Showing 6001 words to 9000 words out of 365093 words

Chapter 3 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5858

kansu a nan ake horasu cikin sirri ba tare da sanin duniya ba!.

Katafaren gate ɗin farko na shiga. Gate ɗin dakakkiyar ƙarfe ce mai ƙarfi tare da tsarin tsaro na zamani mai matukar ban mamaki, akwai kamar CCTV mai karfin gani daga nesa kilomita 5, da na'urorin tantance mutane wato biometric scanner wanda in dai zaka gifta wannan gate ɗin to sai ta yi scanning ɗinka ta turawa ɗakin da jami'ai na musamman ke kallon shige da fice na Barrack ɗin. Akwai katafaren office a bakin gate ta ciki dan karin masu gadin da zasu tarbi masu shigowa!.

Mu kutsa ciki ta shinfiɗaɗɗiyar titin da ta miƙe tin daga gate na farko har izuwa can cikin Barrack ɗin, ta ko'ina ka juya a cikin barikin nan dakakkun jiga-jigan jami'ai ne ke shawagi, ga fuskokinsu sam babu kyan gani saboda yadda suka ɗaure tamau, suna wani muzurai tamkar ba mutane ba!.

Manya-manyan gine-gine ne masu balain kyau a cikin wannan bariki, har da upstairs masu matukar tsayi dan manyan jiga-jigan sojoji. Akwai babban parade ground, babban fili mai ɗaukar mutane da yawa dan horo da taruka. Filin ya kasance da tsananin kyau tare da alamomi dan sauƙaƙa atisaye. Ga abubuwan training daban-daban a cikin wannan waje.

Yankin da offices na jiga-jigan soja yake watau headquarters yana gefe guda cikin tsari da tsaruwa. Office ɗin The General Of The Army, watau shugaban dikkan sojoji kenan, daga kansa babu wata muƙami a soji, office ɗinsa babban gini ne mai ɗauke da offisoshi daban-daban dan manyan Generals na soji kamarsu Brigadier General, Lieutenant General, Major General, General, Colonel, Captain da dai sauransu. Kowani office cike yake da kayan more rayuwa dan jin daɗisu suma. Dik wanda bai san ya barikin soja take ba to yau zai sani.

Akwai katafaren Training Academy, watau makarantar horarwa. Babban gini mai cike da ɗakunan karatu, laboratories, da ɗakunan nazarin makamai. A gefe ga filin horar da dabarun yaki da training na jiki. Ga tsarin dijital dan koyarwa, akwai allunan zamani irinsu smartboards da na'urorin koyarwa ta yanar gizo kai tsaye.

Gefe guda akwai katafaren masaukin sojoji watau Barracks. Ƙayatattun ɗakuna masu tsabta da kyau, tare da kwanciyar kula ga sojoji ko ɗalibai na musamman masu bincike tamkar aljanu, yadda kuka san hostel haka Academy ɗinsu yake, ɓangaren mata daban ɓangaren maza daban, ga tsari mai kyau. Gidan kowane soja mai muƙami ba wai ɗalibai ba ya kasance tare da wutar lantarki, ruwan famfo, da tsarin ɗumama ko sanyaya wuri.

Daga gefe can kuma akwai Military Hospital. Babban asibiti mai ɗauke da dukkan kayan aiki tamkar a wajen barrack, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan tiyata, da ɗakin kulawa na musamman watau ICU. Likitoci da ma'aikata masu kwarewa amma dikkansu sojojine, kuma su ake yiwa lakabi da surgeon Brigadiers ko surgeon Generals, to su ne likitocin sojoji.

Sannan akwai sports complex, filin wasanni daban-daban kamar na kwallon kafa, kwando, da gudun tsere. Wurin motsa jiki watau gym na zamani tare da kayan zamani.

Sai uwa uba wajen obstacle course, filin ne da aka tsara dan gwaje-gwaje da horaswa na sojoji kamar hawan igiya, gudun duwatsu, da tsallake rami, ko shiga ruwan teku, daga jin wanna abin da na kirga nasan kun gane ya yanayin wajen yake, cike da duwatse, tsaunika, bishiyoyi da kuma teku a gefe, shi a can nesa da barrack ɗin yake, dik a ciki ne, amma yana da nisa da wajen da sojoji suke rayuwa.

