Showing 3001 words to 6000 words out of 365093 words
"Ina mutumin da ya shigo gidan nan?". Wannan da ya kyasta hannu shi ya yi maganar, ba zaka taɓa iya tantance voice ɗinsa wace iriya ce bace saboda nose mask ɗin ta hana fitar muryar da kyau.
"Ba..... Babu wanda ya shigo gidan nan!". Da kyar ta basu amsa saboda tsoro........ Shiru gabaɗaya suka yi, tamkar ba zasu tanka mata ba, har ta ɗan saki jiki unexpected ta ji wani irin gigitaccen marin da yasa ta yi baya-baya kamar zata faɗi. Wanda ya yi maganar ne ya dallah mata wannan marin, lokaci guda ta ji kunnuwanta sun ɗauke ji na ɗan lokaci kafin ta sake dawowa daidai.
A karo na biyu ya sake cewa. "Ina mutumin da ya shigo cikin gidan nan? Bana magana sau biyu, a kanki na fara, kada ki bari hannuna ya sake motsawa! Dan innai duka na biyu sabauta ake yi".
Zazzare idanu ta yi a kansa ko zata iya rike komai kankantar makama da zata iya ganesu ko a gaba ne, sai dai babu wani abin da take iya hangowa. Tana cikin tinanin neman makama a tattare da su ta ji wani irin azaba ya ziyarci gaban goshinta, kan kace me jini ya fara wanke mata fuska, duka ya yi mata da gindin bindigar da ya fitar daga aljihunsa, irin police pistol gun ɗin nan ne.
Wani irin jiri ne ta ji ya kwasheta, tana ƙoƙarin faɗuwa ɗaya daga cikinsu ya damki gashin kanta ta baya, hakan yasa ta tsaya a kan kafafunta. Da hannun wannan na tsakiyar ya yi masu nuni da upstairs a kan su haura sama. Tsabar rashin imanin da gashin kanta suka jata da karfin gaske suka yi sama da ita, suna wani irin taku dake nuna koma su waye su lallai gurayene ba ragwaye ba, sannan basu da tausayi.
Sai da suka fara hawa upstairs ɗin suka lura da blood da ya yi ta ɗiga a ƙasa, na mutumin da ta yi treating kenan. Blood ɗin suka fara bibiya suna haurawa har zuwa bakin wanna room ɗin. A nan eagle ɗin nasu ya dakata tare da ɗan matsawa gefe, ɗaya daga cikin yaransa ne ya yi gaggawar shigowa gabansa ya sanya kafarsa ɗaya ya take door ɗin da karfi sai gata ta wagale gabaɗaya.
Biyu daga cikin yaran dake bayansa ne suka yi gaggawar wucewa gaba suka shige ciki. Sai da suka shiga eagle ya tako cikin ƙatsaita. A tsakiyar ɗakin suka dakata suna muzurai, zazzare idanu suka hau yi a cikin room ɗin ko zasu hango wani abin. Sai dai kuma ɗakin wayam babu kowa.
INA MUTUMIN YAKE?.
Eagle ne ya fara wuwwurga idanunsa ta ko'ina yana bin ɗakin da kallo, can ya tsaida kallonsa a kan bullet dake cikin silver bowl da ta ajiye saman table, sai kuma alamar jini-jini dake jikin bedsheet da bata gama gogewa da kyau ba, saboda mutumin na kwance. Kasa da idanu eagle ya yi sai ya ga alot of blood a kasa ya malala har karkashin gadan.
Cikin natsuwa eagle ya taka zuwa gaban bed ɗin, hannu yasa cikin bowl ɗin ya tsamo wannan bullet ɗin, kura mashi idanu ya yi na ƴan sakanni kafin ya juyo da kallonsa a kan sauran yaran nasa.
"This bullet is mine, daga gun ɗina ya fita, dan haka yana cikin gidan nan, weeding 2 mins ku kawo shi nan". Yana rufe baki uku daga cikin yaran suka bazama waje dan nemosa. Ɗayan kuma ya cigaba da rike matan, shi kuma eagle ya hau kewaye room ɗin yana dube-dube. Har toilet ya buɗe ya leƙa babu kowa.
