Showing 330001 words to 333000 words out of 365093 words

Chapter 111 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5934

ce. "Daga nan ki wuce cikin tantinku! Dare ya yi". Yana tamke fuska ya faɗa, babu wasa a tattare da shi. Cikin girmamawa ta ce. "Okey sir". Ta faɗa tare da ficewa.

Duka Noor ya kai mashi a damtsen hannunsa yana faɗin. "Ya da tamke fuska mutumin, ko dai ko dai?"..... Kara tamke fuskan ya yi. "Ko dai ko dai me?". Ya tambaya irin ban gane komai ɗin nan ba.

Noor ya ce. "Ko dai kana ciki da sister ɗin tamu ce?"....…... Kai ya girgiza game da cewa. "Kawai dare ya yi ne, amma ni bana cikin komai"........ Zaynish ya ce. "In ta yi wari zamu ji"....... Murmushi Noor ya yi. "Kyalesa my Tiger, zai yi bayani ne". Cewar Noor ɗin.

Leo dai aikinsa ya cigaba da yi a laptop ɗinsa, ya fito da email na Arya, ta nan ya yi mata hello game da cewa it's Nirash, dik wani information ki saka mun shi tanan, zan duba...... Sosai Arya ta ji babu daɗin ganin ya ce ta tura mashi ta email, hakan na nufin ba zai dawo tantinsu ba, ta so ne ya dawo ko kallonsa ta sake yi kafin ta yi barci, to amma ya zata yi? Haka ta danne tana shafa kan Jehan da ta tada kai da cinyarta tana aiki da hannu ɗaya, dik wani sabon abu da zata gani sai ta yi screen record ta tura mashi.

Shi ma ya tasa laptop gaba yana aiki ba kama hannun yaro, tin yana ɗan jiyo hiransu Noor sama-sama na shakiyancin da suke yi wa juna har hankalinsa gabaɗaya ya bar kansu, bai ma san time ɗin da suka fice daga tantin kowanne ya wuce nasa tantin ba....... Wajen wuta Noor ya nufa, yana zuwa yasa hannu ya ɗauki V cak a yadda take zaune ɗin, ta baya ya ɗauketa.

Bai direta a ko'ina ba sai cikin tantinsa. A tsakiyar electric mattress ɗinsa ya direta game da sauƙowa, ya zare rigan jikinsa ya ajiye kafin ya haye. Kwanciya ya yi a miƙe, cike da shagwaɓa sosai a muryansa ya ce. "My Juliet, tausa nike so, jikina na mun zafi".

Miƙewa zaune V ta yi, ta haye kan flat tummy ɗinsa, damatsan hannunsa dake a murɗen nan ta fara matsa mashi da lausasan tafukanta tana faɗin. "Sorry my Romeo"........ Lumshe idanu ya yi laushin tafukanta na ratsa shi.

Ganin haka yasa ta dage ta kara yi mashi sosai tana ta faman yi mashi sannu, ya ɗaura hannunsa ɗaya a kan mazaunanta ta baya yana aikin shafe mata su.

Ta jima tana matsa mashi jikin kafin ya juya da ita, ta koma ƙasa shi ya dawo sama, kurawa juna ido suka yi, ya ɗan turo mata baki, a shagwaɓe sosai ya ce. "Julie, I'm in need of something very urgen".

Tana binsa da wani irin kallon ƙauna ta amsa da. "What's that?"...... Sumbatar ɗan bakinta ya yi kafin ya amsa da. "You"........... Lumshe ido ta ɗan yi game da sake buɗewa. "I'm yours already"..... "Sure?". Yana shagwaɓe fuska ya faɗa. Kai ta gyaɗa mashi alamar very sure ma kuwa. Sumbatar gefen kumatunta ya yi game da komawa gefe ya kwanta, sai ya kawota jikinsa ya rungume. Daga nan ya ce su yi barci.