Kada mu yi tuya mu manta da albasa, akwai mess hall, watau wajen cin abinci kenan. Babban ɗakin cin abinci mai iya ɗaukar mutane da yawa. Kayan more rayuwa kamar ɗakunan girki na zamani masu manya-manyan gas, da tsarin rarraba abinci cikin tsari da natsuwa.

Sannan akwai armory and tech hu, waje ne dan ajiya da gwajin makamai, kamar irin su drones na yaki haka da sauransu, nasan tin daga nan zaku gane girman wanna GIDAN SOJA ya wuci yadda na faɗa a bakina ko? Sannan a cikin armory tech hu akwai gefe da aka tanada dan bincike da kirkire-kirkiren kayan fasaha na soja. Ina daurewa ne in yo maku bayanin komai dan ba zan sake dogon bayani a kan Barrack ɗin ba, Sannan kusan yadda yake da kyau idan ina rubutu kan wani ɓangare ba sai na sake tsayawa dogon bayanin yadda yake ba.

Security control center, wannan ba sai na yi magana ba tin da na ce maku waje ne da ake yaye gifted jami'ai nasan kun san tsaron wajen ai ba'a magana.

Muleƙa senior officers quarters. Gidaje masu kyau tare da kayan more rayuwa ga manya-manyan mukaman soja. Harabar gidan kowani babban jami'i ta kasance mai tsabta da shuke-shuke masu kyau dan morewarsu suma, ba iya yaki kawai aka sansu da shi ba.

Lastly akwai recreation center, wajen nishaɗi a yayin hutun aiki, akwai irinsu sinima, ɗakin wasa na zamani, da wurin zama dan shakatawa a lokacin da ba lokacin aiki ba. Lambunan zamani da shuke-shuke masu kyau dan ƙara kyawun wuri, fitillu masu kyau a kowanne ɓangare dan inganta tsaro da kyau, wutar lantarki 24h ba ɗaukewa. Hanyoyi masu kyau da babu gargada, da alamomi na kwatance watau alamomin nambobi a kan titin. Dik wani barrack na kasashen ƙetare haka suke gwanin ban sha'awa da burgewa. Bari in yi tambaya! Shin ya barrack na kasarku take? Wani tsari aka yi wa sojojinku dan suma su ji daɗi kamar kowani ɗan kasa? Wani irin yanayi ake barinsu a ciki? Suda suka sadaukar da rayukansu saboda kare ƙasa, al'umma da dukiyansu, wani irin sakayya ake yi masu?. ALLAH YA TSARE MANA KU SOJOJINMU YA INGANTA AIKIN NAN NAKU!.

------------------------🔥

Yau takama Monday, dubbannin sojoji ne suke shawagi a ko'ina, tamkar za'ayi yaƙin duniya ta uku, sai kai komo suke yi, kowanne ka ɗaga ido ka kalla ba zaka sake sha'awar kallonsa ba, dan sai hantar cikinka ta kaɗa, idanunsu jajir kamar wuta, sai wasu muzurai suke yi, ga jiga-jigan makamai rirrike a hannayensu.

A gefe guda kuma ga matasan sojojin da aka ɗauka cikin satin nan dan horarwa, kowani matashi yana shirye cikin kayansa masu balain kyau, dik sabbin matasan da suka zo suna tsaitsai ne a cikin tsakiyar assembly hall ɗinsu, kowani matashi ka ɗaga idanu ka kallah zaka gansa cike da tsantsar muradinsa na son wanna aiki game da kwarin gwiwa, dayawansu suna tsaye ne da abokansu, wasu zaka gansu group uku, wasu su huɗu a wajen, wasu ma su biyu, sai hira suke yi, kuma dikkansu suna sanye da p-cap na sojoji a kansu, kowa jinsa yake yi a sama yau, suna jin tamkar sun zama sojoji, dan dik wanda yake wajen burinsa kenan.

TO ALLAH yasa kuna da rabon haye atisaye ku zama sojojin da kuke fata, kuma ALLAH yasa aikin ya zame maku alkhairi har ku yi alfahari da shi!.

