Showing 117001 words to 120000 words out of 250912 words
kichen. Abinda ta gani ya saka gabanta ya fa
ɗ
i, kaji ne masu yawa sosa
i, ta nuna mata alamun ta gyara.
Umma ta ji kamar ta kurma ihu saboda takaici, ta bi kajin da kallo dan a ƙalla zasu kai hamsin. Matar ta ware wanda in aka gyara za a saka a fridge, da wanda Umma zata gasa.
Umma ta ƙarasa ta fara gyarawa, tana yi tana h
awaye saboda gajiya. Tana tsaka da yi aka ce ta zo ta gyara waje an
ɓ
ata. Ta fito ta gyara ta koma ta cigaba da aikin.
Aikin sai da ya
ɗ
auke ta awa biyu da wani, ta gaji matuƙa, bayanta kamar zai
ɓ
alle saboda gajiya mai tarin yawa. Daƙyar ta ke jan ƙafa
ta shiga
ɗ
aki, ta cire kaya ta shiga wanka dan khamshin gashin kaza kawai take yi. Tana fitowa daga wanka ta ji an rufe ƙofa, tana juyowa ta ga mutuminta a tsaye yana kallon ta.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Umma ta fa
ɗ
a hawaye cikin tashin hanka
li.
Ya fara takowa zuwa inda take a hankali, Umma ta fara ja baya tana kalle kalle tana so ta samu wani abun da zai zamar mata makami.
Babu komai a wajan sai ta
ɗ
auki wayar ta tana muna masa, cikin turancinsu na manya ta ce, "Police, zan kira Police zu
zo su kama ka wallahi, kar ka matso kusa dani." Jin ta ambaci police sai ya tsaya, kafin ya juya ya fita daga
ɗ
akin.
Umma ta zube a kan gado kwai ta fashe sa kukan takaici da sanasani. Whatsapp call
ɗ
in Atika ne ya shigo, tana
ɗ
auka kawai ta fashe da kuk
a.
Atika daga can
ɓ
angaren ta ce, "Maimuna me ya faru ki ke kuka?."
Umma cikin kuka ta ce, "Na gaji Atika, gida nake son dawowa. Na gaji da zama a nan, aikin ya fita daga raina, ina so nazo na riƙe ƴaƴana. Wahala nake sha, ga tsawa, ga aiki, ga raini.
Na gaji wallahi."
Atika ta ce, "da wuri haka? Gaba
ɗ
aya kwanan ku nawa da tafiya da ki ke son dawowa? Ko har kin tara da yawa ne?."
"Wallahi babu abinda na tara, hasalima bani da ko sisi a hannuna. Ɗazu layin waya na je siya, sai ranta min ku
ɗ
in aka yi da
n bani da komai. Na gaji Atika, Ki ta ya ni da addu'a, Allah ya ku
ɓ
utar dani daga hannunsu."
"Kin san dawowar ki yanzu bazai yu ba ko? Dole sai kin gama biyan wa
ɗ
anda suka kai ki ku
ɗ
insu ko?."
Kukan Umma ya ƙaru ta ce, "na sani, shiyasa na ce ki taya ni
da addu'a."
Atika ta ce, "ki yi haƙuri, zaki saba a hankali."
"baza ki gane halin da nake ciki ba. Ga wahala, ga fargaba, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Haka kawai zan bu
ɗ
e ido na ga magidanci tsirarara a gabana. Ya zan yi?."
Atika ta ce, "haƙuri zaka y
i, a hankali komai zai zama labari."
Umma ta ja numfashi ta ce, "Safeera har yanzu fushi take yi dani, ki bata haƙuri ki ce ko sau
ɗ
aya ne ta yi magana dani."
Atika ta ce, "zan yi mata magana in na shiga gidan. Ki cigaba da haƙuri, ki ta addu'a, Allah
ya kare ki daga sharrin shai
ɗ
anin can."
Umma ta
ɗ
aga kai kamar tana gabanta ta ce, "ki ta ya ni, ki saka su Rukayya su ta ya ni. Ina so na nemi afuwar su Yayan Katsina ban san ta ya zan fara ba."
Atika ta ce, "Allah zai kawo mafita, ki cigaba da haƙur
i." Umma ta amsa suka yi sallama zuciyarta cike da abubuwa kala kala......
Nana Haleema.
[7/7, 6:25 PM] KRBBK: RDB2P43
Nana Haleema.