Ba musu ta lafe luff a kirjinsa, ba jimawa barci yai awon gaba da su. A ɓangare Leo da Arya kuwa, tamkar yadda dare yake matsayin rana a wajen ƴan ta'addan nan, haka yakasance a wajensu. Aiki suka sha har karfe 3, tana tare da laptop ɗinta shima yana tare da na shi, sai da nasa ta ɗauke caji ya kare, sannan ya hakura, yai mata dropping messages through sms kan da safe zasu cigaba, da yake dik suna da number abokan aikin nasu, sai ya laluɓo nata ya turo mata saƙon.

Yana tura mata ya kashe wayar, yai addu'ar barci ya kwanta. Ba jimawa barci tai awon gaba da shi. Ita ma kashe nata laptop ɗin ta yi, dama ba caji sosai, batteryn solar takusa ɗaukewa, tana kashewa ta miƙe ta ɗauki Jehan da ta yi barci a jikinta ta kwantar da ita saman mattress, ta gyara ta kwanta a gefenta, already su Angelina sun jima da yin barci.

Saura sojojin dake sansanin suna bakin wuta suna ta hira tamkar rana ce ba dare ba, su Juraiz dik sun shiga tantunansu. ASUBA TA GARI.

MORNING D----O----L 🌅🔥

Asubarsu ta fara ne da farar asuba, shirin yin sallah suka yi, suka yi zaman karatun Alkur'ani mai girma kafin su yi askar ɗin safiya, Leo ya koyawa Noor karatun Alkur'ani na surori biyu daga ta ƙasa, ya fara ɗaukar haddarsu.

Around 7 daidai suka tashi daga wajen sallar, suka nufi cikin tantunansu, a nan ne kowanne ya buƙaci ganin macen da zai yi aiki da ita.

A can gefe kuwa, safiyar Arya ta fara ne da yi wa Jehan wanka, ta shafeta da mai, sai ta sanya mata kayanta tin da Jehan ɗin bata da kaya, wandon jeans baki da top fari, kayan sun ɗan yi mata yawa, amma haka ta sanya. Arya zata fita zuwa wajen koramarta Jehan ta ce zata bita. Hannunta takama suka nufi wajen koramar.

Da zuwansu Arya ta shiga ruwa, Jehan ta tsaya bakin ruwa tana ta faman kallonta, tana murnushin dake kara mata kyau sosai. Watso mata ruwa a fuska Arya ta yi tana faɗin. "Zaki shiga ne?". Ta faɗa game da yi mata nuni da hannu ta alama tana ɗaga mata gera guda

Da sauri Jehan ga jinjina kai, dan mayyar son ruwa ce. Alama Arya tai mata da hannu kan ta shigo, da sauri ta cire wandon jeans ɗinta, sai taki cire riga dan an fara kirgan dangi, girma ya fara zuwa, dik tana kunyar cire rigarta a gaba kowa, idan Arya zata yi mata wanka sosai take jin kunya, kawai daurewa takeyi.

Arya ta fahimci hakan shiyasa bata takura mata kan ta cire rigar ba. Da rigar ta faɗo cikin ruwa. Angelina dake tsaye a can nesa ne take mamakin yadda Arya take wasa da Jehan, sun dai san Arya macece miskisla mai mugun shariya ga mutane, ko su da suke ƴan huɗunta ma bata sakewa da su har haka bare mutanen waje, makaranta wannan ba'a gani a waje sai dole, bata murmushi bata magana sai aiki, abin ya yi mugun basu mamaki, lallai sun yarda so gamon jini ne. ALLAH ne ya haɗa jinin Arya da Jehan.

Jawota kusa da ita Arya ta yi tana faɗin. "Kada ki je ta bakin nan ruwa ya tafi mun dake". Riko hannun Arya ɗin ita ma ta yi suka cigaba da juyi a cikin ruwan..... Unexpected suka ji hayaniya ya fara tashi daga cikin sansaninsu, Arya na ƙoƙarin saurarawa ta gano menene sai ga Manassa da gudu tana faɗin. "Bloody, waɗan nan masu kiwon shanun da kika ɗauko Jehan a wajensu har kika daki mutanensu ne suka yi gangami da sanduna suka shigo sansaninmu wai zasu kashemu".......... Toh fah, Fulani sun biyo sahu, sun zo ɗaukar fansa.


