Showing 18001 words to 21000 words out of 365093 words

Chapter 7 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5879

kacal! Idan soja ya yi kuskure ko ya kasa gama cin abincinsa a cikin waɗan nan ƴan mintocin, to za a tura shi ya yi tsalle kwaɗo guda 100 ko gudu na musamman kafin a bar shi ya tafi, kuma ba zai cinye sauran abincinsa ba.

A haka su Noor suka kariso suka sami su Leo, zama suka yi suka hau cin abincin suma a cikin gaggawa, dan saura 5 mins 30 mins da aka ɗeba masu ya cika. Kafin 8 ya cika sun kammala cin abincin nasu, a nan Captain ya umarcesu da su tashi su nufi wajen da aka tanada dan ɗan miƙe kafafunsu kafin 8:30 ya cika. Da sauri suka miƙe suka nufi wajen.

Zama suka yi Zaysh and Vash suna ta gulmar Leo, kai Vash har da cewa. "Tun da ya zo yana wani naɗe yatsu ko me yake yi haka oho?".......... Zaysh ya ce. "Ni ban yarda da shi ba, daga gani daga familyn gangsters ya fito, ji wani kitso dake kansa ta bayan wuya fa". Da sauri Noor da Vash suka kai kallonsu kan bayan wuyansa ta ƙasan p-cap ɗin, a nan suka lura yana da wani abu a wajen dab gashin kansa tamkar wani zanen fuskar wani abu haka, kurawa wajen idanu Vash ya yi.

Shi kuma Noor da ɗan ba ruwana ne sai ya ɗauke kallonsa daga wajen tare da cewa. "Kuma kyakkyawa ne sosai wlh guys"........ "Ana cin kyau ne?". Zaysh ya faɗa a kufule. Murmushi kaɗan Noor ya yi wacce ta kara fito da kyansa. "To ai kaima Zaysh kyakkyawa ne, ni wlh suna mun kama da Vash ma wani zubin"...... Vash ɗin ne ne ya yi sauri cewa. "Noor banda kalaman yaudara, ta ina muke kama?".

"Seriously kun mun kama". Cewar Noor. Da sauri Vash ya sake cewa. "Baka son gaskiya dai"........ Zaysh ne ya ce. "Ku daina wannan zancen muyi focusing akan abin dake gabanmu na horo".

Kun san wani abu? Shi fa Zaynash so yake yi ya zama na ɗaya, yana jajircewa ne sosai dan ya tsallake horo lafiya ya fita da result mai kayu da karfi, ya fita a babban soja, to ya ga kuma dik ƙoƙarinsa Leo yana wucesa, ya yi iya yinsa ya isa waje sai ya samu Leo ya rigasa, to wannan abin ne yasa yake jin haushin Leo ba komai ba, yana son idan suka kammala horon nan ya zamana shi zai fito da matsayin shugaban rukuninsu, dik matasan sojijin nan su zama a karkashin ikonsa, amma yaga Leo na ƙoƙarin kawo mashi cikas.

Kuma a cikin wannan rukuni na horon shekarar nan, su uku ne zakwaƙurai wanɗan da tin a horon farkon nan manyan sojojin suka gane hakan, da Leo, Zaynash sai wani ɗan Nigeria mai suna Unays a room number 2 yake, suna da jajircewa matuƙa, dan dik horon da suka yi yau su ukun nan ne a gaba, sai dai da alama za'ayi zazzafan gasa a tsakanin su ukun nan wajen tsai da goni ɗaya, saboda yadda suke jin haushin juna, Zaynash yana jin haushin Unays da Leo, while Leo baka gane ainahin ina ma ya dosa, yana jin haushinsu ko baya ji dik ba'a gane mashi, shi ma Unays haushin Zaynash and Leo yake ji, saboda suna zuwa daidai da shi, ya so ace ya fi kowa, ga shi ɗakinsu makwabtan juna ne. KAI AKWAI KALLO FA A GIDAN SOJA WLH, ZAZZAFAR GASA, KU DAI MU JE ZUWA.

8:30 daidai Captain ya dawo hannunsa rike da wata sharɓeɓiyar bulala wacce ganinta kawai tashin hankali ne. A saman stage dake wajen ya tsaya yana faɗin. "Ready! Zaku fara horon daidaito a yanzu, zaku koyi yadda za ku tsaya da ƙafafunku ba tare da fargaba ba a lokacin harbi ko farmaki ƴan ta'adda".

