Showing 171001 words to 174000 words out of 365093 words

Chapter 58 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5906

da tambayansa me yake faruwa?. Tamkar zai haɗiyi zuciya ya mutu, sai da ya yi shirun good 5 mins, har sun fidda ran zai yi magana, sannan in a harsh way ya ce. "Ta ya za'ayi duniya ta gyaru? Ta ko'ina gurɓatattu ne! Son kai, zalunci, cin amana, son duniya, son abin duniya, dik ya cika zuƙatan kowa! A haka ta ya za'ayi duniyar ta gyaru?".

Shiru dik suka yi, saboda sun san gaskiya yake faɗe, shegen son duniya ya mayar da kowa azzalumi mara imani. Gudun kada ta kwaɓe masu yasa suka yi shiru suka kyalesa, shi ma shirun ya yi, can kuma ya dunkule hannu ya daki glass na kofar motar sai da ta tarwatse saboda ba dukan wasa yai mata ba, gabaɗaya glass ɗin kuma ta farfasa mashi hannu sai jini jajir ta fara malala, takaici tamkar zai mutu, dik ta in da ya juya azzalumai ne masu son kai, su sha wahala su yi aiki tukuru amma tamkar basa yi saboda yadda zalunci ya cika ko'ina, dole ya fusata, dole ransa ta ɓaci, dole ya daki abin da ya fi glass.

Cikin zafa Aryan da guru suka damki hannun nasa, har suna rige-rigen damƙa. Sai dai ina, kwace hannun ya yi tare da sake dunkuleta ya daki jikin marfin motar har sai da ta girgiza, take glass ɗin suka sake natsawa cikin hannunsa, yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta, with harsh voice ya ce. "Is better for me to die a kan irin wannan murɗaɗɗen rayuwa, kowa burinsa ya sami duniya, kowa ya manta da ALLAH da ranar tashin alkiyama, kana ƙoƙarin gyara gabas laanannun nan na kwance maka da lalata maka yamma!". Ya kai karshe tare da daddagewa ya buga kansa da jikin marfin motar ta wajen glass da ya fashe ya bar sauran guntu-guntu.

Cikin fusata ya sake ɗaga kan nasa zai buga Aryan ya rikesa da karfi yana ƙoƙarin dannansa. Dik glass ɗin ta fashe mashi goshi, abin akwai mugun cin rai da kayan takaici ne, ace jami'an da yakamata ku haɗa kai ku gyara kasar suke da alhakin wasu kaifukan? Dole ya shiga wannan mood ɗin.

Wani irin jiri ne ta fara ɗibansa a lokacin da yake ƙoƙarin kwace kansa daga damkar da Aryan ya yi mashi. Rikesa gam Aryan ɗin ya yi jini na ketowa daga gaban goshinsa in da ya buga kan izuwa kan tongue ɗinsa da ya ciza da hakwaransa tamkar zai fasa harshen nasa saboda tsananin takaici.

Guru ne ya cewa driver ɗin nasu ya taka motar da gudu sosai tin da sun kusa isa cikin airport. Basu ƙara wani tafiya sosai ba Lion ya ɗauke wuta a jikin Aryan saboda zafin da zuciyansa ta ɗauka, sumewa ya yi, ga zafin da kansa take mashi tamkar zata fashe.

Godiya suka yi wa ALLAH da ya sanya ya suma, zasu samu sauki. Shi ma Aryan ɗin dauriyar ce kawai, amma ji yake tamkar yai ta buga kansa a bango kada ya dakata, wannan musifa dame tai kama.

To a haka dai suka dawo CRYSTAL PALACE, kai tsaye gida suka koma, Aryan da kansa ya yi treating Lion yadda yakamata, ya gyara mashi gaban goshinsa da hannun nasa, sannan ya bisa da alluran barci na good 5 hours dan ya samu barci, hakan zai sanya ya samu natsuwa kuma zuciyar ta sassauto.

