Showing 105001 words to 108000 words out of 365093 words

Chapter 36 - Zakuna Biyar

26 Sep 2026

5903

عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E_____________16



Ihu amarya ta fara kurmawa, ta gudu cikin bedroom, cikin zafa ya bita ciki, tamkar babu hankali a kansa, ko da yake dama a irin wannan lokaci ba man kai suka cika ba na faɗa maku, dan a lokacin su kaɗai suka san ya suke jinsu, bare sun karɓi alluran karshe na fita horo, amarya tana tsakiyar dajin dake kewaye da zakuna, dan kuwa a kanta wannan allura zai fara aiki, kunga kuwa ita ai ta bar tarihi.

Duka ɗaya yai wa kofar bedroom ɗin nata ya ruguje, dan shi irin kofar wood ɗin nan ne. Ciki ya shiga, saman gado ta haye tana ihu. Aikuwa taka saman gadon ya yi da takalmarsa, tana ƙoƙarin gudu ya damki gashin kanta, dama ɗankwalinta ya cire tin da ta gudo ta baro parlo.

Tsabar razana da tashin hankali fitsari ta saki a zaninta a wajen. Ina ai bai san tana yi ba, waje ya jata da gashin kan nata, yana fitowa ya daddage ya buga mata kai da jikin bango kusa da ɗakin nata. Wani irin azababben ihun da ta zunduma sai da gabaɗaya unguwar ta amsa.

Ummie fa ja da baya ta yi, dan wlh ta ji tsoron tinkararsa, ta ce ba shi bane, an canza mata shi, bata tashi sanin haɗarin soja ba sai yau, kun san shi fa soja ko kakinsa firgita zuciya yake yi bare shi da yake horon AZURE kuma sabon passing out daga bar two bama bar one ba, ai amarya sai sorry.

Da gudu Ummie ta nufi kofar gida dan ta buɗe jama'a su kawo masu ɗauki, ita da kanin nata yau tsoron tinkararsa take yi. Tana buɗe kofar ta ga jama'a a tsaitsaye a kofar gidan, da sauri ta ce. "Jamilu ku zo ku taimaka mun kada ya kashe amarya!". Muryanta na rawa ta yiwa matasan unguwar magana.

Da gudu suka faɗo cikin gidan, daidai lokacin Zaynish ya kwashe kafafun amarya ta zube ƙasa kamar kayan wanki, kun san sojoji sun kware wajen iya kwashe kafafun mutane su zubar dasu a ƙasa.

Dik matashin da ya shigo da gudu yana ganin kalar uniform ɗin sai ya ja wata uwar birki, ba ɗan sanda ba ne bare a iya zuwa a sasanta, shi wannan daga nesa idan aka ga kakin kawai canza hanya ake yi in dai akwai tsama a tsakani. Matasa sun fi goma babu wanda ya iya karisawa wajen ya rikesa, wasu ma ai a miliyan suka juya da gudu suka bar gidan.

Makwabta mata da sun shigo sun ga mai dukan amarya zasu juya da gudu. Hankalin Ummie ya yi mugun tashi, ga shi ko kaɗan bata da zarrar iya zuwa ta kama shi, kuma ita kaɗai ce in ta kama shi kun san ba zai kai mata duka ba, zai daure, amma ina ta tsorata.

Wannan shegiyar takalmar tasu yasa ya fara ball da amarya, daga karshe ya kwance wannan shagiyar tattauran belt ɗin nasu, dukanta ya fara yi tamkar wanda aka saukarwa wahayin duka. Wani irin gigita Ummie ta yi, tsoronta kada ya yi kisan kai. Da sauri ta ce. "Jamilu dan ALLAH ku kama mun shi".

Wanda aka kira da Jamilu ne ya ce. "Aunty Ummie kina gani soja ne fa ba police ba, gaskiya ni ban shirya mutuwa ba"...... Da sauri na jefensa ya ce. "Kai ma kenan da kake matsayin abokin ɗan banga, mu kuma mu ce me? Ai kawai sai dai mu ce ALLAH ya jikan amarya idan ta mutu, dama ta ishemu a layin nan".

