Showing 54001 words to 57000 words out of 250912 words

Chapter 19 - RAGAYAR DUTSE BOOK2 COMPLETE

06 Oct 2026

1687

iya tara ku

ɗ

in wanda ta aro a ƙasa da shekara

ɗ

aya.

Ta yi ajiyar zuciya tana tunani, ta

ɗ

an sauke

numfashi cikin tunanin abinda ya kamata ta yi, dan gaskiya sai ta biya ku

ɗ

in nan hankalin ta zai kwanta. Ya kamata ta yi tunanin da ya kamata, indai zata samu ku

ɗ

i ta sauke nauyin bashi ko meye zata yi.

Dafata ta ji anyi daga baya, ta juya a firgice tana

kallon wanda yake tsaye a bayan ta.....

[6/25, 11:14 AM] KRBBK: RDB2P20

Nana Haleema

Tana juyawa suka ha

ɗ

a ido da Zainab, Islaha ta

ɗ

an sauke numfashi cikin tsoro ta ce, "kin bani tsoro Zainab." Zainab ta bita da kallo, kafin ta rungume ta cikin kewar ta

ta ce, "na yi kewar rashin ki sosai Adda Islaha, na yi kewar ki."

Islaha ta riƙe hannunta tana murmushi ta ce, "nima na yi kewar ki Zainab. Ya na ganki haka, akwai matsala ne?."

Zainab ta

ɗ

an yi shiru kafin ta ce, "Adda Islaha Mama ce ta saka a sace k

i, na ji da kunnena tana waya tana cewa a tabbatar an

ɗ

auke ki."

Islaha ta ja hannunta suka zauna a inda babu jama'a sosai, ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce, "ban gane ba, yi min bayani yadda ya kamata."

Zainab ta ce, "Ina nufin Mama ce ta saka a sace ki,

saboda kina saka mata ido akan abubuwan da take aikatawa."

Islaha ta yi shiru tana tunani cikin ru

ɗ

ani, kenan mutanen da suka sako ta a gaba suna da yawa, tunda ga wata maganar ma ta sake

ɓ

ullowa daga inda bata yi tunani ba. Bata nunawa Zainab firgici a

kan haka ba sai ta ce, "fa

ɗ

a min damuwar ki Zainab."

Zainab ta sauke nunfashi ta ce, "Zaman gidan ya yi min zafi Adda, na gaji da zaman gidan wallahi. Abubuwan da ban yi zato ba suna ta faruwa, na kasa tsallake wasu abubuwan."

"Me ya faru?."

"Adda gaba

ɗ

aya kowa na gidan da kowa na gidan canjawa yake yi, ma'aikatan gidan Mama ta siye su, kowa a ƙarƙashin ta yake, shiyasa ba a ta

ɓ

a jin

ɓ

arnar da take cikinsa a bakin kowa ba. Da zarar maganar ku

ɗ

i ta shiga shikenan sai a canja.."

"Akwai wata mata da ta tak

urawa Mama akan a kaini gidanta, kullum sai an takura min da maganar matar. Wai in na je za a canja min makaranta, za a yi kaza da kaza. Ni na gaji, da kin yi aure gidanki zan dawo da zama kawai, gaba

ɗ

aya zaman gidan ya fita daga raina."

Islaha ta

ɗ

an yi

shiru sannan ta sauke numfashi ta ce, "in aka kai ki gidan me zaki yi a can?."

"Nima ban sani ba, amma kamar ba abin arzuƙi zan aikata ba, dan matar kwata-kwata bata kwantan min a raina ba."

Ta girgiza kai ta ce, "kina ji, ki kwantar da hankali ki, babu

abinda zai same ki sai alkhairi. Ina tare dake a ko yaushe a ko ina. Ki nutsu ki ji abinda zan fa

ɗ

a miki."

