Showing 123001 words to 126000 words out of 365093 words

Chapter 42 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5918

intensification na haske, komai duhu in dai yana fuskansu zasu iya yin aiki kuma zasu iya ganin abu!. Sannan dik an sanya masu ɗan karamin thermal imagers, na'ura ce ta gano zafi ko a cikin duhu, idan abu mai zafi ya nufosu zai yi alerting nasu da sauri.

Sannan dikkansu an mallakawa kowannensu handheld radio dan sadarwa ga juna, ƴan rundunan zasu dinga amfani da shi saboda sanarwa ga juna halin da suke ciki, an yi masu connecting na shi dikka, in ɗaya ya yi magana dikkansu zasu ji, kuma zasu dinga karɓar umarni daga ogansu Leo, fatan kun ganesa?.

Dik da wannan sai da aka kara masu da headset with boom mic, shima dik na sauraran juna ne da magana da su kai tsaye, gudun ko ta kwana ne, ida wancan baya bada abin da akeso sai su ɗauki wannan.

An basu data mai karfi dan satarwa, an saita wayoyinsu da na'urorin su Arya. Dikka waɗan nan abubuwa fa wannan shegen rucksack ɗin nasu ya kwashesa, ga kayan sakawansu still a ciki, jakar ta cika dam, sai da aka sanya masu belt aka iya rufe jakar, ta yi mugun nauyi, amma a haka zasu ɗauka a bayansu. Mazan fama ba, soja ba dik kai ba!.

A ɓangaren Manassa an zuba mata Individual first aid kit mai shaƙe da kayan farko na taimakon gaggawa, a cikin akwai irinsu bandages, tourniquet, hemostatic agent da sauransu dan ceto ran soja da gaggawa. Sannan an sanya mata combat medic kit, kayan aikin likita masu yawa sosai kuma masu amfani da za'a buƙata a gaggauce dan jinyar raunin filin daga ƙananan zuwa matsakaita a yayin mission.

Dikkansu an basu water bladder dan su samawa kansu ruwa a koma ina suke, kuma ruwan zai zama mai tsabta har su sha su yi abin da zasu yi. Dik an basu ƙananan sleeping system mai caji da rana dan in suna barci wani motsi ya zo komai nisan shi wannan ya ankarar da su. An basu entrenching tool na karfe wanda ake haɗa shi da notika, idan sun isa wajen da zasu kafa tantina suna iya haɗa shi, kamar shovel haka yake, dan su tona rami aka basu.

Sannan dikkansu an basu gas mask wasu kuma cbrn mask, mask ne dan kare numfashi daga iskar guba, iskar sinadarai ko biological hazards dake yanki, takan iya yuwuwa akwai gurɓacewar yanayi a in da suka nufa, wannan mask zai hanasu shaƙar gubar. Sannan an basu cbrn suit mai kama da jacket, yana kare gangar jikinsu daga iskan sinadarai ko gurɓacewar yanayi. An basu cbrn hands gloves, da kuma ear protection dan kare kunne daga ƙarar makami, suna sanya shi kada su rasa jinsu saboda karar bindigu.

Su Arya jami'an computer na musamman kuma an shirya masu compass & maps gps unit a laptops ɗinsu, kuma dik abin da aka basu mai caji da rana ne, dan shi rana a ko'ina akwaisa, lantarki kuwa kun san babu, shiyasa aka masu masu amfani da rana kamar solar kenan. Sannan an haɗa masu gps enabled devices, wannan zai taimaka masu wajen daidaita matsayi daga nesa sosai. An shirya masu na'urar hangen sama, ga su unmanned aerial vehicles, ƙananan drones dan hango sama daga nesa, ga portable drone controllers dan sarrafa uvn na waje.

Uwa uba an haɗa masu counter drone systems wanda zai iya gano drones na abokan gaba idan sun turo masu, su suna iya turawa abokan gaba ƙananan drone ɗinsu, su yi control ɗinsa ya je har in da miyagun suke, suna zaune a cikin tantin da suka kafa a sansani suna kallon dik wani motsin ƴan ta'adda a laptop ɗinsu suna kwasan bayanansu suna sanarwa sojojinsu. Kai an fa shirya masu kaya dayawa, sannan aka shirya masu ɗanyen abinci, su zasu girka kayansu da kansu, su Arya aka shirya masu laptops ɗinsu a cikin rucksack, sannan aka basu bututun iska saboda faɗawa kogi ko wani rami na ruwa.