Kuka hawaye bibbiyu Ummie take yi, da kyar ta iya cewa. "Ku kama shi ba zai yi maku komai ba, kanina ne, dan ALLAH ku dakatar da shi"...... Ai ina dik cikinsu babu wanda ya motsa bare su yi yunkurin kama shi...... Dukan ALLAH tsine uwar mai karya Zaynish ya yi wa amarya, farfashe mata jiki ta ko'ina
, har sai da yaga ta daina motsi, sannan ne ya dakata yana cigaba da huci.

A fusace ya juyo da kallonsa a kan Ummie, haba ai a miliyan su Jamilu suka yanka kofar gida, sun ga zaki ya juyo, ka ji gudun karti wasu ta saman gini suka dira waje. Ita kanta Ummie kaɗan ya hana ta saki fitsari a in da take tsaye, ba dan tasan ciki ɗaya suka kwanta ba, ko mai wuya ba zai cutar da ita ba da wlh babu abin da zai tsayar da ita itama, tuni zata gudu, amma ta daure ta tsaya.

Dimfarota ya yi tamkar wani mayinwacin zaki, a gabanta ya tsaya, with harsh voice ya ce. "Dama irin zaman da kike yi a gidan nan kenan? Meyasa baki sanar dani ba? Ina Faisal ɗin yake? Sai ya faɗa mun idan jaka aka bashi ko ance mashi baki da gata ne!". Tashin sense, yau babu batun Yaya Faisal, Faisal kai tsaye, ba shakka da comrade Faisal na nan yau da shi ma ya gane ALLAH da girma yake.

Wani irin kerma da jikinta yake yi ne yasa ta gagara iya rike kanta, kasa ta durkushe tana cigaba da kallonsa har cikin ido, ta gagara bashi amsa. Tsawa ya daka mata da karfi wajen cewa. "Wacece wannan? Kuma ina Faisal ɗin na ce? Sai sun faɗa mun a gidan uban waye kika bi maza? Idan basu faɗa mun sun bani shaida ba billahil lazi sai na lahira ya fisu jin daɗi".

Hannu bibbiyu tasa ta dafe kirjinta dake barazanar tarwatsewa, still kallonsa take yi ta gagara yin magana, allurar tasa ta motsa, baya iya fahimtar a wani hali take ciki bare ya sassauta mata murya, sai ma tsawa da ya sake daka mata tamkar zai kai mata duka, daga karshe ma yasa hannu ya miƙar da ita tsaye, yana cigaba da huci ya ce ta lissafa mashi masu ce mata tana bin baza, da alama wannan kalma ta fi komai ƙona mashi rai. Har lokacin baiwar ALLAH ta gagara yin magana.

Jama'a sun cika kofar gidan dam, amma kowa yana tsoron shigowa, wasu matasa ma aka samu suka kira ƴan sanda. Mota biyu ƴan sanda suka zo, take jiniya ya karaɗe umguwar, zaku ce yaki ake yi, jama'a an yi cirko-cirko.

Ƴan sanda biyar ne suka diro ƙasa daga bayan motocinsu, da farko sun tsaya a waje, sai su Jamilu suka faɗa masu ai kisan kai za'ayi a cikin gidan, hakan yasa suka danno kai ciki da gudun gaske, a lokacin shi kuma yana tsaye gaban Ummie ya titseyeta kan lallai ta faɗi masu mata ƙazafin zina, yau sai sun bashi hujja ko kuma dik su ci ubansu ne, ba zai ɗauki nonsense ba, yana matsayin position 3 a bar 2 ɗin za'a kawowa rainin wayau? Tab!.

Da gudu ƴan sandan suka kewayesa suna faɗin ya natsu ko su harbesa har da ɗaga bindigu su nunnuna shi. Nan fa su Jamilu suka dawo cikin gidan dan ganin gulma, da a basu kabari gara su bayar.

Ai a miliyan Ummie ta ware, sai kuma ta fara ƙoƙarin kare Zaynish ɗin, muryanta na rawa a fara ƙoƙarin cewa ƴan sandan su yi hakuri su je rigimace ta cikin gida. Bata kai ga yin magana bama wani ɗan sanda ya ce. "Madam bai yi maki komai ba ko?"........ Da kyar ta iya ƙoƙarin buɗe baki zata yi magana, amma ta gagara saboda rawar da jikinta yake yi.