After two minutes sai ga waɗan nan yara nasa sun dawo da yar gudunsu mai kama da jungling. "Eagle babu kowa fa a cikin gidan nan, ita kaɗai ce".
Gabanta Eagle ya dawo ya tsaya. "Ina yake?!". Ya faɗa in a harsh way. Tana kokarin dawowa cikin hayyacinta na azabar ja mata gashi da suka yi ta sake rasa sauran hayyacin da ta yi ƙoƙarin tattarowa saboda marin da Eagle ɗin ya sake ɗauketa da shi. Taga-taga ta yi tin daga nan ta rasa hayyacinta.
Hannuna yasa ya damki gashin kanta da ɗayan yaronsa yake rike da shi, jijjigata da karfi da gashin ya yi kafin ya hankaɗeta ta tafi ta bugu da jikin bango ta yi baya-baya ta faɗi kasa. Takowa ya yi zuwa in da take, kafa yasa babu imani ba tausayi ya fara kai mata hamɓari a ciki da karfin gaske, ga wannan uban boot ɗin nasu mai balain tauri.
Matsawa kusa da shi dikka sauran yaran nasa suka yi suka yi mashi zube suna kallonsu. Hamɓari bana wasa ba yake kai mata a ciki, tin sautin kukanta haɗe da nishi yana fita da ɗan karfi-karfi har ya koma fita a hankali numfashinta na sama-sama. Sai da ya ga bakinta ya fara fitar da aman jini sannan ya duka ya sake damko gashin kanta, da shi ya sake ɗagata, ya hau janta har izuwa gaban mirron dake ɗakin.
Da karfi ya sake jijjigata kafin ya rotsa kanta a jikin mirror ɗin. Wani irin marayar kara ta saki mai ɗauke da nishin gaske. Jawota baya da gashin nata ya yi, take fuskarta ta yi damege, jini ta ko'ina yana ketowa ne, glass na mirror dik ya caccake mata fuska.
Ko kaɗan babu alamar Eagle zai tausaya mata, ya sake janta zuwa jikin bango, da karfi ya jijjiga kanta ya sake bugata da bangon, ji kake dum. A daidai wannan lokaci ko numfashi bata yi, jifa da ita a ƙasa ya yi, ta kwanta flat. Wannan shegiyar boot ɗin nasu yasa ya take mata wuya da shi.
Sai da ya ga alamar ta daina numfashi gabaɗaya, sannan ya zare kafarsa tare da ɗagowa ya kalli yaran nasa. "Nasan tabbas yana cikin gidan nan, dan ta yi mashi aiki, kuma ba zai iya gudu ba saboda yaranmu dake bakin kofa, dan haka ku sake bazama ciki, dik wata halitta mai rai dake ciki ku tabbatar kun kashesa koda kare ne, sannan dik wasu tankar gas dake gidan nan ku kunnata, in har bai fito da kansa ba to zai mutu a cikin wuta ne!!". With harsh voice ya yi magana, kuma cikin bada umarni.
Da okey suka amsa mashi kafin su bazama waje dan cika aiki. Shi kuma waje ya samu a saman gefen bed ya zauna tare da ciro wata waya yar karama irin wacce ake haɗata da tauraron ɗan adam, wayace da dik balain mutum bai isa ya bi diddiginka ba, sannan wayace da sam-sam ba'a isa a kiraka ba sai dai kai ka kira mutum, ita akewa labari da s-phone, dayawa daga cikin shugabannin manyan kasashe na duniya da ita suke amfani dan tana da mahaukacin tsaron gaske, gata yar karama tamkar nokia mai sim card guda ɗaya.
Latsa botiran wayar ya yi for some minute da ba zasu gaza biyu ba kafin ya karata a kunnesa. Ba'a iya jin me ake faɗe on the other side, shi dai ya ce. "Done the work isn't means success for you, but for me......". Yana gama faɗin hakan ya kase kiran tare da mai da wayar cikin aljihunsa, sannan ya yunkura zai miƙe kenan yaran nasa suka shigo da gudu irin na shahararrun gangsters.
