Showing 66001 words to 69000 words out of 365093 words

Chapter 23 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5902

dan ma dai yana sanye da winter jacket mai ɗan tsawo zuwa gwiwa da ta rufe kakkarfa kuma kyakkyawan surar jikinsa, amma dik da haka an kafesa da idanu. A gaban Leo ya tsaya a dake tare da karɓar star ɗin ya sanya mashi sannan suka rungumi juna. Dik wanda ɗan uwansa ya sanyawa star ɗin nan sai an buga bindiga sama alamar girmamawa!.

Kama hannun Leo ya yi suka koma gefe dan ganawa, saboda an gama dik wasu important abin da za'a ayi saura ci da sha, suna da damar ganawa da ƴan uwansu.

To mu koma baya kaɗan, tin da su Leo suka shigo hall ɗin nan su V suka rikice. Tana sauke idanunta a kan Noor bata san time da ta miƙe tana faɗa masu su tayata ganin shin da gaske na jikin robar mansu take gani ne ko bashi bane. Arya ce ta jata ta zaunar da ita dan kada ta tara masu jama'a, sannan ta ce shi ne mana, amma ta natsu taga jama'a a nan ai. Da kyar ta natsu, ba ita kaɗai ba har su Angelina da kyar suka natsu saboda gigicewa da suka yi a ganin Noor and Leo, ita kanta Arya ta gigice da ganin Leo, ya kara kwarjini da zarra, da ta kalli face ɗinsa sai da ta sha jinin jikinta, sai da gabanta ya faɗi.

Ita kuwa V matsawa jikin Angelina ta yi tana ta faman santin kyan Noor, wai a hoto ma ashe an rage mashi kyau, tuni ta manta da tana son Leo, to taga first love, wanda ta fara so a rayuwanta tin buta wuci 8 years ba, kuma kun san so ba ruwansa da kyau, dik da Leo ya fi Noor kyau ita dai Noor ne ya fara shiga ranta, dama saboda tinanin ba zata samu ganinsa bane yasa ta bada kofar Leo ya shiga zuciyanta.

Angelina ɗin ma sai tayata santin kyansa take yi, dik sun rikice, Arya dai tana zaune a natse, tamkar babu abin dake damunta, daga karshe ma ta ɗan yi ƙasa da kai ta daina kallon Leo saboda tsananin sara mata da kan nata yake yi idan tana kallonsa.

Bayan an gama karramasu sun koma gefe da ƴan uwansu, manyan baki sun fara cin abinci ne V ta ce. "Angelie ni zan je in gana da love ɗina, ALLAH zan je in yi mashi magana". Riketa Angelie ta yi tare da cewa. "Baki da hankali ko? Bari daddy ya kamaki zaki sani ne, ai kin san ya hana boys ɗinsa su kulamu, kuma muma ya hanamu kulasu ko?".

Tana turo baki ta ce. "Wannan ba boy ɗin daddy bane, baki ji me aka ce bane? Kwararrun jami'an ESS ne, emagemcy secret service. Dan haka shi ba boy ɗin dad bane". ........ "Amma ai kin san kowani kaki yana karkashin GAT ne ko?!". A cewar Arya dake jinsu, ta yi maganar a natse sosai cikin dakewa ga class.

Marairace murya ta yi tamkar zata yi kuka, a shagwaɓe ta ce. "Please bloody, ku barni in je in gansa, in ba haka ba zan yi ciwo, ko kuna son in kamu da ciwo ne?"........ Da sauri suka girgiza kai, har suna haɗa baki wajen cewa a'a basu son ta kamu da ciwo. "To please ku kare mun wajen daddy bari in je in gansa in dawo, two mins kawai".