Bayan sun tabbatar yana cikin aminci da kariyar UBANGIJI sai suka nufi room dake kusa da wanda yake a ciki, suka yi wanka, sannan suka shirya cikin pjs dan shan iska. Parlo suka dawo suka zauna, gabaɗaya Aryan bai nemi Seraphina ba, kuma tana ransa, dik wannan abin da yake yi tinaninta na cikin ransa, amma ya daure dan ya gwada mata yana fushi da ita har sai ta bashi hakuri.

Wayarsa ya ciro, ya kunne other sim ɗin tare da fara ƙoƙarin nemo number Faryan dan ya ji ya gida suke. Saƙonnin ne suka fara shigowa kamar ruwa, wasu tin daren jiya, sakonni sun kai 30, kuma dik na Seraphina ne. Kin buɗe saƙonta ya yi, ya nufi fita kan saƙonnin kawai unexpected idanunsa suka sauƙa kan sako da number Madam Rohisha.

Da farko kamar ba zai buɗe ba, amma da ya tina kila wani abin ne sai ya buɗe. Saƙo ne a rubuce kamar haka. "Tin da rana muke nemanka a waya a kashe, please idan ka buɗe waya ka gani ka zo gida baby taki cin abinci, taki yin magana sai kuka kawai take yi, na yi rarrashin duniyar nan amma ta ce idan baka zo ba sai dai yunwa ya kasheta".

Yana gama karanta saƙon ta duba time da ta turo saƙon 11:30 na dare. Ya ALLAH salati ya yi a fili tare da miƙewa da sauri, ya duba time yanzu karfe 10:30 na safe, ya yi daidai da lokacin da ya bar wajenta jiya. Dafe kansa ya ɗan yi, bai yi zaton abin zai kai haka ba, ya san tana da saurin kuka, to ya ɗauka idan ta yi kukan na ɗan lokaci zata mance komai ta koma walwalarta, ban san soyayyarsa ta yi matuƙar ginuwa a ranta ba, ba laifinta bane, bata san tana yi ba, laifin zuciya ce, a hankali soyayyar daddyn nata ya gama mamaye zuciyarta ba tare da saninta ba kamar yadda shi ma soyayyarta ya gama mamaye dikkan jinin jikinsa ba tare da ya sani ba.

Jin ya yi salati ne yasa guru tambayarsa lafiya! Ai ina, bai bi ta kan guru ba ya nufi waje da sauri tamkar zai tashi sama. Kai tsaye benensu ya nufa. Yana shigowa ya shiga cikin ɗakinta kai tsaye.

A bakin door ya tsaya ya zuba mata ido, tana zaune a tsakiyar gado, ta rungumo katuwar teddy ɗin fari tas da girmansu kusan ɗaya da ita, sai yazamana tamkar ita da kawarta Rimsha ne suka rungumi juna, tana manne da waya a kunne, tana kuka tana faɗawa Rimsha daddynta yana fushi da ita, tin jiya da ya fita cikin fushi bai dawo ba kuma bai kirata ba, da ta kirasa yaki ɗauka, da ta matsa ya kashe wayarsa, Rimsha ta taimaka mata ba zata iya jurewa ba.

Ya so ace ya ji amsar da Rimsha ɗin ta bata, amma ya cigaba da zuba mata ido yana kallon yadda take kuka tana turo baki, idanunta sun kumbura sosai, sun yi jajir, while ƙasan idanunta ya yi jajir, tsinin hancinta ma jajir, sai shessheƙa take yi. Har cikin ransa ya ji zafin ganin yadda ta sha kukan, amma ya daure yana jiran ta gama wayar, ta ɗan kifa kanta a jikin Teddy ɗin.

Ba yadda Rimsha bata yi da ita kan ta faɗa mata meyasa daddyn nata ya yi fushi ba amma taki faɗe, me ta yi mashi sai ta ce babu, ta ɗaukarwa kanta alkawari ne kan ba zata sake gigin maganar hotonsa da kowa ba, shiyasa taki faɗawa Rimsha a kan hoto ne. Daga karshe dai rarrashinta Rimsha ta yi, ta ce tin da Monday zasu haɗu a school ai kada ta damu zasu san yadda zasu yi da daddyn nan.