*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*

https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-46-by-princess-teema

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
[10/01, 9:16 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.


For more information 08161390581 Whatsapp me only.


STEP 1🔥

2025-12-30.🔥



اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E_____________ 46

D-------O-------L🔥

"Bloody, waɗan nan masu kiwon shanun da kika ɗauko Jehan a wajensu har kika daki mutanensu ne suka yi gangami da sanduna suka shigo sansaninmu wai zasu kashemu".

Siririn tsaki Arya ta ja tare da kama hannun Jehan suka fito daga cikin ruwan, bathrobe ɗinta ta sanya game da ɗaukar sauran kayanta suka nufi sansanin nasu. Sai dai suna isa suka isko gabaɗaya fulanin a tare waje guda, sun durkusa a kan gwiwowinsu, dik sun yi tsuru-tsuru da idanunsu da suka yi jajir, ido ya raina fata, sun ci jibga a hannun sojojin AZURE. Zaynish ne ya umarci sojojinsu da su tattabkesu da bulala, su zanesu da kyau sai sun gane wajen wuta suka kawo kansu.

Aikuwa sojojin suka ciro zabga-zabgan bilalu suka rakasu, suka fara basu a jikinsu, suka daka masu tsawa kan su taru waje guda, sannan suka dinga zane masu jiki har wajen huts ɗinsu suka je suka kamo waɗan da suka gudu suka dawo da su, zanesu da kyau suka yi, Leo yana ɗaki ko leƙowa bai yi ba, Noor ma yana ɗaki da V dake barci, while Vash yana ta baya yana waya da su Ammie. Shi ma Zaynish ya fito yana waya da Aunty Ummie ne Fulanin suka iso kansa da sanduna, wai zasu dakesa, aikuwa ya ce bashi da lokacinsu, ya umarci sojojinsu da su zanesu, kada su harbesu da bindiga ko su ji masu ciwo, a'a, bulala zasu masu shi ne daidai da su, dan rashin duka ne yake damunsu.

Ganin dik suna durkushe a tsakiyar tantunan nasu suna kuka ne yasa Arya dawo da kallonta a kan Manassa kafin ta ce. "Waɗan nan ne suka zo kashe mu ɗin?"...... Waige-waige Manassa ta fara yi..... "Yeah su ne".

Tsaki Arya ta ja game da wucewa cikin tantinsu tana jan hannun Arya, dan in ta tsaya tana iya sumar da mutum, dik takaici ya rufeta. A gurguje ta shirya dan tasan Leo na jiranta, a hanzarce ta ɗauko breakfast ɗinta suka ci tare da Jehan, ta dinga baiwa yarinyar a baki har sai da ta tabbatar ta ƙoshi, sannan ta ci nata, bayan sun kammala ta ɗauko biscuit daga rucksack ɗinta ta baiwa Jehan kan ta ci, sannan ta jawo laptop ɗinta.

A gefenta Manassa da Angelina suka zauna, Angelina ta ce. "Manassa ina son sir Zaynish fiye da yanda kike tinani, ya haɗu fiye da yadda kike tinani, jiya kin san har mafarkinsa na yi?". Wani irin harara da Arya ta dalla mata bata san ma ta yi shi ba, ta ɗauke kallonta daga kansu ta mayar kan laptop ɗinta.

Manassa ta ce. "Gaskiya ya haɗu, amma fa zaki sha bakar wahala a kansa, dan naga ko kallon mutane baya yi, ga fuskansa kullum a tamke"...... Angelina zata sake yin magana Arya ta katseta da cewa. "Aiki nike yi, kuna damuna da shirmen banza, ku je waje idan hira zaku yi".