Tambayana a nan shi ne, shin masu karatu sojijin ƙasarku haka ake basu kwararrun kayan aiki a lokacin da za'a turasu faɗa da wasu ƴan ta'adda? Ko iya bindiga kawai ake basu?.

Dikkansu suna sanye da uniform a jikinsu, har da su Arya yau an basu uniform, sun kuwa yi balain kyau, tamkar dan su aka yi kayan, sun kara kwarjini da firgita makiya.

Dikka sojojin ƴan uwansu suna wajen dan yin bankwana dasu, ta yiwu su dawo a raye ko kuma akasin haka, kowa zai ga ɗan uwansa na karshe ne a yanzu. Ummie bata zo ba, dan Zaysh ya ɓoye mata, ya ce mata dai zasu shiga wani aiki, zata iya kiran wayansa ta ji a kashe idan babu rana basu yi caji ba, amma dik in ya kunna waya zai kirata. A haka ya kyaleta, dan baya son ɗaga mata hankali.

Babban soldiers eagle aka kawo dan ɗaukarsu ya yi dropping ɗinsu a bakin dajin da zasu shiga mission na farko, idan ya saukesu a wajen sai su kutsa cikin daji da ƙafarsu. Suna ta ɗagawa ƴan uwansu hannu suka fara shiga jirgin a jere cikin tsari haɗe da ɗan pareti, da haka suka shige cikin jirgin suna kallon ƴan uwansu, Leo yana ta kallon Champion and Lion da guru dake tsaye a babban filin tashin jirgin AZURE, dikkansu suna sanye da nose mask, ga katuwar jacket da suka sanya, p-cap a ciki kafin su sanya hukar jacket ɗin, sun yi kyau kam matuƙa.

Sai da jirgin su Leo ya ɗaga sannan IRON FIST suka bar barrack ɗin, suka koma hotel da suka sauƙa, ba yau zasu koma ba, dan akwai binciken da suka zo yi dan tabbatar da wata gaskiya da basu faɗi ba, so zasu ɗan yi kwana biyu a nan.

Daddy Noor ma sai da ya ga tashin jirginsu sannan ya koma gidan GAT ya hau shirin komawa US.

Su V da suka zo tafiya sai da zuciyarsu ta ɗan kaɗa, dan basu taɓa tafiya aiki ba kun sani, dole su ɗan tsorata, amma Arya yarinyar nan tamkar babu zuciya a kirjinta sai dutse, ko kaɗan bata tsorata ba, sai ma cewa da ta yi su yi sauri su tafi, dan ita ma ta shiryawa mutuwa, bata da tsoro ko kaɗan yarinyar, ita dai V ta ji kwarin gwiwa ne kawai a waje ɗaya shi ne Noor yana tare da ita, tasan dik wuya zai tsaya mata.

Manassa and Angelina kam ba'a magana, ita Manassa komai normal ne, baka gane tana farinciki ko bata yi, kamar Vash take, komai daidai ne, ko su mutu ko su rayu dik daidai ne, ita kuwa Angelina har da guntun hawayenta, wai na kewar daddynta ne hawayen, kuma karya ne, zuciyarta ne ya fara karaya, ta ji tsoron su mutu, dama a cikinsu dik ita ce mai tsoro gaskiya fiye da Manassa, tana da saurin karaya, karfin hali ai sai Arya, balai, yarinyar nan ko mutuwa ake yi ba zata fasa abin da ta sanya a gaba ba, ita ta gado daddynta sak, dan kafin ya taka matakin GAT ai sai da taurin zuciya da jajircewa, to ita dai da kwarin gwiwarta suka nufi can.

Jama'a an iso in da nike son mu iso, sojojinmu sun tafi Mission, yanzu zamu shiga ainahin labarin ZAKUNA BIYAR, yanzu zamu isa ga ainahin jigon labarin, masu hawan jini, masu low bp ayi hakuri da abin da alkalamina zai rubuta a wannan karon, na san fore sure zuƙata zasu kaɗa, hankula zasu tashi, amma amin afuwa, ilimi da farkar da al'umma nike burin yi! Sannan zan so wannan ɓangare dana kira da jigon labarin nan kada ku tsallake waje ko ɗaya, da daɗi da ba daɗi dik ku yi hakuri ku karanta, dan amfananku ne, ba karamin amfani zai yi maku ba!! Muje zuwa kan jigon labarinmu a yanzu!.