A gabansa suka tsaitsaya, cikin girmamawa suka ce. "Aiki ya cika, harta karen dake gidan nan bamu barshi da rai ba, sannan akwai gas har guda uku a kitchen na kasa, sai kuma fetur da muka sami a gen room three jarecan, shi ma mun bi ko'ina a gidan mun daddala shi, bamu bar wata alama ta makama da za'a iya gane ba wuta ce ta tashi ba!". Yadda suke magana cike da kwarewa a aiki, da alama sun jima a wanna harka sun kware.
Jinjina kai ya yi cikin nuna alamar yarda da aikinsu, sannan ya miƙe tsaye ya nufi bakin kofar fita. Sai da ya fita ta waje sannan ya ce. "Kuna sauka parlon kasa ku danna wuta". Yana gama faɗar hakan ya yi gaggawa wucewa.
Da sauri suka rufa mashi baya. Kamar yadda ya faɗa suna fitowa suka dannawa gidan wuta tare da yin gaggawar ficewa waje. Take ko'ina ya kama bal-bal-bal.
A jere suka fito waje, suna fitowa suka nufi wasu jiga-jigan motoci masu rai da lafiya bakake kirin dake can nesa da gidan. Motoci biyar ne cir, da gudu irin na gangstars suka karisa wajen motocin. Nan suka isko Eagle DA sauran yaransa a cikin motocin yana zaune, ciki suka shiga, da gudun gaske suka figi motocin nasu suka danna kan shararriyar titin dake shinfiɗe har barin unguwar.
Wutar kuwa ci take bal-bal-bal har sama wanda hakan ya yi sanadiyar farkawar al'umma daga barci. Nan fa aka fara ihun gobara-boraba, take suka kira fire service. Abinku da babban ƙasa cikin ƙanƙanin lokaci sai ga fire service guda uku manya-manya. Basu ɓata lokaci wajen ƙoƙarin kashe wutar ba, sai dai kuma ina, ta rigada ta kama over, har tana shalle ta capki makota. Wani gas da ya fashe wutar ta yi sama sai ga shi ta kama gidan dake kusa da su.
Hankalin jama'a ne ya kara tashi, kowa faɗi yake ina Dr Hushaima da ɗiyarta suke?. Nan fa hankalin al'umma ya kara tashi sosai, take aka kira hukumar cetar rai daga gobara, abin ku da manya kasashe ko mintuna biyar ba'ayi ba sai ga jami'an sun iso, wasu jiga-jigai da su, suna sanye da kayan karisa daga gobara mai ɗauke da chemicals da dama.
Ji kake dirim dim suna dirowa daga saman bayan motocinsu da wani mahaukacin gudu, hannunsu rike da wani talanki mai karfin gaske da zai taimaka wajen kare masu wutar. Kan kace me ga jeri gwanon motocin jiga-jigan sojoji, ƴan sanda da kuma hukumar CIA. A wannan rana dai wannan unguwa sun ga tashin hankali na kin karawa.
Da gudu jami'ai biyar suka kutsa cikin gidan, wutar nan kara ci take tamkar ana kara rurata, gabaɗaya fire service da suka zo tamkar basa yunkurin kasheta, saboda gaba take ci over.
Jami'an sun samu sun shiga tsakiyar harabar gidan, amma babu hanyar kutsawa ciki, saboda door ɗin parlo ya fi ko'ina kamawa da wuta, su Eagle sun san za'ayi yunkurin kawo taimako shiyasa yaransa suka fi zubawa jikin door fetur sosai, sun kware a iya aE_____________5pp7a.
Dik yadda waɗan nan jami'ai da jama'ar unguwa suka so cetar Dr Hushaima da yarta abin ya faskara, domin babu hanya, suna ji suna gani suka ja da baya dan wutar ta zarce yadda suke tinani. Tin karfe 5 na asuba ake abu ɗaya sai karfe 12 na rana suka samu damar iya kashe wutar, amma ya ci gidaje almost 10 zuwa sama. Gidan Dr Hushaima ko tsinke ba'a iya fitarwa ba, komai ya kone kurmus, gwara ma sauran gidajen akwai abubuwan da suka ɗan ragu, amma nata gidan abin ya munana sosai. Jama'a sai jimami suke yi, sunga balai yau.