Lokaci guda dikkan sojojin hankalinsu ya tattare izuwa kan hanyar shigowa hall ɗin sakamakon karar sautin tsaro da suka ji yana tashi alamar an dinfaro hall ɗin. Kan ka ce me kuma sun jera line by line tamkar assembly a primary school, sai dai tsayuwarsu cikin jarumta da karfafa kai ne.

Wani kyakkyawan matashi fari tas da ba zai wuci 33 years haka bane ya shigo cikin hall ɗin, sanye yake cikin kakinsa, kana ganinsa kaga jarumi dakakken namiji, fuskansa babu annuri babu alamar wasa, kai tsaye kan stage dake hall ɗin ya nufa cikin takun dake nuna lallai jininsa a tafashe yake. Yana hawa ya furta attention babu wasa yana kara haɗe rai. Da karfi suka buga kafa ɗaya a ƙasa game da sara mashi, wannan ma yana daga cikin dokokin GIDAN SOJA da suka karanta kafin su zo nan.

CAPTAIN ONBISH CO shi ne sunan dake a gaban uniform ɗinsa.

Captain kallonsu ya fara yi one by one yana karawa kamar yana karantar wani abin a tattare da su kuma kamar yana karantar yanayinsu. A daidai wannan lokacin commander ya shigo, shi ma cikin jarumta da nuna kwarin jiki, amma shi zai iya kai 43 to 45 years haka. A saman stage ɗin shi ma ya zo ya tsaya yana kallon yadda matasan sojojin nan suke a tsaitsaye cikin ƙamewa, ya ji daɗi har cikin ransa, dan tin daga kan yanayin tsayuwarsu ya fahimci suna da zumman cinwa abin da suka sa a gaba. Hall ɗin nan gabaɗaya kewaye yake jiga-jigan sojoji jaruman gaske.

Captain ne ya ɗaga hannu ya sarawa Commander cikin girmamawa da kwarewa a aiki. Sara mashi Commander ma ya yi kafin ya juya ya fuskanci matasan nan, a take suma suka ɗaga hannu suka sara mashi, jinjina masu kai ya yi kafin cikin kakkaifar harshe ya ce. "Attention!". Kafa ɗaya suka sake bugawa a kasa da karfi tare da kara kamewa kam!.

"1, 2, 3 start". Commander ya sake faɗa cikin ɗaga muryar!.

Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA da suke yi a kowacce safiya kamar haka...... "We march through fire, through storm and rain, With steel in heart, we bear the pain. For land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall.
Oh, we rise, we fight, we stand as one,
Through darkest nights, til battle's won.
With fearless hearts, our banners wave,
We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground,
A thunderous beat, a mighty sound.
No chains can break the will we hold,
Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, Our oath is strong, we'll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one,
Through darkest nights, til battle's won.
With fearless hearts, our banners wave,
We are the strong, we are the brave!".

Bakinsu a haɗe suka rera wanna zazzafar taken nasu, dan yana rubuce cikin document ɗinsu, kafin su zo sai da suka haddace taken da dik wani dokan soja.

Suna kai karshe suka daddage suka buga kafa ɗaya tare da sarawa manyan nasu. Watau tun da suka fara rera wannan take dik wani soja dake AZURE sai da ya miƙe ya kame a in da yake, wannan take nasu yana sanya sojojin su ji tamkar a filin daga suke, yana balain kara masu kwarin gwiwa, motsa zuƙata da gangan jikinsu da tsumasu yake, ga shi assembly hall ɗin akwai las speaker a ciki da in suna taken dik wanda yake cikin GIDAN SOJA sai ya ji, hakan zai sanya su mimmiƙe su tsaya cak game da sanya hannu a goshi alamar girmamawa ga GIDAN SOJA GIDAN WUTA!!!!. Idan aka kamaka ana rera taken baka miƙe ka ƙame saboda girmamawa ga taken ba ma sai ka sha horo sosai! Haddace taken wajibi ne a gareka!.

Bayan sun kammala suna sauke ajiyar zuciya a hankali hankali ne Commander ya ce "Ina yi maku barka da zuwa AZURE BARRACK, Ina fatan zaku mai da hankali a kan aiki yadda yakamata?".