Da haka dai ta lallaɓata har ta samu ta yi shiru. Daga haka suka yi sallama, tana ajiye wayar ta ɗago kai tana jan hanci. Unexpected idanunta suka sauƙa a kansa, ya yi holding hands ɗinsa a saman chest ɗinsa, kallonta kawai yake yi. Ai wani irin zabura ta yi, da gudu ta diro kasan gadon tare da sakin Teddy ɗin nata.

Sake hannayensa ya yi tare da buɗe mata, ta zo da gudu ta faɗa jikinsa tare da fashewa da sabon kukan da muryanta sam baya fita. Rungume sosai ya yi tare da ɗagata sama suka koma cikin room ɗin, a gefen bed ya sauketa, ya zaunar da ita tare da tsuggunnawa a gabanta, tana cigaba da kuka sosai mai taɓa zuciya.

Hannu yasa ya ɗago haɓarta, suna fuskantar juna, ɗan shanyewa ya yi ganin yadda face ɗinta ya yi jaga-jaga da hawaye ga kumburi ido. Can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "For give me my Cherry Bloom". Ya faɗa tare da kamo hannunta yana ɗan rarraba ƴan yatsunta kuma yana ɗan mammatsatsu, idanunsa a kan face ɗinta.

Cikin kuka tana shessheƙa ta ce. "Daddy for give me, na san na yi maka ba daidai ba, amma baka bani damar in baka hakuri, dana kiraka ma kashe wayarka ka yi"....... Manna ɗan hannun nata a kumatunsa ya yi, yana kallon cikin idanunta ya ce. "Ba saboda ke na kashe waya ba, kuma daddy ba zai taɓa yin fushi da Cherry Bloom ɗinsa ba, na yi tafiya ne zuwa........ ". Kome ya tina sai kuma ya fasa faɗa, da ya so ce mata ya je Washington ne sai ya fasa.

Ɗayan hannunta ta ɗaura a saman kyakkyawan madaidaicin sajensa dake kwance a gefen da gefen kyakkyawan face ɗinsa, ɗan shafawa ta yi izuwa lallausan kumatunsa kafin ta ce. "To daddy for give me, I promised you that ba zan sake kwatanta abin da na yi ba"....... "Daddy ya yafe maki, yanzu faɗa mun burikanki guda uku daga cikin burukanki da kike son cikawa a duniya!". So yake ya sanyata farinciki, ya faɗa yana matsa ƴan yatsunta dake saman kumatunsa.

"Ina da buri huɗu dama". Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. Zuba mata idanu ya yi ba tare da ya yi magana ba alamar yana saurarenta kenan......... A shagwaɓe ta ce. "Daddy ina son zuwa in da rana yake fitowa, ina sun zuwa garin, ina son ganin rana ya fito a kan idona, ina son yawo a tsakiyar teku cikin jirgin ruwa ina ganin manyan shark suna yawi, ina da wannan buri, kuma shi ne babban burina a duniya bayan son ganin Annabi Muhammad ko da a mafarki ne! Ka ji buri biyu! Na farko son ganin Annabi, na biyu zuwa in da rana yake fitowa, da yawo cikin tsakiyar katon teku, na uku ganin daddyna da uncle ɗina, ina son in gansu, in rungumi daddyna in ji ɗumin jikinsa, in faɗa mashi wani mugu ya shigo gidanmu ya kashe mammyna dan ya ɗauka mana fansa, daddyna fa soja ne daddy, yana da karfi kuma yana da bindiga, mammyna ta ce babban jami'i ne, shiyasa nake son in gansa sai in faɗa mashi ya ɗauka mana fansa, burina na huɗu ganin fuskan SSO jarumaina kenan a duniya".

Kamar wasa ya ce mata. "To idan kika ga wanda ya kashe mammyn naki zaki ganesa ne?"........ Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e, kafin ta ce. "Yana sanye da nose mask, amma for sure idan na ga idanunsa zan ganesa, he have jade eyes, very big and sexy, zan iya gane waɗan nan idanun nasa masu zubin ƙanƙara".