-----------------W-S-Hospital🔥

Cikin wajen tamkar ba'a duniya take ba, ta ko'ina glasses ne da wutar lantarki, zaku rantse da ALLAH dik lantarki duniya a nan wajen ake karar da shi, ko da sunan wasa wuta bata motsawa a wannan waje bare a ɗauke, jikin bangon ainahin wajen kakkafar bango ce da zaku yi zaton samudawan da ne suka gina shi ba mutane ba, dan gini ne da aka yi su da duwatsu masu karfi sosai. Amma daga ciki ko'ina na glass ne, ga kayan zamani ta ko'ina. A dunkule kenan, mu kara kutsawa ciki dan ganin meke going.

Ƙofofin wajen masu ƙarfi ne sosai haɗe da kimiyar tsaro na zamani mai ban mamaki, suna amfani da fasahar tsaro mai ƙarfi, tare da makullai na lantarki, akwai wani sashen ma da babu wanda yake iya shiga sai mutane uku, dan wajen door ɗin kuna taɓawa shocking ne a jikin, sai dai a ga mutum ya ƙandare in ya taɓa.

A gefe guda ga wani side tamkar fagen kwaje-kwaje na hospital haka aka yisa, dan ga ɗakuna da beds dayawa a side ɗin, kowani ɗaki da dalilin hasasarsa a wajen. A wani side ɗin kuma ɗakuna ne masu kyau da gadaje masu rai da lafiya na majinyata, ta kowani kusurwa akwai CCTV, a saman bene kuma akwai wani ɗaki mai cike da computer dan kula da cameras dake ta ko'ina.

Hospital ɗin yakasance da ɓangarori guda biyar, kai tsaye mu je ɗayan ɓangaren.

Wajen cike yake da glass, dik ɗakunan wajen glass wall ne, filin cike yake da dabbobi kala-kala masu haɗarin gaske, dabobin da idanu bai taɓa ganin irinsu ba, kowacce dabba tana cikin glass tamkar a gidan zoo, ga manya-manyan macizai, kunama, kifaye, kai harta cinnaka akwai wajensu, suna cikin glass, side ɗinsu yana da mugun girma sosai, kuma dik cike yake da waɗan nan dabbobi. Ɓangarorin hospital ɗin nan kowanne da abin da ya kunsa, ba zan fayyace maku me a ciki gabaɗay ba, sai tafiya ta yi tafiya, dan haka mu je zuwa, kun dai ji ɓangare na farko na dabbobi ne kawai!.

Akwai nurses dayawa a hospital ɗin, amma dikka mata ne babu namiji ko ɗaya, sai dai dik nurse da zaku gani a wajen sai kun kalleta kun sake kallo, babu munana a wannan waje, ga su da zubin ƴar tsana, sirara ga shape, farare tas-tas da su, rigarsu na aiki guntaye ne zuwa tsala-tsalan cinyoyinsu masu kama da madara saboda hasken jikinsu, suna da hakin gashin mai shegen kyau wanda suka ɗauresa a tsakiyar kai, kansu da hular aikinsu, ga su da tsabtar balai, komai nasu cikin tsantsar kula da natsuwa suke yi, one thing about them, dik wata malamar asibit dake wannan Hospital ɗin shekarunta ɗaya da sauran, dikkansu they're age mate, babu wacce ta girmi wata a cikinsu, kuma dikkansu yanzu 18 years suke da shi, sannan abin da zai baku mamaki dayawa daga cikinsu suna ɗan kamanceceniya da juna, wasu ma ida ka gansu zaka zaci twins ne, sannan sun kai su 40 a hospital ɗin.

Abin da mamaki ko? Ace shekarunsu su 40 ko sama da haka dikka ɗaya, sannan dikkansu mata ne ba maza tamkar dama zaɓosu aka yi, kai ko zaɓosu aka yi sai haka!.