Mimmiƙewa tsaye suka yi, sai suka fara kallon juna. Muryan Captain ɗin ne ya katse masu kallon da suke yi da cewa. "Kowannenku ya kama abonkin matsaya a tare"........ Basu gane nufinsa ba, hakan yasa suka sake binsa da kallo.

Ɗan gyara murya ya yi tare da sake cewa. "Ku shiga rukuni guda, dik ƴan ɗaki ɗaya su kasance a tare waje guda, zaku tsaya ne da kafafunku ɗaya a kasa, ɗaya zaku ɗangalesa a sama, dik wanda ya saki kafansa ɗayan kafin lokaci ta cika, to dikka saura mutane ukun da suke ɗaki guda zasu je da gudun gaske su taɓa wancan post dake can, wanda ya yi karshen dawowa kuma zai karɓi bulalu guda biyu masu kyau".

A miliyan suka juya suka kalli post ɗin da yake magana a kai, mugun nisa ne da shi, suka sake juyowa suka kalli bulala dake hannunsa, lallai fa babban aiki, kuma dikka wannan ace farko ne ake masu kaɗan-kaɗan? Tab gaba sai yaya kenan? Kallon juna suka sake yi, a fili Noor ya ce. "Wani kaddara ya kawoni aikin soja ne wai?". Yana kwaɓe fuska ya faɗa. Sai kuma ya juyo da kallonsa a kan Vash, Zaynash da kuma oga Leo.

Wani irin kallo Leo ya wurga mashi har sai da ya ji maƙoshinsa ta bushe yana buƙatar ruwa, in a cool way sosai Leo ya ce. "If you people cause us to fail, then what?". Then he went silent as if they already knew what would come next.

"Ready". Captain ya faɗa yana kallonsu. "Start"....... Da sauri dik suka ɗaɗɗage kafafunsu ɗaya sama suna bubbuɗe hannaye tamkar zasu tashi sama. Zubawa lokacin ido Captain ya yi a agogon dake hannunsa, lokacinsu ya fara daga yanzu kenan.

Unexpected from nowhere suka ji karar harbi da bindiga, ai kusan rabi da kwatan waɗan dake wajen sai da suka sauke kafafunsu, wasu ma har ƙoƙarin gudu suka yi, su da ake koyawa yadda zasu saita natsuwarsu a lokacin yaki, amma sune suka razana har haka daga jin karar bindiga, tab da aiki kenan, da gangan aka buga bindigar dan a gwadasu dama.

Nan fa Captain ya sanyasu gudu zuwa taɓa post, bayan sun dawo waɗan da suka yi last a kowani team suka sha bulalu bibbiyu a gadan baya, haka ya sake cewa su ɗage kafafunsu, Leo and Zaynash da Unays makocinsu sun jajirce sosai, ko da wasa basu sauke kafafunsu a lokacin karar bindigar ba, dik da cewa sun ɗan razana.

A karo na biyu suna ɗage kafafu da ƴan mintuna aka sake buga bindigar da karfi, a yanzu ma dai su dayawa suka sauke ƙafafuwa suka kuma razana, haka suka sha gudu suka kuma sha bulala. Sai a karo na uku ne suka fahimci lallai wannan bindigar saboda su ake bugawa, dan haka sai basu sake razana ba, suka tsaya, a karo na huɗu aka sake buga bindigar, nan ma dai suka tsaya cak, abin ya yi mugun burge Captain, lallai ya shaida suna da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin gane abu, sun fahimci saboda su ake buga gun ɗin har sun ɗauki mataki, lallai suna da jajircewa da zafi nama, ya jinjina masu.

Lokacin da suka saba da karar bindigar suka gano saboda su ake yi, sai suka tsaya kyam tamkar saƙaguguna, ana buga bindigar ko a jikinsu, sai dai kuma basu fi minti uku da fara tsayawa cak ko da karar bindigar ba Noor ya sake ɗayan kafansa yana faɗin. "Wlh na gaji"........ Zaysh and Leo a tare suka haɗiyi wani irin yawun takaici, dan dikkansu burinsu team nasu ya zo na ɗaya, ransu ya sosu. Vash ma ya ji haushin sake kafa da Noor ya yi.