Da yake suna bala'in son juna sai suka aminta, har da cewa zasu ce da daddy ta je toilet ne, kuma ta yi sauri ya dawo, da okey ta amsa tare da lallaɓawa ta zame jiki ta fice. A lokacin Noor yana tare da Auntys ɗinsa a can waje gefe da hall ɗin, daddynsa kuma ya nemi zama da GAT dan ya ga yadda za'ayi a cire Noor a wannan mission kawai ya koma da ɗansa gida, gara mashi ya je ya yi aiki cikin Us army kusa da gida!.

Tin daga nesa ta hangosa kewaye da mata, haba take ta ji ranta ya ɓaci tin ma bata san me alaƙarsu ba, bai ma san da ita ba wai tana kishinsa, har da yin sauri ta kariso wajen. Excuse ta yi mashi a natse. Da sauri su Luna suka kai kallonsu a kanta, shi kuwa Noor yana rike da Auntynsa da yake bi wajen haihuwa watau Aunty Lisa, ya rike hannunta sai hira suke yi, ya yi kewansu sosai, so bai ɗago ya kalli V ba!.

Aunty Lisa ta fi kowa saukin kai, da sauri ta ce. "Like wow, fine girl, pleasure look at this beautiful lady, wajenka ta zo ko?". ...... Sai a lokacin ya ɗago ido, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai tare da girgizawa Aunty Lisa kai game da cewa. "No Aunty, I don't even know her, this is my first time seeing her".

Da sauri Lisa ta saki hannunsa tare da riko hannun V, tana yaba kyanta musamman ash hair ɗinta dake ta faman kyalli, ga wannan na gaban goshi da ya kara fito da kyanta, cike da kulawa ta ce. "Fine girl lafiya?"...... Mamaki ne ya kama Noor ganin har da sake hannunsa ta kama wata, sai ya ja baya tare da komawa kusa da Aunty Luna yana hararar Lisa ta kasan ido, irin like zamu haɗu dake ne, amma bai to magana ba.

Ta gansa sarai, amma ta share kamar bata gani ba, saboda ita dai V ta tafi da imaninta..... Jin ya kira su da Aunty yasa V ta ce. "Good evening aunty"...... "Evening my love, kema a nan barrack ɗin kike? Wajen pleasure ɗinmu kika zo ko? Ya sanki ko?". Cikin rawan jiki take tambayarta, dan tana ganin kamar Noor ya santa kawai kunyansu yasa ya ce bai santa ba.
V da tsiya sai ta ce. "Yeah Aunty, he knows me, kuma shi ne ya ce in zo in gaisa da Aunty's ɗinsa, amma kada na nuna kaman nasan shi, wai yana kunyanku ne"......... Ai a miliyan Noor ya juyo da kallonsa a kanta, ɗan turo baki ta yi, bata ma san time da ta ɗan hararesa ba, sai da ta ga ya waro idanunsa sosai a kanta, da sauri ta yi ƙasa da nata idon kirjinta na bugawa da kari, gabaɗaya kwarjininsa ya rikitata.

Wani irin fara'a ne ya bayyana a kan fuskokin Aunty's ɗin nasa gabaɗaya, dan su suna tsananin son abin da yake so, a tinaninsu yana son V tin da ya ce ta zo ta gaisa da su......... Cike da so da kauna suka jawota jikinsu, Aunty babba watau Aunty Luna ce ta ce. "Pleasure ɓoye mana ita da kake son yi ko?". ...Lisa ta amsa da. "Baka son mu ganta ko?"...... Lusi ta ce. "Gata makurar haɗuwa, zo mu je wajen daddy mu kaita ya ganta shi ma"......... Luna ta sake cewa. "Pleasure gaskiya na yi matuƙar farinciki, gata natsastsiya, a ina ka samota?"......... "Dik ba wannan ba, mu kaita wajen daddy kafin mu dawo mu ji daga in da ya samo ta". Cewar Lisa. Na'am da hakan suka yi, da sauri suka ja hannun V zasu wuce.