Shi kuwa wani irin juyowa ya yi tamkar bujumin zaki, dikka ƴan sandan sai da gabansu ya faɗi, baya suka ɗan ja suna faɗin kada ya motsa. Kallon tsab ya yi masu kafin ya ce. "Your gun down!". A sigar bada umarni ya yi maganar, dan ya ga dik ya fi ƴan sandan rank, dikkansu constables ne, ko soja dake bar one ya fisu rank bare shi da yake na uku a bar 2, ai ya wuci waɗan nan.

Jin yadda ya yi magana cikin bada umarni in a harsh way ne yasa suka ɗan ja baya, sun sha jinin jikinsu, slowly suka yi ƙasa da bindigunsu kamar yadda ya umarta. Ganin basu yi gardama ba sun yi biyayya ne yasa ya ɗan sauko ya yi masu bayanin waye shi, da sun yi gardama lallai da sun ɗanɗani karfin dukan hannun horon Azure yau, dan wlh yadda yake jin kansa tsab zai iya dukan zaratan maza 20 ko sama da haka, shi fa abokin balai ma yake nema yanzu ko zai sosa hannunsa dake mashi ƙaiƙayi, wai baku ga Vash a gida yana can yana ta faɗa da neman masifa bane? Ai haka suke bayan horo, dik su rikiɗe su zama wasu zakuna.

Ba karamin girgiza ƴan sandan suka yi ba jin waye shi, sannan ya ce masu zasu iya tafiya babu ruwansu da case ɗin nan. Sai a lokacin Ummie ta ce. "Ku yi hakuri kanina ne, faɗar gida ne, ba wani abin zai mun ba". Tana magana dai idanunta a kansa sosai.

Ganin tsananin kamanninsu na buzayen nan ne yasa suka yarda ƙaninta ne, dan dik wanda ya ganta ya gansa, dan ma dai shi wannan gashin nasu ma buzaye ya cika mashi kai sosai, yasa fuskansa ta ɗan rame, amma dik da hakan kamanninsu sosai.

Da sauri ƴan sandan suka karɓi umarni tin da sama da su yake, da gudu suka fice a gidan, sam basu lura da an sumar da amarya ba, su a zatonsu iya Ummie ce kawai. Ai suna fita su Jamilu suka bi bayansu, dan tsoron kada Zaynish ya bi ta kansu.

Suna fita Ummie ta yi ta mazan kama hannun Zaysh ɗin tin da taga ya ɗan sauƙo, shi ma sai a lokacin alluran ta ɗan sauƙa ya iya ganin firgicin dake kan fuskanta, ɗan rungomo shoulder ɗinta ya yi tare da cewa. "Sorry Ummie, wannan firgita dik na mecece?".

Ai da sauri ta rumgumesa ganin dama ya samu ya ɗan sauƙo, sabbin hawaye ne suka fara wanke mata fuska, da kyar ta iya cewa ya je ɗaki dan ALLAH ya basu dama ta kira jama'a a kai amarya asibiti, zai yi mata gardama ta ce. "Zaynish ALLAH idan ka mun gardama zuciyata zata iya bugawa, ka je ɗaki dan ALLAH".

Ganin yadda ta firgita sosai ne yasa ya hakura ya wuce cikin room ɗinsa, da sauri ta ɗauko wayarta ta kunna, number Faisal ɗin ta kira. Bugu ɗaya ya ɗauka, da yake bai san me yakefaruwa ba sai ya ce. "My ƴar aljanna yanzu nike son kiranki in ji kun iso ne, dik kewarki ta dameni".

Da kyar ya iya danne kukanta, ta harhaɗo natsuwa tare da girmamawa a garesa kafin ta fara faɗa mashi abin dake faruwa, bata ɓoye mashi komai ba. Fusata ya yi, ya fara yi mata faɗa da cewa dama amarya na jifarta da kalmar mazinaciya shi ne bata taɓa faɗa mashi ba? Meyasa dik rashin kunyar da amarya take yi mata take ɓoyewa bata faɗa mashi?.

