Showing 255001 words to 258000 words out of 365093 words
sai sun yi tafiya mai nisa zuwa cikin daji, a can aka yi wani waje da aka haɗa, aka yi shinfiɗaɗiyar titi har cikin WS-HOSPITAL, ta nan Dr Mark yake fito da motar jarirai idan an saya a wani waje, hmmmm babu wanda zai taɓa expecting akwai hanyar zuwa ga 3D palace a cikin wannan asibiti ta gwamnati...... Hmmmmm, shiyasa a wannan asibitin ba ko'ina ake barin mutane su shiga ba, wannan ma iya abin da kuka gani yanzu ne, ainahin labarin yana book 2 jama'a, ALLAH yasa kanmu ya iya ɗaukar wasu abubuwa, kai ya ALLAH ƙazantar dake duniyar nan, ALLAH ne kaɗai zai iya maganin komai! Ni dai yanzu addu'a ta ɗaya, ALLAH ka bamu cikawa da kalmar shahada da ni da mutanena na kirki, In Sha ALLAH wlh mutuwar shahada zamu yi my people!.
Amma ku daga ganin iya hospital na World system kun san ba mutane ne da zasu kamu ta sauƙi ba, basu fito ba sai da suka shirya, kai akwai abubuwa idan muka natsa cikin labarin nan, baku ha komai ba.
Cikin asibitin Dr James ya shiga, kewaye ya fara yi yana duba yadda ɗakunan da majinyata suke yake, babu abin da zaku ɗaga a asibitin nan ku kirasa mai kyau sosai, komai a gurɓace a lalace da yake government hospital ne, amma ku duba irin aljannar duniyar da suka shinfiɗa a ƙarƙashin ƙasa dan biyar buƙatar kansu kawai, ya ALLAH gwamnatin Avarsi ku ji tsoron ALLAH, ita duniya dai wuni muka zo yi, kowa zai koma ga ALLAH, tabbas zaku tsaya ne a gaban ALLAH da abubuwan da kuka shuka a duniya, ku tuba tin kuna da sauran lokaci.
Ya jima yana kewaye cikin asibitin nan, wani sashe ma idan ya shiga yawu yake tofarwa saboda lalacewar asibitin, daga karshe ya koma wannan private room ɗin, suka koma cikin WS-HOSPITAL ɗinsu, dan abin da ya kawosu kawowa kenan maganin, daga wannan asibitin kuma za'a fitar da magungunar ne zuwa ƙasashen ketare, manyan dattawan alhazawa da masu mulki ake sayarwa magungunan.
Can na tina lokacin da su oooo suke cewa basu son bakaken fata, wai fararen fata suke so, su jikinsu baya tsufa, bakaken fatanmu su yi ta tada hankalinsu suna damuwa a kan su suna tsufa! Su yi ta sha'awar jikinsu ooo, wai yana da kyau basa tsufa, my sister zauna yadda ALLAH ya ajiyeki shi ne ya fi maki alkhairi, baki san me yake behind rashin tsufar nan ba! MAGANIN MAI DA TSOHUWA YARINYA! MAGANIN HANA TSUFA! HMMMMMMM.
Saura mu ji me suke yi da ɓargon ƙashin da kuma shi kansa garin ƙashi da tsokar jariran kuma!.
Kai tsaye SECTION D suka wuce, Dr Mark ya koma room ɗinsa ya kwanta tin da shi babu ruwansa da love.
To mu ɗan koma baya kaɗan a kan su Zinta kafin mu cigaba. Bayan sun kammala baiwa babys ɗin nan madara mai ɗumi, zama suka yi a gefen gado, sister Zinta ta buga uban tagumi tamkar mai tinanin wani abin. Taɓata sister Maya ta yi tare da cewa. "Tinanin me kike yi?".
Nisawa ta ɗan yi. "Darling nike tinani, sister ina jin tamkar bashi da lafiya, anya ba zan fita in je in duba shi ba kuwa? Zan binciko shi a gidan nan, nasan wani ɗakin suka kaisa"........ Shiru sis Maya ta yi, sai kuma da yake soyayyar ƙanin nasu ya rufe masu idanu sai ta ce. "Mu je mu duba shi, na tabbata yana kusa da mu".