_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments
ɗ
in ku a first five
episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link
ɗ
in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode
ɗ
in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L
••••
••••••••
*YOLA.*
"Ummi meyasa bakwa yin aiki yadda ya kamata ne? Har yanzu ƴan kallo complain suke yi akan rashin Islaha, mun rasa mabiya da yawa saboda rashin ta. Da Saleem ya duba shafin mu na tiktok mutane sama da dubu uku sun yi unfllowing
ɗ
inmu sabo
da rashin fuskar Islaha. In mu ka yi posting a ko yaushe magana
ɗ
aya ce, su dai a dawo da Islaha ko su daina bibiyarmu. Shirin Rayuwatatalkshow views sun ragu sosai, lokacin da Islaha tana nan sai a samu masu kallo sama da dubu
ɗ
ari biyar, amma tun bayan t
afiyar ta ba a wuce dubu hamsin, wani har dubu ashirin. Me yake faruwa ne?."
Tunda ya fara magana Ummi da Jamila suka yi shiru, sai da ya gama sannan Jamila ta ce, "Chairman tsakani da Allah sun fi son fuskar Islaha, saboda son da masu kallo suke yi mata
ya saka ta sama permanent a
ɓ
angaren interview da talkshow, sai ta ƙure ake canja ta a
ɓ
angaren. Ba laifin bane, mun iya aiki daidai ƙarfinmu, kawai zuciyarsu tana tare da Islaha ne shiyasa ake samun matsala. Kuma baza mu maye gurbinta ba, sai dai mu yi ab
inda zamu iya."
Chairman ya ce, "Yanzu haka za a cigaba da zama kenan? Muna samun masu kallo dubu
ɗ
ari uku zuwa
ɗ
ari mun dawo dubu ashirin?. Ko interview
ɗ
in da Muslim ya yi da minister tsaro akan satar yaran nan, har yafi interview
ɗ
in Ummi views. Asara
mu ke ta tafkawa, kwata-kwata bata yi sati uku da tafiya ba, amma muna ta samun naƙasu akan harkokin mu."
Ummi ranta
ɓ
aci yake yi, baƙin ciki da hassadarta suka sake ninkuwa fiye da baya, hassada ta
ɗ
aure mata harshe ta kasa cewa komai balle ta yi magana.
Chairman ya ce, "ina magana Ummi kin yi yi shiru."
Daƙyar ta bu
ɗ
e baki ta ce, "To Chairman na rasa me zan ce ba, gani ka ke kamar ba ma yin ƙoƙari a aikin nan, ka manta tun kafin Islaha mu ne muke tafiyar da komai yadda ya kamata, zuwan ta ne ta asiri
ci kowa ya zama babu mai son fuskar mu sai fuskar ta."
"Ke Ummi bana son shirme, wanne irin asiri kuma?."
Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, shi kuma ya ce, "baza ki iya bakin ki ba? Baki daddara da abinda ya faru ba ko?."
"Chairman ai ba wani abun
na ce ba, gaskiya ce ba wani abun ba."
Chairman ya ce, "ke ki ka sani kuma, ni dai in aka cigaba da samun akasi wallahi zan canja ku gaba
ɗ
aya na zuba wasu. Bazai yu na dinga asara saboda ku ba."
Jamila a tausashe ta ce, "ka yi haƙuri Chairman."
Ya ja
tsaki ya ce, "ku je. Sannan ku aiko min da Safeera."Basu jima da fita ba Sfeera ta shiga da sallama.
Ta ce, "Chairman gani."
Chairman ya ce, "Safeera ban tabbatar rashin ƙawarki zai ta
ɓ
a mu har haka ba sai yanzu da mu ke ta samun raguwar mabiya. In ki
ka duba comments section zancen Islaha ne, in bamu dawo da ita ba su dai zasu daina bibiyar mu."
Safeera ta ce, "ina lura da komai Chaairman."
"babu batun dawowar ƙawar ki nan kusa Safeera? Kina gani bata rufe sati uku ba har yanzu, amma mun rasa mutan
e masu yawa. Ya ki ke ganin abinda zai kasance in ta sake kwanaki bata nan?."
Safeera ta ce, "In sha Allah baza a sake rasawa ba, zan tambaye ta in na koma na ji yaushe zata dawo, in sha Allah zata dawo a cigaba da komai kamar yadda aka sa ba."
"Don All
ah ki tambayar mana ita, rashinta zai iya sakawa mu rasa abubuwa da yawa. Guest uku muka kaiwa katin gayyata amma sun bamu uzuri, abinda bai ta
ɓ
a faruwa damu ba kenan. Da zarar Islaha ta kaiwa mutum iv yake saka mana lokaci, wani ma shi zai ce ta saka loka
cin da ya yi mata. Don Allah ku yi magana da ita."
Safeera ta ce, "in Allah ya yarda zamu yi magana, zata dawo komai zai dawo."
Chairman ya ce, "na gode Safeera, ki je ku cigaba da aiki."
