Showing 285001 words to 288000 words out of 365093 words
ka biye mace ka lalata mana aiki, yanzu ma jibeka fa? Ka biye mata ko jurar tafiya ba zaka iya yi ba sai an goyaka, dik gaɓɓanka jikinka sun mutu, ga kasala da nauyin wando"........🤯
Wasa-wasa Zaynish mafa ya iya tsiya, baya magana amma idan yana yi da Noor sai kun sha mamaki, sai ma ku zaci bashi bane yai, kuma sai ya yi magana ya fuske tamkar ba shi ya yi ba, bai taɓa murmushi ba bare dariya ko wacce iriyar magana zai faɗa. Vash dai baya tare da su a halin yanzu, yana can yana baiwa aljana hakuri.
A shagwaɓe Noor ya ce. "Ni ku kyaleni in ji da ɗaya mana, my Juliet want kill me with her sweet, na samu da kyar na shawo kaina, na danni kaina, na biyoku shi ne zaku takura mun?". Ya faɗa yana langwaɓar da kansa a gefen wuyan Leo.
"Ai zaka iya komawa ka ƙarisar da abin da ka fara, nasan ita ma tana can tana fama da abin da kake mana a nan, dan haka ka koma kawai, kuma dama ni banga amfaninka ba, ko tafiya da kafafunka baka da kuzarin yi, yanzu idan aka farmakemu fa?". Zaynish ya faɗa yana ƙara kai mashi dundu a gadon baya.
A dake Leo ya ce. "Zaysh ka yi na kuɗinka, in ka ƙara sai ka ci wahala a hannuna, babu ruwanka da my pleasure"....... Sumbata Noor ya mannawa Leo a wuya yana faɗin. "This is my brother, love you more heartbeat". Gyarasa da kyau a bayansa Leo ya yi yana faɗin. "Love you too baby".... Ƙara rukunkume Leo tightly ya yi yana ɗan sakin shirin murmushi.
Shiru Zaysh bai sake yin magana ba, sai dai ya kama kunnen Noor ya murɗa da ɗan karfi. Turo baki Noor ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shi kuwa Vash hankali ya yi nisa, ya shiga damuwa sosai ta yadda har zufa yake haɗawa, saboda aljana ta ce zata kashe Manassa a daren yau, ga shi sun barosu a sansani, ya ALLAH.
Hannu Noor ya miƙa ya taɓo Vash yana faɗin. "Vash lafiya?"...... A ɗan firgice ya ɗago, nisawa ya ɗan yi tare da cewa. "Akwai matsala bro"...... Dikkansu dawo da hankalinsu a kansa suka yi, cikin sanyin murya Noor ya ce. "Matsalar me?"......... Wayansa Vash ya miƙo mashi kan ya duba ya ga matsalar.
Karɓa ya yi, suna cigaba da tafiya farinwata tankar ta fito sosai yanzu, hakan yasa ta ƙara haskaka masu hanya sosai. Fara bin chat ɗin Noor ya yi, wani waje ya yi murmushi, wani waje ya haɗe rai, har dai ya iso kan in da take cewa daren yau zata kashe Manassa, ya duba reply da Vash yai mata, na zunzurutun magiya da ban hakuri, ya damu sosai.
Hakan ne ya ɓatawa Noor rai, sai ya ce gaskiya ba zai iya barin Vash a cikin damuwa ba, dan haka zai faɗa mashi gaskiya, miƙa mashi wayan ya yi yana faɗin. "Aljanar zata kashe kanta kenan?".
Cike da mamaki Vash ya ce. "Me kake nufi?"....... "Manassa da ita kake wannan chat ɗin ai, tin ranar na san da haka, na ɗauka zata cigaba da zolayarka irin na masoya ne kawai shiyasa na rufa mata asiri, ban zaci zata jefaka a damuwa ba, tin da haka ne bari in faɗa maka ita ce".
Ina Vash bai yarda ba, sai ya fara girgiza kai alamar kai ba ita bace, a dake Noor ya ce bari in tabbatar maka. Wayansa ya fitar, ya kira number V, bugu ɗaya ta ɗauka, dama ta koma ɗakinsu ta ɗauki wayar. Tana ɗauka ta shagwaɓe murya da cewa. "My Romeo, har yanzu baka dawo ba".