Kai sister Zinta ta jinjina, sai kuma ta ce. "Sister kina ganin da gaske alluran magani suka yi mashi?". .... Kai tsaye Maya ta girgiza kai alamar a'a kafin ta amsa da. "Wlh ba magani bane, cuta ce, baki ga yanayin kalar ruwan ba? Kin lura akwai chemicals da muka haɗa a cikin cutar da yake ikirarin maganin ne?".
Jinjina kai sister Zinta ta yi. "Tabbas cuta ce, amma koma menene zan ɗaukosa, zan gwadasa, in dai cuta ce tabbas zan yi mashi magani, ai mu muka haɗa chemicals ɗin, dik kuma mun san makarin chemicals ɗin".
Kai sister Maya ta jinjina. "Ko ni nasan makarin dikka chemicals da muka haɗa, kuma zan iya haɗa mashi magani"..... Shiru sister Zinta ta ɗan yi, can ta ce. "Kina tinanin meyasa 3D zasu saka mashi cuta? Baki tinanin kamar wani mugun abu ake shiryawa? Meyasa muke haɗa waɗan nan chemicals ɗin? Me suke yi da su da kullum sai su je SECTION C sun ɗeba? Me kike tinanin ake yi da su?".
Abinku da jinin daddy Haiza'an, shiru Maya ta ɗan yi, can ta ce. "Ina tunanin cuta suke kirkira, to anma ina suke kai cutar? Me suke yi da shi?"....... Sister Zinta ta ce. "Kina ganin bai kamata ace mun san me suke yi ba?".
Kai ta jinjina. "Yakamata ace mun sani, to amma ina suke kai dikka waɗan nan abubuwa? Baki ganin shi ma yakamata mu sani?".
Jama'a na faɗa zan sake faɗa, dan jiya na samu tambayoyi a kan abin da na faɗa na sake faɗa! Dik nurses dake wannan asibitin kyankyasarsu suka yi, basu ɗaukar ma'aikata daga waje, su suka kyankyashi kayansu, suka renesu, suka basu ilimi ta ɓangaren da suke son su sani, a cikin 3D ɗin nan kowanne da abin da ya fi kwarewa, Dr Mark yana da ilimi kan sanin chemicals fiye da yadda kuke tinani, shi ya karantar da su Dr Maya, Dr Kamal yana da sani ɓangaren kafiya sosai, shi yakarantar da sauran nurses dake aikin lafiya, waɗan da ke duba yaran da ake cire eggs ɗinsu, su yi treating babys idan basu da lafiya, Dr James ubansu kenan, yana da ilimi da baiwar sani a dikka ɓangarorin, dan haka basu ɗaukar ma'aikata daga waje, babu wanda yake shigowa wannan asibitin face abin da suke fitarwa, komai da kuke gani a nan asibitin aka kirkiresa, basa amfani da abubuwan waje face kayan abinci da ruwan roba sa ake shigo masu da shi. Haka zalika bayan 3D babu nurses da suke fita bare su je su yi aiki a waje a wani asibitin, ko sperm da suke saye 3D suke fita su ɗauko shi, dan haka take note! Basa ɗaukar wasu ma'aikatan daga waje, kuma nasu ma'aikatan ma basa fita waje su yi aiki a wani asibitin.
"Gaskiya yakamata mu sani, zuciyata ta fara rawa, ina jin kamar akwai wani abin da ya saɓa". Sister Maya ta faɗa. Sister Zinta zata yi magana suka lura sauran nurses ɗin su suke kallo, da sauri suka ja baki suka yi shiru. Sister Maya ta ɗauko wani baby, yana barcinsa, amma saboda tsabar son yara ba zata barshi ya huta ba, ta kwanta tare da kwantar da shi a saman cikinta, tana shafa bayansa, tana jin tamkar ta mai da shi cikin cikinta saboda so, a haka barci ya saceta.
Ita kuma sister Zinta shiru ta yi, ta buga tagumi tana tinanin maganganun da suka yi, lallai dole akwai in da suke kai waɗan nan abubuwa, kuma tana zargin cuta ce, idan kuwa cuta ce lallai zuwa yanzu darling baya raye, dan kuwa in har waɗan can mugayen chemicals ɗin da suka haɗa dikka aka juye cikin wannan aiki to ba shakka wannan cutar ƙare dangi yakamata a sanya mata suna.