Lokacin da ta fito office ta koma, tana shiga Saleem yan shigow
a ta kalle sa ta ce, "Chairman ne ya yi min magana akan rashin Islaha, ba ka gani ba kamar ya yi kuka. Da yana da iko da ya yi fuffuke ya je ya
ɗ
auko Islaha ta dawo, ta
ɗ
ora daga inda ta tsaya."
Ya yi murmushi ya ce, "Rashin ta ya ta
ɓ
a gidan gaba
ɗ
aya, ha
r bana son bu
ɗ
e tiktok saboda yadda za ki ga ana wulaƙanci dan ba ita bace."
Safeera ta yi dariya ta ce, "Hajiya Ummi uwar hassada, tana murna ta rabu da targa
ɗ
e sai ga karaya ta samu. Bata rabu da bukar ba an haifi Habu."
Saleem ya yi dariya ya ce, "A
i na san ji zata yi kamar ta kashe Islaha ta huta."
"Ai da tana da dama wallahi zata iya. A haka zata ƙare, babu abinda ta isa ta yiwa Islaha wallahi. Bara na koma gida na kira ta na bata labari." Saleem ya yi murmuahi suka cigaba da hirar su.
Ummi t
ana barin office
ɗ
in Chairman office
ɗ
in Muslim ta nufa, yadda ta shigo ya fahimci akwai damuwa, kuma daman ya san zata zo saboda irin cin kashin da ƴan comments section suke yi mata. Kamar sun fi tsanar Ummi akan kowa, har gwara shi in ya yi ba a cewa a c
anjasa, amma in Ummi ce yanzu za a cika comments section da magana.
Ummi a firgice ta ce, "babu yadda za a yi a kashe Islaha ne? Babu wanda zamu biya ya kai ta har a shafe labarin ta daga duniya gaba
ɗ
aya?."
Muslim bai ce komai ba, sai da ya miƙe ya bu
ɗ
e
office
ɗ
in ya leƙa dama da haggu ya ga babu kowa sannan ya dawo ya saka mukulli ya ce, "me yake damun ki? Wannan
ɗ
aga muryar da ki ke yi na meye? In wani ya ji abinda ki ke fa
ɗ
a fa?."
Ummi cikin ƙunar zuciya ta ce, "Islaha! Ta tafi
ɗ
in ma ban daina ƙunsar
baƙin ciki saboda ita ba, bata garin nan, bata cikin gidan nan amma tana bakin kowa, harda masu kallon mu. Ka kalli wulaƙancin da aka yi min a hirar jiya? Ka kalli yadda ake saka hoton Islaha a commets section ana cewa in ba ita ba an daina kallon mu?."
Muslim ya ce, "na gani."
"Haukacewa ake so na yi ne? So ake na kashe kaina saboda baƙin cikin Islaha?. Chairman ne ya kira mu yanzu, wai fa
ɗ
a mana yake yi in aka cigaba da samun low views sai canja wasu presenters
ɗ
in. Ya manta kafin Islaha ni ce highest
presnter da ta fi kowa na gidan nan farin jini da samun views, ya manta ni na fara aiki a nam kafin ita?. Tunda ta zo na koma baya, yanzu akan rashinta yake cewa zai canja mu, ni Ummi ni za a canja na koma bayan camera saboda ita!. Wallahi bazan bar yariny
ar nan ba, bazan ƙyale ta ba, sai na yi mata abinda har ta mutu bazata manta dani ba."
Muslim a tausashe ya ce, "kwantar da hankalin ki, mafita ya kamata mu samu akan hakan ba wannan
ɗ
aga muryar ba. Ki zauna mu yi magana."
Ta zauna kamar zata farka kuje
rar, sai jan numfashin mugunta take yi hassada da baƙin ciki suna nuƙurƙusar zuciyata.
Muslim ya bita da kallo ya ce, "a hankali zamu yi maganinta, yadda ta bar aikin nan baza ta sake dawowa ba. Baƙin fenti ya kamata mu shafa mata, yadda ƴan kallon ma za
su dinga son ganin fuskar ta ba balle har su ce suna son ganinta."
"Me zamu yi? Ni a ganina batun acid
ɗ
in nan ya kamata a dawo dashi, da zarar ta dawo a lalata fuskar shegiya, sai na ga wacce fuskar za a dinga gani ana yabawa."
"Wannan ma shawara ce mai
kyau. Bayan haka ma akwai abinda nake tunani, amma dole sai na yi bincike na ga ina ta tafi, me ta tafi yi, me ya kai ta garin, yaushe zata dawo?."
"Ka tambayi Salim, na san shi ya san inda take ai."
Ya yi murmushi ya ce, "ta yadda za ki san abun munaf
urci ne ya ƙi fa
ɗ
a min, sai ya ce shi bai san inda take ba. Safeera ma da na tambaye ta sai ta ce min ta yi tafiya, nace zuwa ina, wai bata sani ba. Hakan ya jefa min zargi a zuciyata, ya tabbatar min akwai abinda aka ƙulla. Ko dai ba waje na gari ta tafi
ba, ko kuma akwai abinda ya faru."