A tare dikkansu suka sauke kafafunsu suna ɗaure fuska, juyawa suka yi da gudu su ukun, suka nufi wannan post ɗin, shi kuma Noor ya sake ɗaga kafansa ɗaya sama bisa umarnin Captain.

Leo ne ya fara dawowa da gudu sai Zaysh ke take mashi baya, Vash ne last ɗin dawowa, ya karɓi bulalu biyu masu lafiya a gadan bayansa. Sake komawa suka yi suka tsaya suna kwaɓe fuska, Zaysh ne yake faɗi a ransa dole a canzawa Noor ɗaki, a raba shi da su tin da rago ne, su kuma ɗakinsu dikka jarumai ne!.

A karo na biyu Noor ya sake sauke kafafunsa har da durkushewa kasa yana numfashi sama-sama. Ai tamkar Zaysh ya rufe shi da duka haka suke ji. Ajiyar zuciya Leo ya sauke tare da kai hannu yana ɗan shafa kirjinsa kafin ya sauke kafafunsa ya juya da gudu ya nufi wajen post ɗin, Zaysh ya rufa mashi baya, sannan Vash.

Kamar ɗazun yanzu ma Vash ne ya sha bulala guda biyu, tamkar zai cinye Noor da harara haka suka sake komawa suka tsaya. Ina short kafin a tashi wannan horon sau uku Noor yana sasu gudu, yasa Vash karɓar bulala.

Da suka kammala sai faɗa Vash yake yi mashi, yana ta zaginsa wai ya cika ragonta, shi dai ban da ALLAH wadarai da aikin soja babu abin da yake faɗi. Shi kuwa Unays wannan faɗuwa ta Noor ta yi mashi daɗi, koba komai a yanzu team ɗinsu ta zo na farko tin da su ko ɗaya babu nasu da ya faɗi, abin ya yi mashi daɗi sosai, ji yake tamkar ya baiwa Noor kyauta.

----------------------------TIME🔥

Karfe 11 daidai suka hallara a katafaren class ɗinsu, class ɗin ya tsaru sosai, tamkar secondary set haka, suna da Ac, tables ɗinsu mai shegen kyau da loca, chairs ɗinsu mai kyau, kowa da kujerarsa. Captain Onbish ne ya hallara a gaban class ɗin nasu hannunsa rike da wata katuwar littafi. Fuskansa babu alamar annuri ko wasa, a saman table dake kusa da smartboard ya ajiye takardan hannunsa, yana sanye da kaki a jikinsa.

Rubutu ya ɗan yi a smartboard ɗin da makar kamar haka FIREARMS kafin ya juyo ya kallesu, while dik shi suke kallo. Dikkansu sun fitar da note books ɗinsu, a natse cikin kakkaifar voice ya fara da faɗin.

"Firearms, watau rabe-raben makamai, yau zamu fara ne da rabe-raben makamai kafin ku san menene makaman na gaske". Ya ɗan dakata yana rarraba idanu a kansu kafin ya cigaba da cewa. "Bindigogi sun rabu rukuni 5 ne, na farko akwai pistols, watau ƙananan bindigogi waɗan da za'a iya rikewa da hannu ɗaya, sannan ana amfani da su ne daga kusa. Misalan pistols akwai glock 17, beretta M9, colt m1911, SIG sauer P226, jimilla nau'ikan kala 10 na pistols gun".

Dafe kai Noor ya yi, a ransa ya ce. "Da sunan waɗan nan makamai kawai idan aka barka sai su kasheka ko ka shiga doguwar suma, kana jin wasu sunaye tamkar na horori wai bindigu, ni dai na shiga uku tin da na shigo aikin soja!".

A fili kuwa ya mayar da hankalinsa kan sauraron Captain Onbish da abin da yake faɗe. Leo, Zaynash and Unays sun natsu sosai karatun yana shiga kansu, saboda sun sanya a ransu zasu zama manyan sojoji masu ji da lafiya dan bawa duniya gabaɗaya tsaro su kori ƴan ta'adda, sun yi alkawarin a dik ranar da suka sanya kaki mai ƴanci, ma'ana suka tsallake horo suka zama sojoji, to tabbas ba za'a sake samun wani ɗan ta'adda a duniya ba kasarsu kawai ba, wannan alƙawari ne suka ɗaukarwa kansu. SHIN WANNAN ALKAWARI NASU ZAI CIKA? ZASU YI NASARAR TSALLAKE HORO SU ZAMA SOJOJI?.