Zainab ta

ɗ

aga kai Islaha ta ce, "kar ku

ɗ

i ko wani abu ya ru

ɗ

e ki kamar Hafsa, ki cigaba da bijirewa, duk abinda za a ce miki kae ki yarda, ki nun

a kw bakya ra'ayi. In aka takura ki amince ki je gidan, da zarar an tafi kai ki ki yi min waya ki fa

ɗ

a min inda aka kai ki. Ni kuma a wannan lokacin zan ha

ɗ

a hujja da nake son ha

ɗ

awa akan su Mama da ma'aikatan gidan, in abin nan ya tabbata wallahi sai na y

a

ɗ

a ta a ko ina, sai gwamnati ta san abinda take aikatawa da sunan riƙe marayu."

Zainab ta share hawaye ta ce, "in na bisu babu matsala?."

"Babu komai, Amma kafin ki tafin ki tabbatar kin sanar dani, yadda zan shirya komai na biyo sawun ki."

"Zan yi duk

abinda ki ka ce Adda."

"Yauwa Zainab. Allah yana tare dake, bazai ta

ɓ

a bari ki wulaƙanta ba in sha Allah."

"Allah yasa."

"Amin."

"Adda kayana duk sun yi min ka

ɗ

an, bani da kayan sakawa sosai."

Islaaha ta dafa ta, tasan yadda ake ƙarancin kaya a gida

n marayu, ta san yadda kayan sakawa suke yankewa, ta san yadda yaran da basu kai matakin sana'a ba suke rasa kayan sakawa. Wani lokacin sai masu ziyara sun zo sun kawo kaya, a nan ne za a za

ɓ

i wanda bashi da kayan sosai a bashi ya rage ko ya ƙara. Ita kant

a ta shiga irin wannan yanayin, har ta kai ta kawo tana cire kaya ta wanke da daddare ta shanya,washe gari ta kuma mayarwa jikinta.

_(Ƴan uwa ga wanda Allah ya bawa dama, in an ha

ɗ

a kayan sakawa na bayarwa, a dinga tunawa da yaran da suka tashi a gidan ma

rayu. Kayan yara ko na manya, na maza ko na mata, a dinga taimkawa ba a san inda za a dace ba. Allah ya sa mu dace amin.)_

Islaha ta ce, "Akwai kayan da zan baki, sannan akwai ku

ɗ

in da zan tura miki, ki shiga kasuwa ki siyi ƙananun atamfofi ki bayar a gid

an a

ɗ

inka miki. Ba su Kamila suna

ɗ

inki ba?."

"Suna yi Adda."

"To ki bayar a

ɗ

inka miki, nawa da zan baki ki basu su rage miki. Zan tambayi Safeera ma in tana dasu ta sake ha

ɗ

o miki, indai ina da rai babu abinda zaki nema ki rasa Zainab."

Ta yi murmush

i ta ce, "Allah ya bar min ke Adda Islaha, Allah ya baki miji na gari, mai ku

ɗ

i wanda zai

ɗ

auke ni na koma gidansa."

Ta yi murmushi ta ce, "Amin Zeey. Ina auren Hamma zan

ɗ

auko ki, kin gama zaman gidan nan in sha Allah." Zainab ta yi murmushi, suka cigaba

da hirar gidan, har Zainab ta yi mata sallama ta tafi.

Bayan tafiyar Zainab Islaha ta yi shiru tana tunani, abubuwa uku suna yi mata yawo a cikin kanta, abubuwa uku suna kai kawo a tsakiyar ƙwaƙwalƙwar ta. Zainab, Mama da ta da ta saka a sace ta, uwa uba

ku

ɗ

in mutumin da ta

ɗ

auko, dan ya fi komai

ɗ

aga mata hankali a halin da ake ciki.

Ta yi ajiyar zuciya cikin nauyin ƙirji, a lokacin Safeera ta ƙaraso ta zauna, suka

ɗ

an cigaba da hira duk da hankalin Islaha baya tare da ita ko ka

ɗ

an, wani abun daban take

tunani.

••••••

*JEDDAH, SAUDI ARBIA*

*AL HAMRA, CORNICHE RESIDENCES.*

Unguwa ce mai kyau da tsari, unguwa ce mai

ɗ

aukar hankali tun daga kallon farko zaka san ko a cikin ƙasar saudia ba ƙananun mutane ne suke zaune a cikin ta ba. Unguwa ce mai ci

ke da tsafta, da tsaro na musamman.