To akwai dai manyan likitoci maza guda uku, sannan akwai masu gadi zaratan maza madaka karti dake sanye cikin uniform ɗinsu mai zubin overall, ga wasu dakakkun takalma a kafafunsu mai balain karfi Kai in takaice maku tsaron wajen nan wane mutum ya iya giftawa, ko tsuntsaye basa iya zuwa wannan waje, dan lantarkin dake wajen ba zai bari dik wata halitta mai rai ta gifta ta sama ko ta ƙasa ba.

Akwai benaye guda biyar daga gefe masu hawa ɗai-ɗai, sannan akwai ƙananan gidaje wa ƙannanan ma'aikatan lafiya da guards masu tsaron wajen, kamar general government hospital ne fa, kun san shi ne ake yi wa ma'aikata gidan zamansu a cikin hospital ɗin. Mu ƙara kutsawa ciki.

---------------------------🔥

Wasu matasan likitoci dake sanya cikin kayan aikinsu ne suka fito daga cikin elvator da ta tsaya a sama a yanzu, maza ne su uku da a kallan shekarunsu zai iya zuwa ɗaya kamar yadda kansu watau tsawonsu yake ɗaya, komai na jikinsu iri ɗaya ne, harta hands gloves na hannayensu da nose masks na fuskokinsu iri ɗaya ne, ankel boot dake kafafunsu ɗaya, kansu na sanye da huluna masu zubin na sanyi, suna sanye da doctors nose mask ne, wanda ya hana ganin fuskokinsu sai idanu kawai. Komai na jikinsu farare ne tas, sun fito a cikakkun kwararrun likitocin nasu

A TAƘAICE SU WAYE SU?!.

DR JAMES. surgeon dr, suna yi mashi laƙabi da likita mai gani har hanji, saboda kwarewarsa a aiki, ga iya tiyata bisa tsari, sannan akwai tsantsar natsuwa da zallar rashin yin magana, dan ko kusa ko alama baya ɗaga ido ya kalli mutane bare magana, baya dariya, kai ko fuskansa ba'a samun gani bare dariyarsa, likita ne da ya shahara a kan aikinsa over, Sai DR KAMAL, bokan turai, assistant surgeon mai gani har hanji ne, kuma halinsu ma iri ɗaya. Sai kuma DR MARK, waɗan nan uku shaƙiƙan aminai ne na gaske, suna kuma kaunar junansu sosai.

Kai tsaye a bakin wani kofa da aka rubuta P-P a jikin door ɗin suka tsaya. Na tsakiyansu watau mai DR JAMES ne ya ɗan gyara hand gloves na hannunsa kafin ya zareta, sannan ya ware yatsunsa ya sanya a jikin fingerprint dake jikin kofar. Take door ɗin ta yi scanning kafin ta buɗe kanta. Turawa ya yi, kusan a tare suka shige ciki.

Ɗaki ne tamkar ɗakin tiyata, an shirya komai da ya danganci tiyata, ko'ina tsab a cikin ɗakin, ga wani sanyin Ac dake tashi, akwai doguwar sofa mai zaman mutum uku a cikin ɗakin, sannan akwai wasu manyan kwalabe da freezers bayan gadon tiyata, gefe guda akwai drawers.

Kusan a tare suka zauna a saman wannan sofa ɗin tare da ɗaura kafafunsu ɗaya bisa ɗaya, dik cikinsu babu wanda ya yi magana da ɗan uwansa, sai DR JAMES ne ya mai da hand gloves ɗinsa tare da duba time a agogon dake manne a hannunsa.

A daidai wannan lokacin wasu nurses mata guda biyu kyawawan gaske suka shigo cikin ɗaki, suna turo wani bed. Wata macece kwance a saman bed ɗin, tana sanye ciki kayan tiyata, an shiryata tsab, da alama an yi mata komai da ake buƙata, dan ga shi tana barci alamar anyi mata alluran barci.

A daidai bed dake cikin ɗakin suka gungura gadon su tsaya, sannan suka kama matar suka mayar da ita saman gadan cikin ɗakin, a natse suka tura gadon da suka zo da shi suka fita waje. Kada ku manta dik nurse's dake cikin wannan hospital ɗin shekarunsu ɗaya watau 18 years, na kara tina maku ne dan yana da muhimmanci ku rike hakan kada ku manta.