Noor da mamakinsu ya hanasa yin magana ne ya yi saurin riko hannun V ɗin dan ya dakatar da su. Sun goge mashi hadda, shi da bai taɓa kallon yarinya ba wai za'a kaita ta gaisa da daddy. Muryansa a sanyaye ga shi yanzu voice ɗinsa ta fashe ta zama lion voice, in a cool way ya ce. "Aunty please stop it, ni fa ban san wannan yarinya ba".

Da sauri Lusi ta ce. "Idan baka son mu kaita wajen daddy ne ma to mun hakura ba zamu kaita ba, amma batun baka santa ba bai ta so ba!"......... Saboda ya dakatar da zancen yasa ya ce. "Okey na ji na santa, ba sai kun kaita wajen daddy ba to".

Fara'arsu ta ninku, fuska cike da murmushi suka dinga yabawa V suna yi masu addu'a kasancewa tare har abada, da ya ga abin nasu ba mai karewa bane sai ya ce. "Ni bari in je wajen daddy".... Da sauri Aunty Lisa ta rikisa tare da cewa. "Ya za'ayi bakuwarka ta zo kuma ka tafi ka barta, ku tsaya a nan mu bari my je wajen daddy muna zuwa".

Basu jira amsar shi ba, suka wuce gaba. Har sun ɗan fara tafiya Lisa ta dawo da sauri, a kunne ta fara yi wa V raɗa kamar haka. "Kinga ɗan autanmu ne shi, muna ji da shi, ki kula da shi sosai, nasan tin da ya zaɓoki har ya ce ki zo ki gaisa da mu to kin ciri tuta kuma kin fita daban, please kada ki bari ransa yana ɓaci, dan muna son shi fiye da kanmu, anjuma zamu dawo kuma zamu zo har gidanku kin ji?"...... Kai kawai V ta gyaɗa alamar to.

Juyawa Lisa ta yi zata tafi Noor ya yi saurin damko gashin kanta, da yake saƙo ne su akwai wasa sosai a tsakaninsu, kuma yanzu ji yake ma shi ne babba tin da ya zama namijin gaske, dama can ya rainata. Buge mashi hannu ta yi tana hararansa kafin ta ce. "Sai ka fara yin budurwa baka faɗa mun ba, bayan ka ce nice zan zaɓa maka mata, zamu haɗu ne, zaka zo ka sameni, ba dan ka yi sa'a yarinyar ma makurar haɗuwa bace ai da na rusa wannan soyayyar, kuma ka kula da ita na faɗa maka". Ta faɗa tana dallah mashi harara cike da kauna da zolaya kafin ta wuce da ɗan gudunta saboda ya kawo mata damka!.

Shiru wajen ya ɗan yi, shi yana kallon ƙasa ita kuma tana kallonsa irin kallon huce haushin tsawon shekaru tana dakon begen ganinsa....... Katse masu shirun ta yi da cewa. "Good evening sir". Cikin girmamawa ta yi maganar...... Shiru kamar bashi a wajen, hakan yasa ta sake faɗe dan tana zaton bai jita ba. Nan ma shiru bai amsa ba, take jikinta ya yi sanyi, ta ji bahu daɗi, muryanta na rawa, a shagwaɓe sosai ta ce. "Ka yi hakuri da abin da ya faru".

Sai a lokacin ya ɗago kai, kallon tsab yai mata kafin in a cool way can ƙasa ya ce. "Meyasa kika mun karyar cewa na sanki?"........... Baya kaɗan ta ɗan ja saboda yadda idanunsa suka firgitata, a ƙoƙarinta na ja da bayan ne wayar dake hannunta ta suɓuce ta faɗo ƙasa. Bata kai ƙasa ba yasa kafa ya tareta.

Dafe kirji V ta yi, ganin ya tare yasa ta sauke ajiyar zuciya. Tamkar ball haka ya yi jifa sama da wayar sai ya capke da hannunsa, akwaisu da saiti ne sosai. Dawo da kallonsa a kanta ya yi, a dake ya ce. "Answer me, a yaushe na sanki? Meyasa zaki yi wa Auntys ɗina karya har kina ƙoƙarin sanyasu ɓata rai dan na ce ban sanki ba? Wacece ke? A ina kika sanni?".

https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-10-by-princess-teema

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.