Ko ina na kan titin unguwar al hamra cike yake da cameras saboda tsaro, unguwa ce da take kusaa da ƙaton tekun Corniches, babban ocean da yake

ɗ

aya daga cikin manya manyan ruwan da ake ji dasu a garin Jeddah. Unguwa ce

da take

ɗ

auke da gidaje masu kamar hotel, wan

ɗ

anda ake yi musu laƙabi da hotel style. To ko wanne

ɓ

angare unguwar Hamra ta yi.

Rehaan yana tsaye daga cikin apartment

ɗ

insa, yana tsaye a bedroom

ɗ

insa ya yaye labule yana kallon ƙaton ocean

ɗ

in da ya mamay

e bayan

ɗ

akinsa.

Hannunsa riƙe da mug yana shan tea a nutse, hannunsa

ɗ

aya yana cikin aljihun wandonsa yana kallon yadda mutane suke hutawa a wajan, suna kai kawo ana shan drink. Ya sauke numfashi yana lumshe idanunsa, haka kawai fuskar Islaha ta zo idan

unsa, ya

ɗ

an runtse ido yana cize bakinsa, irin ka tuna abinda baka so ka tuna

ɗ

in nan. Ya yi ƙoƙarin kawar da hotonta daga idanunsa, ya cigaba da shan tea

ɗ

in amma still ita yake gani tana harararsa.

Kalamanta ya tuna, sai ya murmusa ya girgiza kai yana

ta

ɓ

e bakinsa. Shi bai ta

ɓ

a ganin yarinya mara hankali kamar ta ba, da zai san danginta da ya basu shawarar a kai ta asibiti a dubu lafiyar ta, dan tana da matsalar ƙwaƙwalwa.

Door bell

ɗ

in da aka danna ya katse masa tunani,ya fito daga

ɗ

akin a nutse, ya s

auka downstairs ya ƙaraso ya bu

ɗ

e ƙofar falon.

Ubaid da Maleek ya gani, maƙotansa mafi kusa, wanda gidansu yake kusa da na juna. Apartment

ɗ

in Rehaan shine a tsakiya, sai na Ubaid a

ɓ

angaren dama, sai Maleek a

ɓ

angaren haggu. Ubaid likita ne shima, sun ta

ɓ

a aiki a asibiti

ɗ

aya shi da Rehaan, ta dalilin haka suka saba dashi.

Sun saba da juna sosai, tare suke ha

ɗ

uwa a buga ball, a

ɗ

an sha tea, a yi hira. Dukkansu larabawa ne, Maleek balaraben Saudiya ne haihuwar Riyad, Ubaid kuma balaraben Egypt ne. Maleek

yana da aure, Ubaid kuma bashi da aure.

Rehaan da ya bu

ɗ

e ƙofa ya gansu sai ya yi murmushi yana kallon su kamar yadda suke kallonsa suna murmushi.

Cikin turanci harshen Maleek ya ce, "Rehaan barka da zuwa." Gaisawa suka yi, suka shiga falon suka zauna.

Rehaan ya zauna shima ya ce, "ya aiki?."

"Alhamdu lillah. Baka fa

ɗ

a mana zaka zo ba, da mun shirya maka abubuwa na musamman."

Ya

ɗ

an murmusa ya ce, "na zo aiki ne, bazan jima ba zan koma."

Ubaid ya ce, "ina Jafar?."

Rehaan ya ce, "Yana Englaand."

Maleek ya ce, "kai ka

ɗ

ai zaka zauna?."

Rehaan ya

ɗ

aga musu kai yana

ɗ

an murmushi bai ce komai ba. Sai kuma Rehaan ya ce, "yauwa ina son house maid, ku tura min maid daga wajan ku, zan dinga biyansu in sha Allah."

Ubaid ya ce, "Bani da House maid, amma

za a kawo min daga Nigeria. Ka san na fi son aiki da yan ƙasar ku, musamman mata."

