Showing 15001 words to 18000 words out of 365093 words

Chapter 6 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

6199

aikin sojan ba wahala, shi ne sai tsoratasu ake yi, ashe iya wannan ɗan tafiya ne, ai wannan sai su kwana suna yi.

Haka a tinanin Noor ma shikenan zasu koma ɗaki su yi barci daga wannan ƴar tafiya, sai kuma me?
Suna kai daidai gaɓar mil biyu wata hanya ta rabe a wannan waje, nan fa Captain dake biye da su amma ta gefe ba'a cikin layinsu ba ya umarcesu da su sauka daga kan wannan hanya su bi ɗayar.

Nan da Noor ya gane lallai already wannan hanya an shiryata ne ma dan horar da su, shi fa wlh bai shirya aikin soja ba, kawai daddynsa ya ja mashi balai yana zaune cikin sisters ɗinsa gwanin burgewa, da yanzu ko shirin tashi barci bai yi ba. A daidai wannan lokacin ne kuma su Zaynash suka lura da shi, da sauri suka isa in da yake, Vash ne ya fara cewa. "Noor yana ga jikinka dik ruwa? Baka canza kaya ba! Kana son mura ta kamaka ne?".

Zaysh (Zaynash) ne ya ce. "Meyasa baka cire wannan kaya ba? Zaka yi ciwo!". Cike da kulawa game da tausayawa haɗe da gaskiyarsu suka faɗa. Amma Noor sai ya dallah masu harara, a fusace ya ce. "Kada ku sake yi mun magana, mugaye kawai, ai kun san me aka mun da zaku wani zo ku nuna kuna sona!".

Da sauri Zaysh ya ce. "Wlh bamu san me aka yi maka ba". Vash ya amsa da. "Noor muna sonka mana"...... A kufule ya amsa da. "Da kuna sona da baku bari waɗan can azzaluman sun azabtar dani ba, dan haka karku sake yi mun magana". Ya kai karshe tare da wucewa. Captain dake kallonsu ya so yi masu magana a kan cewa ba'a tsayawa magana da juna haka, amma kasancewar ranarsu ta farko ce sai ya kyalesu.

Jiki ba kwari suka bi bayansa, dan wlh ya basu tausayi tin ma basu san me matsalarsa ba.

Tafiya mai ɗan nisa suka yi a wannan hanya da suka sauka kafin su isa wani tapkeken fili mai girman gaske wanda ya fi hall ɗinsu sau goma, fili ne mai cike da duwatsu, tsaunuka da shinge, daga karshen filin wani dogon bene ne mai step-step sun kai 100 zuwa 150, tsawon staricase ɗin nan ya yi mugun basu mamaki, kuma ba ɗaki bane, just steps ɗin ne kawai aka yi har sama, kuma saman ma babu komai, dan horon gwarin gwiwa kawai aka yi wanna bene.

A bakin wannan fili Captain ya umarcesu da su dakata, dik tsayawa suka yi suna mai da nunfashi a hankali-hankali. Sai dai Captain bai bari sun huta ba ya yi cauting from one to 3 ya ce su je da gudun gaske su isa wancan steps ɗin.

Da yake har yanzu da ɗan sauran karfinsu sai suka kwasa da gudu sosai, Noor shi ne na karshen zuwa wannan waje, dan tsabar ragwanta da barci da yake kansa, ga ruwan da ya sha, while NIRASH and ZAYSH sun rigasu isa wajen.
Shi kuma Captain cikin zafa ya ɗan taka har ya isa wajen, hakan ya basu damar ɗan hutawa kafin ya iso. Dan yana zuwa ya umarcesu da su tattakawa su haura wannan steps har sama a cikin mintuna ƙasa da biyar su kuma sauƙo.

Ai zazzaro idanu Noor ya yi, cike da damuwa ya matsa kusa da VASH tare da cewa. "Bro I'm tied wlh, ba zan iya ba, hawa sama fa, no, my legs done tied over". Bawan ALLAH fushinsa na ɗan lokaci ne, har ya manta ya ce kada su sake yi mashi magana ma.