Ai wani sabon feeling ɗinta ya ji, a sanyaya ya ce. "Ina dawowa yanzu, ina son ki mun wani abin ne yanzu"..... Ƙara shagwaɓe murya ta yi wajen cewa. "Me kenan?"......... "Jeki ari wayar Manassa yanzu, kada ki faɗa mata me zaki yi da ita, ki karɓo ki zo cikin tantina ke kaɗai akwai abin da zaki mun da shi"..
Da okey ta amsa tare da miƙewa ta fita, jim kaɗan ta dawo game da cewa. "Ga wayar a hannuna"....... Hannu ya miƙa ya karɓi wayar Vash kafin ya sanya wayansa a H-free ta yadda Vash zai ji komai kafin ya kaluɓo number Vash ɗin. "Shi ga contact ki saka wannan number da zan kira maki yanzu". Da okey ta amsa. A natse ta shiga.
Number Vash ya fara kira mata ta fara shigarwa kenan sai ta ce. "Akwai number a wayar, gata ta fito da saving my flower"....... Ɗago idanu ya yi ya kalli Vash kafin ya ce. "Shiga Whatsapp ɗinta ki nemo mun member". ....... Da sauri ta shiga, sai ta ce. "Number ce a sama, da ita take chat yanzu".
"Okey to shiga kan number ki yi clicking voice, a cikin voice ɗin ki ce I am mrs Noor ya wadatar"....... A natse ta aiwatar da abin da ya ce, bata tambayesa me dalili ba, saboda tasan haka kawai ba zai tsaya wannan dogon magana ba.
"Na yi na tura". Ta faɗa.….... "Okey to goge voice ɗin yazama tamkar ma baki shiga kan chat ɗin ba". Da okey ta amsa kafin ya aiwatar da abin da ya ce, daga nan ya ce mata. "Je ki mayar mata da wayar, yanzu zan dawo ba jimawa, wait for me don't sleep"........ "Okey my Romeo, love you more"...... "Love you too". Kit ya kashe kiran tare da miƙawa Vash wayansa dan ya duba voice ɗin.
A hanzarce ya karɓa, aikuwa yana dubawa ita ce, tabbas ba aljana bace Manassa ce, aikuwa ya ce zai yi mata tsiya shi ma, ba zai bari ta gane ya gane ita ba aljana ba ce, su cigaba da tafiya haka, ranar da zai damketa yana nan zuwa, zata san ta taɓo jinin Champion na IRON FIST, yadda ta dinga bashi wahala yana magiya ba zai kyaleta haka ba.
Daidai lokacin suka isa bakin tekun nan amma ta can nesa da tantinsu, wani ɓangare ne da ake sauƙe ƙaya, amma ba ainahin in da ake sauƙe kayan bane, nan wani gefe ne kamar na sirri wanda ba kowa yasan ana sauƙe kaya a wajen ba, watau idan jiragen ruwan suka kusa isowa madakata in da ake sauƙe ƙaya, sai su ratse hanya, su ratso gefe can nesa daga in da ake sauƙe ƙaya, sai su dakata a wannan waje, kuma jiragen ruwa basa wannan ratsen sai tsakar dare, suna tsara tafiyarsu yadda sai dare zasu kusa isa madaka in da ake sauƙe ƙaya.
Tin da suka doso wajen wasu mahaukatan karnika suka fara haushi da karfi-karfi, alamar securitys dogs ne, waɗan da aka horar da su dan gadi, kun san su dik yadda suka ji motsi sai sun yi haushi. Aikuwa suna wannan haushin wasu kartin maza suka fara firfitowa daga cikin jiragen ruwan dake faffake a bakin ruwa, wasu ma ba'a sauƙe lodin kayan dake kansu ba.
Maza ne mada karti da a ƙallah zasu kai 30, dikkansu yawancinsu babu riga a cikinsu, suna murɗe sosai, dama kun san tsaron irin wannan waje sai masu rai da lafiya game da jini a jiki ake baiwa, dan kome zai zo su iya tarewa.