A tare waɗan nan likitocin suka miƙe tsaye, wajen drawers ɗin nan suka nufa. Kowa ya sanya kayan tiyata, gloves, mask, gown, suka cire wanda suka zo da shi kenan.

DR JAMES ne ya umarci DR JAMES da ya je ya duba kayan aikin da nurses ɗin nan suka shirya komai yana na intact ko?. Karisawa gaban table dake kusa da gadon DR KAMAL ya yi, duba kayan ya hau yi, an shirya irinsu scalpel wukar tiyata, retractors na buɗe ciki, forceps & clamps, needle holder & surgical needle, electrocautery machine na goge jini, suction machine na fitar da jini ko ruwa, sutures zaren da ake ɗinki, sterile drapes na rufe jikin maras lafiya, catheter na fitar da fitsari.

Hannu ya ɗaga tare da ɗaga yatsa ɗaya yana yi wa DR JAMES alamar da komai yana nan yadda yakamata. A tare suka kariso wajen domin fara aikinsu.

DR JAMES ne ya fara checking na bp, pulse, oxygen, da heart rate na mara lafiyar, sai da ya tabbatar bata a cikin haɗari sannan ya sanya mata catheter dan fitar da fitsari.

DR MARK ne ya matso ya fara tsabtace wajen ciki zuwa gwiwa da ƙafa na maras lafiyar, ya yi amfani da disinfectant watau chlorhexidine. DR JAMES ya rufe maras lafiya da sterile drapes, sannan ya duba lokaci a agogon hannunsa dan ya tantance matakin da Anesthesia da suka bata yake. A natse ya ɗago ya kalli DR MARK, da sauri ya ɗauki scapel ya miƙo mashi tare da ɗaukar cutton ya matsa kusa da shi.

Ta sama suprapubic incision bikini cut ya fara yankawa a natse game da kula sosai. Ya buɗe tsoka da peritoneum har ya isa mahaifa. DR MARK ya ɗauko retractors ya miƙa mashi, da shi ya yi amfani wajen buɗe wajen sosai ta yadda zasu ga abin da suke yi da kyau.

Da fallopian tubes suka yi amfani dan gani mahaifar, DR JAMES ne ya fara da yanke ligaments da jijiyoyin dake rike da mahaifar, cikin kula sosai suke yi ta yadda ba zasu samu matsala ko su rasa wata jijiya da zai yi sanadiyar kashe mahaifar ba. DR MARK ya gyara electrocautery dan hana zubar da jini sosai.

Kun san me? Tin daga ovaries suka tsinke mahaifan nan, suka ciresa gabaɗaya, da alama wannan mata bata son ta sake haihuwa ne, domin kuwa idan ovaries suna nan za'a iya yi mata dashen wata mahaifa lokacin da ta buƙata, amma babu su yana da matuƙar wahala, a yanzu ma ba'a samu hanyar dashe ovarries ba.

DR KAMAL ne ya ɗauko wani kwalba mai kama da cikin mace DR JAMES ya sanya wannan mahaifa a ciki, suka rufe kwalbar, DR KAMAL ya karɓi kwalbar ya fita da ita ta wata kofa dake cikin ɗakin wacce zata fidda shi ta part na kwajinsu.

Kallon DR MARK DR JAMES ya yi. "Done my work!". Yana gama faɗar hakan ya bi bayan DR KAMAL ta kofar da ya fita. Binsu da kallo DR MARK ya yi, sai da suka fita sannan ya sauke ajiyar zuciya tare da juyawa ya fara ƙoƙarin karisa nasa aiki.

Rufe duct ɗin mahaifa and vaginal cuff ya fara yi da zaren ɗinki. Sai da ya ɗinke peritoneum, fascia, muscles, subcutaneous tissue, sannan fata a hankali cikin kula sosai, yana yi yana mai da idanunsa kan fuskar matar, ga idanun nasa dara-dara da su Masha ALLAH.

Bayan ya kammala komai ya duba yanayin lafiyar maras lafiyar, ya duba yanayin jininta ko tana buƙatar ƙari ko kuwa aa, ya duba bp, hr, fitsari, da zafin jiki, ya duba komai a natse, ya yi sa'a komai lafiya, dama ya tsammaci hakan, saboda sun saba wannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login