STEP 1________🔥


11-11-2025.🔥


FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥





E_____________10


Bamar zata yi kuka ta amsa da. "To ai ni na sanka in kai baka sanni ba, kuma dama kai na zo gani"....... Ɗan waro eyes ɗinsa kaɗan ya yi, sai kuma ya yi saurin ɗauke kallonsa daga kanta. Ita kuma kara ja da baya ta yi tana turo baki............. "Your lion voice is so sweet that touch and melting my heart!". Ta faɗa cikin sigar tsantsar so! Tana magana kuma tana kara ja da baya wai dan ma kada ta ɓata mashi rai ya damketa.

Shiru bai yi magana ba, yana dai satar kallonta ta ƙasan ido........ "Baka son ka yi magana dani ne? Aunty ta ce in kula da kai fa"....... Still dai bai yi magana ba kuma bai ɗago ya sake kallonta ba. A daidai lokacin Angelina ta iso wajen tana faɗin. "V ki yi sauri, daddy yana jiranmu a motar zai mayar damu gida". A ruɗe take maganar, dan idan GAT ya gane V bata wajen sun shiga uku, kun san kuma doka ce ya kafa masu cewa babu ruwansu da sojojin barrack ɗinnan, and bugu da kari manyan sojoji basa aurar da ƴaƴansu ga sojiji ƴan uwansu sai in ALLAH ya tsaga da rabo, amma basa taɓa yarda, shiyasa zakuga ga mata kyawawa a cikin barrack amma sojiji zasu fita waje neman aure, kowa baya son ƴarsa ta yi takaba, sojoji a kowani lokaci suna iya rasa ransu ko da sabbin aure ne!

Angelina na zuwa ta ja hannunta, da sauri suka wuce tana waigosa hankalinsu a tashe. Da sauri Noor ya ɗago yana kallonsu, ya yi mamakin ganin tsananin kamannin dake tsakanin yaran, zuba masu idanu ya yi har suka kurewa ganinsa. Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa zai bar wajen, a nan ya lura da wayarta dake hannunsa.

Da sauri ya bi bayansu, sai dai ko da ya je bai gansu ba, daddynsu ya ɗaukesu. Zubawa wayar ido na ɗan lokaci ya yi kafin ya kunna light ɗin screen, hotonta ne a gaban screen ɗin, ga wayar babu password, dan haka sai ya ɗan shiga cikinta. Videos na soyayya kawai ya fara cin karo da shi, fita ya yi ya kashe wutar screen ɗin, cike da tinanin ina zai sake ganinta ya bata wayarta ya nufi wajensu Leo.

A ɗayan side na hall ɗin ya isko Leo tsaye da Big Bro ɗinsa suna magana, Leo ya ce yayan nasa ya bari sai gobe su wuce Us, shi kuma yayan nasa ya so su wuce yau ne, amma Leo yaki fir, wai akwai aikin da bai kammala ba, akwai sauran shirye-shirye da yake yi.

Baki a ɗauke da excuse Noor ya iso wajen. Zayra'an yana tsaye tsayuwar jarumai Noor ya ɗaga mashi gaisuwa cikin girmamawa. Shiru tamkar ba zai amsa ba, sai kuma can har sun fidda rana zai yi magana ya amsa a kalma ɗaya watau lafiya. Daga haka ya wuce ya nufi gidan da ya kasance yanzu mallakin su Leo. Bayan passing out ɗinsu sun baro yankin barrack kai tsaye, an basu gida cikin layin gidajen senior staff, gida mai shegen kyau, bene ne, mai ɗauke da ɗakuna 6, uku a ƙasa da parlo sai uku a sama shi ma da parlo, kitchen ɗaya da harabar gida, toilet a kowani room, tsarin ginin ya yi kyau matuƙa, dikka jami'ai 12 da zasu tafi mission ɗin nan a wannan gida zasu zauna kafin tafiyar tasu! Su 12 ɗakuna 6, kowani ɗaki mutane biyu kenan, saɓanin mutane 4 a lokacin da suke horo bar one!.