Bayan lafawar gobar fire investigation, ATF sun halacci wajen domin binciken menene ya jawo wanna gobara mai karfi haka?. Sai dai iya bincikensu ya nuna masu cewa gas ce ta fashe, bayan ita basu samu wata makama ba. Jama'ar unguwa faɗi suke Dr Hushaima tana da balain kula, ya aka yi aka samu wanna matsala, amsar da mutane suka rasa kenan.
TO FARKO KENAN DAGA LITTAFIN ZAKUNA BIYAR, SHIN YAZATA KAYA? INA YAR DR? SHIN HAR DA ITA TA RASA RANTA NE? INA WANDA DR TA CETA? MEYASA DR TA ZAƁI TA RASA RANTA A KAN TA BUƊI BAKI TA FAƊI IN DA YAKE? MENENE ZAI BIYO BAYA BAYAN MUTUWA DR DA YARTA? MUJE ZUWA AKWAI KALLO NAN GABA KAƊAN.
SHIN MUTANE NE ZAKUNA BIYAR ƊIN? DABBOBI NE? WHY ZAKUNA BIYAR? BA ZAKI TAƁA SANIN ZAKUNA BIYAR BA HAR SAI KIN BIBIYI WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSA HAR KARSHE, KAMAR YADDA NA CE A FARKO, BA ZAN CE KOMAI BA, NA BARKU DA ALKALANCI.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA STAR LADY TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-2-by-princess-teema
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
FIVE LIONS🦁🦁🦁🦁🦁
MALLAKIN
FATEEMA ZAHRA MUSA. A-K-A
PRINCESS TEEMA STAR LADY.
1-11-2025.🔥
THE STORY OF DEATH OF LIFE🔥🧠
E_____________2.
NEW YORK.🔥
Jami'an sun yi iya bincikensu amma ba su iya gano menene ya haddasa wannan gobara a cikin gidan ba, iya abunda suka sani kawai shine gas ne ya fashe.
Haka suka kwashi jiki suka bar gidan jama'a cike da jimami kowa ya koma bakin aikinsa. A gaskiya jama'a sunyi babbar rashi, domin dr mace ce wace kowa ya shaida tana da kyawawan ɗabi'u da kyawawan halaye, duk anguwan kowa yana alfahari da ita kuma kowa yana son kasancewa tare da ita, ko me dare in baka da lafiya ka kirata zata fita ta duba maka, bugu da kari abin hanunta bai rufe mata ido ba, kome ka tambaye ta zata baka kyauta in dai bai fi karfin ta ba, gaskiya jama'a sun ji babu daɗi sosai.
Haka unguwar yau ta kasance shiru, dik da dama suna kasancewa a cikin shirun babu hayaniya, amma na yau daban ne saboda mutuwar doctor da ƴarta.
9:00PM.
Agogon birnin new york ya sake bugawa, kasancewar unguwar ta manyan mutane ne sai ya zama kowa ya shiga gida, ga kuma mutuwar da ya faru sai ya kara sanyawa ko'ina yai tsit sosai, then akwai alamar ruwan sama a sararin samaniya, hadari bakin kiri, shi ya kara kora kowa gida........ A hankali sauti na wasu irin jiga-jigan motoci da suka amsa sunansu motoci ya fara ratsowa cikin unguwar, tun daga kan yanayin sautin kukansu zaka san motoci ne na manyan kai, ajere suka keto titin wannan unguwa suna tafiya a wani irin slow montion. Motoci ne guda biyar cip.
Kai tsaye a ƙofar gate ɗin gidan dr suka paka, suna parking a tare aka buɗe kofofin motocin, kan ka ce me wasu irin jiga-jiga mutane madaka katti sun danno waje, dikkansu sanye suke da baƙar wando da kuma farar t-shirt a jikinsu, while sun ɗaura tail coat a saman T-shirt ɗin wacce ta kai masu har gwiwa. Da ka gansu ko ba a faɗa maka ba kasan wasu tawaga ne na daban, imma jami'ai ko kuma gangsters, mutane biyar ne suka fito a cikin motoci biyar, kowane daga nashi motan daban-daban.