Shiru ta yi tana sauraron faɗar tasa har ya kammala, sannan ne ta ce. "Ka yi hakuri, ban son haɗaka faɗa da matarka ce, amma ka yafe mun mijina"..... Shiru shi ma ya ɗan yi kafin ya ce. "Zaynish ya mun daidai, dan ko ni ne hukuncin da zan yi mata kenan, na sha faɗa mata tai maki biyayya, dan ita ƙaƙaba mun ita aka yi, ke kuma ni na ganki na ce ina so, kuna da bambanci, idan tana son zaman lafiya dani ta girmamaki, watau shi ne idan na fita take maki abin da take so ko? To ku kyaleta a wajen babu wani asibiti da za'a kaita!". Cikin faɗa da iya gaskiyansa yake maganar.

Ummie baiwar ALLAH ba zata iya ɗauke kai ba'a kai amarya asibiti ba, da sauri ta hau rokonsa kan ya yi hakuri a kaita. Da kyar ya yarda, sannan ya ce bari ya kira kannensa da kannenta su zo su ɗauketa.

Cike da mamaki ta ce. "Kai ka yi nisa ne da ba zaka zo ka kaita ba?"..... A natse ya ce. "Bana garin ne, na je tsakanin Adamawa da Taraba". ...... Zazzaro ido ta yi kafin ta ce. "Ma ka je yi can?".

"Wani abokina ne ya ce mu je haƙar gold a wajen, ya ce ana samun alkhairi sosai a wajen, akwai sabon wajen da aka gano yake da gold a wajen, to shi ne na ce bari in jarraba tin da aiki ya gagara samuwa, ki tayani da addu'a ƴar aljanna, ki mun addu'a in yi farar tafiya"..... Dik da bata so tafiyar ba dan tasan yadda ake mutuwa a wajen harkar gold ga wahala, amma hakan bai hana ta daure ta zuba mashi addu'a sosai ba, ya ji daɗi ya dinga amsawa da amin, sai da ya zuba mata kalaman kauna sosai, sannan suka yi sallama yana faɗa mata zai turo kannen amarya yanzu, kuma yana umartanta da ta shige ɗaki yanzu, sannan ta gaida mashi da kaninsa Zaynish ta kuma bashi hakuri da abin da ya faru.

Da okey ta amsa tare da yi mashi fatan alkhairi, daga haka suka yi sallama ya katse kiran, gagara komawa ɗaki ta yi, haka ta samu fili a wajen ta zauna har lokacin da ƴan uwan amarya suka zo suka ɗauketa, basu yi wa kowa magana ba, dan already Faisal ya faɗa masu cewa akwai zaki jarumin jarumai a gidan, su kula su kuma haɗe malaman jikinsu waje guda, idan ba haka ba jikinsu ya faɗa masu ma, shiyasa basu yi magana da kowa ba suka ɗauketa suka fita, hegiya ta ji maza ta sume.

Ita kuma Ummie da aka tafi da amarya sai ta bi bayan Zaysh izuwa ɗakinsa dake gidan, kuma yana ma da ɗaki a gidan uncle ɗinsa, kawai Ummie ta matsa mashi su sauƙa a gidanta da safe sai suje gidan uncle ɗin ne, baya son zama a gidanta yanzu da ya kara girma, a da dai lafiya lou ya zauna lokacin yana yaro.

Zaune ta iskosa yana danna waya, ya sanya sim card ɗinsa ta nan gida Naija, da alama wani abin yake son yi. A kusa da shi ta zauna zata fara magana kenan taga yasa waya a kunne, cikin sanyin murya suka gaisa da uncle ɗin nasa, sannan ya faɗi mashi ya dawo, sun iso lafiya. Watau Zaysh ɗan halak ne na gasken-gaske, dik da halin da matar uncle ɗinsu ta jefasu a ciki hakan bai hana shi yana yabawa uncle ɗin nasa kuma yana kara gode mashi ba, and kome zai yi sai ya fara sanar mashi kafin ya yi, tamkar uba haka ya ɗaukesa dan yasan ba laifinsa bane, ba shi ya muzguna masu ba, matarsa ce ta yi komai.