Harararta Angelina ta yi game da cewa. "Bari ki ga wani abu Manassa, ke kula Arya ki yi abin dake gabanki babu ruwanki damu". Ta faɗa tare da jawo wayarta. Number Aunty Ummie ta fitar, kira ta danna mata tana cewa Manassa. "Sister ɗinsa ce, daren jiya sun yi waya, bana jin yarensu but na fahimci sun shaƙu sosai, tana da kyau matuƙa, kin ganta kuwa? Kamar tauraruwa, har cikin raina ina sonta sosai". Angelina ta faɗa a lokacin da wayar ya fara ringing.

Zazzaro idanu a kanta Manassa ta yi. "Ke ina kika samo nunber sister ɗinsa kuma?". Cike da mamaki Manassa ta tambaya..... Yatsa Angelina ta ɗaura mata a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru, shirun ta yi a daidai lokacin Aunty Ummie ta ɗaga kiran tana sallama.

Cikin harshen turanci Angelina ta ce. "Hello Aunty"...... Mamaki ne ya ɗan kama Aunty Ummie jin turancin turawa, sai kuma ta tina kila daga wajen aikin su Zaynish ne, dan haka sai ta natsu sosai saboda ta iya fahimtar turancin, kunga ba wani iyawa sosai ta yi ba.

Cike da girmamawa sosai Angelina ta ce. "Good morning Aunty"....... "Morning how was your night?". Cikin rawar murya Aunty Ummie ta faɗa....... Angelina na murmushi ta ce. "Cool. My name is Angelina, from AZURE barrack, babban friend ɗin sir Zaynish, shi ne ya ce in kiraki mu gaisa". Cike da tsoron abin da zai je ya zo na karyar da ta yi mashi ta yi maganar.

Aikuwa washe baki Aunty Ummie ta yi, abinku da jininmu mutanen amana, kun sanmu da alkunya, Aunty Ummie ta ɗauka budurwarsa ce ya ce ta kirata, ta ɗauka kunya ce yasa Angelina bata ce ita budurwarsa ba ce, aikuwa ta yi matuƙar farinciki, ta tarbi Angelina da kalamai masu daɗi, cikin zolaya ma ta ce. "Ko dai kece surukar tawa?".

Angelina murmushi sosai tamkar ba zata dakata ba, ta ji matuƙar daɗin yadda Aunty Ummie ta karɓeta, sai ta ce. "Eh...... A'a..... Kawai na kira ne in gaidaki, muna aiki, in ba damuwa zan iya dinga kiranki muna gaisawa Aunty?".

Aunty Ummie ta ɗauka Angelina kunyarta take ji yasa take mata kwana kwana, bata san nan yaran GAT basu san kunya ba, kawai tsoron Zaynish take ji yasa taki sakan jiki su sha hira. Cike da nuna kulawa Aunty Ummie macen kirki ta ce. "Ko baki kirani bama ni zan dinga kiranki ina jin ya kike! Tin da daga ke har shi kunki faɗa mun kece surukata to ki kula mun da shi sosai, kada ki bari komai ya damesa, sannan ki saki jikinki, ni Auntynku ce gabaɗaya, dake da shi dik ɗaya na ɗaukeku". A goggece ta yi turancin, amma zaka iya fahimta sosai. Ta faɗa a cikin ranta tana cewa. "Watau already yana da budurwarsa, kunya ce yasa yaki faɗa mata, amma da jiya ta ce zata samo mashi mata shi ne kenan yau yasa budurwar tasa ta kirata, lallai ma, to tasan me zata yi mashi ɗan ƙaniya". A fili kuwa murmushi kawai take yi tana sauraran Angelina ɗin.

Angelina ta fahimci turancin Aunty Ummie sosai, sai ta ce. "Thank you so much Aunty, i really appreciate"....... Cike da zumuɗi Aunty ta ce. "Ki tura mun hotunanki ta Whatsapp mana, ina son ganinki kanwata".