Ganin ya nuna manta da kalamansa na ɗazun ne yasa suma suka manta, Vash ya ce mashi. "Noor this is just the beginning for our training, saboda yau ranarmu ta farko na karɓar horone ma yasa kake ga ake mana ƙananan abubuwa, i promised you in the next one week dik wannan tafiya for two mil zai canza zuwa 10 mil to up, dik horo zai ninka kansa, kawai abin da zance shi ne, kada ka kunyata daddynka, kaga ni na shiga soja ne for my dad, kafin ya mutu kullum maganansa ɗanya in zama soja, shiyasa granny ɗina ya horar da zuciyata da kaunar aikin, i will do all my best dan ganin na cika burin daddyna, i wish yana raye a lokacin da zai ganni da kaki, amma ba komai".

Tin da ya fara magana idanun Noor suka cika da kwallah. "Sorry for the rashin dad bro". Jinjina kai kawai ya yi kafin ya rike hannun Noor da kyau..... "Be strong, zaka iya my brother".

Noor da yasan ba zai iya jurewa bane ya ce. "I will try, but not sure zan iya". Jansa ya yi suka fara tattaka steps ɗin da sauri yana faɗin. "By the grace of God zamu fito da good result mai kyau and a rukuni guda zamu fito, zamu yi aiki a tare".

"I wish that". Noor ya faɗa tare da zaro idanunsa waje, dan yaga NIRASH har ya hau yana saukowa su yanzu suka yi rabi, mamaki ne ya kamasu daga shi har VASH, yanzu ya kara tabbatarwa da gaske NIRASH yake wannan aiki ba wasa ba.
Haka suka sha faman hayewa sama da kyar suka sauko, suna saukowa Noor ya durkushe kasa a waje yana wani irin haki da ɗan karfi-karfi.

Hutun five mins Captain dake tsaye yana kallonsu ya basu kafin ya sake umartansu da su yi gudu sosai zuwa wajen waɗan nan duwatsu da tsaunuka, ba musu suka dallah da gudu suka nufi wajen, amma fa a wannan karon ma Noor ne na karshen zuwa, dan shi wlh bai huta bama Captain ya sake tashinsu, ga shi idan baka tashi ba wasu zaratan sojojin huɗu dake binku a baya da manyan bulalu su baka a jikinka.

Da suka isa sai da suka ɗan jira Captain, hakan ya kara basu damar hutawa kaɗan.

Yana zuwa ya umarcesu da su fara tsallaka ƙananan tsaunika da duwatsun nan. Nan fa Noor ya ce shi ba zai iya bafa, dan kafafunsa zafi suke yi mashi, abinku da renon madara and ice cream.

Hannunsa VASH ya ja yana faɗin. "Wlh a wannan gida babu tausayi babu tausayawa, shiyasa idan soja yakama mutum babu imani yake jibgar bawa, a wannan horo dakake ganin mun fara ake cire masu dik wata tausayi da imani, saboda bakin azaban da suke sha, in har baka tashi ba, wlh Captain na iya sanya wannan shegiyar takalmar tasa ya tattakaka, ko kaɗan ba zasu tausaya maka ba, so is better for you to stand up".

Tabbas Noor yasan gaskiya VASH yake faɗa mashi, saboda yasan dokokin gidan soja, yakaranta komai ya kuma cika komai, dan haka babu uwa, babu uba, babu ƴan uwa, wlh ya yi gardama mugun azaba da bakin duka zai ci, kuma a banza ya daku in an dakesa, babu mai tausaya mashi daga cikin manyan sojojin nan, su gama dukansa su haɗa shi da horo mai azaba, a haka zai goge, ya fi mashi sauƙi ya miƙe ya bi umarni kawai.

Idanunsa sun cicciko da kwallah haka ya miƙe ya nufi waɗan nan duwatsu ƙanana dake gefen manya-manyan, da kyar Noor yake iya tsallakasu. A wannan waje good 20 mins Captain ya basu suka yi wannan aiki kafin ya wuce da su wajen wasu igiyoyi dake ɗaɗɗaure, kasansu ruwan taɓone mai ɗan zurfi.