Cigaba Captain ya yi da cewa. "Na biyu akwai rifles, bindigogi masu dogon murfi, ana amfani da su daga nesa, kuma suna da ƙarfi da daidaito sosai. Suna da nau'ika kamar haka, bolt-Action rifles, kamar mosin-nagant, kar98k, sai semi-automatic rifles, kamar m1 garand, SKS, da kuma assault rifles, kamar AK-47, M16, FN SCAR, G36, F2000, suna da nau'ikandai fiye da 30, amma ana koyar da nau'i 10 zuwa 12 a wannan Barrack ɗin, ba'a cika amfani da sauran nau'ikan ba". (Sai ga jami'ai na musamman ake koya sauran nau'ikan, misali idan suka gama karɓar horo, yanzu haka manyansu suna nan suna kula da dik wani motsinsu, idan suka kammala aiki za'a zaƙulo jarumai kuma ƴan baiwa, sai a sake basu horon da a nan ne zasu zama manyan jami'ai na sirri dana ambata maku a farko, za'a koya masu harbi na musamman wanda ko a ina ne a faɗin duniya komai nisan da suke zasu iya saita mutum su yi harbi kai tsaye.)

Ya ɗan dakata ya basu 2 mins suka rubuta abin da yake karanta masu, dan shi ma yana bayani yana ɗan kara rubutawa ne.

"Na uku muna da machine guns, bindigogi masu harbi da yawa a lokaci guda, ana amfani da su wajen mamaye wuri, suna harba bullets da yawa a lokaci ɗaya. Sannan suna da nau'ika kamar haka, akwai light machine guns (LMG) RPK, M249 SAW sai general purpose MGs PKM, FN MAG, akwai heavy MGs DShK, browning M2 .50 Cal, suma sun kai kala 10". Nan ma ya ɗan dakata ya basu damar rubuta wannan karatun kafin ya cigaba da cewa.

"Na huɗu muna da shotguns, watau bindiga mai fashewar bullets, suna amfani da pellets ko slug, masu amfani daga kusa. Misali remington 870, mossberg 500, benelli M4, winchester model 1897, a taƙaice irinsu 6 zuwa 10 ne kawai da aka fi sani".

"A karshe muna da sniper rifles, bindigar kwantena masu harbin nesa, suna da tsawo da ƙwarewar harbi daga nesa sosai, misalinsu akwai dragunov SVD, barrett M82 .50 cal, M24 sniper weapon system, L96A1, cheyTac M200, su 8 ne zuwa 12 da aka fi amfani da su".

"Amma akwai sauran makamai masu harbi irinsu submachine guns SMG kamar MP5, Uzi, PPSh-41, grenade launchers, kamar M203, GP-25, Rocket launchers, RPG-7, AT4, anti-material rifles, NTW-20, denel mechem, flamethrowers, kaɗan ake amfani da su yanzu, kamar M2. nau'ukan bindigogin, a taƙaice gasu kamar haka pistols 10, rifles duk nau'i 30, machine guns 10, shotguns 8, snipers10, gabaɗaya sama da 80 zuwa100 na nau'i bindigogi ake koyarwa a aji na nan GIDAN SOJA, amma ana mayar da hankali kan 25–30 na asali ne wanda kuma shi ne kuma zaku fi mayar da hankali, yau ku rike na'ikan da na faɗa maku, gobe zamu fara duba ne daga kan menene pistols gun da yadda suke, yadda ake amfani da su!". Ya dakata yana sauke numfashi a hankali.

Shi dai Noor gabaɗaya sunan makaman ma kawai sun hargitsa mashi lissafin ƙwaƙwalwa ne, wai sunan makaman kawai ma ai sai su sa mutum ya mutu da ransa, dan haka shi wlh ragonta zai dinga nuna masu har a gama horon ya fito bai samu result ba ko za'a barshi ya koma gida. Cike da wannan tinani a ransa har suka kammala class, suka tashi around 1 na rana, a nan ne kuma musulman cikinsu suka nufi masallaci dan yin sallah.