Hannayensu rike da gabza-gabzan torchlight masu masifar haske, suna wani bubbuɗewa suka fito da nufin su ga su wanene?......... Ganin haka yasa Leo ya ce. "Is time for game"...... Yana faɗar haka tin bai rufe baki ba Noor ya diro ƙasa daga bayan nasa. Da gudun gaske suka dare suka rabu.
Dik suka kama wajen ɓuya, wasu suka ɓuya bayan kwantainars, wasu kuma bayan jiragen ruwa. Haske ko'ina waɗan nan karti suka fara yi suna wani irin numfashi irin na gardawa. Kewaye lungu da saƙo suka fara yi da haske, while dik in da suka yo sai sojojin AZURE sun kauce sun ƙara ɓuya.
Wani shirgegen ƙato ne ya zo ya wuce saitin in da Noor ya laɓe, ya wuce gaba yana haske-haskensa. Ai yana wucewa Noor ya fito, dik da baya jin kuzari a jikinsa, haka ya bi bayan mutumin, yana zuwa ya sanya hannunsa ya shaƙo wuyan mutumin ta baya, ya matse da hannu ɗaya tare da sanya ɗayan hannun ya toshe mashi baki.
Fafutuka ya fara yi yana neman yadda zai kwaci kansa, sa dai ina, renon AZURE ba wasa ba, sai da Noor ya kaisa ƙasa, sai da Noor ɗin ya tabbatar baya numfashi, sannan ya sakesa tare da karɓar light ɗin hannunsa, ya kasheta game da turata cikin aljihu kafin ya damƙi ƙafar mutumin, ya ja shi a ƙasa tamkar kayan wanki, bakin ruwa ya kaisa ya jefar sannan ya dawo ya laɓe.
A daidai lokacin shi ma Zaynish ya muɗe wuyan wani da ya zo ta kusa da shi, aikuwa yana dab zai haskasa Zaysh ya yi kukan kura ya danke wuyansa, ya murɗe ya karyeta. Yana karyewa Noor ya sake damke wani, shi ma murɗe mashi wuya ya yi ya karya. A tare Leo da Zaynish suka damki wasu biyun, dikkansu murɗe masu wuya suka yi suka karya. Daidai lokacin shi ma Vash ya damƙi wani shirgegen ƙato, ya murɗe mashi wuya.
Faɗar ta koma yaƙin sunkuru, suka dinga yi masu ɗauki ɗaiɗai har sai da suka kashesu tas, sannan suka kutsa cikin kwantainars ɗin. Har lokacin karnukan suna haushi, sun bi dik wanda suka kashe sun ɗauke torchlight ɗinsa sun kashe. Nufar in da suka ɗaure karnukan a jikin wata bishiya Leo ya yi, ya je da nufin ya kashe karnukan, amma sai ya ga suna da mugun kyau sosai, irin manya-manyan karnukan nan ne masu tulin gashi a jiki, ga su farare tas, hakan yasa suka burgesa, su biyu ne, ɗaya gashin jikinsa har yana jan ƙasa, ɗaya kuma bai ƙarisa kai na wancan ba, bujumaye da su tamkar zakuna.
Shafa kawunansu ya yi, hakan yasa suka yi shiru, sai ya wuce ya kyalesu da nufin idan sun gama abin da ya kawosu zai kwance karnukan su wuce da su.
Gaban wani ƙaton kwantaina suka tsaya, hannu Leo ya sanya wajen jikin container, sai ya ga alamar gari-gari. Tsanin dake jikin container ya kama ya hau, Noor na rike da light yana haska mashi, ya haye zuwa wajen da aka sanya sarƙa aka ɗaure container sosai. Ƙasa ya sauƙo, suka shiga cikin wata jirgin ruwa, a nan ya samu almakashin tsinka sarƙa.
Dawowa ya yi, Noor na haska mashi haske ya sake hayewa sama, karfi yasa ya datse sarkar, sannan ya sauƙo, Zaynish da Noor suka haɗu suka buɗe marfin container. Dallah light a ciki suka yi. Kaya ne shirye a cikin kwalaye, an shiryasu datsan-datsan. Leo ya ce Zaynish ya sauƙo da kwali ɗaya su gani.