Cikin kakkausar murya ya ce. "Zaku rarrafa cikin ruwan nan ne a kasa da minti biyu ku fita ta gefen can, kada wanda ya bari kansa ya taɓa igoyiyin nan, idan kanka ya taɓasu tabbas zaka sako ne daga farko, kuma kada wanda ya bari kansa ya taɓa ruwan!!". TOH FAH!

Ai dukkansu bin ruwan da kallo suka yi, yana da tsawon taku 30, sannan suka ga igiyoyin da aka ce kada kansu ya taɓa, lallai aiki ne babba. UHM BASU SAN AIKI BABBA MA YANA GABA BA, AI YANZU MATAKIN PRIMARY SUKE, SAI GABA.

Wasu kuma takaici suke yi na fararen t-shirt dake jikinsu, yanzu shikenan rigarsu ya tashi a aiki kenan? Ga shi basu ga alamar fuska a wajen Captain ba bare su ce ya yi hakuri ya bari sai gobe zasu shiga kada kayansu ya ɓaci, gobe sai su sako bakaken kaya, ba hali, dole suka ɗaura ɗamara, sun fi su 100 a wajen, amma mutane uku ne suka fara faɗawa cikin ruwan kai tsaye, ciki harda NIRASH wanda shi ne farkon faɗawa bayan ya ajiye littafin da yake karantawa ɗazun da watch dake ɗaure a hannunsa a gefe kusa da Captain, ya faɗa cikin ruwa ya fara rarrrafawa da gwiwowinsa.

Zaysh ya rufa mashi baya, sai wani kyakkyawan chocolate guy dake tsaye a kusa da su shi ma ya faɗa.

Shi kansa VASH a wannan karon tsayawa ya yi yana kallon Noor cike da tashin hankali, dan wlh bai kawo a ransa zasu shiga ruwa ba, ga balain sanyi da ake yi.

Muryar Captain ce ta karaɗe kunnuwansu da cewa. "Mintuna biyu gareku, dik wanda minti biyu ta gota bai fito ba sai ya sake farowa, zai yi ta farowa har sai ya fito a mintuna biyu ko ƙasa da hakan"...... Ai tin kafin ya rufe baki mutasa sun kai 30 suka faffaɗa, still dai Noor and VASH suna tsaye, saboda sun gaji.

Ɗaya bayan ɗaya matasan nan kaf suka faɗa saura su biyu, suka ci minti ɗaya a tsaye a wajen, sai da sukaga babu wani sarki sai ALLAH sannan suka faɗa cikin ruwan suna aikin haɗe rai. Sai dai ko tsakiya basu kai ba mintuna biyu suka cika, Captain ya yi wa waɗan da suka fito kafin mintuna biyu alama da su ja baya, su sun tsira.

Waɗan da basu fito ba har mintuna biyu ya cika suna fitowa aka ce su sake farawa, tamkar zasu yi kuka haka suka sake komawa, a karo na biyu ma Noor and VASH basu fito a mintina biyun ba, kun ga rarrafe ba kamar tafiya a ƙafa bane.
Hakan yasa aka sake mayar da su, da dai VASH yaga babu mai iya kwatarsa a wannan gida, Mama no dey baba no dey fa sai ya zage a karo na uku ya fito a ƙasa da mintina biyu. Shi kuma Noor tin yana da sauran karfi har ya gaza, amma bai iya fita a kasa da mintuna biyu ba.

A tinaninsa taimaka mashi za'ayi idan ya gaza, ina ai sai ya ga akasin haka, dan a horon soja ba'a taimako, shiyasa zaku ga suna tashi a marasa tausayi, to ba'a gwada masu tausayi da imani ba a yayin horo, ubansu suke ci har zuƙatansu su bushe ba kaɗan ba.