Haka kawai ta ji zuciyarta na raya mata lallai ta fara bincike, lallai ta nemo maganin wannan cuta, tana jin zata iya, kuma tabbas zata iya, dan kuwa in baku manta ba su suka haɗa kaso 60 na kwayar cutar, in kuwa ta ce zata yi bincike ta ɗauki chemicals da zasu karya waɗan can tsab zata iya haɗa magungunar, ko bata yi komai complete ba za'a samu kaso 85 cikin ɗari.
A haka ta dinga wannan tinani har sister Maya ta farka daga barci around 8 na dare, ganinta zaune shiru yasa ta ce. "Sister, yadda na barki baki motsa ba? Lafiya dai ko?"....... Kai ta girgiza alamar ba lafiya ba, idanunta take suka kawo ruwa taf, murya a raunace ta ce. "Sister dole akwai wani abin da yakamata mu sani a kan darling, ina son ganinsa, yau ba zan yi barci ba, zan jira oga ya zo sai ya kaini wajensa".
Jinjina kai Maya ta yi, tana saɓa wannan baby a shoulder ɗinta, ta amsa da ita ma ba zata yi barci ba, zata jira 3D. Haka suka kasance, suka dinga hidima da babys ɗin har yaran suka yi barci, sannan ne suka zauna zaman hira, ko abinci basu ci ba, da suka ji yunwa suka ɗauko crispy chicken ɗinsu, suka cinyesa su biyu basu tsanwa kowa ba.
Haka suka kasance har karfe 12, da yake sister Zinta tasha barcin rana yau, ita kuma sister Maya ta sha na mangrib, sai yazama basa jin barci sam, da karfin hali irin nasu sai da suka jira around 1 na dare, sun fara fidda rai da zuwan 3D, unexpected suka ji an turo glass door ɗinsu.
3D sun yi mamaki ganin wutar ɗakin a kunne, da suka shigo kuma sai suka yi mamakin ganin matan nasu idanunsu biyu, su kuwa suna ganinsu suka ɗan miƙe tsaye, amma basu razana irin razanar da suke yi a baya idan sun gansu ba, bare ma sister Zinta da ita yanzu gabaɗaya ta ji tsoron Dr James ya fara fita a zuciyarta tin da ya cire kayansa gabaɗaya a gabanta, ya yi wasa da jikinta, tin daga wannan lokaci take jin tamkar ita da shi abu ɗaya ne, and ta fara fahimtar yana sonta sosai, dan haka ba zai yi mata komai ba ko da ta yi mashi laifi.
A gabanta Dr James ya tsaya, cikin sanyin murya ya ce. "Me kike yi baki yi barci ba?"....... Murmushin dole ta ƙaƙalo kafin ta ce. "Waiting for you my oga".
Har cikin ransa ya ji wani irin daɗi, hannunsa ya ware mata tafukansa game da miƙa mata, ɗaura nata kyawawan hannun a kai ta yi, tana ɗan shagwaɓe fuska ta ce. "Ba zaka ɗaukeni kamar ɗazun ba?".......... Ya ALLAH, wani irin madarar daɗin da ya ji ba, baisan lokacin da ya jawota jikinsa ba, ya rungumeta yana ɗan shafa bayanta.
"Muje side ɗinmu ko?". Ya faɗa can ƙasa....... Ɗan shagwaɓe fuska ta yi kafin ta ce. "Ka kaini in ga darling ɗin please"...... Kai ya jinjina mata alamar to, sannan ya rage tsawonsa, cak ya ɗauketa suka fito waje. Bai zame da ita ko'ina ba sai side ɗinsu. A saman katafaren bed ɗinsa ya direta, zai sauƙa ƙasa ta yi saurin riƙo hannunsa.
"Baka nuna mun darling ɗin ba". Tana narai-narai da fararen idanun nata ta faɗa. Ɗan riko shoulder ɗinta ya yi. "One minute"....... Ya faɗa tare da saketa, ya wuce ya nufi wajen laptop ɗinsa, ɗaukota ya yi, a kusa da ita ya zauna tare da kunna laptop ɗin. Tana kallon dik abin da yake yi, bai yi zaton tana naɗar komai a kanta ba.