Bawai iya su biyar ba ne a cikin motoci, a'a, akwai wasu sannan da drivers daban, dan dukansu daga back seat suka fito, cikin gidan dr suka wuce, a tare suke tafiya, in short a tare suke ɗaga kafa su kuma sauke, yadda kuka san kwararru kuma shahararrun gangster's, a haka suka shiga cikin gida.
Gabaɗaya mutanen unguwa suna cikin gida babu wanda ya san meke faruwa, saboda motocinsu ba irin motoci masu karan nan ba ne, mota ce da saita matsa kusa da kai zaka san tana zuwa, asali irin wannan motocin jami'an sirri sun fi amfani da ita ko kuma manyan gangsters da suka shahara a duniya, mota ce bata kowa ba.
Sun ɗauki a kalla minti 10 a cikin gidan dr kafin su fito a jere, ɗaya daga cikinsu hannunsa ɗauke da wata ƙatuwar abu kamar kwali aka nannaɗe, dikka sauran huɗu akwai abubuwan da suka rike a hannunsu, da alama daga cikin kayan doctor wa inda basu ƙone ba suka tattaro ko dai wani abin, dik yadda aka yi suna da alaka da ita ko makamancin haka. Cikin motocinsu suka koma, a jere suka bar unguwar kamar da suka shigo TO FA, TAFIYAR YANZU TA FARA FA WACECE DR? ME KUKE TINANIN ZAI FARU? SU WANENE WAƊAN NAN MUTANE? MU JE ZUWA DAI.
-------------------------------🔥
KASAR AVARIS.
Avaris kasa ce dake makotaka da Us a kudu ta tsakiya. Kasa ce wacce take da tarin tattalin arziki, kama daga kan man fetur, gold, red diamond, har da su uranion suna da shi, suna da tattalin arziki daga albarkatun kasa da ruwa fiye da yadda mutum yake zata. Kasa ce dake cin gashin kanta, kasa ce dake da karfin siyasa da soji, sai dai gabaɗaya mafiya yawa daga cikin states na kasan a lalace suke, ga fama da yunwa da talauci, dik da wannan tarin arziki da suke da shi, ƴan ta'addan sun hana wasu daga cikin yankunan kasan zaman lafiya, kidnappers, da ɓarayin fili dana ɓoye, cin hanci da rashawa, gurɓatattun shuwagabanni, a wasu yankunan ma ƴan'ta'addan sun fi gwamnati karfi, su ke juya gari har da karɓar haraji da sauransu, abu kamar shirin film, amma zallar gaskiya ce!! Amma mu kutsa cikin labarin zamu fahimci daga ina matsalar Avaris ta samo asali.
Eldoria State. Nan ne babban birnin kasar Avaris wanda suke ji da ita, birnine da ta ƙawatu matuƙa, domin a nan Diamon palace take, wato fadar shugaban kasar Avaris, birni ne na manyan alhazai mai ɗauke da dogayen gine-gine na alfarma, benayen da aka yi su high rise building masu design daban-daban, ga manya-manyan estate na gani na faɗa masu tsarin ginin turai, da su urban complex, glass towers, residential towers da dai sauransu. Wannan kasa tana da kyakkyawar alaƙa da turawan yamma, akan kasuwancin fili dana ɓoye, kai akwai fa abubuwa sosai sai mun kutsa ciki zaku gane karatun.
-----------------------🔥
AZURE BARRACK. Babban barikin soji na birnin Eldoria.
Shinfidaɗɗen ginine wanda aka shinfiɗa tamkar ba za'a mutu ba, ka kai iya kallonka baka iya ganin karshen wannan gini saboda girmansa, gini ne dake ɗauke da Academys kala biyu bayan sansanin soja, sannan gini ne da sai mun kutsa ciki kawai zaku iya ganeta. Dik wasu manyan jami'an da suka shahara a manyan kasashe duniya ta sansu, to AZURE BARRACK ne ta kyankyashesu, daga ƙasashe da dama ana kawo manyan gifted jami'ai dan a horar da su, dik manyan jami'an manyan kasashen dake ji da