Rehaan ya bisa da harara cikin takaicin wanann

ɗ

abi'a ta Ubaid. Ubaid ya yi dariya ya ce, "da gaske nake, za a kawo min house maid daga can. In sun zo sai mu dinga sharing

, is normal."

Rehaan ya yi masa banza, dan in akwai abinda yake jin haushi bai wuce matan ƙasar sa da suke barin ƙasarsu su taho aikin gidajen larabawa ba, abin yana yi masa ciwo matuƙa, dan bashi da damar da zai hanawa ne, amma wallahi da sai ya hana

ɗ

a

n nigeria zuwa Saudia aiki a gidan larabawa.

Ƙ

asa mai girma da daraja kamar Nigeria, amma matan cikin ta sun saka ƙasa suna tuntsurar da mutuncinta. Da ace aiki ne mai tsafta da tsari da sauƙi, to yawancin wannan aikin da shirme da watsewa yake ƙarewa. Du

k da ba duka ne

ɗ

aya ba, amma majority haka ce take faruwa.

Ya san kalar rayuwar da suke yi a ƙasar, ya san babu abinda larabawa suka raina a yanzu kamar ƴan Nigeria, saboda ƙasƙantar da kansu da suke yi a ƙasar da sunan aikatau. Yana zama cikin larabawa,

yana jin yadda suka mayar da matan nigeria kamar toys, wasu matan sune suke kawo musu kansu dan su samu ku

ɗ

in abinci.

Ya san halin Ubaid sosai, mayen ƴan mata ne lamba

ɗ

aya, duk macen da ta yi aiki a gidansa sai dai Allah ya kyauta kawai, dan yana da ku

ɗ

in da yake sakar musu, lokaci

ɗ

aya mata suke rikicewa, su ru

ɗ

e duk abinda yake so zasu yi masa shi. Shiyasa har rige rigen kawo masa ƴan mata ake yi daga nigeria. Dan wanda ya kawo ma zai samu, itama in ta bada kanta babu abinda bazai yi ba, baya jin ƙyash

in kashewa ƴan mata ku

ɗ

i, ƴan matan ma na Nigeria, musamman baƙar fata. In aka ce mace baƙa ce ta shiga uku a wajen Ubaid, ya dinga nacewa mace kenan har sai ta amince masa, dan yana da kyau da ku

ɗ

i, da wuri suks fa

ɗ

awa.

Shi kuma Rehaan haushin hakan shi

yasa basu cika shiri da Ubaid ba, Maleek ne mai halin kirki, sun fi shiri dashi sosai akan Ubaid. Bai shiga shiga harkar Ubaid ba, dan ya tsani

ɗ

abi'unsa sosai.

Maleek ganin yadda Rehaan yake hararar Ubaid sai ya yi dariya ya ce,"Kar ka damu Dr, zan turo

maka housemaid daga gidana, duk da nima babu sosai, amma za a kawo. Matsalar suna jin tsoron cheetah da ka ke kiwo ne fa."

Ya

ɗ

an yi murmusui yan shafa kansa, sai a lokacin ya tuna bai ma je ya

ɗ

auko ajiyarsa ba, daman Jafar ne yake takura masa akan a

ɗ

a

uke su, amma shi kam yana son kiwo, musmaman kiwo irin na su Cheetah wanda ba a ko ina ake yin su ba sai a gidajen larabawa. Kiwon damisa ko zaki a manyan gidajen larabawa ba komai bane, sun saba yi sosai. Ya so ya yi a gida Nigeria Abba ya hana, sai da ƙa

nanun abubuwa irinsu

ɗ

awisu.

Ya ce, "in anjima zan je na

ɗ

auko ta, kuma baza ta yi musu komai ba. Ƙarama ce sosai, bata cutarwa."

Maleek ya ce, "nima tsoron gidan nan naka nake ji indai har suna nan."

Ya sake yin dariya ka

ɗ

an, kafin ya tashi da niyar

kawo musu black tea, sai da ya shiga kitchen

ɗ

in ya yi tsaki, dan shi ya tsani aiki, yafi so komai ayi masa.