Wani folder da aka rubuta new project ya shiga, nan ya yi mata playing video ɗin darling a cikin kwalba, a yadda ya ɗauke shi video yaron yana kwance shiru tamkar mai tinanin wani abin.
Kura mashi ido ta yi, sai ta hau murmushi, rashin sani ya fi dare duhu, da tasan balain da yaron nan yake a ciki da bata yi murmushi ba, amma tana murmushi, ta matsa kusa da laptop ɗin sosai, dama ta yi wa desktop computer farin sani, dan a cikinsa aka koyar da su ilimin sanin chemicals, dan haka laptop bai bata mamaki ba.
Video ɗin ta kare ta sake dawo da shi baya, tana ta murmushi, a tinaninta darling yana cikin farinciki ne, ya sha madara ya ƙoshi ne ya yi shiru. Dr James ya ɗan rungumota yana faɗin. "Babynku yana nan lafiya, muna wani gwaji ne, amma zai dawo gareku"........ Da yake bata ga zahiri ba, a video ne sai ta yarda darling yana nan lafiya, ta dinga murna, har da rungume Dr James, cikin shagwaɓa ta ce. "Sir ina son nunawa Maya darling ɗinta".
Yana shafa kanta izuwa bayanta ya ce. "Zan sanya Dr Kamal ya nuna mata, ba sai kin je ba". Ya faɗa tare da jawo laptop ɗin kusa, ko kaɗan bai yi tinanin ta yi wani tinani a kansu ba tare har ya ce ba zai yi wani abin a gabanta ba, a kan idanunta ya turawa Dr Kamal video ɗin ta email, ya ce mashi ya nunawa Maya.
Daga haka ya kashe laptop ɗin, ya ɗaura saman side sofa dake kusan da bed ɗin. Dik yadda ya yi a laptop ɗin ta naɗi komai. Jawota jikinsa da kyau ya yi, in a romantic way ya fara sarrafata, yana juyata son ransa. Cikin ƙanƙanin lokacin ya rabata da kayan jikinta, ya cire nasa shi ma, ya dinga wasanni da ita, sai da ya tabbatar da ya gama kiɗimata da salonsa, sannan ya saita penis ɗin, ya shigeta, dan yau ya yi alkawarin mayar da ita matarsa da gasken kuwa.
Sosai ta ji zafi, ta fara ƙoƙarin turesa tana mashi magiyan ya kyaleta, amma bai kyaleta ɗin ba, sai da ya mai da ita mace, ta yi kuka har ta godewa ALLAH, ta dinga dukansa tana turesa, amma ina, bai raga mata ba....... Sai da ya gama bidirinsa, sannan ya kwanta tare da jawota jikinsa, ya hau rarrashi yana bata baki, ya dinga lallaɓata har ya samu barci ya ɗauketa. Lokaci guda wani irin zazzafar sonta ne ya ƙara shigarsa, ya zubawa kyakkyawan face ɗinta idanu, yana jin tamkar ya ƙara shigarta, dan wani sabon sha'awarta yake ƙara taso mashi.
Duba time ya yi a wayarsa, karfe 3:30 na dare, dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, sannan ya sauko ƙasan bed ɗin. Message yai typing wa su Dr Kamal, sannan ya shige cikin toilet. After 30 mins ya fito, a gurguje ya shirya, gaban bed ɗinta ya dawo, sumbatar cheek ɗinta ya yi kafin ya jawo bargo ya lulluɓeta, a gaggauce ya nufi waje dan lokaci na neman ƙure masu.
Yana fitowa parlo ya isko su Dr Kamal a tsaye, suna haɗa idanu Dr Kamal ya ce. "Jammy kar dai ka aikata abin da ka faɗa? Naga face ɗinka sai wani kyalli yake yi". Hararansa Dr James ya yi, shi kaɗai yasan irin tsananin farincikin da yake ciki, ya ALLAH, yau ya mori daɗinsa.
Gaba ya wuce ba tare da ya yi masu magana ba, da sauri suka rufa mashi baya. Kai tsaye SECTION D suka nufa, suna zuwa ba ɓata lokacin suka sake ɗaukan jarirai guda biyar suka fita da su izuwa ɗakin niƙa jarirai, biyu daga cikin babys ɗin sai feket-feket suke yi alamar suna son yin kuka, sun farka, ɗayan sai buɗe baki yake yi, alamar yana jin yunwa, yana son ya yi kuka a bashi madara, da alama sarkin ci ne.