Dik cikinsu babu wanda ya yi magana, tamkar saƙaguna haka suka ƙame, doka ce baka isa manya suna magana ka yi magana ba tare da an baka izini ba.
Kallon Captain Commander ya yi ba tare da ya yi magana ba. Da sauri Captain ya matsa gaba tare da fara magana cikin tsantsar jarumta. "Nasan kun san dokokin GIDAN SOJA, amma zan sake tinasar daku kafin mu bada umarnin zuwa mataki na gaba". Ya ɗan dakata yana kallonsu. Still ba wanda ya motsa a cikinsu.

"Doka ta farko a GIDAN SOJA shi ne biyayya ga manyan Hafsoshi sojoji wajibi ne a kanku, bin umarnin manyan ba tare da gardama ba, ba shawara bace, wajibi ce! Ana buƙatar sojoji su kiyaye dokokin soja da na ƙasa bakiɗaya, abu na biyu shi ne shaye-shaye, an haramta amfani da miyagun ƙwayoyi da barasa a yayin aiki. An hana sata, cin hanci, fyaɗe, da sauran manyan laifukan da nasan kun sansu kuma kun karanta kundin dokokinmu, tunatarwa nike kara yi maku, dan a GIDAN SOJA dik wanda ya karya doka kun san sauran, to gargaɗi ne da jan kunne mai karfi a matsayin na sabbin sabbin ɗauka".
Ya ɗan ja numfashi kafin ya cigaba. "Sai doka ta gaba shi ne yin aure ba bisa ƙa'ida ba. Sojoji suna da ƙa'idoji kan lokacin da za su iya yin aure, misali, a wani lokaci baya an tsare wata soja da ta amince ta auri mai bautan ƙasa (NYSC) ba tare da izinin manyanta ba, aka tsareta a prison na soja saboda ta karya dokokin soja kan aure, nasan kun samu wanna labarin a document ɗin da aka baku, sojoji suna da lokacin yin aure wanda sai sun karɓi umarni daga sama! Ba raɗin kansu suke yi ba". Dakatawa ya ɗan yi yana mai da numfashi kafin ya cigaba da cewa.

"Horon fisika da na Ilimi wajibi ne a kanku, sojoji dole ne su halarci horo na jiki da na ilimi dan inganta kwarewarsu. Dole ne sojoji su kula da tsabtar kayan aikinsu da muhalli. Ana buƙatar sojoji su kasance a shirye dan kowane aiki a kowane lokaci. Yin ritaya daga aiki yana da tsari da dokoki da dole ne a bi. Sojoji da suka karya dokoki suna fuskantar shari'a a kotun soja dake cikin Barrack ɗin nan. Wannan shi ne dokokin GIDAN SOJA, fatan kun ji da kyau?". Ya kai karshen maganar yana rarraba idanunsa a kansu.

Nisawa ya ɗan yi kafin ya cigaba da cewa. "A yau zaku karɓi manyan allurorin da ake yi wa dik wani sabon ɗalibin soja na kariya da sauransu, cikin alluran da zaku karɓa sun haɗa da allurar rigakafin cutar tetanus da diphtheria Tdap, waɗanda ka iya zama haɗari ga rayuwar soja, wannan allura ana yi wa sojoji a lokacin horo na farko kamar ku kenan, idan aka yi maku yanzu kuma sai bayan shekaru 10 za'a sake yi maku. Allurar na biyu kuma shi ne rigakafin cutar hepatitis A da B. Alluran yana kare hanta daga ƙwayoyin cutar Hepatitis A da B. Allura na uku shi ne allurar meningitis, watau meningococcal vaccine, yana kare kai daga cutar kumburin kwakwalwa watau meningitis, abin da yasa za'ayi maku shi dan horon da zaku fuskanta, gujewa ƙwaƙwalenku su kumbura ko su taɓu. Sai Rigakafin zazzaɓin cizon sauro watau yellow fever, yana kare sojoji daga wannan cutar da ake samu a yankunan tropic, musamman a Afirka da kudancin Amurka, so aikin zai iya kaiku ko'ina, dole ayi maku wannan alluran". Ya dakata yana ɗan nisawa.