Ɗan ɗauke wuta Aryan ya yi jin ta ambaci halittar idanun Lion, a zuciyansa ya ce babbar magana, watau kallon makashin da ya kashe mammynta take yiwa mashi, lallai akwai gagarumin matsala randa gaskiya zata bayyana.

Ganin ya yi shiru yasa ta ce. "Daddy kaga labarai daren jiya? SSO sun je Washington zaka da mr President da suke yi dik karshen wata? I saw them in television, daddy i really love SSO with all my heart, amma basu son a kalli face ɗinsu suna ɓoyewa, ina burin in ga face ɗinsu ko sau ɗaya ne"....... Jin waɗan nan kalamai nata ya sanya shi sauke ajiyar zuciya, yana ƙoƙarin yi mata magana sai ta rigasa da cewa. "Very soon zasu kama mana waɗan nan azzaluman IRON FISR ɗin su yi masu kisan walaƙanci, su bauwa karnuka gawarwakinsu".

Jin waɗan nan kalamai kuma yasa ya dafe kai, a ransa ya ce. "Mu dai mun shiga uku a hannun Seraphina, daga an tsanemu, sai ana kaunarmu, sai kuma aka ce Lion ne ya kashe Mammy an tsanesa, to wanne ɗaya zamu rike ne?".

Yana cikin tinani ya tsinkayo muryarta tana cigaba da yabon SSO. Nisawa ya yi kafin ya ce. "My Cherry Bloom, ke da kike cikin ɓacin rai kina ta kuka jiya yaushe kika samu damar ganin labarai kan SSO? Ko dai dama kukan gulma ne da rigima?". Ya faɗa yana jifanta da wani irin kallo mai kama da tuhuma.

Turo baki ta ɗan yi tare da fara rarraba eyes ɗinta daga nasa idanun zuwa ɗan bakinsa, sai kuma ta kawar da zancen da cewa. "Daddy I'm feeling hungry". Tana shagwaɓe fuska ta faɗa....... Gera guda ya ɗaga mata kafin ya ce. "Answer my question first, a yaushe aka samu damar ganin labarai kan SSO?. Zaki mun wayau ki canza topic na hira ko?".

"Kai daddy kai daddy, ni kada ka tambayeni". Ta faɗa tana kai hannu ta ja dogon hancinsa, yadda ya ɗaga mata gera gudan nan har sai da ta ji zuciyarta ta motsa, ya yi balain tafiya da ita.

"See your eyes na marasa gaskiya, zaki yi bayani ne anjuma, now go and bring your breakfast so I can feed you, da wani ɗan bakinki a wajen, wai kema kin yi wayau, a haifeki a gaban nawa ne zaki mun wayau yanzu?". Sam ba da wata manufa ya faɗi wannan magana ba face kawai hira..... Zazzaro ido a kansa ta yi, sai kuma ta ce. "Daddy dama a gabanka aka haifeni?"..... Kai ya gyaɗa mata alamar e ba tare da ya kawo komai a ransa ba.

Kara zazzaro ido ta yi kafin ta ce. "Yauwa daddy to bari in baka two questions"...... Jinjina kai ya yi alamar yana jinta......... "Time da muke Jss3 an faɗa mana sai mace da namiji sun yi having sex sannan ake samun cikin da za'a haifi babys, to ina son sanin yadda ake haihuwar, then one of my classmate show me the video na yadda ake having sex between ladies and mens, and i saw the lady is crying i time da suke having sex ɗin, ina son sanin shin dama .......". Ai ɗauke wuta da maganar ta yi ɗiff ta gagara ƙarisawa saboda zazzaro mata ido da ya yi, ya yi mugun razanata ba kaɗan ba, bare ma yadda ta ga face ɗinsa ya canza lokaci guda, take tsananin tsoronsa yakamata.

Muryanta har yana ɗan rawa ta ce. "Da...... Dadd........ Daddy.... Are you okey?"........ Ai bai san time da ya wani irin..............