Ai Noor bai tashi sanin a GIDAN SOJA GIDAN WUTA yake ba sai da ya ji saukar wannan uwar kwandorom ɗin takalman Captain a tsakiyar bayansa, ya takashi da karfi a cikin ruwan yana daka mashi tsawan ya yi sauri, dan kowa ya fita saura shi kaɗai, yana ɓata masu lokaci.
Dole tasa Noor ya cije, yana zafafan hawaye ya fara iyo a cikin ruwan nan, da kyar da suɗin goshi, ya maimaita sama da sau biyar, sannan ya iya fitowa a mintuna biyu daidai.

Da ya fito a tinaninsa barinsa zasu yi ya huta, sai fa ya ga akasin haka, domin kuwa sake zangon tafiya suka fara yi dan komawa ainahin cikin Barrack in da suka fito kenan, a lokacin karfe 7 daidai ta buga, sun ɗauki awa ɗaya da rabi a wannan waje kenan suna horo.

Da kyar Noor ya iya kai labari, ya ja kafafunsa suka karisa wajen, suna zuwa suka tsaitsaya a wannan katan fili da suka tsaya bayan fitowarsu daga ɗakunansu, a nan ne Captain ya ce. "Mintuna 30 gareku na yin wanka da canza kaya, 7:30 daidai zaku fara breakfast, zuwa 8 dole kun gama, 30 mins na ɗan hutawa dan kuna sabbin zuwa, 8:30 zaku fara gwada horon hannun zuwa 11 zaku shiga class! Lokacinku ya fara daga yanzu!". With harsh voice ya faɗa.

Ai da gudu suka fara watsewa, ji kake dam! Dam! Dam! Suna taka kasa, dik suka watse ya rage Noor da baya iya tafiya da kafafunsa sosai. Da gudu VASH ya dawo baya ya zo ya taimaka mashi suka koma room ɗinsu.

Da yake suna girmama lokacin, dayawansu cikin kasa da mintuna 15 suka kammala shiri except Noor da suna shiga ɗaki ma bajewa ya yi a kasa yana jan doguwar numfashi game da saukewa a hankali-hankali, har su VASH suka gama wanka, dik suka shirya cikin wandunan jeans and t-shirts masu balain kyau shi yana zaune.

Vash ne ya ce. "Noor 30 mins garemu fa, kasan dokoki da tsare-tsaren gidan nan, ba'a kauce lokaci!".... Yana kwaɓe fuska ya ce. "Ni babu in da zan sake zuwa!"........ "Noor baka son lafiyar jikinka na lura, gara maka fa ka tashi, dan wlh in muka gama breakfast ko baka yi ba lokacin horo dole Captain ya fito da kai da duka".

Noor zai sake yin magana, Leo ya riga shi da cewa. "Make sure you clean this floor before I come back". Maganansa ta farko a garesu keman. A natse ya yi magana, yana da murya mai sanyi da kaifi ga balain daɗin saurara, yana gama faɗa bai jira amsarsu ba, infact bai ɗaga ido ya kalli in da suke ba ya sa kai ya wuce da sauri abinsa, dan ya kammala shirinsa cikin wasu zafafan kayan dake nuna shi ɗan royal family ne, kansa sanye da army p-cap........ Yana yawan sanya p-cap ne saboda baya son kallo, in dai zai bar gashin kansa a buɗe sai an dinga kallonsa ko ina ya juya, shiyasa yake yawan rufewa, bugu da kari p-cap ɗin na ɗan hana ganin face ɗinsa sosai, ya huta da idanun jama'a a kansa, ga kuma kitso a kansa da ya yi, ai dole ayi ta kallonsa, kyan gashi kyan kitso da kyan halitta. Say Masha ALLAH.

Bayansa suka bi da kallo. ZAYSH ne ya ce. "This guy acting like he's our parents, ji yadda yake bamu umarni". ......... VASH ne ya ce. "I don't know why I like his character".......... "Same to me bro, and I like his sharp voice, ji yadda ya yi magana yanzu fa, like wow". Noor ya faɗa yana cigaba da kwaɓe fuska.