A kawo masa tea kuma a

ɗ

auke cup

ɗ

in, inda dama a bashi a baki hakan yafi masa da

ɗ

i. Ya tsani sai ya dawo daga aiki ya dafa tea, shiyasa yake tsa

ywa a cafe ya siya,  yana tuƙa mota yana sha. Gaba

ɗ

aya ya sangarce, babu abinda ya iya sai dafa tea

ɗ

in kawai, shima daga ruwa sai lipton da sugar, bayan hakan babu abinda ya iya sakawa. Shiyasa ya damu da rashin housemaid

ɗ

in, sai danasani yake da bai tah

o da chef ba.

Yana dafa ruwa a kettle yana tsaki, yana ji ransa yana

ɓ

aci, yana jin dole ma a samu masu aiki, dan shi bazai iya wata wahala ba, daman Jazy ne ya sallame, gashi ya rasa yadda zai yi. A haka ya kawo musu suna sha suna ƴar hira ka

ɗ

an ka

ɗ

an.

Nana Haleema.

[6/25, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P021

Nana Haleema.

Ummi ta bi Muslim da kallo lokacin da ya shiga office

ɗ

inta, bayan ya zauna ta miƙe ta rufe ƙofar ta jingina da ƙofar ta ce, "meye plan na gaba?."

Ya bita da kallon mamaki da tsoro ya ce, "k

ina nufin baki zubar da makamanki ba duk abinda ya faru?."

Ta sauke numfashi tare da har

ɗ

e hannu a ƙirji ta ce, "Yanzu aka fara wallahi, dan an kama ni an kai ni gaban hukuma ba hakan yana nufin zan ja da baya ba."

Muslim ya girgiza kai ya ce, "kina ban

i tsoro Ummi, har yanzu akwai zargi a kan ki fa"

"Sai me?."

"Hmmm! Na

ɗ

auka kin yi sanyi ai."

"Har abada wallahi, sai na ga bayan Islaha."

"Dakyau! Kin san in aka kama mai keken nan akwai damuwa ko?."

"Yana ina yanzu haka?."

"Na ce ya

ɓ

uya, kar ya sa

ke ya fito inda mutane zasu ganshi, in aka kama sa kema kin san mu ma nun kamu."

Ta dafe kai ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Ni so nake na ji ka shirya wani abu akan Islaha, so nake na ji ka ha

ɗ

a gagarumin plan

ɗ

in da zai tarwatsata ita da rayuwarta gaba

ɗ

aya.

"

Muslim ya ce, "

ɗ

aukar mataki a kanta ba abu ne mai wahala ba, amma zamu

ɗ

an jinkirta saboda idon mutane da yake kanta a yanzu. Duk wani motsinta an saka hukuma tana bibiya, samun galaba a kanta a wannan lokacin abu ne mai wahalar yuwa. Amma akwai babban

shirin da zan yi a kanta, farin jinin da take dashi a duniya nake so na lalata, ta yi baƙi a idanun al'ammu, a daina ganin farin ta ko ka

ɗ

an."

Ummi ta ce, "da zarar an ga fuskarta a dinga bad comments, sannan a dinga cewa ba a buƙatar fuskarta."

"Haka n

ake so na yi Ummi. Ina so na samu wani abun da zan yi posting wanda zai tarwatsa rayuwar ta gaba

ɗ

aya."

"Me zai hana baza muyi amfani da AI ba?."

"Kusan kowa ya gano AI yanzu, ana gani za a iya fahimtar sa ba tare da dogon nazari ba. Ita da kanta nake da

buƙata ta aikata ba AI ba."

Ummi ta yi shiru tana tunani kafin ta ce, "to ya za a yi yanzu?."

Ya sauke numfashi ya ce, "ni na san abinda ya kamata nayi, tunda acid bai yi aiki ba, wani abun zai yi mana amfani. Ke dai ki zama cikin shiri, ko yaushe zaki

iya jin labari akan Islaha."

Ta yi dariya ta ce, "ko yaushe a shirye nake, indai akan ganin bayan Islaha ne, na

ɗ

aura

ɗ

ammara."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login