Kallon tsab Leo ya yi wa Noor kafin in a cool way ya ce. "Wannan wayar fa?". Kallon wayar Noor ya yi kan ya amsa da. "Na wata ce da ban santa ba, yanzu ma nemanta nike yi in bata"........ Wani irin kallon tuhuma Leo ya jefa mashi wanda bai san lokacin da ya ce. "Bro da gaske ban santa ba, kawai ina tsaye ta zo ta sameni, ka yarda dani".

Zura hannayensa a cikin aljuhu Leo ya yi, ya ɗan taka baya step biyu gaba kafin ya ce. "Ya da saurin tsarguwa boy? Ko ka ji na ce wani abin ne?"....... "Naga kana bina da kallon tuhuma ne". Ya faɗa yana tura wayar a aljihunsa!. "Uhm". Leo ya faɗa tare da juyawa zai bar wajen.

Da sauri Noor ya bisa yana faɗin. "Bro, believe me, I don't know this girl shaaa". Cigaba da tafiya Leo ya yi, har suka kusa shiga cikin gidan nasu kafin can ƙasa a natse ya ce. "Ita ce ta mafarkin da aka damemu da yinsa tsawon shekaru biyu kenan ko?"........ Da sauri ya girgiza kai tare da tare gaban Leo, yana ɗan shagwaɓe fuska ya amsa da. "Bro, ka bari mana, ni fa na faɗa maka wacce nake mafarki ban taɓa ganin face ɗinta ba, sai dai kyakkyawan surar jikinta".

"Uhm". Leo ya sake faɗa tare da sa kai zai raɓa gefensa. Sake tare gabansa Noor ya yi. "Baka yarda dani bane bro?"...... Tsayawa ya yi, suka kalli juna ido cikin ido kafin ya amsa da. "Asalin yarda kuwa, sai dai ina mamaki ne, anyway ka dai mai hankalinka a kan aiki, idan ka ce zaka biyewa mace zata shashantar da kai ne, ba zaka cinwa abin da kake so ba!". A dake da iya gaskiyansa ya faɗa, dan shi yana ganin in dai ka haɗa hanya da mace to zaka zama ragon namiji ne, wai ba zata barka ka yi abin da yakamata ba, sai ta sa ka zama mai rauni.

"For sure bro, zan yi ƙoƙarin ganin ban kauce hanya ba, kuma zan yi ƙoƙarin ganin na jajirce. But bro she's so cutie, pretty and.......". Sai kuma ya yi shiru.......... "Ta mafarkin ko ta zahirin?". Leo ya faɗa a taƙaice. Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. "Both, amma ta zahirin karshe ce"......... "Uhm". Leo ya sake faɗe tare da sa kai ya wuce, ya shige cikin gida, da sauri Noor ya bi bayansa, sun zo daidai tsakiyar gidan Leo ya ce. "Ba zan hanaka kula mata ba, saboda ni da kai akwai banbanci, but in ka bari ta fara ɗauke maka hankali fiye da tinani zan katse dik wata alaƙar ne".

A ɗan shagwaɓe ya ce. "Ba za ayi haka bama, aiki shi ne gaba da komai, ba zan bari ta shafi aikina ba"...... Jinjina kai Leo ya yi, a daidai lokacin suka fara tattaka staircase zasu haura sama izuwa room ɗinsu........ "Wacece ita kuma ƴar waye?". Leo ya faɗa can ƙasa, tamkar mai raɗa dan yana gudun yayansa ya ji suna maganar mata ya ce dama ba aiki ne a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login