Commander ne ya karɓi zancen da cewa. "Waɗan nan su ne alluran da zaku karɓa a yanzu, dan haka ku shirya". Ya kai karshe yana dawo da kallonsa kan wasu zakwakuran sojojin dake gefe suna kallonsu, basu shiga cikin line ba, horarrun jami'ai ne ta ɓangaren harbi, basu da wasa.

"Ku shigo da surgeons generals and nurses yanzu". Captain ya faɗa a dake. Daddagewa sojoji biyun nan suka yi suka sara mashi kafin su nufi gate na hall ɗin. Jim kaɗan suka shigo tare da malaman asibiti da surgeons brigadiers. Nan Captain ya umarci matasan sojojin nan da su gyara tsayuwarsu da kyau su kuma ɗage hannun rigarsu sama dan dikka alluran a damatsan hannu za'a daddanna masu.

Haka kuwa aka yi, dik suka gyara suka tsaitsaya da kyau, nurses ɗin nan suka hau bin line by line suka fara yi masu alluran. Abin ku da jarumai, tamkar ba jikkunansu ake fasawa a danna alluran nan ba, suna tsaye kyam tsabar ma sun sanya aikin a ransu.

--------------------🔥

A yayin da dikka wannan abin yake faruwa su kuma manyan zaratan general's na sojoji suna can cikin COMMAND HQ suna tattaunawa dangane da yanayin tsaron kasar Avaris, taro na gaggawa ne suka shiga. To mu leƙa Command HQ ɗin mana mu ga me suke tattaunawa, dan yana da amfani a garemu kwarai da gaske..

COMMAND HQ.
Ɗakin meeting na sirri na AZURE, bangon ɗakin ma Soundproof, common view bulletproof ne wanda babu wani bullet da zai iya fasashi, dik da ya kasance ɗaki ne mai matuƙar tsaro, amma an saka bulletproof glass sosai saboda tsaro, ga na'urorin leƙen asiri da ke bin duk motsi waɗan dake ciki da waɗan dake waje ko in ce tunkaro ɗakin.

Wurin yana da ƙofar shigowa ɗaya da kuma ɗakunan bincike guda biyu kafin a isa ciki. Kai bincike sosai fa ake yi kafin kowa ya shiga, ma'ana kafin manyan Generals ɗin ma su shiga, sai an binciki ID, fingerprint, retina scan. Sannan ga wasu jiga-jigan sojoji guda biyu masu rike da jiga-jigan bindigogi suna tsaye a ƙofar ɗakin ta ciki da waje, ma'ana biyu ta ciki biyu ta waje, sai ka rantse da ALLAH sojojin nan basa numfashi saboda yadda suka kame kam.

An kunna jammer na'urorin hana leƙen asiri, anti-drone radar, da surveillance 360 wacce ko yaya aka motsa dan leƙen sirrin cikin ɗakin sai an gano mutum, ko wata na'ura ka tura dan leƙen asiri jammer sai ta ganota. Daga nan zaku san ba ɗakin wasan yara bane a wajen! Kuma ƙananan kai basu zuwa wannan waje!.

Manyan Generals na zaune a saman chair na table dake zagaye da ɗakin, irin round table ɗin nan ne, sannan a saman tables ɗin gaban kowani chair akwai sunan jami'in da zai zauna a wajen, wani ɗan karamin sing post ne da sunanyesu.
Shugaban sojojin watau THE GENERAL OF THE ARMY THOMAS (G.A.T) yana zaune a tsakiya ta gaba, sauran Generals na a gefen dama da hagunsa bisa rank ɗinsu.

A tsakiyar round na table ɗin ga jagorar rubuce-rubuce, da sashen bayanan leƙen asiri, da kuma wani soja mai ɗaukar hoto da recording idan an buƙata. Ƴan jaridu basu isa shiga wannan waje dan ɗaukar bayanai ba, sai dai su jira a waje idan an fito wani daga cikin General ya faɗa masu ga abin dake wakana dangane da tsaro ga kuma irin tattaunawar da aka yi!.

Dikka dakakkun Generals ɗin dake wajen suna zaune ne cikin ladabi da biyayya game da nuna alamar girmamawa ga GAT dake wajen, kama daga kan lieutenant


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login