E lallai Seraphina ta ɓaro babban aiki, da matsala kuwa, watau daman tasan sex? Har video ta taɓa gani, ba shakka yau Aryan zai ɓallata kuma ya kaita asibiti ayi ɗori, baby Cherry Bloom team yau kuma ruwa tsundum.

https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/zakuna-biyar-page-25-by-princess-teema

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
[10/01, 9:15 am] PRINCESS TEEMA YOLA: 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥



PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.





STEP 1🔥


2025-12-2.🔥



اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E_____________ 25



Muryanta har yana ɗan rawa ta ce. "Da...... Dadd........ Daddy.... Are you okey?"........ Ai bai san time da ya wani irin jan dogon numfashi ba. Kome ya tina kuma sai ya sassauta kallon da yake yi mata tare da cewa. "Cigaba da tambayarki". Ya mata haka ne dan yana son sanin iya abin da ta sani kenan ko akwai wani abin.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Some of my classmate they said if you want to have sax ka yi using protection dan kada ka samu pregnant parents ɗinka and uncles ɗinka zasu hukuntaka". Ta ɗan yi shiru tana kallon fuskansa.

Watau idan ya fahimceta tana magan a kan zina, idan kuwa haka ne classmate ɗinta and roommates ɗinta suna aikatawa kenan? Room ɗinsu ɗaya da Rimsha, yasan da haka, kuma shi ya ce a haɗasu ɗaki ɗaya lokacin da ya kaita, shiyasa aka cire cikon yarinyar da take ɗakin aka canza mata room aka barwa Seraph filinta, kenan idan haka ne Rimsha ma ta taɓa yin zina?. Lokacin guda ya ji wani irin buga mashi kansa ta yi, kalaman daddyn Rimsha ne ya dawo mashi cikin kai, in da yake cewa. "Ko na mutu a yau ba zan taɓa yin danasani ba, saboda ina da Aryan, ba shakka zai kula da Rimsha tamkar shi ya haifeta, dan haka bana jin zafin cewa zan mutu in barta". Waɗan nan sune kalaman daddynta na karshe-karshe a tsakaninsu kenan, hakika mahaifin Rimsha yana tsananin sonta tamkar ya yi mata numfashi, haka kuma yake kaunar Aryan.

Tabbas Aryan ya yi iya kokarinsa a kan Rimsha, kawai baya son ganinta a kusa da shi ne saboda tana tuna mashi da mahaifiyarta, kun sa dole zai ji zafi, ku tina yadda ya shaku da daddynta, amma muguwar uwarta ta zo ta shiga tsakaninsu, ta karya mashi zuciya, ya mutu adalilinta, dole Aryan ya ji zafi, amma a bayan fage ya tsayawa Rimsha sosai, dik familyn Abba babu wanda ya tsaya a tarbiyarta kamar yadda ya tsaya mata, dik da ya tsani ganinta amma yana ƙoƙarin ganin ba nemi wani abu ta rasa ba, kuma shi ya kaita boarding school dan kada ya dinga ganin fuskarta a gidan, amma ya sanya mata matakan tsaro sosai wanda bata sani ba, kawai in da yake ne ya tsani ganinta.

Hankalinsa ya yi balain tashi jin kalaman Seraphina, amma sai ya daure dan ya kara jin wasu bayanai, da kyar ya iya ce mata. "What's next?"........ Jujjuya idanunta sama ta ɗan yi kafin ta ce. "My roommate said that sex between ladies ya fi ladies and mens daɗi, wai idan zaku yi sex da mace ya fi, Laurat said that sex is sweet especially idan zaka yi sucking penis na boyfriend ɗinka with your mouth, and Aana tana taking wasu drugs wai dan kada ta samu pregnant idan zata bi su Robert yawon dare, to ranar da Senior ya ce in zo mu je ni da Rimsha Aana ta bamu drugs ɗin dan mu sha ni da Rimsha wai kada mu samu pregnant, wai sunan grugs


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login