa ga in da ake so?".

Shiru Dr James ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login