Ba musu ya sauƙo da shi, suka farka bakin suka buɗe. A tare suka ɗago suka kalli juna, wasu irin sinadarai ne na haɗa ƙananan boma-bomai, shegen tsada ne da waɗan nan sinadaran. Kai kawai Leo ya jinjina, bai yi magana ba, ya ɗauki almakashin ya matsa zuwa container na gaba, ya datse sarkar da aka rufeta. Zaynish da Vash suka buɗe marfin, while Noor yana ƙoƙarin rufe kwalin sinadarin boma-boman nan, a matsayinsu na sojoji dik wannan karatu sun san shi, hmmmmm su suka san me aka shirya a wajen, shiyasa kuka ga Leo ya girgiza kai kawai.
Suna buɗe container na biyun kuwa kwalayen drugs ne a cike a ciki. Leo ya ce Vash ya sauƙo da kwali ɗaya. Da sauri ya sauƙo da shi. Buɗe kwalin suka yi, wasu irin magunguna ne wanda aka ɓuye ainahin manufar drugs ɗin, aka ɓuye ainahin daga ina suke, a jikin kwalin maganin an rubuta made in Avaris, amma sai ga shi sun kama maganin a bakin tekun shigo da shi ƙasar, kunga kenan dama daga waje ake shigo da su aka ɓoyewa ƴan Avaris gaskiya, aka ce a ƙasar ake haɗa masu.
MAGANIN ME?. Mu haɗu a page na gaba dan jin wani irin magani ne? Gaskiya mutanen ƙasar Avaris suna ganin rayuwa, daga ganin wannan magani ba gaskiya aka ƙullah ba, saboda an rubuta cewa a ƙasar ake haɗa maganin a jikin kwalin, to ga shi kuma ashe daga waje ake shigo da shi, ya ALLAH! Ana cutar da su dayawa, ALLAH sarki, idan gaskiya maganin ya ƙunsa ba za'a ɓuye daga in da ake haɗa shi ba!.
Littafin nan jinsa nike tamkar true life story, kamar rayuwar gaske......😭💔
https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-40-by-princess-teema
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
[10/01, 9:16 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-22.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Dedicated to all Aryan and Zayra'an fans.🫀♥️
E_____________ 40
DEATH OR LIFE. (DOL)
Waɗan nan wasu magunguna ne da ake yi wa yara da sunan rigakafi, amma batu na gaskiya magunguna ne dake kashe garguwar jikin yara, tin yaro yana ƙarami zasu kashe mashi garkuwar jiki, hakan zai sanya jikinsa zata yi saurin karɓar kowacce irin cuta ce ta shigo, sannan jikinsa za yi wahalar karɓar magani.
Kuga yaro yana ciwo ayi ta magani amma dik na banza, sai kuga kamar ba'a mashi komai, kuma ko sun girma jikinsu ba zai dinga karɓar magani ba, already an kashe masu garkuwar jiki tin suna yara, ba wanda zai zaci cewa maganin matsala ce, za'a ce rigakafi ne kawai, hmmmm bayan rigakafi babban cutarce a wajen.
Al'ummar ƙasar Avaris sun gagara gane wani abu ɗaya, babu ta yadda za'ayi gwamnatinsu ta basu abu kyauta, kuma ta dinga binsu har gidaje da sunan yi masu, idan gaskiya ne a bisu gidaje ana raba masu kayan abinci da jari da ake cewa ana fitar masu mana, meyasa idan sun fitar da tallafin gwamnati sai dai su ce ka je ka cika form, ka bi layi, ka yi kaza, ka yi kaza?.
Amma shi rigakafi za'a bisu har gida ne ana masu, har da rabawa yara sweet ko wani abin makamancin haka idan sun yi, kai mutanen cikin Avaris wani lokaci tamkar an toshe ƙwaƙwalwalensu, abin takaici sun kasa ganewa, wlh tallahi gwamnatinku ba zata taɓa binku in da kuke ta baku abin arziki ba, sai in cuta, cuta ce wannan za'a biku ko'ina a lallaɓaku, har kuɗi zasu raba maku dan ku yarda da su, da yake cutarku za'ayi, wlh dik wanda ya ci abin gwamnatin kyauta yasan akwai abin da zaka biya da shi, waɗan nan mutane nasa bada abu haka kawai, sai da babban dalili! Ku rubuta wannan ku ajiye.