"Yeah, yana da tsari mai kyau for his life, but why baya mana magana bayan we're together in the same room?". Cewar ZAYSH da abin ke bawa haushi..... "That's why a like his style, he don't want to talk, and hakan girmama kai ne, amma dai yakamata ace yana yi mana magana like friends tinda we're the same now, and kuma ba wani finmu shekaru ya yi ba fa". Cewar VASH.

"We lost 5 mins again, ba lokacin wasa bane yanzu, let's go guys". Zaysh ne ya faɗa. Da sauri Vash ya ce. "Noor I don't want to see you in this situation, please tashi ka yi wanka, kaga dattin jikinka ya ɓata mana floor har wannan mai fuska irin na gangsters ɗin yana baka command na ka gyara masa waje ko?".

"Ai ba zan gyara ba, da wani nuna isa da iyayin nan nasa". Noor ya faɗa yana ɗaure fuska kafin ya daure ya miƙe, da kyar yana tangaɗi ya afka cikin toilet.

"Bari in taimaka mashi in gyara wajen". Cewar Vash yaro mai saukin kai, kuma iyayensa manyan kai ne, amma yana da sauki sosai. Da sauri Zaysh ya ce. "Don't do that, ku bar wajen haka in ga uban me wancan ɗan rainin hankalin zai yi idan ya dawo, ba ya wani ce mu gyara mashi waje ba? To ku bari mu ga me zai iya".

Ɗan zazzaro idanu Vash ya yi. "But not for him kawai ai, cleaning the place is for our healthy all"........ "I know that, but for now ka bari mu ga gudun ruwan shi, me zai iya yi mana, kasan fa idan bamu gwada mashi muma guraye bane ba zamu zauna lafiya da shi ba, yana wani ɗaga mana kai like ya fimu ne, idan ya yi wasa ma muka gama horon nan result ya fito a karkashinmu zai yi aiki".

Noor da ya fito yanzu ɗaure da towel ne ya jingina da jikin bangon wajen toilet ɗin tare da cewa. "Da kuwa ya gane kuransa, ni dan in bashi wahala har takalmata zai rinƙa wankewa".

"Zaysh, Noor kuna da matsala, idan aka biye ta ku zamu ɓata breakfast time ɗinmu a nan". Vash ya faɗa....... Karisowa ciki Noor ya yi, da sauri ya hau shiryawa yana tinanin yadda zai rinƙa gujewa horon nan. Waje Zaynash ya nufa yana jin haushin Leo a ransa, saboda yadda yake nuna masu shariya.

Hall na cin abincinsu ya nufa, yadda tsarin hall ɗin yake wajen cin abinci ne da kowani table yake ɗauƙe da four chairs, kuma kowani table da number ɗakin mutane a jiki, kamar su Leo da ɗakinsu yake room number 1, to haka table ɗinsu ma yake da number 1 a jiki, su huɗu ne a ɗakin kazalika chairs huɗu ne a wajen.

Zaune Zaynash ya isko Leo yana cin abincinsa cikin natsuwa da tsari yana kuma ɗan naɗe yatsun hannunsa kamar yana tasbihi, ya duƙar da kai ƙasa, dikkan sauran matasan ma suna zazzaune suna cin nasu abincin cikin tsari da natsuwa. Saman chair Zaynash ya zauna tare da jawo plate ɗinsa dake rufe ya buɗe.Wake ne da ƙwai dafaffa domin ƙarfafa jikinsu da ƙara masu kuzari, sai black tea mara madara, dan madara tana sanya kasala, su kuma ba'a buƙatarsu da kasala, ga bread a gefe, sannan ga lemu guda ɗaya domin kuzari da rage gajiya. Waken Zaysh ya fara ci yana ɗan satar kallon yadda Leo yake cin abincinsa tamkar baya son motsa baki, shi da yake namiji ma sai da abin ta burgesa bare mace.

A lokacin cin abincinsu fa ba a yarda a yi magana ba. Kowa yana ci da gaggawa, saboda su gama cikin 30 zuwa kasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login