Bayan sun gama gaisawa da uncle sun yi sallama ne ya miƙe tsaye, da sauri Ummie ta rike hannunsa tare da cewa. "Ina zaka je?"....... A taƙaice ya amsa da. "Wanka". Sakesa ta yi tare da miƙewa tana faɗin ya zauna bari ta haɗa mashi ruwa. Da a'a ya amsa mata, ya kara da cewa ita da bata da lafiya, ta zauna shi bari ya haɗa da kansa tin da shi ai ba bakon gidan bane.

Zama ta yi tana sauke numfashi a hankali-hankali, shi kuma ya fito ya ɗebi ruwa a bokiti ya wuce toilet dan ya yi wanka.

-------------------------🔥

C-P.

Basu dawo gidan ba sai da suka yi sallar ishai, sannan suka shigo. One by one suka tsala wanka, suka shirya cikin sleeping dress iri guda, sannan suka shiga ɗakin aikinsu.

A gaban computers ɗinsu suka zauna, Lion ne ya kunna wani video na zanga-zanga da ake yi a ƙasar AVARIS, natsuwa dik suka yi suna kallon video mai tsawon mintuna 33, sai da suka gama kallo tsab sannan ya tsayar da video tare da cireta gabaɗaya.

"What are you thinking?". Lion ya faɗa tare da kunna wata recorder. Shiru dikkansu suka yi na a ƙallah 2 mins, sannan guru ya ce. "Batu ne a kan rashin tsaron dake Avaris ko?"....... Kai kawai Lion ya ɗan girgiza alamar a'a kallonsa a kan Champion da ya shiga duniyar tinani na daban.

"Yakamata mu sanya ido a kan Avaris sosai, saboda rashin tsaro ya yi yawa, wahala da yunwa sun yawaita, abin mamakin kuma kasar Avaris ita ce ta uku a dukiya da karfin tattalin arziki da albarkatun ƙasa, meyasa kuma take zuwa matsayin sahu na gaba a yunwa, wahala, rashin tsaro, ma'aikata babu albashi, sojoji ba'a biyansu yadda yakamata, dik duniya babu barrack ɗin da ya kai AZURE yaye ɗalibai masu kaifi, fikira da basira, ga horo na musamman da ko ba bindiga zasu iya gwabza yaki, to amma meyasa sojojin basa iya kama ƴan ta'addan? Meyasa komai yake tafiya a juye?". Guru ne ya faɗa cike da damuwa sosai a ransa.

Champion ne ya ce. "Babu wani abin da yake tafiya a juye guru, komai a daidai yake tafiya cikin tsarinsu, sai dai ƴan kasar ne suke ganin kamar komai a juye masu yake saboda an juya tunanin kwakwalensu". Ya faɗa without looking at them, da alama yana jinsu amma ba dikkan hankalinsa bane a kansu.

One thing, da guru da Lion suna da alaƙa mai karfe da AVARIS and AZURE BARRACK shiyasa suke damuwa da ƙasar sosai, kullum aikinsu a kan shawo kan matsalar kasar ne, dan Avaris tana daga cikin top ten ƙasa masu shan bakar wahala a duniya, kuma tana cikin top ten na ƙasashe masu karfin tattalin arziki da albarkatun ƙasa da ruwa, to me matsalar? Abin da kowa ya gagara ganewa kenan, amma alƙalamina zai faɗa maku me matsalar!.

"Zancenka gaskiya ne Champion, amma a tinaninka meyasa Avaris tana da yelwar arziki, ga wadataccen noma, idan ka duba a kididdigar da muka yi suna iya noma abincin da ƙasar zata iya ci ba tare da sun ji yunwa ba, meyasa suke fitowa neman abinci? Manoman dake noma suna fama da yunwa da bakar wahala, meyasa?". Cewar guru.... A wannan karon Champion baya tare da su, so bai ma ji tambayar ba.

Shiru ne ya biyo baya for almost 5 mins, dama shi Lion kullum a karshe yake magana, sai ya gama jin dik abin da zasu faɗ, ya gama jin ra'ayin kowa kafin ya faɗi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login