Dr James na rike da babys biyu, Dr Kamal na rike da ɗaya, Dr Mark na rike da biyu, to na hannun Dr James ne suke ta faman ƙoƙarin fara kuka, ga alamar suna jin yunwa sosai, sai zuro harshe waje ɗayan yake yi.
Basu diresu a ko'ina ba sai saman wannan gado na lantarki. Kunna lantarki Dr James ya yi, take yaran suka fara wani irin girgiza kamar yadda waɗan can na baya suka yi. Wannan baby mai zuro harshe waje yana son cin abincin nan gwanin ban tausayi, ya ƙara zuro harshen nasa waje, jikinsa na wani irin kakkarwa sosai, dadashinsa na garuwa da juna, yatsunsa na wani irin kerma, sun zazzare idanuwansu waje gwanin ban tausayi.
Haka wannan shocking ya dinga jansu na ɗan lokaci, sannan Dr James ya kashe bayan ya tabbatar jikinsu ya saki waɗan nan sinadarai da ake so. Ya danna gadon tai sama da su, wannan jariri dake jin yunwa ne ya fashe da kuka a lokacin da shocking ɗin ta tsaya, kuka sosai yake yi, jininsa na ɓari sosai, harshensa ya zazzago waje.
Yana wannan kuka suka tura shi cikin wannan ball ɗin. Kara fashewa da kuka mai tsanani ya yi, da alama ball ɗin cikinsa akwai zafi matuƙa. Ko gezau 3D basu yi ba, tamkar ba rai suke gani a cikin mawuyacin halin nan ba.
Ya rabb, suna jiyo kukan jariri mai jin yunwar nan a lokacin da suka sanyasu cikin injin nan, yana shiga da suka kunna injin ihu ɗaya ya yi, daga nan ji kake ɗiff ya ɗauke wuta, injin ya murɗe mashi wuya kenan. Ya ilahil alamina, wace iriyar musifa ce wannan, ya ji da yunwar ne ko kuwa da azaban nan? Ya ALLAH ka sakawa waɗan nan jariran, dik masu sayar da mahaifa da sperm ɗinsu ALLAH ka walaƙanta rayuwansu!.
Haka suka ɗauki bokitaye suka tari jini, garin ƙashi da tsoƙa, ɓargon ƙashi, suka ɗauka zuwa freezers room ɗinsu, suka shiryasu ciki, sannan suka koma side ɗinsu dan su je su yi wanka su yi shirin fitowa aiki, a lokacin 5 na asuba ta yi!.
My people a wannan ɗauki ɗaiɗai da sukewa jariran kowani dare suna niƙasu kuna tinanin one day one time su sister Zinta ba zasu farga bane? Yanzu saura babys 45, watau shiyasa kenan yaran basa taɓa wuce 3 months a asibitin, watau irin ɗauki ɗaiɗai ɗin nan ake masu kenan!.
Bayan ya yi wanka ya shirya, sai ya tada sister Zinta, da sabon kuka ta tashi mashi, rarrashinta ya dinga yi, da kyar ya samu ta yi shiru, a sanyayye ya ce. "Sorry my wife, zan je office, zan dawo by 1 in duba ki, yau ina da aiki sosai, amma ke yau na hutar dake aiki, ki kwanta a nan ki huta, za'a kawo maki dik abin da kike so".
Cikin muryan kuka ta ce. "Ni ka turo mun sister Maya, ita kaɗai nike son gani".... Nisawa ya ɗan yi, ya sunbaci goshinta kafin ya ce. "Yanzu zan turota, amma ki mun murmushi"...... Din da tana cikin ciwo hakan bai hanata murmurawa kaɗan ba, kara sumbatar goshinta ya yi tare da miƙewa, yai mata sallama ya fito.
Tsaye ya isko Dr Kamal da Maya a tsakiyar parlon, yana faɗa mata ta je ta yi wanka ta fita wajen aiki, sai dare zai sake zuwa ya ɗauketa, shi kuma Dr Mark da ba ruwansa da soyayya tini ya yi gaba abinsa.
A dake Dr James ya ce. "Maya ki je