Sosai ta ji daɗi game da rungume Manassa da ta kafeta da kallo tana faɗin bari ta tura mata yanzu, ita ma Aunty Ummie sosai ta ji daɗi, da haka suka yi sallama cikin mutunta juna da girmamawa. Whatsapp Angelina ta shiga, a take ta zaɓo hotunanta tsala-tsala masu kyau ta tura mata guda biyu, sai ta ɗauko wanda suke su huɗu gabaɗaya ta tura mata game da ce mata su ƴan huɗu ne ga sauran sisters ɗinta.

Aikuwa Aunty Ummie na online, da sauri ta buɗe hotunan, har hannunta na rawa wajen ganin ta buɗe. Ya rabb, tana yin tozali da ɗiyar GAT ta ji Angelina ta kwanta mata a rai, yarinyar ta haɗu, bata damu da yanayin shigarta na ƙananan kaya ga kai ba ɗan'kwali ta saki gashi har baya ba, ita dai yarinyar ta kwanta mata tin da Zaynish da kansa ya ce ta kirata ai shikenan.

Tana buɗe hotonsu su huɗu sai ta ruɗe, a take a wajen ta ce lallai Zaynish ya samu mata, ai ko dan fatan da take yi na ya haifa masu yara dayawa zata so ya auri Angelina, ALLAH yasa a haihuwar farko ta haifa masu ƴan huɗu kamarta, su biyu iyayensu suka haifa, ga shi ita bata taɓa haihuwa ba, shiyasa ta matsu ya yi aure ko daga gefensa za'a samu haihuwar, ta matuƙar matsuwa ya yi aure, dan haka tana jin Angelina ƴan huɗu ne ta ce shikenan ga matarsa.

Cike da farinciki ta dinga yabon kyan Angelina ta hanyar yi mata typing ta tura. Angelina ta ji mugun daɗin wannan abin, ta dinga yi mata godiya, Aunty Ummie ta tsare hotonsu su huɗun da kallo, lokaci guda ta ji V ta kwanta mata a rai bayan Angelina, V akwai shiga rai sosai, sai addu'a take yi ALLAH yasa rabon Zaynish ne Angelina, ALLAH yasa tashin farko su haifa mata ƴan huɗu dikka maza, sai ta sake haifa masu ƴan huɗu dikka mata, addu'a sosai ta dinga yi kafin ta turowa Angelina hotunanta kala uku ita ma, ɗayan ita da Zaynish ne wancan zuwansa gida hutu suka ɗauka, biyun kuma ita kaɗai ne a shagonya.

Wai jama'a a ina Angelina ta samo number Aunty Ummie ne? Ku bini in faɗa maku. Datsan wayar Zaynish ta yi, kun sansu mayun computer, a nan ta ciro number, shi bashi da number mutane dayawa ma, daga na uncle ɗinsa, sai na Aunty Ummie, sai kuma nasu Leo watau sojojin da suka taho Mission tare, aikuwa number Aunty Ummie ne kawai ya yi saving da special suna, sauran kowanne sunansa ya sanya mashi, dan haka ta ɗauki number, da farko ta zaci budurwarsa ce ganin irin sunan da ya sanyawa number, sai da ta shigar da number laptop ɗinta ta yi bincike, a nan ta samo hoton Aunty Ummie da aka yi register sim ɗin, sai taga ai hoton matan jiya ne, nan ta gane ashe number sister ɗinsa ce ba budurwa ba, kun ji yadda aka yi.

Angelina ta yi murna matuƙa, ta dinga kallon Aunty Ummie tana ƙarawa, ta kira Manassa kan ta ganta, tsare hoton da kallo Manassa ta yi, sai ta hau yaba kyan Aunty Ummie, kai Aunty Ummie akwai shiga rai ita ma, saboda kyawawan ɗabi'unta.

Hoton Aunty Ummie da Zaynish Angelina ta sanya a wallpaper ɗinta, ta dinga yabon African hair ɗinsa, na buzaye dake gwanin burgewa, ya rungumo shoulder ɗin Aunty Ummie game da ɗan rage tsawonsa ya kwanto da kansa ta gefen wuyanta, ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login