Ya rabb, ya ALLAH, ALLAH ka karkato da hankalin jama'ar annabi, ka ganar dasu! Musamman iyaye mata, sune ke bari anaiwa yara wannan gayyar tsiya, basu san cutar da rayuwar yaransu suke yi ba, da anyiwa yaro sau ɗaya shikenan an gama da garkuwar jikinsa, ya ALLAH ko shekara ɗari zai yi a duniya jikinsa ba zata dinga karɓar magani ba, sai dai ya samu sauki daga ALLAH, amma in bai da lafiya kun dinga kashe kuɗi a banza.
Zubawa maganin idanu Leo ya yi, sai da ya karance rubutun jiki kaf, sun ɓoye ainahin manufar maganin da rubuce-rubuce na karya. Nisawa ya ɗan yi tare da zarar magani guda ya zura a cikin aljihunsa, ya sanya su Zaysh suka mayar da sauran a cikin kwali, da alama bincike zai yi a kan wanda ya ɗauka.
Wucewa container gaba suka yi, a nan ma shi ya buɗe container. Ya rabb, Tramadol mai karfi sosai a cikin wannan container, waɗan da basu san me Tramadol ba, wani maganani da ake shigo da shi daga India, China, Pakistan, ana sayarwa da sunan maganin cuta amma batu na gaskiya wannan magani yana haddasa lalacewar kwakwalwa, im kasha sosai yana sanya hauka, tashin hankali, mantuwa, ga sa jaraba sosai.
Leo sai da ya ɗan girgiza ganim waɗan nan uban tulin kwalin Tramadol ɗin nan, katon container irin wannan cire da manyan kwalinsa, ya rabb. Umarni ya baiwa su Noor da su mayar su rufe, sannan ya wuce gaba. A nan ma da kansa ya buɗe container.
Ya rabb Codeine Syrup ne a cike a ciki. Codeine a idanun al'umma ana kiran sa maganin tari, amma ana sha ne dan maye, kuma mugun illatar da lafiya yake yi. Yana lalata hanta, hassasa matsalar numfashi, mutuwa idan an sha fiye da misali, manyan ƙasashe da dama sun haramta shigo da shi ƙasashensu, amma Avaris ta zama kwanton sharar ƙasashen dake son cin karensu babu babbaka, komai shigo masu da shi ake yi, saboda ƴan ƙasar har yanzu a kwance suke, sun ki tashi su farka su fatattaci dik wannan abin su tsabtace kasarsu daga gurɓatattu!.
Kai kawai Leo ya jinjina game da cewa su rufe su shiga wata container. Haka kuwa aka yi, suka mayar suka rufe, suka wuce container na gaba.
A wannan container na gaban cike yake da fake drugs, copyn magungunar gaske kenan, sunayensu da komai tamkar na gaske, sai dai ko kaɗan babu sinadarin magani a ciki, sai dai sinadarin guba mai cutarwa ne a ciki. Waɗan nan magunguna suna sanya ciwon koda, ciwon hanta, mutuwa a hankali, ka je sayen magani dan ka samu lafiya, sai a ƙara maka wata cuta, ya ALLAH kana ganin al'ummar annabi yadda ake yi mana, ya ALLAH ba zamu iya ba, sun fi karfinmu amma basu fi karfinƙa ka ba, ya ALLAH ka kawo mana ɗauki.
Wucewa container gaba Leo ya yi. Wannan container shi kuma cike yake tab da manpower, king power, double action da makamantansu, ina maza masu shan man power? To albashirinku! Kuma ga naku ta iso! Dan balai ba zaka zauna yadda ALLAH ya ajiyeka ba, to ai zaka shawa kanka balai. To waɗan nan magunguna da ake shigo dasu da sunan man power ba