Bayan sun fito daga sallah suka wuce hall ɗin cin abinci dan yin lunch. Kamar dai ɗazu group-group suka zauna kowane da ƴan ɗakinsu suka ci abincin su, sannan aka basu hutun 30 minutes kamar ɗazu. Dik wani motsin matasan sojojin nan a kan idanun manyansu suke yi, kun san meyasa ake saka masu ido sosai?. Saboda a yanzu ne ake zaƙulo sojijin ɓangare na musamman, a yanzu ne ake ciro sojoji masu kaifin barisa, suna lura da su ne dan su ga su waye suka fi kaifin basira ta yadda ko sun kammala horo za'a sake basu horo na musamman na sirri dan zama zakwaƙuran kuma su kasance masu iya gano mai laifi da kallo ɗaya, shiyasa ake saka masu ido sosai a wannan lokaci.

Karfe 2:30 Captain ya umarcesu da su tsaya bisa tsari, sannan su yi tafiya a kan tsari izuwa wani katafaren fili mai girman gaske wanda shi ma a cikin GIDAN SOJAN yake.

Bayan sun isa wajen a nan Captain ya fara karantar da su me ake nufi da discipline da ladabi, yadda zasu kasance masu ladabi da girmama manyansu, bin umarni ba tare da gardama ba, tsabtace kaya da gyaran ɗakunansu, tsari a rayuwa, da tsarkin jiki. Ai ya zame masu dole su yi ladabi da tsabta ne ma, idan ba haka ba su gwammaci mutuwa!!.

Sun yi wannan horo na discipline har zuwa karfe 4 na yamma, sannan suka wuce masallaci. Bayan sun yi sallah sun dawo suka ɗaura da horon gwajin ƙarfin hannu, ana koya musu yadda ake riƙe makami da ɗagawa ba tare da gajiya ba, amma ba kai tsaye shi aka koya masu ba, domin yau ne ranar farkonsu ko makaman basu gani da ido ba, kawai gwada karfin hannayen nasu aka fara yi ta hanyar haɗa mutane biyu, zasu rike hannun juna, dik wanda ya kwantar da hannun ɗan uwansa shi ya yi nasara, kai da baka yi kokarin ba za'a sake haɗaka da wasu har sau uku, idan baka yi ba yau za'a ɗaga maka kafa tin da ranar farko ce, daga gobe ka sake aka yi winning a kanka zaka karɓi wani horon ne na daban!.

Sun yi wannan horo zuwa karfe 5 na yamma, daga nan aka basu hutun 30min, bayan sun huta suka ɗaura da horon daidaito, aka koya musu yadda za su tsaya da ƙafafunsu ba tare da fargaba ba a lokacin harbi ko farmaki.

Dik horon da suka yi yau Noor shi yake cariying last, kwata-kwata babu alamar zai yi abin arziki a rayuwarsu na matasan sojoji, shi fata ma yake yi a koresa daga school ɗin shiyasa yaki mayar da hankali.

Sarai Captain ya lura da shi, kuma da daddynsa ya karɓa mashi Form ɗin ya kawosa ya faɗawa G.A.T a bashi horo na musamman, dan haka shi kuma ya sanar da Captain cewa ya saka ido kan Noor ya tabbatar da cewa horo na musamman ya bashi, daddyn Noor suna da kyakkyawar alaƙa da GAT, Dan haka ya ce kada ya barsa ya yi lalaci dan renon mata ne shi.

Da misalin ƙarfe 6 aka basu horon zuciya, karatu da darussa kan jarumta, sadaukarwa, da ƙaunar ƙasa, aka zafafa masu kan batun kaunar kasa da yin komai a kan ƙasa da aikinsu, aka nuna masu cewa rai ba'a bakin komai yake ba, su kashe ko a kashesu, Captain ya zafafa masu cewa karaya ba halin namiji bane, tsoro ba dabi'a bace, jajircewa ita ce mutum, su tsaya tsayin daka dan kare kasa, ko sun mutu ƙasa zata yi alfahari da su. Sosai zafafan kalaman Captain suka fasa zuƙatan dayawa daga ciki, shi kansa Noor


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login