Ummi ta
ɗ
an daki table ta ce, "ya kamata ka samo mana inda take, jikina yana bani wani abu akan hakan."
Ya gya
ɗ
a kai ya ce, "dole zan nemo, wannam itace hanya ta farko ta yaƙi da ita. In muka samo labari mara da
ɗ
i a ka
nta, zamu ya
ɗ
a sa ya shiga duniya gaba
ɗ
aya. Iya wannan zai rage mata farin jini da masoya sosai."
Ummi ta ce, "yaushe zaka nemo
ɗ
in?."
Ya bita da harara ya ce, "bana son gaggawa, na ce zan yi ai. Ki tashi ki koma, kar ace muna kulle ƙofa ni dake a offi
ce."
Ta miƙe ta ce, "meye in ance
ɗ
in, mun kai mu kulle
ɗ
in ai."
Ya
ɗ
an yi dariya bai ce komai ba ta fita. Ya jingina da kujera yana tunanin hanyar da zai bi ya gano inda Islaha ta tafi.
Safeera tana komawa gida ta tarar su Humaira suna nan, ta cire h
ijjab
ɗ
inta, Rukayya ta shiga wajanta ta ce, "Adda Maman su Kausar ta aiko mana da dafaffiyar awara ta ce mu soya. Gata na soya in za ki ci."
Safeera ta murmusa ta ce, "bana jin yunwa Ruky, ki bari sai anjima. Baba ya dawo?."
"A'a bai dawo ba. Nima so n
ake ya dawo, Maman su Kausar ta ji ina maganar ku
ɗ
in handout, shine ta bani ku
ɗ
in ta ce na ƙyale Baba ya huta. Kin gansu dubu biyu."
Safeera da mamaki ta ce, "Mamansu Kausar
ɗ
in ce ta ba ki?."
Ta
ɗ
aga kai ta ce, "itace wallahi."
Safeera ta ce, "Kai h
idimar da take yi mana nan ta yi yawa sosai, ta bakin Baba ya kamata ta rage kar ta
ɗ
orawa kanta nauyin mu."
Ruky ta ce, "Nima haka na ce Adda, amma bara ya dawo mu ji me zai ce."
Safeera ta
ɗ
aga kai ta ce, "bara na
ɗ
an huta kafin lokacin sallah. Ko ak
wai abinda ku ke so?."
Ruky ta ce, "Babu komai Adda."
Safeera ta shiga
ɗ
aki ta kwanta sai kuma ya jawo waya ta kira layin Islaha na saudia.
Tana
ɗ
auka ta ce, "ki hau whatsapp, yanzu za a janye min
ɗ
an katin nawa" tana fa
ɗ
a ta kashe wayar.
Ba jimawa
sai ga kiran Islaha video call ya shigo, Safeera ta yi murmushi ta
ɗ
auka tana kallon Islaha da take zaune kanta babu
ɗ
ankwali tana cin apple.
Safeera ta ce, "Lallai matar nan kina huta, kin ga yadda ki ka ƙara kyau? Ga wani haske, anya larabawa baza su ƙw
acewa Hamma ke ba?."
Islaha ta yi dariya ta ce, "ke yanzu kina tunanin akwai halittar da zata iya kasa Hamma? Duk ku
ɗ
i da kyaun mutum bazai ta
ɓ
a kaiwa matsayin Hamma ba"
"Ban da cika baki dai, kar mu ga kin maƙalewa wani balaraben fa."
"Wuce wannan wal
lahi, Hamma shine farko kuma shine ƙarshe."
"Amma duk da haka kin yi kyau. Waye ya yi miki kitson kan ki?."
"Ni na yi Safeera, ina yi ina kuka saboda sagewar hannu."
"Kema waye ya kai ki, wannan tulin gashin naki mai yawa da tsaho ai tufke shi zai yi mi
ki wahala."
"In san in ina yanayin nan kaina in ba a haka yake ba damuna yake yi wallahi, hasken ma da ki ka ga na yi shine" ta fa
ɗ
a dan bata so su dinga cewa ta yi haske, kar a ga kamar hutawa take yi, ita kuma ta san wahala take sha.
Nana Haleema.
[7/7
, 6:26 PM] KRBBK: RDB2P44
Nana Haleema.
_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments
ɗ
in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link
ɗ
in ku je Youtube, ku danna min
like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode
ɗ
in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L
Safeera ta yi dariya tana kallon Islaha ta ce, "ashe period ki ke yi, to a kan wa ki ka sauke kwan
don masifar